Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
trolley. Samha ce ta shigo d'akin da sauri jin kamar ana shasheqan kuka, sai ta karaso gaban lubna ta dafa ta tace aunty lubna meya faru kike kuka?
Lubna da fuskarta tayi shab'e-shab'e da hawaye tace samha gidan mu zan koma gabad'aya. Zaro ido samha tayi tace gida kuma? " toh saboda me zaki koma gida"?
Lubna tace wai saboda yaya Abdul. Ji fah? "Sai kace ni na dorawa kaina sonshi" shine fa umma tazo d'aukana wai ta gaji da k'orafi na, tunda shi baya sona miye amfanin zamana a gidan nan? Kwalla ce cike da idonta na tausayinta dan itama tasan cewar lubna na bala'in son Abdulrahman.
Sai samha ta dafata tace aunty kiyi hakuri kibar wa Allah komai kuma kibi umma ku tafi. Idan har Allah ya k'addari yaya Abdul mijinki ne insha Allah babu makawa duk nisar da kikayi dashi zai dawo gareki.
Share hawayenta lubna tayi tace nagode yar'uwata da shawarar ki zanbi umma na amma kema ki tayani da addu'a Allah ya cire mun son yaya Abdul a raina kinji?? Samha ta amsa da toh had'e da rungumar junan su.
Kusan minti biyu suna a haka sai samha ta tuna da ance da kira lubna, aikuwa da sauri ta zame jikinta tace aunty na manta fa mummy na kiran ki. Murmushi lubna tayi tace kin ganki da mantuwa ko, ta fad'a had'e da ja mata karen hancinta.
Itama murmushin tayi kafin suka fice a d'akin.
Palour suka tarar da umma da mummy. Umma sai faman hararan lubna takeyi dan wani haushin takeji na yadda ta hak'ik'ice akan son wanda baiko damu da ita ba balle har tayi tunanin ko zai sota.
Wata zuciyar umma tace toh ai ba ita ta d'aura wa kanta ba tunda gashi nan itama tanason ta cire shi ta k'arfi da yaji.
Kawar da tunanin umma tayi dan jin mummy na cewa lubna su shiga daga ciki. Tsuki tayi ta kara jawo samha kusa da ita suna hira. Mummy kuma dariya taja hannun lubna suka haura sama.
Washe gari
Abdulrahman ne sanye cikin wani yadi mekyau kalar bak'i da hula bak'a.
Sai k'amshi yake zubawa yana murmushi sai kace wanda akayi wa albishir da aljanna.
Fitowa yayi rik'e da makullin motar shi a hannu ya nufi part din mummy. Nan ya tarar da ita tana Lallashin samha dake kwance saman cinyarta tana kuka akan lubna da yanzu suka wuce.
Gaishe da mummy yayi kafin yasa kai zai fice sai mummy tace Abdul ina zakaje ne haka? Komi bai ce ba ya dawo kusa da ita ya zauna, idanun shi na kan samha yace mummy wai kukan me takeyi ne haka duk ta cikawa mutane kunnuwa.
Murmushi mummy tayi dan ta fahimci wayo wai yakeson yayi mata danta tambaye shi ina zashi shine ya kawar da zancen. Sai tace ai dole tayi kuka tunda yar'uwarta ta tafi.
D'an bata rai yayi dan jin wai akan lubna take kuka haka sai kace wadda aka rabata da ranta. A fili sai kawai yace tau ayi hakuri gami da mik'ewa yana cewa mummy zan d'an fita wurin wani aboki na. murmushi mummy tayi irin nasu na manya tace a dawo lafiya.
Amsawa yayi da ameen kafin yasa kai ya fice daga palon. Wurin motar shi nufa kirar Mercedes Benz ya shiga ya bata wuta.
Yana duk'i ne a yayin da yake sauraron wata wak'ar wizkid ta I love my my baby dat's my baby....murmushi kawai yake yana bin wak'ar har ya iso gidansu Amatullahi.
Horn yayi me gadi yayi sauri ya bud'e mashi amma baiyi yunk'urin zuwa inda yake ba dan har yanzu bai manta da marin da yasha ba.
