Chapter 14 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 27

39K to 42K   out of 79.1K words

d'aki tana kiran number abdul but switched off. Duk hankalinta ya tashi dan bata tab'a kiran wayanshi taji ta kashe ba irin haka.

"Cigaba da kiran nashi tayi tayi har taci sa'a ya bud'e wayar, wani farinciki ne ya ziyarce ta. Take kuma yanayin ta ya sauya sakamakon, rejecting d'inta da yayi.

"Zata sake dialing kenan taji text d'inshi ya shigo. Cikin yatsine fuska ta duba ta gani, murmushi ta saki gami da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya "jin yace mata yana asibiti ne kuma daya fito zai kirata.

"Tashi tayi da kwarin jiki  ta nupi toilet dan watsa ruwa. Bada jimawa ba sai gata nan ta fito, d'aure da towel.

"Zama tayi gaban dressing mirror ta shafe jikinta da mai da kuma turarukka masu kamshin gaske. Simple make-up tayi wa fuskarta sannan ta shirya cikin doguwar riga light blue, "tayi rolling da gyelen shi, " sannan ta d'auko handbag d'inta dake rayate jikin gadonta, had'e da bude drawer ta d'auko wasu takardu.

Fitowa tayi palour, nan ta tarar da mummy da daddy zaune suna hira. "Da murmushi a fuskarta ta karasa wurin su ta duka har kasa ta gaida su. "Cikin fara'a suka amsa mata".

Daddy "yace yauwa daman ke nake jira ki kawo mun takardun. Dan murmushi tayi taje har gaban shi ta mika mashi. Daddy "yace gaskiya naji dadin ganin result dinku keda ameera, yanzu nan zanje can BASE UNIVERSITY nakai musu dan naji ance sun fara bada admission.

Murmushi amatu tayi "tace eh daddy nima naji haka, daddy "yace karku damu insha Allah zaku dace Allah yayi muku albarka. "Suka amsa da ameen harda mummy dake wurin.

"Sallama tayi musu, kafin ta fita, dan tana son ta leka saloon taga yadda abubuwan suke gudana dan tun ranar da aka kai ameera asibiti bata kara zuwa ba".

Wurin hadaddiyar motar ta kiran range rover ta nupa, inda sai sheqi take dan kuwa tasha wanka. Shiga tayi ta tayar megadi ya wangale mata gate, " ta nupi gidan su ameerah dan tanason taga ya jikin nata yake duk da jiya taga jikin nata da sauki sosai.

A bakin gate d'in gidan ta paka motar ta sannan ta fito ta nupi cikin gidan. Da shigar ta Mubarak d'an Aunty hajara wanda be wuci shekaru hudu ba yazo da gudu ya rungume ta yana cewa anci cuwit, da hausan shi wadda bai gama iyawa ba.

Murmushi Amatullahi tayi ta d'agashi sama sannan ta dire shi, ta bud'e jakarta ta dauko sweet ta bashi. "Cike da murna ya ruga da gudu wurin aunty hajara da jin motsin su yasa ta fito. Murmushi ta sakarwa amatu sannan ta nemi wuri ta zauna.

Itama amatu zama tayi suka gaisa sai ga ameerah ta fito. Mikewa amatu tayi taje ta tarbo ameerah suka zauna. Cikin kulawa "tace mata ya jiki. Ameerah "tace alhamdulillah besty ai naji sauki. Murmushin jindadi amatu tayi "tace yauwa daddy ya anshi takardun mu.

Cikin jindadi ameerah "tace da gaske?? Amatu a'a da wasa. Dariya sukayi dukan su harda aunty hajara. Aunty hajara tace Allah sarki daddy, mukam babu abunda zamuce dashi sai Allah ya saka mashi da gidan Aljannah dan gaskiya ya kyautata mana da yawa".

Ameerah ta amsa da "cewa wallahi kam aunty ai daddyn amatu ya maye gurbin abban mu. Allah sarki Allah yaji kan Abba, duk suka amsa da ameen.

"Amatullahi kuwa sai murmushi take ana yabon daddy, ita kanta tasan daddyn ta mutumin kirki ne domin kuwa sau da yawa tasha jin ana yabonshi akan halayyar shi. Kuma ba shakka shi mutum ne mai tausayi, da hakuri da kuma tawakkali.

