Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
aje kusa da ita sannan taja hannunshi alamar ya miƙe, ba musu ya tashi ya zauna kusa da ita ya ɗauko robar zuman ya buɗe ya fara bata a baki, yace amma yau cokali ɗaya zakiyi ba uku ba, murguɗa mashi baki tayi shiko yayi saurin cafke bakin ya fara bata hot kiss, suna tsaka da haka sukaji ana knocking.
Da sauri ya zare bakinshi daga nata yaje ya buɗe kofar, umar ya gani tare da samha, murmushi suka sakar wa juna kan yayi musu iso suka shigo ciki, samha ta ƙarasa wurin Amatu data miƙe tsaye ta fara zuwa wurin su danjin muryar su suka rungume juna, Abdulrahman ya wani bankawa samha harara wanda a take ta saki Amatu tana ɗan murmushin dole, danta gane abunda yake nupi da hararar. "Amatullahi kuma bata lura ba, jan hannuta tayi suka zauna suka fara hira dan samha akwai surutu ga kuma jininta ya haɗu dana amatu kullum idan tazo gidan haka zasuyi ta hira har cewa take bazata gida ba nan zata kwana, "Abdulrahman kuwa kallo ɗaya yake mata ta figi gyalenta ta wuce dan tasan halinshi.
Suna tsaka ga hira samha ta fiddo wasu haɗaɗɗun invitation card daga jakarta ta miƙawa Amatu tana murmushi tace aunty ga wannan na auran aunty lubna ce, Umar dake gefe yace keeee bakijin magana ko, wayace kikawo? Ba saida mummy tace karki kawo ba? Abdulrahman ya wani ɓata rai danjin an anbaci lubna yace toh koma dai menene babu inda matata zataje ke kuma da kikawo shi sai ki ansa ki komar dashi, yana gama faɗar haka ya fice waje, umar ma ya take masa baya.
""Cike da jin kunya da kuma haushin karan banin datayi ta kalli Amatu, zatayi magana ta katseta tace karki wani damu kanki danya faɗi haka anjima zan lallashe shi kuma zai bari muje kinji ko?cike dajin daɗi samha ta amsa da toh, Amatu kuwa tadai faɗa ne dan ita bata ko taɓa ganin lubnan bama hasalima a bakin samha taji labarin lubna, sedai haryau samha bata faɗa mata cewar ai lubna tayi son Abdulrahman ba...
Readers wai ina labarin lubna????uhhhhh ku biyoni dan jin labarinta
Lashminzy cehhhh
[3/15, 5:47 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا ۚ وَاذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ أَعْدَاءً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ إِخْوَانًا وَكُنْتُمْ عَلَىٰ شَفَا حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
And hold firmly to the rope of Allah all together and do not become divided. And remember the favor of Allah upon you - when you were enemies and He brought your hearts together and you became, by His favor, brothers. And you were on the edge of a pit of the Fire, and He saved you from it. Thus does Allah make clear to you His verses that you may be guided.
Juma'at mubarak
Page 93-94
"Lubna tun lokacin dataso zubawa Abdulrahman magani su mummy suka kamata, tun daga ranar ta shiga damuwa da kuma
danasanin abunda ta aikata, kwanan ta biyu a gidan su khadeejah inda ta bata shawarar taje ta nemi yafiyar mummy da kuma mahaifiyar ta dake fushi da ita, sedai me daƙyar taje ta nemi yafiyar mummy dan tsananin jin kunyarta data dabaibaye ta bisa ga abunda ta aikata. "ummanta dake ita kuma mai zafin kai ce ƙin haƙura tayi saida lubna ta sanarwa mummy halin da ake ciki, mummy ta kira umma tayi ta mata faɗa akan bai dace tana gaba da ƴarta ba, kuma tunda ta nuna nadamarta ai ya kamata ta yafe mata, sannan umma ta janye fushin da tayi ta ita sukaci gaba da zaman su kamar yadda suka saba.
