Chapter 10 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 27

27K to 30K   out of 79.1K words

tana murmushi batare da kowa ya kula da ita ba.

Suna nan tsaye sai ga umar ya yazo, nan yayi musu sallama ya wuce. Suna fita ana kiran sallah sai suka tsaya nan wani masallaci dake unguwar su sukayi sallah sannan suka wuce.

Tafiya kawai suke babu me magana cikin su dan umar ba ma'abocin hira bane dan harma gwara abdulraheem wannan abun ne yasashi zama silent amma idan jininku ya hadu dashi toh fah sai ka kaji dashi dan akwai barkwanci.

Tafiyar su bata wuce minti goma sha biyar ba sai gasu sun iso gidan su abdulraheem. Sallama sukayi wa juna ya wuce.

Abdulraheem na shiga gida part din ammie ya nupa, lokacin ammie kuma tana palo ita da hanan tana labarta mata abunda ya faru. Suna cikin hirar ne sai ga abdul ya shigo, da gudu hanan taje ta rungume shi tace laa yaya ashe ku yan biyu neh??? hmmm tau nidai ina bayan yaya abdulrahman kawai kabar masa aunty amat.......

Wani irin damka yayi mata, kamar wani zaki yana huci, ammie tayi saurin zuwa wurinshi ta fisge hanan daga damkar da yayi mata.

Cikin fada tace abdul kana da hankali kuwa? miye haka? akan dan tace haka shine zaka wani shaqo ta? ko so kake ka kashe mun ita? toh wallahi ka fita a idona kanaji na ko?

Kamar yayi kuka dan har yanayin shi ya sauya yace ammie kiyi hakuri nima bansan nayi haka ba. Da fadar haka sai yayi shuru.

ba'afi dakika talatin ba sai yace amm ammie plss ki taimakeni karki bari a rabani da amatullahi wallahi itace farinciki na kuma kinfi kowa sanin irin sonda nake mata "plss my ammie help me

Cikin tausaya mashi tace abdul kenan dukan ku ya'ya na ne kuma ina sonku, da'ace wani ne can daban zan iya tsaya maka dakin daka, toh amma kaga yadda abun yake, yanxu shida yake fama da ciwon zuciya ya kake tunanin zan iya tunkarar shi da ince ya hakura yabar maka ita?

haka kaima idan nace ka hakura kabar mashi ita zakayi tunanin ko nafison shi fiye da kaine shiyasa abbanku ma ya yanke hukunci yace ku sasanta kanku saboda karku ce yayi sonkai.

Nidai abunda zance shine kayi hakuri, kaje ka zauna da dan uwanka zama na fahimta ku fahimci junan ku. kaga nima idan ina ganinku tare cikin farinciki da kwanciyar hankali nima zanji dadi.

jikinshi ne yayi sanyi sai kawai yace insha Allah ammie zamu daidaita. Yana fadar haka ya fice.

Ammie kuma waigawa tayi bata ga hanan ba, dan hanan tunda ammie ta kwaceta ta sheqa da gudu daki ta fada saman gado tana kuka dan ba karamin jin zafin rikon da yayi mata tayi ba.

***********
Daddy ne zaune yana labartawa mummy da amatu abunda ya faru. Mummy kam ta hakikice tace ita kam bazata yadda da wata shawara ba. saboda me za'a ace sai sun yanke shawara bayan ansan cewa amatullahi nasan abdulraheem wace irin ace su sasanta kuma?

Daddy yace haba rukayyatu wai ya ina baki kina roko? yanxu fa nace maki shekarun baya da suka wuce yaron nan da amatullahi ke soyayya dashi abdulrahman ba abdulraheem ba kuma shi abdulrahman ya tabbatar mun da cewa tana sonsa, koba haka ba ya fada yana kallon amatu data dukar da kanta kasa.

Cikin rawar murya tace eh daddy.

Mayar da kallon shi yayi wurin mummy yace to kingani, ko? yanxu haka yaron nan a dalilin soyayyarta harya kai ga kamuwa da ciwon zuciya kuma bayan haka ma abunda yasa muka yanke wannan shawarar dan munga yan uwan juna ne dan a samu sulhu a tsakanin su mukace su sasanta kansu.

