Chapter 3 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 27

6K to 9K   out of 79.1K words

bude aiko sai taci karo da text message, mika mashi wayar tayi tana cewa yaya an turo maka sako ansa ka gani.

Harara ya balla mata yace dalla kiyi abunda zakiyi ki mikon waya ta. Dariya tayi da yadda taga ya fusata tace to saina bude na gani kuma na ka ranta kaji. Ko kala bece mata ba sai jin yayi ta fara cewa barkan ka da war haka amintacce da............
da sauri ya fisge wayan ya banka mata harara sannan ya kara gaba.

Ammie data fito yanzu murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace ke in banda abunki wake karanta sirrin wani? Shuru tayi tazo ta rungumeta tana cewa plsss ammie ki bani wayana nayi alkawari bazan sake ba. Kallonta ammie tayi tace to naji kije dakina cikin drower ki dauko. Cikin jindadi ta sumbaci ammie a kumatu ta wuce da gudu.

Shiko yana fita part dinshi ya koma ya bude message din yana karantawa. Cikin tsantsar farinciki yayi saving number kafin ya shiga dailing din number amma sai dai kash a kashe take, haka yayi ta kira a kashe daga karshe kuma ya tashi ya fita amma yaji dadin ganin sakonta.

Bangaren ta kuwa tunda ta tura mashi sakon ta kashe wayanta saboda ta dauki alkawarin tunda harya iya guje mata na tsawon shekara biyu toh itama sai ta rama ta hanyar wahalar da zuciyar shi shima ya dan dana irin zafin dataji

Cikin ranta kuma take cewa toh idan bashi bane fah? Ya kenan? Tsuki tayi ta kawar da maganar dan ita har yanzu bata yadda ba Abdul dinta bane.

Washe gari
Da misalin karfe goma na safe ya kira daddyn amatu da ainihin number shi, nidai banji abunda aka ce ba sai dai daga gani maganar tayi mishi dadi.

Da yamma ya shirya tsaf cikin shiga ta alfarma sai kanshi yake zubawa da ammie ta ganshi tace Allah yasa suruka za'aje samo min. Murmushi yayi yana Sosa keya ya fice daga gidan.

Tafiya yake cikin annashuwa harya kawo dai dai gate din gidan, batare da bata lokaci ba megadi ya wangale mishi gate sai gashi cikin farfajiyar gidansu.

Kiran daddy yayi sai gashi ya turo an shigo dashi palon baki. Cikin girmamawa ya gaida daddy kafin ya koma ya zauna,

Kallonshi daddy yayi yace bari in dawo kaji yaro. Amsawa da toh Abdul yayi yana mai jindadin yadda daddy ya yarbe shi sai dai addu'ar shi daya Allah yasa ya amince da kudirin shi.

Yana cikin haka sai gashi nan ya dawo, zama yayi kan kujerar dake facing dinshi yace ayi mun afuwa na bata maka lokaci ko.

Murmushi Abdul yayi yace ai babu komai. Tau yaro ina saurarenka

Daddy nasan baka sanni ba amma dan Allah ina rokonka daka amince da batu na. Shuru daddy yayi na seconds kafin yace indai bukatar ka bata kauce wa addini ba insha Allah zan biya maka ita

Cikin dadi Abdul yace nagode daddy sunana Abdul........ Sai akayi sallama daga waje, dake daddy yasan da zuwanta babu wani bata lokaci ya bata izinin shigowa.

Shigowa palon tayi dauke da paranti a hannunta duk da cewar tayi mamakin ganin shi amma haka ta daure ta karasa gabanshi ta ajiye mashi parantin, ji tayi ameerah dake bayanta ta gaishe shi shiyasa itama tayi kokarin saita kanta ta gaishe shi, shiko kamar ma bai taba ganinta ba dan kawar da kanshi yayi daga gareta yana fuskantar daddy.

Suna fita Amatu ta sheka da gudu zuwa dakinta dan yadda taji gabanta na mugun faduwa

Daddy kuma bayan fitar su kallon Abdul yayi yace toh yaro cigaba da maganar ka



Muje zuwa πŸ‘‰πŸΏ
[2/5, 11:47 PM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Wannan shafin sadaukarwa neh ga my real Momcy (haleemah) ina sonki ina kaunarki fiye da yadda kike tunani, Allah yabar mu tare πŸ’‹πŸ’‹

Vote me on wattpad @lashminzy
Email; bilkisualiyu248 @gmail.com

Page 13_14

"Sunana Abdulraheem Ibrahim kanta" cikin tsoro da mamaki daddy yace kana nupin kai dan gidan Ibrahim kanta neh aboki na kuma aminina?? Eh daddy. Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace cigaba da maganar ka ina jinka.