"Bayan wani lokaci da faruwar haka can wani ɗan uwansu wanda ake kira da jafar yazo neman auran ta daman tunda daɗewa yake sonta sedai rashin ganin fuska yasa yaɗan janye bawai dan ya haƙura ba, tunda yaji labarin ta dawo kano ya fara bibiyar ta kamar yadda a da yake bibiyarta tun kafin ta koma Abuja. Wata rana ran juma'a yazo gidan su, sedai bai nuna wurinta yazo ba, cewa yayi wurin umma yazo ya gaisheta.
Bayan sun gaisa da umma yake tambayar ina lubna take, dake tun a da tana jin ɗan jita-jitar cewa wai yana son lubna, sedai ita bata yadda ba dan bataga wata alama ba a tattare dashi ba, amma a wannan karon ta gasgata dan cikin satin nan kusan kullum sai yazo kuma tambayar shi ɗaya ina lubna, "haka umma zataje ta kirawo mashi lubna wanda a ƙalla suna kwashe tsawon awa biyu suna hira duk da bawani surutu take ba, shi kaɗai yake ƙiɗinsa da rawarsa
harya gaji ya wuce.
"Shi kuma shurun nata sam baya damunsa, burinsa kawai ta bashi dama, dan yasan idan harya kai ga mallakarta a matsayin mata toh pah an wuce wurin dan acewar shi sai ya saita ta kuma ya sanya mata sonshi a zuciyarta. Haka kullum yake jawo ƙafa kamar wani marasa aiki, yazo yayi ta mata surutu wanda a yanzu ta ɗan fara sabawa dan inyayi magana tana bashi amsa ba kamar da da in yayi magana take share sa ba.
""""Yau ta kama juma'a babbar rana, ranar da jafar bazai taɓa mantawa ba a rayuwar shi domin kuwa yau ne lubna ta furta cewar tana sonshi kuma ta amince zata aure shi, saboda ta lura yana tsanin sonta ga kuma shawarwarin da khadija ke bata akan ta amince dan mace lokacinta kaɗan ne da zarar wannan lokacin ya wuce ko mashinshini ɗaya bazata samu ba.
"Aiko data sanar ma jafar bakin shi sam yaƙi rufuwa saboda murna, bada daɗewa ba ya sanar ma ƴan gidansu, "dake abu na gida ne kuma duk danginsu sun san halinshi yaro ne mai nutsatse mai hankali da tarbiya domin kuwa yayi gado a wurin mahaifin shi da mahaifiyar sa domin mahaifin shi malami ne, "mahaifiyar sa ma haka, malama ce sabida tana koyarwa a wani makarantar islamiya dake anguwar su wanda tun tasowar shi yasan makarantar dan shima can yayi har zuwa lokacin daya sauke al qur'ani mai girma.
Ba'a wani dauki lokaci me tsawo ba akasa ranar aure nan da wata ɗaya, "saboda a shirye suke daga su har zuwa su lubna ɗin. "Mummy taji daɗi sosai da taga invitation card ɗin lubna, haka ma samha harda ɗauka tayi zata kaiwa Amatu mummy ta hanata ashe ɗan yau da baƙin taurin kai sai da samha ta ɓoye guda ɗaya ta kaiwa Amatu.
Wannan kenan
"A ɓangaren su Amatu kuwa hira sukaci gaba dayi har kusan la'asar sai ga Abdulrahman da umar sun dawo dan tunda suka fita basu dawo ba sai yanzu. "ko zama umar beyi ba yacewa samha su wuce wacce ke bayan Amatu sai wani noƙe-noƙe takeyi a ɓoye gudun kar Abdulrahman ya ganta dan kar tasan kar. "Amatu dake gabanta dan samha na bayanta tana leƙo umar tana mashi gwalo wai anan zata kwana cikin yin ƙasa-ƙasa da murya yadda babu wanda zai iya jiyota sai shi da hankalinshi ke kanta kuma yake kallon saitun bakinta yake gane abunda take faɗa.
"Aikuwa yace mata zai faɗawa ya Abdulrahman idan batazo sun wuce ba, "sai gata ta fito daga bayan Amatu duk ranta ɓace, haka sukayi musu sallama suka wuce. "Umar sai dariya yake ta mata a hanya. Bayan sun tafi ne Amatu ke tambayar shi wacece lubna wai? Dan duk lokacin da samha tazo gidan sai tayi ta bata labarin lubna, "Abdulrahman yace lubna ƴar'uwar mummyn su ce kuma tayi zama a gidan su samha ne, so sun matuƙar shaƙu da juns sai kuma ta koma garinsu, kuma... Da kamar zaice mata ai tayi son Abdulrahman sai kuma ya fasa kawai dan nashi ra'ayin.