Bayan ya faka motar shi ne ya kira megadi dake shirin shiga d'an k'aramin dakin shi. "Gaban shi ne ya fara dukan uku, uku, cikin dauriya ya k'araso wurin Abdulrahman ya duk'a har kasa yace yallabai gani.
Kallon shi Abdulrahman yayi yace dan Allah kayi mun sallama da Amatullahi. Ajiyar zuciya ya sauke gami da mik'ewa ya nufi cikin gida.
Bada dad'ewa ba sai gashi ya fito ya sanar mashi da gata nan zuwa. Ko cikakken minti biyar ba'ayi ba sai gata nan ta fito.
A hankali ta fara takowa har zuwa inda yake, murmushin dake fuskarta ya kara yalwaita, a yayin da shi kuma yana tsaye ya zubawa kyakyawar halittar ta ido. Bayan ta karaso gaban shi ne tasa hannuwanta biyu ta tafa wuri guda danta lura baiko san ta iso ba.
Karan tafa hannuwanta ne ya dawo dashi daga duniyar daya shiga, yana sakar mata murmushi yace baby na kinyi kyau sosai.
Cunno bakinta gaba tayi tace Allah Abdul bana son zolaya, ji fa ko kwalliya banyi ba ka wani ce nayi kyau, ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka.
Duka hannuwan shi yasa ya rike kunnuwan shi had'e da marairaicewa yace a fuwan my baby amma ni kin fi mun kyau idan bakiyi kwalliyar bama. Hararan shi tayi ta gefen ido batare daya gani ba tace ya aiki? Abdulrahman yace alhamdulillah baby na ya mummyn mu?
Hmmmm tana fushi dakai tunda bakazo ka gaishe ta ba. Cike da jindad'in maganar ta yace ai karki damu insha Allah zuwa na musamman zanyi dan in gaishe ta kuma in kin koma ciki ki isar mun da gaisauwa ta kinji?
Amatu ta amsa da toh, daga nan suka shiga hirar soyayya kowannen su na fad'in sirrin zuciyar shi.
Sunan har kusan k'arfe biyar na yamma kafin yayi mata sallama ya wuce. Yana fita wayar amatu ta fara ringing. Dubawa tayi taga Abdulraheem ne ke kiranta.
Cike da mamaki tana tunanin kodai ya manta da wani abun ne? Kawar da tunanin tayi ta amsa wayar. Daga can yace baby ki fito gani k'ofar gidan ku.
Batare da yaji amsarta ba ya katse wayar. Ita kuma tsayawa jiran shi tayi a wurin.
Ya shawo kwanan gidan su kenan yaga wata mota ta taho a guje. Da yan dabaru irin nashi na kwararren matuk'i ya kauce mata sannan ya juyar da kan motar shi zuwa saitin gate d'in gidan su amatu......
Ku biyoni dan jin yadda zata kasance 😎
[2/19, 7:28 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 49-50
Abdulrahman kam ko ajikin shi dan beko yi kokarin ganin na cikin motar ba yaci gaba da tsala gudu kamar wanda zai tashi sama. Daman hake yake tuki, Allah ne dai kawai ke kare shi amma da yanzu ya dade da zuwa barzahu
Abdulraheem na isa ya danna horn da k'arfi me gadi ya bud'e mashi. Lokacin daya shigo Amatullahi na tsaye dan bata koma cikin gida ba.
Cike da tsoro ta k'araso wurin shi tace Abdul ya naga ka canza kaya da mota?? Abdulraheem yace kamar ya na canza kaya da mota?? Amatullahi tace Abdul ba yanzu kabar gidan nan ba?
Daf da ita ya matso yace kina nufin yanzu nabar gidan nan? Girgiza kai tayi alamar eh sai yace toh bani bane Abdulrahman ne.
Zaro ido tayi muryar ta na rawa tace Abdul baa...kai... bane? Ko ansata beyi ba rai a b'ace yace kina nupin kice mun bazaka iya banbance tsakanin na da Abdulrahman ba??
Hawaye ne ya fara ambaliya a fuskarta tace wallahi Abdul kuma matuk'ar kama sosai, kuma naga kullum cikin canza mota kake shiyasa da naga yazo da wannan motar banyi wani tunanin komai ba kuma bai nuna mun wata alama da zan gane bakai bane, sai ya kyaleni ina ta zuba surutu.
