Chapter 7 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 27

18K to 21K   out of 79.1K words

ya dau alwashin shi daya dawo Cyprus sai kuma wani ikon Allah dan a karamin tunanin shi duk wannan zuwa Cyprus dinne ya janyo mashi da yanxu kila ma anyi auren su.

Toh masu karatu a nashi ganin fah 😁

Da saukar shi gida ko wani hutawa bai tsaya yi ba ya fice daga gidan baki daya,

Direct gidansu Amatu ya nupa, kodaya je a bakin gate ya paka motar shi, yana shirin fitowa sai ga megadi ya fito.

Cikin girmamawa megadi ya fara gaishe shi, gogan kuma dake ba gaisuwar ce a gabanshi ba ko amsawa beyi ba yace Amatullahi na gida kuwa???

Dan murmushi megadi yayi yace eh yallabai tana ciki sedai kuma hajiya tace kar a bari ta fita kuma duk wanda yazo nemanta ace bata na

Cikin damuwa ya fara tunanin dalilin da zaisa ayi  mata irin wannan dokan sai can yaji megadi na cewa toh yallabai ka kirata a waya mana? Shuru yayi  Kamar mai tunani sai can yace a'a ai na kira wayanta a kashe shiyasa ma nazo gidan.

Kallonshi megadi yayi yace toh toh yallabai kasan harkar mata in suna biki sai a hankali, ko nima da nake nan duk hayaniyar su ta isheni amma ba abun ayi magana ba dansu farinciki suke sosai dan zasu aurar da yar su kwalli daya tak wadda sukeji da ita kamar gwal ai abunda yafi hayaniya ma suna iya y..................................





Plsss share
[2/12, 4:38 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

     Page 31-32

What??? Me kake fada haka? Kana cikin hankalinka kuwa?? Shuru megadi yayi yana kallonshi saboda tsananin mamaki,"shidai yasan babu wani wanda ke zuwa wurin Amatu in bashi ba kuma yasan cewa dashi za'ayi auren to miye kuma na damuwa??

Abdulrahman dake wani irin huci sai kace zakin daya ga nama, ya matso gaf da megadi rai bace yace wallahi ka kuskura ka kara ambaton Amatu gami da danganata da wani bani bai sai nayi maganinka! Banza kawai.

Megadi ko sai hakuri yake bashi dan yaga kamar kishi ne ke dawainiya dashi shiyasa bai fahimci inda maganar tasa ta dosa ba.

Wasu yammata neh guda biyu suka fito daga cikin wata mota zasu shiga gidan, sai nacikin motar, waton wanda ya kawosu ya leko kanshi ta window dan har sun kusan kai gate din shiga gidan yace ku gaida mun da amarya sai nazo ganinta.

Murmushi sukayi dukansu kafin suka isa cikin gidan, Abdulrahman kuma yana tsaye kamar wani gunki yana kallon su.

Karan wayar shine ya dawo dashi cikin hayyacin shi, yana ganin mummy ce ke kiran shi yayi saurin dagawa. Ko minti biyu basuyi ba ya katse wayar.

Kallon megadi yayi yace wai bikin wa akeyi dan ni ban fahimta ba, washe baki megadi yayi "yace yallabai auren Amatullahi akeyi..........tas tas kakeji har sau biyu ya mare shi, dafe kumatu megadi yayi idanunwa duk sun zurmo waje ya fara ba Abdulrahman hakuri sai Abdul ya katse shi, zai yi magana kenan sai ga kiran mummy ya shigo,

Amsawa yayi yace toh sai ya shige motar shi ya bata wuta kamar me shirin tashi sama hake yake ta faman tsala gudu  baji ba gani, duk ya burkice ga kuma mummy dake faman kiransa a waya. Garin ya dauki wayar ne motar ta kufce masa saura kadan ya bugi wata motar sai Allah ya takaita be bugeta ba dan me motar ya kauce.

Fitowa yayi da sauri yana bawa mai motar hakuri amma mai motar sai faman zaginshi yakeyi yana mishi Allah ya isa.

Tsuki kawai yaja ya shige motarsa dan a halin da yake ciki hankalin shi ba a jikinsa yake ba. Dakyar ya samu ya dawo gida dan a hanya sai kaucewa yake saman titi saboda irin gudun da yake tsalawa.