"Daddy duk da nasan cewar a kwanakin baya da suka wuce kun samu sabani da mahaifina inason karka fasa cika alkawarin daka dauka. Daddy bakomai ya kawoni wurinka face Yar gidanka dana gani kuma tayi mun shiyasa nazo neman izini a wurinka. Ya karasa maganar neh gami da sunkuyar da kanshi wai ala dole yaji kunya.

A firgice daddy ya mike tsaye yace Abdul ka kuwa San abunda kake fada kuwa? Kasan irin rikicin da muka samu da mahaifinka a sakamakon abun duniya? Girgiza kai Daddy yayi yace kai ina bazai yiwu ba saboda koda ni na amince shi bazai taba amincewa ba. Amma kasani tunda nayi maka alkawari kayi hakuri ka jira zuwa karshen wata zan biya mahaifinka kudin shi kuma zamu sasanta kaga daga nan kai kuma sai ka bijiro da taka maganar ko?

Eh daddy amma wani hanzari ba gudu ba. Dan Allah Inason kamun izinin zuwa gidanka. Murmushi daddy yayi ya dafa shi yace karka damu na maka izini kuma nagode maka da kokarin ka koba komai zumuncin mu zai karu.

Cike da farinciki ya fara gode ma daddy. Daga nan suka fara hira, hira tayi hira daddy ke bawa Abdul labarin kidnapping din Amatu da akayi. Abdul ko kamar bashi ya aikata ba harda wani cewa Allah ya toni asirin su. Haka sukaci gaba da hira kamar wa'anda sukayi sabo, sai kusan magariba Abdul yabar gidan.

Ko daya koma gida karfe goma na dare dan sai daya biya wurin abokan shi suka dan taba hira kafin ya dawo gida.

Part dinsa ya nupa, da shigarsa ba bata lokaci ya watsa ruwa ya shirya cikin kayan bacci sannan ya kashe wuta ya kwanta. Wayar shi ya dauko da niyar ya kira Amatu sai ga sakonta ya shigo kamar haka "Slm Abdul me kazo yi gidan mu??

Tsuki yaja bayan ya karanta ya fara dailing number ta amma yaji ta a kashe. Ranshi neh ya baci yace wai me yarinyar nan ke nupi dani ne? Tace ta amince dani amma kuma take wulakanta ni? Toh wallahi bazai yiwu ba gobe goben nan zata ganni a gidansu kuwa.

************
Bangaren Amatu kuma tana aika sakon ta kashe wayanta amma da biyu. Na farko karya kirata ya balbaleta dan ta tuna da kashedin dayayi mata akan duk abunda ta gani tayi kamar bata gani ba. Na biyu kuma tanason ta wahalar da zuciyar shi har sai yagaji ya dawo ainihin Abdul dinshi.

Niko nace Amatu kina da aiki kuwa

Washe gari da maraice ya shirya tsaf cikin yadi me ruwan madara da bakin hula da bakin takalmi sai zuba kamshi yake kamar wani sabon ango. Part din ammie ya nupa, Kodaya shiga ammie na zaune saman one tana kallo hanan kuma tana aikin latsar waya

Kallonshi ammie tayi cikin zolaya tace Abdul nipa kwana biyu na kasa kagane maka? Daga dawowarka daga aiki harka sake sabon wanka? Toh wai ma ina zakaje neh haka? Dan shafa sajenshi yayi yace ammie babu komai fa kawai zan raka abokina wani wuri neh.

Toh Allah ya bada sa'a amma fah inka rakashi ka tabbatar kaima ya raka ka kaji ko? Dariya yayi dan ya fahimci inda maganar ta nupa ya fice daga palon gami da kwalawa hanan kira.

Wurin motar shi ta sameshi yana latsar wayanshi. Kallonta yayi yace sis dauko gyalenki muje ki rakani wani wuri kinji? Ko amsawa batayi ba ta zura aguje taje ta dauko mayafinta ta dawo. Shiga motar sukayi ya kama hanya sai gudu yakeyi kamar wanda zai tashi sama.