Dan sassautowa mummy tayi tace toh bakomai Allah ya zaba wanda yafi zama alkhairi a cikinsu. Cikin jindadi daddy yace ameen ko ke fah!

murmushi tayi ta kalli gefen amatu tace amatullahi jeki daki ki kwanta. sum sum ta mike ta wuce dakin ta, tana shiga wayar ta na kara.

Da kamar bazata dauka ba sai tayi tunanin ko abdul dinta ne shiyasa tayi gaggawar daukan wayar kafin ta tsinke.

Cikin yanayi na damuwa yace baby ina cikin tashin hankali. Zai fara bata labarin abunda ya faru ta katse shi tace my abdul daddy ya fada mun komai, amma ni ban yarda da shawarar su ba saboda ni gaskiya banason abdul a yanxu.

Duba fa kaga tsawon shekaru biyu ya gujeni sai yanzu da yaji labarin zan aureka shine zai wani dawo? toh nikam banason shi kai nake so.

Plss my abdul kayi wani abu karka bari ya samu nasarar rabamu. Ta fada hawayene na zuba a kumatunta.

Cikin lallashi da samun karfin gwiwar maganar data fada yace baby ki daina kuka insha Allah babu abunda zai rabamu.

Kuma koda yazo gidan ku karki sake ki bashi fuska, ki nuna bakya sonshi, ki karyar mashi zuciya da barazana nasan zai hakura ya barmun ke kinji ko baby? tau my abdul.

Sai yace tau yanzu ki share hawayenki ki kwanta kiyi bacci, insha Allah gobe idan na fito daga asibiti zan biyo gidanku.

Toh tace daga nan sukayi sallam ya katse wayar

**********
Bayan kwana biyu
mummy ce a dakin abdulrahman tana mashi fada akan yaje ya gaida ammie dan tun jiya taketa mashi naci amma sam yaki zuwa.

Ita gani tayi tunda yaji sauki ai ya kamata yaje ya gana da mahaifiyar shi amma kamar wata makiyiyar shi tayi-tayi yaki zuwa shiyasa yau dinnan cikin fada da bada umarni tace dole sai yaje ya ganta.

Shima yanason ganawa da ammin shi kawai dae haushin abdulraheem yakeji dan bayason ganin shi dalilin dayasa kenan yaji bayason zuwa gidan.

Ganin ran mummy ya baci sosai ne yasa yayi saurin isowa gabanta yana murmushi yace mummy nah kiyi hakuri ki dan saki fuskar ki yanzu zan wuce.

Dukan wasa takai mishi hade da cewa sai dakaga nakai kololuwa zaka wani ce inyi hakuri? tayi kyacci tace zaka gamu dani ne ai.

murmushi yayi ya dauki wayar shi daman a shirye yake sai yabi bayan ta suka nupi part dinta. Dan umar ne zai kaishi saboda besan gida ba.

Samha kuma dagewa tayi akan saita bi abdul mummy tace bazata ba sai da abdul ya roki mummy sannan ta yadda zasuje. Da murnar ta taje tana yiwa labna gwalo sannan tasa kai ta fice. Lubna ko haushi kamar ya kasheta dan jitayi kamar ta bisu.

Bayan sun fita umar ne driving, abdul na daga gefe yana yan kalle-kallen shi ta tagar mota. Samha kuma na baya suna hira da umar jefi jefi har suka iso gidan.

Cikin farfajiyar gidan umar ya paka motar, suna fita ya tada motar ya wuce, dan akwai inda zashi.

Samha ce ta fara kalle-kalle tana tunanin inda zasu bi dan plat uku ta gani kuma duk iri daya guda daya ne kawai ya bambanta a wurin penti. Abdul kuma tsaye yake yana waya.

Bayan ya katse wayar neh ta nuna mashi plat din farko dan nan zuciyar ta raya mata dasu shiga tace yaya muje ko? ba musu ya bi bayanta dan da badan itaba komawa zeyi.

Wani kofa ta gani wanda ya bata damar gane cewa nan ne hanyar shiga cikin gidan, dan handle din dake makale a jikin kofar ta hau bugawa. Tayi bugu daya, biyu, uku sai ta dan jinkirta. Jin basu bude bane gashi sunkai kusan minti biyar tsaye sai taji abdul yaja tsuki yace dalla mu wuce.

