Chapter 15 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 27

42K to 45K   out of 79.1K words

take motsawa a hankali.

Kafin "yace kullum ina zuwa wurin Amatullahi amma yau ba wurinta nazo ba wurinki nazo. "Waro ido tayi cike da mamaki gami da pointing d'in kanta tana son tayi magana ya katse ta "yace karkiyi mamakin ganina saboda a halin yanzu ba Amatu ce a gabana ba kece a gabana.

"Idonta taf da kwalla dan gani take kamar mafarki take ba gaskiya bane, cikin son ta gasgata kanta tace Abdul kaine kuwa? Kaine abdul d'in amatu??

"Murmushi yayi mai sauti ganin yadda ta rud'e "yace ameerah ki saurareni kiji abunda zan fad'a maki. Yi tayi kamar bata jishi ba ta juya zata koma cikin gida dan gani take kamar ba cikin hayyacin shi yake ba.

"Cikin izza yace ameerah!! Cak ta tsaya tana jin wani zafi a zuciyar ta dan ta matsu bai wuce ba saboda ita duk wani abu dazai had'a ta dashi ba sonshi take ba saboda had'uwa dashi tamkar an fama mata wani ciwo ne.

"Tsaye tayi ta kasa juyowa sai hawayen dake bin k'uncinta, shi kuma ganin bata da alamun dawowa yasa ya taka har zuwa inda take ya tsaya a gabanta yana kallonta yace share hawayen ki kiji abunda zan fad'a maki.

Da sauri tasa gyalenta zata share, yayi saurin dakatar da ita had'e da zaro handkerchief daga cikin aljihun rigan shi ya mika mata. K'in karb'a tai cikin wasa "yace toh idan baki ansa ba zan share maki da kaina.

Da sauri ta ansa ta share hawayenta ta mika mashi, sai ya girgiza kai alamar ta barshi kawai. K'ura mata ido yayi na yan mintuna ayayin da ita kuma ta rusunar da kanta kasa dan bazata iya jure irin kallon da yake mata ba.

A hankali cikin sweet voice dinshi "yace nasan kinsan abunda ke faruwa tsakani na da d'an uwana da Kuma Amatu ko?? Ameera ta amsa da eh, can yayi nisa "yace toh a halin da ake ciki yanzu nabar wa Abdulrahman Amatullahi.

"Da karfi tace me kace?? Ya bata amsa yace abunda kunnenki ya jiye maki. Sannan yace karki damu kanki fa saboda ko Amatu batasan Abdulrahman zata aura ba kuma ni nace kar a fad'a mata sai bayan aure, saboda banason a samu matsala.

"Kuma kinfi kowa sanin yadda take wulakanta d'an uwana, alhalin shi yana masifar sonta, ta dalilin sonta komai yana iya faruwa dashi, shiyasa na hakura da ita.

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tace yanzu shikenan Abdulrahman shi zai auri Amatu amtsayin kai?? Yace eh sai tace Abdul yanzu kana ganin an mata adalci kenan??

Abdul "yace meyasa kike fad'an haka bakiga halin da d'an uwana zai shiga bane? Ameerah meyasa d'an uwan zai nemi abun ya rasa al halin ina dashi?? Meyasa zan kasance cikin farinciki al halin d'an uwana yana cikin k'unci??

Ameerah kina ganin iyayen mu zasuyi farinciki da aure na nida Amatullahi bayan sunsan cewa akanta d'an uwana yake fama da ciwon da a kowane lokaci zai iya    tashi?? Hmmm na sadaukar da soyayyar amatu ne saboda farincikin shi da kuma samun zaman lafiya a tsakanin mu.

"Iska ya fesar me zafi sannan ya kalli ameerah dake cikin tension yace plsss ameerah karki fad'a mata komai kinji ko? Ta amsa da toh.

Juyawa yayi ya nupi inda motar shi take sai ya hangi hasken mota ta fito daga gidan su Amatullahi, murmushi yayi dan yasan ko waye, sai ya kira ameerah da tazo ta gani. Tana zuwa motar na wucewa. Murmushi ne ya subuce mata. Dan ganin rainin wayon da akayi wa amatu.