Kodaya dawo gida ko rufe motar be samu damar yi ba, part dinshi ya nupa, yana shiga ya fada saman gado yana kurma ihu sai kace wani karamin yaro.

Mikewa tsaye yayi ya nupi inda mirror yana kallon fuskar shi data kumbura ta koma ja saboda bacin rai ga jijiyoyin kanshi duk sun fito rado rado, tuno abunda megadin gidansu Amatu ya fada mishi yayi, aikuwa nan hauka ta tashi dan sambatu ya farayi gami da watsi da duk wani kaya dake saman mirron yana cewa wallahi baka isa ba, bazan taba bari ka auri farinciki na ba

Kai waye wallahi sai naga bayan ka

Yana magana yana huci kamar wani zaki

Haka yayi ta surutai har na tsawon wani lokaci sai kuma naji ko'ina yayi dif

Karasawa nayi daidai wurin da yake naganshi kwance a kasa bakin shi cike da bakin jini.

Lubna da taga lokacin da Abdulrahman ya shigo taso ta biyoshi sai kuma tana tsoron wulakancin da zaiyi mata sai ta fasa zuwa.

Tana tsaye a wurin sai takejin kamar hayaniya daga bangare shi, bata gasgata ba sai data ji karar wani abu ya fashe kamar glass, aikuwa da sauri ta nupi part dinshi, babu wani tsoro ko shakkar shi ta karasa cikin dakin.

Ihu ta kurma ganin Abdulrahman a sume, da gudu ta fito daga dakin zataje wurin mummy ta fada mata sai kawai sukaci Karo, cikin rikicewa mummy tace lafiya lubna meya faru??

Lubna kasa magana tayi sai hannunta data daga tana yiwa mummy nuni data shiga dakin, da sauri mummy ta shiga dakin inda ta tarar da Abdul kwance kamar gawa. Salati mummy ta farayi tayi waje da gudu ta kira musa direba.

Yana shigowa ya kama Abdulrahman sukasa shi a mota suka wuce asibiti, suna shiga babu wani bata lokaci akayi emergency room dashi aka fara bashi taimakon gaggawa, duk iya kokarin su akan ya farfafo, sunyi amma bai farfado ba.

     After two hours

Wani likita ne ya fito ya sami mummy a tsaye tayi tagumi sai hawaye ne ke fita daga idanunta, kallon inda take yayi yace hajiya kece mahaifiyar yaron nan?? Eh nice ya tashi???

A'a ki kwantar da hankalinki insha Allah zai tashi amma yanxu muje office dina. Yana gaba tana baya, kafarta har wani sarkewa take saboda ta matsu bataji abunda zai fada mata ba. Bayan sun shiga wuri ya bata ta zauna kafin ya maida duban shi zuwa gareta yace hajiya a gaskiya yaron ki na cikin matsala.

Dumm taji gabanta ya fadi, tace likita meke damun dana dan Allah ka fada mun ta karasa maganar hawaye na zuba daga fuskarta. Dan Jim kadan yayi dan mummy ta bashi tausayi yadda yaga hankalinta ya tashi,

  lallaminta ya farayi yana kwantar mata da hankali har daga karshe dai ya fada mata Abdul ya kamu da ciwon zuciya Kuma mafita daya neh shine duk wani abu dayake so ayi mashi kuma a guji bacin ranshi.

Cikin tsantsar damuwa mummy tace likita tau yaushe ze farfado ne??

Nan bada dadewa ba zai farfado. wasu yan rubuce-rubuce yayi kafin ya mika mata wata takarda yace gashi kije banki ki biya Wannan kudin. Amma kafin ki fita ki tabbatar kin bar wani nashi kusa saboda karya farfado ya bukaci wani abu babu kowa kusa dashi.

Amsawa tayi da toh sannan ta fita, daddy ta tarar sai kai kawo yakeyi, gabanshi taje ta mika mashi takaddar da likita ya bata, karba yayi yasa a aljihun shi kafin yace hajiya ta ya jikin nashi??

Fuskarta cike da damuwa tace Alhaji Abdulrahman yana cikin matsala sbd likita yace wai ya kamu da ciwon zuciya. Ciwon zuciya ya kara maimaitawa.