Ita kuma hanan sai faman tambayar shi ina zasu take amma ko kallonta beyi ba yace tasa ido ta gani. Hhhhh nima nace bari insa ido in gani hhhhh masu karatu kuma kusa ido ku gani.

Daidai bakin kofar gidan ya tsaya dan ba shiga zeyi ba. Fitowa yayi daga cikin motar ya isa wurin me gadin gidan da niyar yayi mishi sallama da Amatu dan ya kira number ta switch off sai gasu nan sun iso ita da ameerah.

Shan toka tayi zata shige sai yayi saurin shan gabanta yace ina da magana dake? Juyowa tayi suka hada ido sai taga alamar babu wasa attare dashi shiyasa bata musa ba ta bishi zuwa wurin motar shi. Ameerah kuma tun bayan ta gaishe shi ta shige gida.

Tsaye tayi kamar wata gunki babu eh balle a'a. Shima murtuke fuska yayi kamar be taba dariya ba yace miye dalilinki na kashe waya? Shuru tayi bata ce kala ba sake maimaitawa yayi kafin ta kalleshi tace babu komai. Yar dariya ya saki ganin yadda ta cuno bakinta yace toh daga yau karki kara kashe wayanki indai har kina sona.

Dago da kanta tayi ta kalleshi zatayi magana sai ya katse ta da cewa "AMATULLAH kar kiga kamar ina tauye miki haka, nop ba haka bane wani abu da ki kaga inayi akwai dalili wani kuma zuciyata ke sani aikatawa kamar yanzu danazo gidanku kunnuwana suna bukatar jin zazzakar muryarki kamar yadda idanuwana ke muradin ganin kakkyawar surarki ammai sedai ke kina mun rowa.

Bansani ba ko kunyata kikeji ko kuma har yanxu kina tunanin wancan Abdul dinne oho amma dai kisani ni Abduraheem masoyinki neh na gaskiya ki saki jikin ki dani, ki manta da wancan Abdul din naki ki rungumeni hannu bibbiyu nayi alkawarin zan baki kulawa har karshen rayuwarki.

Hawayene suka gangaro mata dajin irin kalaman da ya fada kamar na wacan Abdul din kusan komai nasu babu banbanci taya za'ayi bazata taba yadda bashi bane??

" AMATULLAH" zuciyarta ceh ta buga da karfi saboda yanayin yadda ya kira sunanta yace indai har zaki soni kuma zaki aureni toh kisa wannan a kwakwalwarki ni "ABDULRAHEEM" nayi miki alkawarin duk sadda Abdul dinki ya dawo zan sakeki ki koma gareshi koda kuwa yin hakan shi zai zamo ajalina.

Da sauri ta dago da kanta suna kallon juna tace Abdul saboda me zakayi haka?? Saboda farincikin ki ya bata amsa.

Hawayenta ta share tana mai jindadin kalaman shi tace nagode Abdul nima nayi maka alkawarin daga yau zaka fara jindadin zama tare dani.

Murmushi ya sakar mata kafin ya zagaya ya budewa hanan kofa danta fito su gaisa da ita. Ja mata kunne yayi akan kada garin surutu ta sakar mishi layi dan hanan akwai iya surutu ga bakinta da kaifi kamar reza.

Suna zuwa inda take hanan ta rungumeta tana cewa aunty ina wuni. Murmushi Amatu tayi karba mata tana kallon Abdul da fuskar shi dauke take da fara'a.

Bayan sun gaisa neh kuma ya gabatar da matsayin hanan a wurin shi kafin suka wuce

Koda suka isa gida ammie na kitchen tana dahuwar abinci, da gudu hanan ta karasa wurinta ta rungumota ta baya tace ammie mun dawo amma fah akwai labari. Abdul dake shigowa kitchen din yace toh sannu magulmaciya ki fada a gabana mana.

Dariya tasa ta fice daga...................





Pls share
[2/7, 10:45 AM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Real Momcy and sweet janaf ina tayaku murnar kammala littafin ku Allah ya kara muku basira Allah yasa kufi haka Allah ya albarkaci rayuwarku Allah ya amfanar damu darussan dake ciki kurakurai kuma Allah ya yafe mana bakidaya

Vote me on wattpad @lashminzy
Email; bilkisualiyu248@gmail.com

Page 15-16
Dariya tasa ta fice daga kitchen din. Abdul kuma taya ammie yayi abinci tana cewa ya bari amma fur yaki. Da hanan ta dawo dariya ta kamayi masa tana cewa dan daudu, ammie kuma murmushi kawai takeyi tana jin son yaranta na kara shigarta.