Wata hirar ya ɗauko musu, sukaci gaba dayi, inda Amatu ke faɗa masa ai gobe tanason taje saloon ɗinta taga yadda abubuwa ke tafiya danta kwan biyu bataje ba, sai yace mata ta bari jibi zai kaita saboda gobe tun ƙarfe bakwai zaije asibiti (a zahiri school zashi saboda gobe yana da classes ɗinda zai ɗauka da yawa) kuma sai yamma zai dawo😃 kuji Abdulrahman da rainin wayo, hmmmm kashinka ya kusan bushewa wollah😏
Dukda bataso ba amma haka ta amince masa dan tasan dama da wuya yabarta ta tafi ita kaɗai, dan ko sau ɗaya bata taɓa fita ita kaɗai ba sai tare dashi ko dasu Ameerah, wanda ba kasafai haka ke faruwa ba.
*********
Abdulraheem kuwa ikon Allah ne kawai ya dawo dashi gida lafiya dan yadda yake driving kamar wani mashayin giya, bayan ya iso gida motar ma daƙyar ya iya paka ta ya fito ya nupi part ɗinsu, da shigar shi direct ɗaki ya wuce dan baiko tsaya kalle-kalle ba bare harya san da mutum a wurin. "Yana shiga ɗakinshi ya yasa key ya rufe dan a halin da yake ciki sam bayason damuwa, "Ameerah dake palour tun jin ƙarar motar shi yasa ta fito palour da niyar ta bashi tsoro irin na wasan nan sedai kuma yanayin data ganshi yasa ta fasa.
"Tsayawa kawai tayi tana kallon shi harya haura sama zuwa ɗakin shi inda take biye dashi a baya sai kafin takai ga isa ɗakin harya rufe ta bam, dan haka kawai ta shige ɗakinta cike da damuwa dan kwana biyun nan ta rasa gane kan mijin nata, gashi bata da halin ta tambaye shi sai inya huce yahau yi mata ƙarya yana cewa aiki ne sukayi mashi yawa wanda sarai tasan ba haka bane akwai abunda yake ɓoye mata shiyasa ta ƙudurtawa ranta cewar sai tayi bincike ta gano abunda yake damunsa har yake ɓoye mata.
Nace anya kuwa ameerah?? Karfa kije garin bincike ki ganowa eyes ɗinki abunda sukafi ƙarfinshi😎
Toilet ya faɗa ya watsa ruwa wanda yakai kusan minti talatin a cikin kafin ya fito, daidai da wayar shi na ringing, sedai damuwar da yake ciki ya hanashi ɗaukar wayar dan bayajin zai iya koda gaisawa da wani balle harya kai gayin hira, shiyasa da shigowar shi ya rufe ƙofar dan bayason Ameerah taga halin da yake ciki tayi ta tambayar shi ko lafiya dan bayason ya huce haushin akanta.
Zama yayi saman gado bayan ya sanya jallabiyar sa yayi tagumi duk ya rasa abunda keyi masa daɗi, yanzu me zai faɗawa abba?? yana ta ƴan saƙe-saƙe, Sedai duk wannan tunanin da yake tayi wayar shi na nan na ringing, "tsuki yaja ya miƙa hannu ya ɗauki wayar da niyar kashewa sai kawai yaga............
Manage with dis, cus am not feeling fyn
Pray for me plzzzz
[3/15, 4:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
My fans plsss kuyi hƙr da rashin jina da kukayi na kwana biyu, wlh banda lfy ne amma yanzu nasamu sauƙi insha Allah zaku dinga jina akai-akai, plsss ku tayani da addu'a
One love ❤
Page 95-96
"Sai kawai yaga daddy ne ke kiranshi, aikuwa da sauri ya ɗauki wayar ya ƙara a kunnenshi, daga can ɓangaren daddy yace ɗana Abdul fushi kakeyi dani saboda na tafi na barka cikin wani yanayi ko?? Kayi haƙuri a lokacin raina ne ya ɓaci saboda abunda abbanka yayi mun "dan a rayuwata ban taɓa tunanin cewar abbanka zai aikata mun irin wannan ɗanyan aiki ba, amma yanxu babu komai ka kwantar da hankalinka komai ya wuce, kuma insha Allah wannan ya zama sirri tsakanin nida kai da abbanka da kuma Amatullahi danko mahaifiyarta bazan faɗa mata ba.