Girgiza kai ya farayi cikin fada yace inaaa wannan ba gaskiya bane, yaron dake cikin jindadi, a koda yaushe? Ni ko damuwa ban taba gani a tare dashi balle ace yakai ga ciwon zuciya!! Ni ban yadda ba ina likita yake???

Likita da yanxu ya fito daga dakin da aka kwantar da Abdulrahman yace alhaji kayi hakuri da sakamakon da kaji amma wannan ba karya bane gama shaida nan, "ya mika masa takaddar gwadin da akayi mashi.

Runtse ido daddy yayi dan ji yake kamar yayi kuka ko zaiji sassaucin zafin da yakeji a zuciyar shi." Shidai a iya sanin shi Abdulrahman be taba neman wani abu ya rasa ba kuma duk wani gata da kulawa yana samu daga garesu" to wace irin damuwace haka har tasa yakai ga kamuwa da heart attack basu sani ba??

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalli inda likita yake yace zamu iya ganin shi?? Eh muje yayi musu iso har zuwa inda Abdulrahman ke kwance,

kallon Abdulrahman daddy yayi yana mai jin tausayin shi.

Mummy kuma sai kuka takeyi, haka lubna da suka shigo yanxu tare da umar da samha sai kuka sukeyi.

Daddy neh yayi musu fada akan su daina kuka suyi mashi  addu'a Allah ya tashi kafadun shi.

Nan suka zauna jugum jugum kamar Wanda akayi musu rasuwa. Suna nan zaune har dare amma Abdul be farfado ba, kowanne su yana cike da damuwar rashin farfadowar shi.

Da karfe Tara na dare daddy yace su koma gida sai abar mummy ta kwana tare dashi su kuma zuwa da safe sai su dawo, duk ransu beso ba amma haka nan suka wuce. Har sunkai daidai shiga mota sai lubna ta tuno da wayar mummy na hannunta dan bayan wucewar su mummy asibiti cikin gida ta shiga ta dauko wayan mummy ta kira daddy, shiyasa ma ya rigasu zuwa.

Bayan takai wa mummy wayar ne ta dawo suka wuce gida.

Bangaren Amatu........




Pls share
[2/13, 1:21 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

RUDANI fans grp ina yinku sosai dinnan👍🏻 Kuma ina kaunar ku sosai❤

'''wannan shafin na aunty na neh maryama a.i gital. Ina sonki kamar yadda nakeson raina, kisha zamanki ki huta Allah yaja zamaninki my best and sweetest aunty, I love u so much, Allah ya raya mana su beauties dinmu.'''

         Page 33-34

Bangaren su Amatu kuwa sai hidimar biki sukeyi dan kuwa yanzu tabar zuwa shago, kai ko nan da can mummy bata bari ta taje saboda yan gyare-gyaren da ake mata.

Ameerah kuwa sai zirga-zirga take bata nan bata can, duk wani shirye -shirye da rabon invitation card itace kan gaba, gashi gidansu Amatu harya fara cika da yan uwa tun kafin akai ga fara events.

Abdulraheem kam ya matsu ba'a daura aure ba, su abokan shi har tsokanan shi sukeyi suna cewa ya fiye zumudi, shikuwa sedai ma yace eh din badai ya fita daga sahun gwauraye ba?? Haka zasuyi ta hira suna tsonkanar shi.

*********
Bangaren Abdulrahman kuwa yau kwanan su uku a asibiti amma sai yau ya farfado, tun daya farfado sunan Amatu yake kira yana cewa tashi ce.

Daddy neh ya matso kusa dashi ya rike shi yana lallashin shi, dakyar ya samu yayi shuru. Lubna kuma wani irin haushi neh ya kamata dan jin yace tashi ce"duk da cewar bata son ko wacece ba amma tasan dai akan macece.

Bayan yan mintuna kadan, daddy neh ya kalli mummy yace hajiyata (hake yake kiranta) anya yaron nan ba zaucewa yayi ba kuwa dan naga sai sambatu yake tayi.

Ajiye hannunta datayi tagumi tayi tace alhaji babu wani maganar zaucewa ina ganin dai ya fada tarkon soyayya neh dan yadda naji yana magana ya tabbatar mun da hakan.