Ameerah ce ta katse ta, "tace besty naga kinsha wanka ina zakije? Kai tsaye amatu tace saloon. Ameerah "tace tau bari in dauko hijabi na muje ko?? Cikin zaro ido amatu tace nikam rufa min asiri nima da kika ganni ba dadewa zanyi ba, zanje inga kayan da babu ne insa a kawo.

Ameerah "tace koma dai mene sai naje, amatu "tace toh nama fasa zuwa. Ameerah "tace hmmm gaba takai ni bari ma ki gani, ta mik'e zata wuce dak'i, ta d'auko hijabi. Aikuwa Amatu tayi saurin rikota tace plsss my ameerah ki zauna ki huta kinga nima abu kawai zanyi na dawo.

"Ameerah ta wani bata rai, alamun ita fa bazata zauna ba. Amatu "tace tau muje tunda kin matsa. Da sauri ta nupi dak'i ta d'auko hijabinta sukayi wa aunty hajara sallama suka fice.


--------
B'angaren lubna kuwa tun sadda ta koma gida, kullum cikin kuka take,  umma kuwa dake bamai daurewa yara gindi bane sedai tayi ta mata fad'a kuma tana tayata da addu'a. Tun tana saran samu abdulrahman harta fitar da ran samun shi domin kuwa ko kiranshi tayi baya d'auka, wani abun haushi ma shine yasa number ta a blacklist, shiyasa data fahimci haka sai taji yama fita a ranta.

" Kuma ga ummanta dake zaunar da ita tana mata nasiha sai hakan yasa jikinta yayi sanyi har tayi alkawarin bazata kara zubar da hawaye akanshi ba.

"Umma kuwa dadi taji dan yar'ta ta fita daga damuwa da kunci. Yanxu haka ko hirar gidan su Abdulrahman batason anayi mata wai zai zama kamar ana tuna mata da Abdulrahman ne".


Bari mu leka bangaren su abdul


••••••••
"Abdulrahman ne tare da abdulraheem sunyi shigar kana nan kaya, duk iri daya, "sai wani sheki fuskar su keyi, kowannensu su yasa facing cap, kai ba karamin kyau sukayi ba".

Masu karatu plsss ku kwatanta kyan yan biyun nan dan innace zan fayyace muku irin kyan da sukayi basira ta zata kare😜😜

Zaune suke a wani hadadden garden suna tattaunawa...abdulrahman "yace bro nifa gaskiya tsoro nakeji. Abdulraheem "yace haba dai kawai kayi yadda nace. Murmushi Abdulrahman yayi yace owk Allah yasa in dace. Abdul yace "insha Allah" zaka dace.

Nan suke har kusan awa daya suna shan hira, inda  hira takai hira Abdul "yace shi kam ya matsu ba'ayi bikin su ya cashe ba. Abdulrahman yakai mashi dukan wasa "yace babu wani ai idan baka sani ba toh kasani, nidai bazanyi aure ba sai ka nemo mata ayi mana tare.

Abdul "yace nikam ban yadda ba, kawai ayi naka inyaso daga baya ayi nawa. Abdulrahman "yace lallai ai ko za'ayi shekaru zakayi baka samu mata ba, ina tabbatar maka da nima bazanyi aure ba.

Abdul "yace tau yayi dan uwa, Allah yasa duk wacce nace ina so taso ni. Abdulrahman ya waro ido yace haba dai sai kace wanda yayi kwantai?? "Hmmm aiko makaho ya sunsunaka yasan farashin ka mai tsada ne, bare kuma mai ido biyu, ya kake ganin zata kasance???

"Murmushi kawai yayi baice komai ba. Abdulrahman yace heyy bro ga lubna yar wajen mummy. Ya fada yana dariya. Bata rai Abdul yayi yace Allah ya sauwaka. Ni wallahi batayi mun ba. Abu sai kace fate.😍

Abdulrahman "ya kyalkyace da dariya harda dafe ciki. Hararan shi Abdul yayi ya mike zai wuce. "Da sauri Abdulrahman yaja hannun shi ya rike gam sannan suka bi hanyar fita daga garden din.

Bayan sun fita Abdulraheem ne ke driving. Cikin yanayi na serious magana yace ya muje zuwa ko?? Abdulrahman yace yeah. Nan sukaci gaba da hirar su har suka iso wani dan karamin gida mai kyau. Fita Abdulraheem yayi da murmushi a fuskar shi yace bro sai na jika.