Juyawar shi keda wuya yaci karo da abdulraheem har................





👇🏽👇🏽👇🏽
   Vote
Comment
And share
[2/18, 6:00 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

     Page 45-46

Juyawar shi keda wuya sukaci karo da abdulraheem har wayar abdulrahman ta fadi a kasa,  a tare suka duka zasu dauki wayar sai abdulraheem ya riga shi dauka ya mika mashi yana cewa sorry plss shima daidai lokacin abdul-rahman ya dago kanshi yana ce mashi sorry.

Samha ce tayi dariya ganin yadda suka duka a tare zasu dauki waya, yanzu kuma sun hada baki wurin bawa junan su hakuri. Hararanta abdulrahman yayi, sai ta gumtse dariyar ta.

Abdulraheem kuma hannu ya mika mashi suka gaisa kafin yayi taku daya zuwa biyu ya kwankwasa kofar. Yana bugawa hanan ta bude kofar daman tun dazu taji ana buga kofar shiyasa bugu daya kawai yayi ta bude.

Tamke fuskarta tayi dan har yanzu tana fushi dashi akan shaqar da yayi mata, tana budewa ta juya zata wuce, shi kuma yayi saurin tsayar da ita yace sis bakiga munyi baki bane??

Dawowa tayi bakin kofar sai idonta ya sarke cikin na samha. Cike da murna da mamakin ganinta taje ta rungume ta tana cewa besty waya kawoki gidan mu? Da fara'a a fuskar samha tace tare da yaya abdul nake.

Juyawa hanan tayi danta ganshi sai bata ganshi ba dan tuni abdulraheem ya isar dashi cikin palo.

Kallon samha, hanan tayi batare da tace mata wani abu ba taja hannunta suka shiga ciki. Lokacin har abdulraheem ya kirawo ammie.

Gaishe da ammie samha tayi sannan suka haura sama ita da hanan. Ammie kuma zama tayi suka gaisa da abdulrahman sannan ta shiga kitchen ta kawo mashi drinks. 

Bayan ta aje mashi parantin dake dauke da drinks din ne ta zauna saman kujerar dake fuskantar shi, tana dan murmushi dan ba karamin farincikin ganin ya'yan nata wuri daya tayi ba musamman ma da suka zauna saman kujera daya sai taji sun kara burgeta.

Dan jan abdulrahman da hira ta farayi dan yaki sakin jikinshi kuma duk da haka nan ta lura shi din ba mutum bane mai son magana. Abdulraheem kuma tashi yayi zai fita sai ammie tace abdul ina zakaje bayan ga dan uwanka ya kawo mana ziyara?  Dan sosa keya ya farayi ya dawo ya zauna yana wani bata rai.

Sai ammie tace toh tunda bakaji dadin ganin shi ba ai sai ka tafiyarka ko?  Kallon ammie yayi yace haba ammie ya zakice haka?  Ai nama fiki jindadin ganin shi, ya karasar maganar ne a yayinda yake kallon abdulrahman da shima jin maganar da ya fada ne yasashi dagowa suka hada ido.

Cikin ran abdulrahman tsuki yayi yace ji kamar da gaske.

A fili kuma sai kawai suka sakar ma junasu murmushin dani kaina bansan amanar shi ba.

Tashi ammie tayi ta basu wuri wai ko kunyarta yakeji shiyasa yaki sakin jiki, hatta drinks din data kawo mishi bai sha ba shiyasa ta shige daki.

Bayan ta wuce ne abdulraheem ya kalli abdulrahman yace dan uwa baka sha ruwa ba?   Abdulrahman yace a'a nagode.

Fakon shi abdulraheem yayi ya harare shi yace waton kai dan iska ne ko? Dan ma kasamu nayi maka magana shine zaka wani dinga basarwa ko?  Toh inma dai akan amatu ne kake wani shan kamshi gwara ma ka daina dan bata lokacin ka kawai kakeyi, ya fada gami da kawar da kanshi gefe.

Abdulrahman kuma baiji abunda ya fada ba dan kasa-kasa yayi maganar.

Shuru sukayi babu wanda ya kara tanka ma wani. Sai dai yan sake-sake da ko wannen su keyi.