Ajiyar zuciya daddy ya sauke gami da cewa eh lallai ba shakka toh amma wacece wannan yarinyar da takeson taga bayan dana? Ya fada a dan tsawace.

Kallon shi mummy tayi tace amsa tana gareshi  dan nima bazan iya cewa gata ba.

Komai daddy baice ba ya kalli inda Abdulrahman yake kwance hawaye na zuba a idanunshi yace son meke damunka, ka fada mun koma menene indai har baifi karfina ba insha Allah zanyi maka.

Share hawayenshi yayi yana mai fuskantar daddy yace daddy aure zatayi ta barni!! Daddy yace wacece ita??

AMATULLAHI aure zatayi kuma alhalin tasan ina sonta kuma itama tana sona. "Hannun daddy ya kamo yasa cikin nashi hawaye na zuba a fuskar shi yace daddy nah plsss ka taimakeni karka bari ayi auren nan auren dole za'ayi mata plsss wallahi idan na rasata mutuwa zanyi daddy! Ya karasa maganar yana mai langabar da kanshi jikin gado.

Mummy ji take kamar ta taya shi kukan dan ya bata tausayi yadda yake kuka shida rabon da taga kukan shi tun yana yaro amma wai yau shine yake kuka," kukan ma akan mace.

Lallashin shi daddy ya shigayi yana mai kwantar mashi da hankali.

Saida yayi shuru tukunna daddy ya tambaye shi yace yarinyar yar' gidan waye? Cikin muryar shi data dishe saboda kuka yace yar gidan Alhaji Muhammad lemi.

A dan razane daddy yace alhaji lemi dai wanda nasani dan kasuwan nan??? Girgiza kai Abdul yayi alamar eh. Nan daddy ya tashi yace yana zuwa ya fita.

Mummy kuma tasowa tayi tazo bakin gadon da yake kwance ta zauna ta gefe tana kallonshi tace Abdul ka kwantar da hankalinka indai wannan ce damuwar ka an gama dan nasan daddynka yana son farincikin ka zaiyi iya kokarin shi wurin ganin an aura maka ita kaji?? Kayi hakuri.

Amsawa yayi da toh.

Mummy waigawa tayi zata yiwa lubna magana sai taga wayam bata nan

Lubna ko tun sadda taji dalilin rashin lafiyar Abdul ta fita waje da gudu tana kuka, bayan asibiti taje ta samu wuri ta zauna ta kira  mummynta ta fada mata abunda ke faruwa.

Duk da cewar mummy bataji dadi ba amma haka tayi ta bata hakuri tana mata fada akan ta rabu dashi tunda shi baya sonta ko an aura mata shi baza taji dadin zama dashi ba kawai tayi hakuri har Allah ya kawo mata nata.

Kuka sosai lubna tayi dan tasan bazata iya daina son Abdul ba tunda tayi iya kokarin wurin cire soyayyar shi a ranta amma ta gaza.

Bayan taci kukanta ta koshi neh taje wurin pampo ta wanke fuskar ta sannan ta nupi dakin. Tunda ta shigo ko kala batace ba, mummy kuma tsaf tana lure da ita dan ta gane cewar tayi kuka.

Har ta danji tausayinta dan tasan yadda lubna ke masifar son Abdul din, ita kanta da badan batason ta takura mashi da tuni ta tilasta mashi ya aureta.

Bayan daddy ya fita office dinshi ya nupa inda yasa aka samar mashi number Alhaji lemi, koda daddy ya kira lemi lokacin yana wani garden yana shan iska.

Babu wani bata lokaci dan alhaji lemi ba irin mutanen nan bane masu wulakanta al'umma ba yace ya sameshi a garden inda yayi mashi kwatance, bada dadewa ba sai ga daddy ya iso wurin.

Can ya hangoshi zaune da drinks a gabanshi, yana zuwa yayi mishi iso ya zauna kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da teburin dake tsakiyar su.

Bashi hannu yayi suka gaisa kafin daddy ya fara bashi labarin halin da danshi ke ciki. Alhaji lemi yace gaskiya dan tausayi na tausayawa danka sedai maganar gaskiya Amatullahi ba auren dole nayi mata ba kuma ma jibi za'a daura auren ta

Abunda zance dakai shine kaba danka hakuri dan  yazo a kurarren lokaci, fatana Allah ya bashi wadda ta fita.