"Kamar irin an watsa wa mutum ruwa mai ƙanƙara haka Abdul yake jin wani irin sanyi na ratsa zuciyar shi, "rasa ma ta ina zai fara godewa daddy yayi dan ba ƙaramin halacci yayi musu ba. Godiya ya shiga yi mashi marasa adadi. Daddy ya ƙara da cewa basai yaje wurin abban ba, shi dakanshi zaije ya sameshi suyi magana cikin lumana. Abdul yace toh. "Bayan sun gama wayar ya miƙe da sauri haɗe da naushin tafin hannunshi da ɗayan hannun nashi yace yeahhh Allah na gode maka da kasa mutumin na ya fahimce mu, Allah ya saka mashi da gidan aljannah.
Cike da murna ya koma bakin gadon ya zauna yana cewa tau an gama da wannan babin saura next part. "Murmushi ya saki wanda bansan ma'anar shi ba kan ya tashi ya fita daga ɗakin ya shuga ɗakin Ameerah, lokacin tana sallar magariba, fita yayi ya ɗauro alawla ya wuce masallaci, wanda bashi ya dawo ba sai da akayi isha'i dan sai daya tsaya nafilfili sannan ya dawo gida.
A palour ya tarar da ita, tana zaune kan two seater tana kallo, da ganin shi tayi saurin tashi ta isa gareshi, dan yanzu taga yanayin shi ya sauya izuwa na farinciki. Murmushi tayi mashi tace sweet Abdul ɗina ya aikin yau? Murmushi yayi mata shima yace aiki zaki tambaya ba lafiyar jikina ba? Ɗan narkewa tayi haɗe da tsuke baki tace toh bana ganka ba kuma lafiyar ka ƙalau, kuma, kuma ɗazu ina ta maka magana ka shige ɗaki ka barni harda sa makulli ka rufeeeee...sai kawai ta fashe da kuka, da sauri ya ƙaraso kusa da ita ya ɗauketa sai bedroom ɗinshi ya direta, kan ya share mata hawaye yace sorry my meerah wallahi abubuwa ne sukayi mun yawa shiyasa amma yanzu an wuce wurin ki kwantar da hankalinki insha Allah hakan bazata taɓa faruwa ba kinji, ya faɗa gami da manna mata kiss a goshi.
Murmushi tayi na jindaɗi sannan tace tana zuwa, bada jimawa ba sai gata ta dawo ɗauke da tray, ajiyewa tayi tazo kusa dashi taja hannun shi ya sauko ƙasa ya zauna, suna fuskantar juna, bismillah sukayi a tare sannan suka fara cin haɗaɗɗiyar jollop ɗin shinkafar da taji haɗi sosai, sai santi yake yana ɗauko hirarraki kala da kala yana bata.
Bayan kwana biyu
"Ya Abdul jiya nayi mafarkin wai na haihu kuma yaron dana haifa yana mugun kama dakai, Amatu ta faɗa tana murmushi, shima murmushin ya sakar mata wanda har seda haƙoransa suka bayyana yace tau Allah ya nuna mana wannan rana, "Amatu ta amsa da ameen, haɗe da tambayar shi yaushe zai kaita saloon ɗin, dan haryau bai kaita ba kuma yaƙi bari taje ita kaɗai.
Cikin sigar lallashi dan yanzu idan ya faɗi wani abun tana iya kwaɓe masa yama rasa ta ina zai fara lallashinta, "yace baby karki damu insha Allah yau zamuje amma sai Abdul ya dawo mun tattauna akan maganar da nace miki zamuyi ta yau. "Cike da jin daɗi ta rungume shi haɗe da manna masa kiss a goshi tace kuma daga nan zamu biya gidan aunty hajaru ko? Ya bata amsa kai tsaye.