"Abdulrahman daya fito ya zagayo ta bangaren shi hannu ya bashi suka sha sannan ya shiga mazaunin direba ya tadar motar.

Tafiya yakeyi a hankali,( a karo na farko kenan da Abdulrahman yake tuki a slow) murmushi yakeyi wanda nikaina na rasa gane kona menene. Bayan ya iso gidansu "Amatullahi ne ya paka motar a daidai gate d'in shiga gidan sannan ya fito.

Megadi daya fito da niyar bud'e mashi gate sai yaga harya paka motar nan waje sai ya fasa bud'ewa kawai ya dan rusuna ya gaida shi. Bayan sun gaisa ne Abdulrahman yace yayi mashi sallama da Amatullahi kuma ace macece ke neman ta.

"Cike da mamaki megadi ke kallon Abdulrahman, sedai kuma  ba abun ya tambayi dalilin ba, "sai kawai ya amsa da toh sannan ya wuce. Bada jimawa ba sai gashi ya dawo. Lokacin har Abdulrahman ya shigo cikin harabar gidan.

"Amatullahi kuwa tana ciki wai bazata fito ba, tunda dai mace ai ba haramun bane danta shigo. Mummy tace a'a kije dai kiga ko wacece. Dakyar ta yafa gyalenta tasha toka sai wani daddage kafa take har ta fita daga palour.

"Dake hankalinta nakan can waje, "dan duk a tunanin ta wacce ke neman nata na can waje shiyasa bata lura da yana tsaye wurin parking space ba. Har tayi kusan kai gate d'in fita Abdulrahman yayi sauri har yana dan hadawa da gudu yasha gabanta.

Cikin faduwar gaba tace Abdul miye haka zaka wani sha gabana??? Kuma banace karka kara zuwa gidan mu ba?? Abdulrahman ya amsa da eh.

Tsaki tayi tabi ta gefen shi zata wuce, yayi saurin tsayar da ita, " yace Amatullahi nike nemanki. Zaro ido tayi had'e ta juyowa ta banka mashi harara, cikin ranta tace shine yace ace macece?? Qyatt tayi kyacci, ta nupi hanyar shiga ciki.

"Cikin muryar shi mai d'an karan dad'i ya kiran sunan ta. Cak ta tsaya dan kuwa ba k'aramin shokin taji ba a yayinda ya kira sunanta sai taji kafarta ta sarke bazata iya koda taku d'aya ba.

Cikin marairaicewa "yace Amatullahi nasan nayi maki laifi da yawa kuma duk wani hukunci da kika yanke ya dace dani, amma sedai abu d'aya nake rokon ki...............




Plsss share
[2/24, 6:41 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Masoyana ina alfahari daku a duk inda kuke, Allah ya kara mana kaunar junan mu ❤❤

     Page 61-62
Amma sedai abu d'aya nake rokon ki, ki yafe mun lafin da nayi maki, ki nuna babu wani abu daya taba shiga tsakani na dake kuma kisawa ranki ni "Abdulrahman na cire sonki a raina kuma na rabu dake har abada".

Dummm taji zuciyarta buga, "sai tunanin wulakancin da tayi ta mashi a baya ya dawo mata". Duk sai taji ta damu domin kuwa ai yaci ace duk nacin nan da yake mata ko bazata karbi soyayyar shi ba yaci ace ta yafe mashi.

"Cikin rashin sanin abunda zatace hawaye ya fara zubowa daga idonta, "sai taji wani irin tausayin shi ya kamata. Hannunta tasa ta share hawayen da batasan ma'anar zubowar su ba. 

Shi kuma yana tsaye yana kallon reaction d'inta, "sai tsinkayota yayi tana "cewa Abdulrahman na yafe maka nima dan Allah ka yafe mun. Har cikin ranshi yaji dad'i amma bai nuna ba sai kawai "yace nagode sannan ya ficewar sa daga gidan.

"Fashewa tayi da kuka ta shige gida a guje, mummy dake palour tayi saurin tarota ta rungume ta gami da tambayar ta ko lafiya. "Cikin shasheqa kuka "tace mummy Abdulrahman ne yazo.

Mummy ta maimaita kalamar cike da mamaki "Abdulrahman kuma??? Amatu ta gyada kai alamar eh. Mummy tace toh meya miki kike kuka??