''Kwance take tana chatting ameerah da yanxu ta shigo kallonta tayi cikin dan bata rai tace Amatu wai bazaki shirya mu fita bane? Tashi tayi a kasalance ta dubi ameerah data bata rai, murmushi tayi tace sorry my meerah bari in shirya mu tafi.

Mikewa ameerah tayi gami da cewa ki biyomin inkin shirya. Bayan fitar ameerah tashi tayi ta shige toilet ta watso ruwa babu wani bata lokaci ta shafa mai sannan ta lailaye jikinta da turaruka masu kamshin gaske. Batayi wata kwalliya me yawa ba tasa riga da skirt na atamfa da bakin hijabi.

Handbag dinta dake rataye ta dauko gami dasa takalminta kafin ta fito. Dakin mummy ta nupa tayi mata sallama sannan ta fito waje, ta dauko wayanta kenan zatayi dailing number ta sai gata nan tazo. Murmushi suka sakarwa juna sannan suka nupi inda motar Amatu me kirar range rover kalar baka mai daukan ido.

Batare da wani bata lokaci ba ta tayar da motar suka fita, sun kai kusan minti goma kafin suka isa bakin wani dan madaidaicin shΓ go mekyau wanda daga sama an rubuta AMATULLAHI BEAUTY SALOON da manyan haruffa, pakawa sukayi ta gefen shagon sannan suka fito suka nupi shagon, mukulli amatu ta zaro daga jakarta ta bude shagon suka shiga.

Dake shagon babu wasu kayaki da yawa saboda rashin zuwanta na kwana biyu kuma tunda akayi kidnapping dinta aka rufe shagon sai shekaranjiya suka fara zuwa. Dan kakkabe dan sauran kayan dake ciki suka farayi suna sharewa kafin titi ta dawo(wadda amatu ta aika ta anso mata kayan datayi order) kuma ta kama yau lahadi neh shiyasa babu yan aiki ciki dan duk ba hausawa bane su kadai neh musulmai sai wata Maryam amma yanxu tabar zuwa saboda tayi aure.

Suna cikin aikin neh sai ga titi ta shigo da kaya niki niki a hannunta, ajiyewa tayi taje ta kwaso sauran kayan ta dawo. Zama tayi saman kujera da gurbataccen hausan ta wanda bata gwanance ba tace sannu aunty nageji sosai fah. Ruwan da amatu ta fito dashi daga mota ta mika mata tace gashi kisha ruwa kyafi jin dadin hutawan ko?

Murmushi tayi ta amsa. Ameerah kuma dariya takeyi wa titi saboda yanayin yadda take magana kamar ansata yin hausan dole. Nan suka fara hira suna jera kayan da aka siyo wanda suka kare kuma a jefa fankwon shi cikin dustbin.

Bayan awa biyu
Abdul neh a bakin kofan shagon su dake maza basa shiga shiyasa daya zo ya yatsaya a bakin kofa yana jiran fitowarta. Ita kuma tana steaming kan wata neh shiyasa ta dan bata lokaci kafin ta fito.

Kodata fito ya koma inda ya faka motar shi yana fuskantar shagon da hannunwan shi zube cikin aljihu. Murmushi ya sakar mata a daidai lokacin data iso wurinshi. Itama mayar masa da martani tayi gami da gaishe shi. Amsawa yayi cikin fara'a yana mai kura mata ido. Itako kunya taji ta rufe fuskanta da hannuwanta.

Dan bata rai yayi yace to miye na rufe fuska kodai ba'aso naga kwalliyar neh?? Janye hannunta tayi ta dubeshi ta gefen ido tace laaaa ah'ah nida ko kwalliya ma banyi ba. Dan zaro ido yayi yace wannan hodar da janbakin fah ko haka Allah ya halicceki dasu?? Dariya ta kyalkyale dashi.

Dan jim sukayi na dan mintuna kowa da abunda yake sakawa a ranshi. Ganin shurun yayi yawa sai amatu tace itakam zata koma shago sunada mutane da yawa. Bata rai yayi alamar beji dadin maganarta ba yace owk sai anjima. Itako ganin yanayin shi yasa jikinta yayi sanyi dan yadda yayi maganar kamar ranshi ya baci.