"Suna cikin hakan ne sai ga Abdulraheem ya shigo tare da Ameerah, gaishe da junan su sukayi kan suka samu wuri suka zauna, Abdul da zolaya yace ango na amarya kullum kana maƙale da ita kamar cingum. "kafin Abdulrahman yace wani abu ameerah ta katse shi tace Allah kuwa kamar ka sani, ai ina ganin duk ranar da aka waye gari babu ita akwai babbar matsa.......Amatu tayi wuf ta karɓe zancen da cewa hmmmm ai shi da sauƙi nikam idan na wayi gari babu shi ai nima biyar shi zanyi, in yaso ma haɗe a can. "Murmushi ameerah tayi tace kedai bari muma rufe wannan babin dan ba babi bane najin daɗi
Hmmm wallahi kam Amatu ta faɗa.
"Shuru dukan su sukayi na ƴan mintuna kowa da abunda yake saƙawa, Abdulrahman kam gabaɗata hankalin shi ya fara tashi dan tsoron abunda zai biyo baya yakeji, Abdul ma haka sedai zuciyar shi na raya mashi cewar kamar bazata damu ba zata ɗauki hakan a matsayin ƙaddara ne. "Ameerah kuma tunaninta ɗaya yadda Amatu zataga kamar cin amanarta tayi ta aure wanda takeso. Amatu kuwa sumul take jinta ta kasa kunne tana sauraro taji abunda zasu faɗi.
"""A hankali cikin sanyin murya me kashe jiki ya fara magana yace Amatullahi, "yadda ya kira sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara yasa tayi saurin ɗagowa ta kalleshi sai kuma ta kawar da kanta dan yadda gabaɗaya taji kwarjininsa ya lulluɓeta. Shuru tayi bata amsa ba sai a karo na biyu ya ƙara kiranta kafin tasamu damar amsa shi, "ɗan jimmm kaɗan yayi cikin ƴan sakanni ya kalli Abdulrahman da har zuciyarshi ta fara karaya ga kuma Ameerah duk yanayinta ya sauya. Amatu ma haka duk ji tayi jikinta ya matu dan yadda taga suma cikin ƙanƙanin lokaci yanayin su ya sauya shiyasa ma ta mayar da hankalinta kan abunda zasu faɗa mata dan har zuciyarta ta fara raya mata cewar ko rasuwa akayi ne.
"Kallonta Abdulraheem yayi yace Amatullahi... Sai kuma yayi shuru, sai Ameerah ta taɓa shi da ƙafarta alamar yaci gaba da magana sannan ya ɗora da cewa a rayuwa duk wani abu da mutum zai aikata a rubuce yake, "duk wani ƙaddara mekyau ko mara kyau dazata samu mutum toh daman a rubuce yake, kuma duniya kamar makaranta ce, idan ka kwantar da hankalinka ka karance ta ka zauna lafiya idan kuma kasa gardama kaga saɓanin haka. "A rayuwa ana son mutum ya kasance mai haƙuri. "Ko cutar ka akayi ka haƙura ka nuna bakomai bane insha Allah wata rana zakaci ribar wannan haƙurin...
""Ya ɗan taƙaita anan. Amatu kam gabaɗaya ta sale dajin irin kalaman da Abdul ke faɗi wanda ta kasa gane ainihin inda maganar tashi ta dosa. Abdulrahman kam shuru yayi ya duƙar da kanshi ƙasa dan ko kallon amatu baya iyayi saboda sabuwar kunyarta data lulluɓeshi lokaci guda. A karo na biyu, Abdul ya sake kiran amatu wanda a yanzu ta gaza amsa shi. Cigaba da maganar shi yai yace da ace mutum yana da ikon komawa baya ya gyara duk wani kuskure nashi da mun gyara. Murmushi ya saki wanda a iya leɓon shi kawai suka tsaya yace Allah sarki ammie sai datace kar muyi haka mu zauna mu fahimci juna kafin mu aikata amma muka bujire mata, yanzu ga sakamakon bujire matan da mukayi..
""Cikn ƙarfi hali amatu tace wai dan Allah meya faru ne haka ku taimaka ku faɗa mun hankalina ya kwanta, kodai wani ne