Duk bacin ran da abdulraheem ke ciki saida yaji kamar yayi dariya saboda yadda tayi maganar. Sai yace daman ina kuwa zai fad'a maki ai basaja yayi maki amma kibar kukan nan ki saurareni kiji abunda zan fad'a maki.
Cikin muryar kuka tace toh. Abdulraheem yace indai har kina sona to dole ki guji Abdulrahman kuma yadda zaki iya banbance mu shine ki dinga lura da zoben nan dake hannu na, yayi mata nuni da farin azurfan dake mak'ale a tsayar shi na tsaka sannan yace da yanayin kalaman mu da kuma d'abi'un mu.
Kuma abu mafi saukin yadda zaki banbance mu shine, tunda bashi da number ki nasan dole aikowa zaiyi, kinga ko da haka kina iya ganewa. Dan haka sai ki lura karkije kiyi kwab'a. Ya fada yana murmushi.
Bata rai tayi ta share hawayenta tace Allah sai naci mashi mutunci idan ya kara zuwa gidan mu, wai kaji irin hirar da mukayi dashi kuwa? Ya girgiza kai yace bana bukatar ji kawai a wuce wurin.
Nan suka rufe wannan shafin suka dauko wata hirar daban.
*****
Bayan wata biyu
Daddyn Amatullahi ne tare da daddyn Abdulrahman da kuma abba suna tattaunawa akan maganar su Abdul dan har yanzu babu wata tsayayyar magana, shi kuma daddyn amatu yaji shurun yayi yawa ne kuma ga kaya da sadaki nan gida shiyasa ya tunkare su da maganar dan yaji inda bakin zaren yake.
Abba ne ya fara magana yace dan Allah ya kara hakuri insha Allah zasu tari yaran suji, indai har babu wata sulhu a tsakanin su za'a tuntub'i ita amatullahi da bakinta ta fad'i wanda takeso.
Daddyn Abdulrahman yace eh wannan hakane dan Allah Alhaji kayi mana hakuri nan bada dadewa ba zakaji mu. Daddyn Amatullahi yace ai babu komai.
Bangaren su Abdul kam ba'acewa komai dan yanzu wata shaquwa ce mai karfi fiye dana da ta kara shiga tsakanin Amatullahi da Abdulraheem. Kullum cikin tattali da kyautatawa junan suke a inda Abdulrahman kuma tun lokacin da Abdulraheem yayi mata hudubar yadda zata banbance su ta farayi wa Abdulrahman wulakanci.
Kuma duk wani wulakanci da batan ci da zatayi mashi bazai hana gobe ya dawo ba. Yanzu haka saboda nacin shi harya kai ga sanin shagon saloon d'inta saboda ranar dayazo gidan su yace ana kiranta kin fitowa tayi shi kuma yaki wucewa yana tsaye harta fito zataje shago.
Nan ne ya fara binta harya fahimci cewa shagon ta ne.
B'angaren Abdulrahman da Abdulraheem kam babu wata jituwa a tsakanin su, Kai suna ma dadewa basu ga juna ba, sai dan wani lokaci haka in Abdulrahman yazo ganin ammie shine in yayi daidai da Abdulraheem na nan zasu ga juna, ko gaisuwa wuya takeyi musu dan kowannensu da irin nashi Jan aji girman kai.
Hatta da Abba da daddy sun tarasu akan su sulhunta kansu amma har yanzu abu yaci tura dan kowannensu gani yake idan ya fara magana ai kamar ya bayar da kanshi ne.
*****
kamar kullum yauma, a hanyar shi ta zuwa wurin ta yake, amma ba gidan su ya nufa ba dan yasan a irin wannan lokacin tana shago. Da Isar sa ta gefen shagon ya paka motar shi yana daga ciki yana kallon daidai saitin kofar shagon.
Kusan awa daya sai gata nan ta nufo wurin motar ta dake pake a gaban nashi. Batare da tayi tunanin komai ba ta karasa inda motar ta take.
Ameerah dake gefenta suna dan hirarsu gwanin sha'awa sai tace laaa amatu na manta da wayata a shago bari inje in dauko. Amatu ta amsa da toh sannan ta karasa wurin motar ta tsaya, ameerah kuma ta koma shago dan dauko wayar ta.