Daddy kamar yayi kuka saboda haushi, shi yanzu ma matsalar shi besan ta ina zai fara yiwa Abdul bayani ba, yana tunanin haka Alhaji lemi yace amma kace danka yace tana sonshi ko??

Saurin amsa shi yayi yace eh eh tabbas kuwa yace tana sonshi. 

Dan Jim kadan Alhaji lemi yayi yace tau Allah dai ya sauwaka nd ina kara baku hakuri, shi kuma danka Allah ya bashi lafiya. Jiki a mace daddy yayi wa Alhaji lemi sallama ya wuce.

Direct asibiti ya nupa, lokacin Abdul yana cin abinci, da ganin daddy ya ajiye abincin yace daddy an fasa auren?? Fuskar daddy cike da damuwa yace son kayi hakuri kawa........ Be idaba yaga Abdul a sume.

A razane yayo kansa, yana bubbuga shi mummy kuma da gudu ta ta fita ta kira likita, likita na zuwa yace su fita waje.

Mummy bayan sun fito waje sai kuka take tana ma daddy mita akan meyasa zai fadawa Abdul magana mara dadi bayan yasan halin da yake ciki.

Dago idanunshi da suka canza launi zuwa ja yayi dan shi a rayuwar shi be taba ganin wani ya kamu da masifaffen so kamar na Abdul ba. Kallon mummy yayi yace hajiyata dole in koma wurin Alhaji lemi dan kuwa bazan bari ina ji ina gani dana ya rasa ranshi akan abunda baifi karfina ba........

Tooo pah 🤔🤔🤔


Plsss kuyi hkr da wannan wlh dazu nayi typing me yawa ya goge😭😭
Ayi manaji da wannan

For comments
09061103352
WhatsApp only
[2/14, 9:33 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote and follow me on wattpad@lashminzy'''

     Page 35-36

Waje ya fita ya dauko wayar shi ya kira Alhaji lemi, bayan sun gaisa yake fada mashi idan bazai damu ba yana bukatar ganin shi da gaggawa.

Bayan ya gama wayar dashi neh ya sanar ma mummy ana neman shi a wani wuri yanxu zai dawo. Daga nan ya fita zuwa gidan shi dan harya koma gida.

Koda daddy ya isa gidan akwai mutane da yawa sai zirga-zirga suke, nan ya kara tabbatar da cewar eh lallai fa bikin yar'shi ake. Har sai da yaji jikinshi yayi sanyi akan kudurin da yazo dashi, amma idan ya duba wani gefen sai ya ga ai rayuwar danshi yakeson ya ceto.

Yana tsaye yana yan sake-sake sai ga Alhaji lemi yazo, nan ya mika masa hannu suka gaisa sannan yayi mishi iso zuwa palon baki. Bayan sun shiga abinci da ruwa Alhaji lemi yasa aka kawo mishi dan kuwa Alhaji lemi akwai iya tarban bako.

Sun dan taba hira kadan kafin daddy ya sauka daga saman kujeran da yake ya matso gaban alhaji lemi, ya marairaice fuska yace Alhaji dan Allah ka taimakeni ka ceci rayuwar dana, wallahi yanzu haka yana asibiti bansan halin da yake ciki ba, "bayan na sanar dashi yadda mukayi dakai shikenan yaron nan ya sume, dan Allah Alhaji ka taimaka a daga aurrrr......

What??Alhaji lemi ya fada a tsawace, "yace me kake nupi in fasa wannan auren?? Inaaa bazai taba yuwuwa ba, "ka kuwa san iya adadin mutanen dana gayyata?? Bama Wannan ba mai kake tunanin zan fadawa baban yaron nan da kuma sauran mutane???

Murmushin da bekai zuci ba yayi yace nayi taimako da yawa, na ceci rayuwar mutane da yawa amma sedai wannan abu daya zan fadamaka shima taimako ne, ka dauki yaronnan kabar kasar nan dashi har zuwa wani lokaci.

Zufa ce ta keto wa daddy jin irin maganar da alhaji

7 / 27