Amatullahi "tace mummy kinsan jiya daddy yace sun sulhunta kansu, Abdulraheem na nan mazaunin shi kuma ya tambaye ni nace amince, kinsan daman abdulrahman yana zuwa wuri na shine yanzu yazo "wai in yafe mashi.

Cikin d'an bata rai mummy tace toh shine abun kuka? Aina d'auka ko wani abun yayi maki. Amatullahi ta girgiza kai tace mummy beyi mun komai ba nima bansani dalilin kukan ba.

Tsaki mummy tayi "tace amma dai Amatu da wawta kike, ai na zaci dad'i zakiji tunda ya rabu dake ko? Amatullahi tace eh mummy naji dad'i kawai irin maganganun da nayi ta fad'a mashi ne nake jin ban kyauta ba.

"Mummy tai nisa tace tau kuskure kam ai an rigada anyi shi kuma tunda yazo ya rokeki gafara ai kam komai ya wuce tunda watakil kema kince ya yafe maki ko??

Amatu ta amsa da eh, mummy "tace tau "alhamdulillah Allah ya shige mana gaba. Amatu ta amsa da ameen.


"Abdulrahman na fita direct gidan da ya ajiye Abdul yaje ya d'auko shi, bayan ya d'auko shi suna tafiya cikin mota, Abdulrahman yace kai wai kaga yadda tayi ne?? Hmmm harda kuka, Abdul yace kuka fah?? Abdulrahman yace wallahi ni nama rasa ko kukan me takeyi.

"Abdulraheem yayi murmushi yace hmmmm ka gani ko, ai nasan yarinyar nan tana sonka, "kawai dai tana kaiwa kasuwa ne, kuma ni a tunani na gani nake kamar dan tana soyayya dani ne yasa bata amince dakai ba har take maka wulakanci".

Abdulrahman "yace hmmm babu wani, kai dai ai aiki na gaba, "waton har naga tana cewa in bata takardar saki idan ta gane bakai bane. "Dariya Abdul yayi yace matsoraci kawai, kaida zaka koya mata sonka, ka koya mata yadda bazata iya rabuwa dakai ba?? Ai idan kayi haka toh ko daga baya ta gano gaskiya bazata taba "cewa ka saketa ba. Sedai tayi fushi dakai na kwana biyu, " kuma ai an wuce wurin.

Abdulrahman ya shafo kanshi yana murmushi "yace kai d'an uwa kwakwalwar ka na mugun ja wallahi. Abdul baice komai ba yaci gaba da tuki danshi ya karbi tukin da Abdulrahman ya dawo d'aukan shi.

"Sun kawo daidai tsakiyar hanya Abdul ya kalli gefen hagu da dama yace ya bro ina muka nufa? Abdulrahman ya kalli hagu ya kalli dama, yace kai muje gidan ammie dan nayi missing d'in girkin ta.

Abdul ya harare shi had'e da "cewa babu wani nikam gidan mummy nakeson mu tafi, Abdulrahman yace babu matsala duk yadda kakeso haka za'ayi kaji d'an kani.

"Abdul ya banka mashi harara kafin ya d'auke hanyar daman shi, gidan ammie kenan. Abdulrahman ko bai kara magana ba har suka isa.

"Wurin parking space ya nupa sannan ya paka motar suka fito, hannun su sarke dana juna suka biyo hanya har suka iso bakin kofa. Abdulrahman ne yayi knocking, nan da nan ammie ta bud'e dan tana palon zaune tana kallo, duk kad'aici ya isheta dan hanan bata nan.

"Murmushi ta sakar musu a lokacin da tayi arba ta kyawawan yan biyun ta. Suma suka mayar mata da martani had'e da shigewa cikin palourn suka zauna.

"Cikin ladabi suka gaishe ta, Itama da fara'a ta amsa musu tana cewa daga ina haka wannan wankan? Abdulrahman yace amsa ta yana dan sosa keya yace ammie muje ganin wani abokin mu ne, "yayi saurin fad'a dan bayason Abdul yace wurin Amatullahi sukaje, dan kuwa ba karamin aikin shi bane.

Ammie tace tau ai kun kyauta da ziyara, Abdul "yace ammie akwai abinci ne? Ammie tace eh, nan yace tasaka musu yunwa sukeji. Batare da bata lokaci ba ta zubo musu hadaddiyar shinkafa da miya da namomi, sannan ta hado musu da drinks ta dire a gaban su.