Abdulrahman kuma ganinta tsaye a jikin motar ne ya bashi daman fitowa, cikin takunshi na kasaita ya nufo ta. Lokacin tana latsar wayanta. Kanshi turaren shi ne ya bugi hancinta, sai lokaci daya kawai taji wani tsanar shi ya kara shigarta. Dan ko ba'a fad'i ko waye ba kamshin turarensa ya bayyana.
Tsuki tayi, tayi kwafa zata shige motar ta yayi saurin shan gabanta, cikin marairaicewa yace Amatullahi ki taimake ni wallahi zan iya mutuwa idan na rasa ki plsss my Amatu help me.....
A hasale ta dago kanta ta kalleshi idonta na cikin nashi tace wai kai wani irin nataccen mutum ne? Wace irin zuciya gareka ne da bakasan an kuntata mata ba?? Cikin daakiya da dauriya yace zuciyar kare gareni!
Sakwakwa take kallonshi, a ranta tace anya yana da hankali kuwa? Sai ya katse ta ta hanyar kiran sunanta yace Amatullahi duk wani abu da zaki fada bazai taba sani in daina sonki ba saboda sonki a jini na yake kuma ki sani indai akan sonki ne sai da na mutu badai sonki ya fita daga zuciyata ba.
Yana fadar haka ya wuce fuu ya shige motar sa ya barta nan tsaye.
Ameerah ce ta karaso wurinta tace Amatullahi shiga muje ki rabu dashi kawai. Dake duk wani abu dake faruwa ameerah tasani shiyasa batayi mamakin ganin shi ba dan ba yau farau ba.
Nan suka shiga mota Amatullahi taja suka wuce, wani dan cafe suka nupa inda zasu duba result dinsu na jamb dan har sun rubuta.
Bayan sun shiga ne suka bada sunan su da kuma jamb slip dinsu. Nan aka duba musu kuma cikin ikon Allah duk sun samu makin da akeso dan amatu nada maki dari biyu da ashiri ameerah kuma nada maki dari biyu da uku. Nan suka fara murna suka bawa me shagon kudi suka wuce.
Direct gidan aunty hajara suka nufa. Cike da murna suka isa palon. Lokacin aunty hajara na kitchen,
aikuwa kitchen din suka nufa kowannensu da slip dinshi a hannu. Amatu ce ta fara mikawa aunty hajara slip dinta tana murmushi.
Aunty hajara na gani ta rungume ta tana cewa Allah mungode maka, muga naki ameerah. Bata rai ameerah tayi ta fice daga gidan tana cewa tunda ba'a damu da ita ba mummy zataje ta nuna ma.
Su kuma dariya sukayi, aunty hajara tace lallai yau daddyn ki zaiji dadi kuwa. Murmushi amatu tayi tace bari taje tabi bayan ameerah
Gidansu ta tafi inda ta tarar da ameerah sai washe baki take mommy na zuba mata albarka. Da amatu ta shigo hararan ta mummy tayi tace me kuma ya kawo ki wurina? Cikin yanayi na shagwaba Amatullahi ta karaso wurinta ta daura mata slip din a cinyarta tace haba mummy duba fa ki gani maki na yama wuce na ameerah.
Cikin wasa mummy tace toh sai me badai duk kun samu yadda akeso ba. Ameerah tace eh mana mummy, yanzu ma yaya Usman (mijin aunty hajara) nake jira ya dawo in nuna mashi.
Amatullahi tace waton yaya kika sani banda daddy ko? Ameerah tayi saurin magana tace injiwa ai daddy shine kan gaba. Shi daya dau nauyin makaranta ta ai dole in nuna mashi dan yaji dadi. Ta karasa maganar gami da mikewa ta nupin kitchen dan jin yadda cikinta ke kugi saboda yunwa.
Amatullahi kuma ansar slip d'in su tayi takai d'aki ta aje, akan in daddy ya dawo ta nuna mashi dan baya ma k'asar baki d'aya.
Bayan ta dawo ne ta tarar da ameerah har ta zuba musu abinci. Nan ta zauna suka fara ci suna hira.