Hanan ce da samha suka  zo palon suna dan kus-kus dinsu, dan tun daga saman staircase suka faro har suka nemi wuri suka zauna basu fasa ba. Samha ce talli hanan cikin yin kasa da murya tace Allah su twins abdul suna kama sosai, wallahi da badan nasan kayan da yaya abdulrahman yasa ba da bazan iya banbance su ba.

Wallahi kuwa, hanan ta fada had'e da dauko wayarta zata kasta musu hoto. Samha ta waro ido tace keyyy hmmm ina ganin yaya abdulraheem ba masifaffe bane shiyasa kika ga fuskar da zaki daukeshi hoto. Hanan tace hmmm kedai ai naga alama dan kodana gaishe shi sama-sama ya amsa mun.

kin gani kuma shine zaki dauka? Nidai kawai ki hakura da daukan hoton nan karki ja mana zagi, samha ta fada. Kallon uku saura hanan ta aika mata tace lallai toh wallahi sai na dauka, ammie fa nakeson in nuna ma.

Dariyar mugunta samha tayi mata ta matsa daga gefenta koda zaiyi fadan sai dai yayi wa hanan ita kadai.

Murmushi hanan din tayi tace ai duk masifar shi dole ya sarara mun tunda bakuwa nake a gurinshi kuma daman ance bakonka annabin ka.

Kallon zaki sani ne samha da aika mata, sannan ta mayar da hamkalinta kan makeken TV dake palon.
Hanan kam daukar wayanta tayi ta shiga camera ta danyi zooming camera din  saboda sun danyi nesa da ita.

Aikuwa tana dauka wayar tayi kara gami da kawo flash.

Abdulraheem da flash din  ya haska mashi ido sosai  yace hanan miye haka kin wani kunna touch din waya, dan baiji karar dauka ba saboda karar TV.

Hanan tace sorry yaya hannu na ne yakai wurin.
Komai bace mata ba ya mike yayi kwafa ya haura sama, dan ya kosa abdulrahman bai tafi ba. Samha kuma da hankalinta yake rabi kan kallo rabi kuma kan hanan, dan tayi tsammanin ko abdulrahman zai ce wani abu sai taji yayi shuru.

Cikin jin haushi tace waton mu ka raina da ko bada gangan mukayi maka laifi ba sai ka hukunta mu ko? Allah sai na fadawa mummy. ta fada gami da yin qyaccin da batasan ya fito fili ba. Hanan na dariya tace samha wannan qyaccin fah? Injin dai lafiya? Harara samha ta watsa mata gami da cewa zamu hadu a school ai. Daman makarantar su daya kuma aji daya suke amma babu wanda yasan gidan wani.

Mintuna kadan da tashin abdulraheem sai gashi tare da ammie, ammie tace abdul harka tashi wucewa Kenan? Cike da mamaki yake kallon abdulraheem dan yasan shine yacewa ammie ya tashi tafiya.

Wayancewa kawai yayi ta hanyar gyada mata kai alamar eh. Ammie tace aina dauka sai dare zaka wuce. Sai abdulrahman yace eh ammie naso mukai dare amma ana nema nane shiyasa zan wuce amma insha Allah bada dadewa ba zan dawo.

Ammie tace tau Allah ya kaimu

Abdulraheem kuma ajiyar zuciyar ya sauke dan ya dauka ko abdulrahman zai ce be tashi bane. kuma shi gashi a matse yake da yabar gidan dan yanason yaje asibiti kuma inson samu ne ma ya biya ta gidansu amatu.

Ammie ji tayi kamar karya tafi, amma bata nuna ba sai kawai tayi mashi sallama kuma ta bashi sako ya gaida yan gidan su. Nan suka musu rakiya har zuwa farfajiyar gidan. Inda abdulrahman ya tuna da baizo da mota ba. Aikuwa yayi tsuru gami da lalubo wayar shi zai kira umar kenan sai ya tsinkayo muryar samha na yacewa yaya tunda umar bai zoba basai mubi yaya abdul ba tunda shima fita zaiyi!

Sai ammie tace tau kuje ya saukeku mana. Abdulraheem saboda haushi sai ya koma kamar wani wawa yana kallon abdulrahman dake shirin shiga gidan baya, samha kuma gaba ta shige tana washe ma hanan baki.