"Cikin jindadin abincin suka fara hira suna santi ammie kuma kallonsu kawai take tana murmushi.


Bayan sati d'aya

"Komai na tafiya normal kamar yadda suka tsara", yanzu Abdulrahman shike zuwa wurin Amatullahi a matsayin Abdulraheem, kullum suna like a waya ga kuma nacin zuwa wurin ta. Ita har mamakin sauyin halin shi take, dan taga da ba kowani lokaci yake zuwa ba saboda yanayin aikin shi amma yanzu bai wuce kwana biyu bezo ganinta ba.

"Abdulraheem kam yana nan shi kadai cikin kadai ci, sai kuma aikin shi daya mayar da hankali kai, kullum cikin addu'a yake Allah ya bashi wacce zata maye mashi gurbin "Amatullahi kuma Allah ya amsa domin kuwa, yau tunda ya wayi gari "yaji yana bala'in son ganinta".

"Gashi ayyuka sunyi mashi yawa, dan asibitin nasu akwai marasa lafiya da dan yawa kuma babu halin ya tafi har sai ya basu isashen kulawa.

Da misalin karfe shida da rabi na yamma yabaro asibitin, "lokacin duk a gajiye yake. Da isowar shi gida part d'in shi ya nufa, ya d'an huta na yan mintuna kafin ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin manyan kaya wanda suka amshi jikin shi.

"Sai kamshi yake zubawa had'e da sakin murmushin daya kara fito da kyan fuskar shi. Wayan shi ya d'auka tare da makullin motar shi ya nupi part d'in ammie. "Bayan ya shiga palon ta hanan kawai ya tarar tana cin abinci.

Da murmushi ta tarbe shi kafin ya k'araso wurin ta ya zauna gami da tankwashe kafafuwan shi, ya kalli fuskarta cikin zolaya yace ko kar nasa maki hannu?? "Murmushi tayi gami da waro idonta tace uhm uhm yaya ai nama koshi bari in karo mak..... Sai suka tsinkayo muryar ammie na cewa a'a zauna bari in kawo mashi.

"Kitchen ammie ta shiga ta zubo mashi abinci ta kawo mashi nan inda yake zaune, a hankali ya faraci harya koshi kafin hanan ta kwashi plate d'in takai kitchen. "Shi kuma tashi yayi yace wa ammie zashi wani wuri sai ya dawo.

Da murmushi a fuskar ammie tace ina zakaje? Cikin jin kunyar ta "yace ammie wani aboki na ke nema na. Ammie tace kullum dai aboki, aboki, tau Allah dai ya bada sa'a. "Murmushi ya saki a yayinda yake fita daga palon.

"Wurin motar shi ya nupa, ya shiga ya bata wuta. Direct maitama store ya nupa, inda ya d'an sayi abubuwa da yawa sedai kuma bai bari naga abunda ya saya ba. Yana fitowa aka fara kiraye kirayen sallar magariba, nan ya shiga masallacin dake wurin yayi sallah har saida akayi isha'i kafin ya baro wurin.

"Tsaye yake a bakin gate d'in gidan su yana jiran ta fito" dan yasa ayi mashi sallama da ita. Kallon daidai saitin kofar yake yana jiran zuwan ta. Ita kuma sanye take da gown mekyau ta yafa gyalen shi sedai fuskarta babu kwalliya amma duk da hakanan kyan ta ya fito domin kuwa Allah yayi ta da natural beauty.

"Murmushi ta saki a lokacin data ganshi gami da karasowa wurin shi, suka gaisa, Bayan sun gaisa take..........


Masu karatu ga assignment kowa ta fad'i min ko wacece Abdulraheem yazo wurin ta 😎😎








Mu had'u a next page insha Allah
[2/25, 9:42 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

       Page 63-64
'Bayan sun gaisa take tambayar shi ina Amatullahi, murmushi yayi "yace aike zan tambaya kuda kuke mak'wafta. D'an murmushi tayi "tace gaskiya kam amma dai kaima ai kamar mak'wafcin  ta kake, tunda ba'a dad'ewa babu had'u ba.

"Hmmm kedai a wuce wurin, kallon shi tayi "tace a wuce wurin kamar ya? Kodai kazo wurinta bata gida ne?? Gyad'a mata kai yayi alamar a'a ayayin da idanuwanshi ke kallon d'an karamin bakinta da

14 / 27