Cikin sanyin murya tace Abdul... Sai kuma tayi shuru dan batasan abunda zatace ba. Juyowa yayi ya kalleta yace akwai wani abu neh?? Saurin bashi amsa tayi tace plsss am sorry nima banso mu rabu yanzu ba kawai dai babu yan aiki cikin shagon neh kuma ga customers na zuwa shine nake sauri in sallamesu.

Tau naji baby ki kula da kanki and karki manta idan kin koma gida ki sanar dani. Amsawa tayi da toh gami da daga mishi hannu har sai daya bace ma ganinta.

************
Zaune yake a dakinshi yana cin abinci sai wayanshi tahau ruri, dubawa yayi yaga Abba neh kiranshi. Da sauri amsa daga bisani kuma naga ya tashi ya fita. Part din Abba ya nupa koda yaje ya tarar da Abba sai safa da marwa yakeyi a tsakiyar palonshi.

Cikin tashin hankali Abdul yace Abba lafiya na ganka haka? Kallonshi Abba yayi da duk ya jike da zufa yace Abdul ina lafiya kuwa dazu Muhammad lemi (daddyn amatu) ya kawo mun kudina harda bani hakuri.

Cikin nuna damuwa Abdul yace toh yanxu miye mafita? Ya zakayi ka mayar mishi da kudin shi? Haba Abdul nakira Kane fah dan ka bani shawara ni wallahi kaina ya kulle sai yanzu nake danasanin aikata abunda nayi. Ni yanzu ma da wani ido zan kalleshi idan yasan ni nasa akayi kidnapping din yar'sa?

Kallonshi Abdul yayi yace hmmm abba kenan abunda nake nunar maka kenan ai gashi yanzu kayi danasani amma a zahiri cewa yayi abba abu mafi sauki kawai ka fada mashi, kaga tunda yana da saurin hakuri zai iya yafe maka.

Wani banzan kallo Abba ya aikawa Abdul yace baka da hankali Abdul yanzu so kake naje har gabanshi ince ni na sace Yar shi? Ya kake tunanin ze kalleni? Wani matsayi zai daukeni ace yadda muke dashi na aikata mashi irin wannan akan abun duniya aiko waye bazai ji dadi ba.

Eh hakane Abba amma ga shawara... Nace tunda ya dawo maka da kudin ka me zai hana ka mayar da zumuncin ku kamar na da sai kuma ka nema mun auren yar shi.

Tswaya Abba ya daka mashi yace wai kai Abdul yau dinnan meke damun kwakwalwar Kane? Ya ina maka magana kana dauko mun wata magana can daban?

Hakuri Abdul ya shiga bashi yace Abba ba wani Abu bane naga kamar idan na auri yar shi zumuncin ku zai karu kuma koda daga baya ka fada mashi haka zai iya yafe maka kodan albarkacin yar shi dake aurena kuma ma zai dubi girman zumuncin ku ya yafe maka. Kaga daga nan komai ya wuce.

Murmushin da bekai zuci ba Abba ya saki yace kana ganin shawarar nan taka tayi kuwa??

Nima dai nace anya kuwa shawarar nan tayi??


Pls share
[2/8, 10:53 AM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŒΓ’Γ‘πŸ’₯

Vote me on wattpad@
lashminzy
Email:bilkisualiyu248@gmail.com

*سْــــــــــــــــمِ Ψ§Ω„Ω„Ω‘ΩŽΩ‡Ω Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­Ω’Ω…ΩŽ* Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­ΩΩŠΩ’Ω…Ω
_*May Allah (SWT) Bless you and your family with a restful mind, useful soul, peaceful home, commendable effort, acceptable worship, and a successful end. May He beautify your tongue with truth, heart with sincerity and count you among the dwellers of Jannatul Firdaus, Insha Allah. Juma'at Mubarak.

Page 17-18

Abba kallon Abdul yayi yace jeka na yadda da shawarar ka kuma duk abunda ake ciki zan sanar dakai kuma wa'yannan kudin ka dawo su a jiye har zuwa lokacin da za'a bashi kaji ko? Amsawa da toh Abdul yayi sannan ya fita.

Dakinshi ya nupa yana mai

3 / 27