Abdulrahman ko a jikinshi ya wani shige gidan baya ya babbaje kamar irin alhaji na jiran jireban shi. Sai wani murmushi kawai yakeyi wanda shi kadai ne kawai yasan manufar yinsa.

Haka abdulraheem ya shiga mota yaja wani irin wawan reverse wanda yasa har saida kan samha ya dan bugu da dashboard.

Sorry kawai yace mata yaci gaba da tukinshi.



Bangaren su mummy................


Ayi manaji da wannan plss
[2/19, 12:09 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

     Page 47-48

B'angaren su mummy, Abdulrahman na fita sai ga umma (yar'uwar mummy) tazo. Cike da fara'a mummy ta tarbeta, lubna kuma bataji dad'in zuwan ta ba dan tasan dalilin zuwan ta". Saboda jiya sunyi waya.

'Bayan sun gama gaisawa ne umma ke cewa ai tazo ta tafi da lubna ne" sai mummy tace lafiya zaki tafi da ita?  Umma tace eh lafiya kawai dai daman naga an kawota gidan ne saboda Abdulrahman. Toh babu wani canji da aka samu, shiyasa na yanke shawarar in mayar da ita gida.

Fuskar mummy cike da damuwa tace umma wallahi da ace ni na haifi Abdulrahman da cikina da zan iya tilasta mashi ya auri lubna, amma sai aka samu akasin haka, dan kinga idan na tilasta mashi ya zamana kamar na tauye mashi hakki ne. "kuma kin dai ga abubuwan da suka faru, dan a dalilin kamuwa da ciwon shi ne yasa wannan abun ya faru.

Kinga koda ina da niyar mashi magana ai baze yiyu ba tunda yana da wadda yakeso. Sai umma tace eh hakane gaskiya nima bazan so a takura mashi ba, shiyasa ma zan d'auketa tabar daga gidan nan tama bar ganin shi bakidaya nasan idan bata ganin shi zata manta dashi.

Ni wallahi har mamakin irin sonda lubna kewa Abdulrahman nake, danni bantaba ganin irin haka ba. Umma ta fad'a.

Mummy tace uhmmm tau Allah yasa tafiyarta shi yafi zama alkhairi. Umma ta amsa da ameen gami da cewa ina yaran gidan, dan tun shigowarta bata ga wulkitawar ko dayan su ba? 

Nan mummy tace sun tafi rakiyar abdulrahman har tafara bata labarin yadda ta tilasta ma abdul zuwa wurin ammie.

Murmushi umma tayi tana fad'in ai yarinta ce, dan inba yarinta ba tunda akace ga uwarka can ai zakayi zumud'in zuwa ganinta. Mummy tace kedai bari ai yaron nan sai a slow dan gabad'aya gidan nan dagani sai daddy ke iya tankwara shi yadda mukeso.

Murmushi umma tayi game da cewa Allah dai ya shirya mana su. Mummy ta amsa da ameen had'e da fad'in zasuyi kewar lubna musamman ma samha da makaranta ce kawai ke rabasu amma komai tare sukeyi.

Suna cikin hirar ne sai ga su Abdulrahman sun dawo. Samha ce tazo da gudu ta rungume umma tana dariya. Cikin jindadin yadda samha ke sonta tace baby na sannunku da dawowa. Samha na murmushi tace yauwa ummana yaushe kikazo??

Itama umma murmushin take yiwa samha tace ban dad'e da zuwa ba.

Shigowar Abdulrahman kenan yanzu, ya duk'a har k'asa ya gaida umma. "Cike da fara'a umma ta amsa tana tambayar shi ya ayyuka. Kamar wani mara gaskiya ya fara sosa k'eyar shi gami da cewa lafiya kalau.

Umma tace tau Allah ya taimaka. Ya amsa da ameen kafin ya mike yabar  falon.

Samha na jikin umma sai surutu take faman zuba mata sai kace wata aku.
Mummy tace wa samha taje ta kira lubna.

Lubna ko tana d'aki sai faman kuka takeyi tana cewa umma batason farincikin ta, tana kuka ne a yayin da take kwashe kayanta tana zubawa cikin

10 / 27