**********
Abdulraheem ne tare da abba suna tattaunawa akan maganar sato Amatullahi da sukayi. Abba yace wa Abdul shi kullum cikin damuwa yake indai ba mayar da kudin nan yayi ba hankalalin shi bazai taba kwanciya ba. Sai Abdul ya fara dan lallashin Abba da kalamai masu dadi yana cewa ai yanzu idan ya fad'a mashi zai iya hanasu auren yar'shi kawai yayi hakuri ya bari bayan aure sai ya sanar dashi.
Abba ya amsa da toh dan ya gamsu da shawarar shi.
Nan suka dan tattaba hira daga bisani Abdul ya wuce.
Bayan Abdul ya fita ne Amatullahi ta kira shi take fad'a mashi ai result dinsu ya fito tun shekaran jiya kuma Allah ya basu sa'a ita da ameerah. B'ata rai yayi kamar tana kallon shi yace shine baki fad'a mun ba sai yau ko?? Hakuri ta fara bashi harya hakura yace gashi nan zuwa gidan basu.
A b'angaren Abdulrahman kuma yanzu ya fito daga lecture, duk yagaji ga wata yunwa da yakeji a d'ayan b'angaren zuciyar shi kuwa babu abunda idanuwan shi ke mararin gani kamar Amatullahi.
Daidai zai shiga motar shi kenan wani sabon aboki da yayi mai suna fahad. Ya tare shi, shima lecturer ne a BASE UNIVERSITY dake cikin garin abuja, nan suka gaisa inda ya nemi Abdulrahman daya sauke shi saman hanya saboda motar shi tad'au zafi bata iya tashi.
Badan yaso ba yace ya shiga ya sauke shi, nan suka fita inda suka kama hanya sai wuraren anguwar su Amatullahi ya ajiye shi.
Shiko da yaga haka da yayi wahala biyu gwara kawai ya wuce gidan su Amatullahi tunda daman yayi niyar zuwa wurinta.
Haka ya d'au hanyar zuwa gidan su amatu ba tare daya dubi halin da yake ciki na jin yunwa ba.
A bakin gate din gidan su ya faka motar shi yana jiran yaga fitowarta, dan yasan koya aika a kirata ba fitowa zatayi ba.
Abdulraheem kuma dake saman hanyar zuwa gidan su Amatullahi, ya kawo kusa da gidan su ya hangi wata had'addd'iyar mota ta paka a daidai gate din shiga gidan.
Be kawo komai ba kawai ya karaso kafin yakai ga saita kan motar shi ta inda zai samu damar shiga kai tsaye sai ya yayi horn da k'arfi dan motar ta bashi hanya saboda ya lura akwai mutum a cikin motar.
Abdulrahman kuma yi yayi kamar bada shi ake ba ya wani sha toka cikin mota yana cewa yau zamu gani ko ni ko kai.
Abdulraheem ko wani haushi ne ya kamashi ya fito a fusace ya............
Plss share
[2/20, 9:56 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 51-52
"Abdulraheem ko wani haushi ne ya kamashi ya fito a "fusace ya karaso wurin motar" Abdulrahman, ya d'an bubbuga motar saboda motar ansa mata tinted glass sai ya zamana baya iya ganin na ciki, "amma shi Abdulrahman sarai yana kallonshi, sai ma ya kawar da kanshi ya fara latsar wayanshi yana murmushi mugunta".
"Abdulraheem dake waje, fuskar nan tashi a murtuke, "yacika yayi taf, jira kawai yake a tab'o shi ya fashe". Wayar shi ya d'auko yayi dialing number Amatullahi. " ji kawai nayi yace am at d gate" sai ya katse kiran.
"Baifi minti uku da kiranta ba sai gata nan ta fito harabar gidansu, "nan taga bata ganshi ba sai tasa kai ta fito waje".
Tana fitowa ta ganshi a tsaye fuskar nan tashi babu walwala.
"Saurin karasowa wurin shi tayi, " muryar ta kasa-kasa tace my Abdul". yana naga Abdulrahman ko tare kuka zo ne? Cikin ranshi yace gaske dai yaki matsa mun in wuce amma a fili wata uwa harara ya watsa mata yace kin tab'a gani da tare dashi ne?? Gyad'a kanta tayi alamar a'a.
"Shi kuma dan ya batawa Abdulrahman