Ledar da yazo da ita ya d'auko zai mika mata, tace a'a, cikin d'aure mata fuska yace shikenan tunda ba'a yadda dani ba zan wuce, ya juwa zai shiga motar shi. "Da sauri tasha gaban shi ta karbi ledar, murmushi yayi "yace ko kefa, itama murmushin ta mayar mashi. Sai yace mata zai tafi kar ace tayi dare, nan sukayi sallama ya wuce.

"Yana wucewa ameerah ta saki murmushi tana mai jindadin hirar da sukayi. Cikin gida ta wuce lokacin aunty hajara na dakin mijinta, itama d'akinta ta shige ta fad'a saman gado had'e da d'aura handkerchief d'in daya bata bisa kirjinta, "tana mai shaqar kamshin shi  tana wani lumshe ido. Ta rasa dalilin da yasa takejin wani dad'i a zuciyar ta.

"Sai ajiyar zuciya take ta saki tana murmushi, mikewa tayi ta rage kayan dake jikinta sannan ta d'auko ledar daya kawo mata ta bud'e. "Waro ido tayi ta fara firfito dasu tana dariya kamar wata zautacciya. Wani had'adden akwati ne d'an karami me d'auke da zobe me shegen kyau. Da kuma kayan maku lashe.

Fito da zoben tayi ta lak'a a yatsar ta me bima manunin ta taga ya zauna cif, yayi mata kyau. Zare shi tayi tana jujjuya shi a hannunta tace toh me wannan yake nupi?? Hmmm nasan dai wannan zoben ba banza ba. Kodai mafarki na ne zai zama gaskiya? Uhmmm da nafi kowa farinciki.

"Mayar da zoben tayi cikin akwatin shi dan cewa tayi baza tayi gaggawar sawa ba, wani chocolate ta gani me shape d'in heart sai taji ya burgeta, d'aya ta d'auka sannan ta mayar da sauran cikin leda ta ajiye can kasa a gefen gadonta, kafin ta dawo saman gadonta ta kwanta tana shan chocolate d'in cikin jindadi.

Haka bacci ya sace ta kwance cikin farincikin dan rabon data kasance a haka an dad'e.

B'angaren Abdul shima yana cikin farinciki, "dukda bai fad'a mata asalin abunda ya kawo shi ba amma yaga alamar nasara a tattare da ita".


       Washe gari
Tunda safe ameerah taje gidan su amatu, lokacin "amatu na bacci amma haka ta tashe ta ta fara bata labarin abunda ke faruwa, sedai bata ce mata Abdulraheem bane, cewa tayi Abdulrahman ne.

Cikin zolaya amatu "tace hmmm kice kin shigo layin mu kenan? Ameerah tace babu wani ai baice yana sona ba kawai yacewa yayi yazo gaishe ni. Dariya Amatu tayi tace toh ai daga gaisuwa ake farawa kuma tunda kikaga ya tako kafa yazo wajenki to ba banza ba kawai ki saurari jin Kalmar so daga bakin shi.

"Kuma shawara ta shine kawai ki amince dashi mu zauna a inuwa d'aya dake. Ameerah tace lallai Amatu waton bama in duba halayyar shi inga ko tayi mun ba zaki wani ce in amince babu koda Jan aji??

Amatu ta harare ta tace ohh Jan aji?? Hmmmmm bari kije garin jan aji ki rasa shi. Ameera tace gaskiya ne fah, nima na d'an fara pola mashi amma bazan nuna mashi hakan ba har sai ya furta mun da bakin shi. Amatu tace yes kina kawo light Allah ya sanya alkhairi.

Ameera tayi murmushi had'e da barin dakin ta wuce gida. Wanka taje tayi ta shirya tazo ta sami Amatu lokacin itama ta shirya suka wuce saloon..

Bayan sati uku






Plsss ayi hakuri da wannan
[2/25, 9:03 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

 
       Page 65-66

Bayan sati uku,
Abdulraheem ne tare da ameera suna hira, dan yanzu sun fahimci juna da ita, har gidan su an sani, kullum suna mak'ale da juna kamar yadda amatu da Abdulrahman suke.

Yau asabar, kuma abdul yana hutu baije asibiti ba kuma kusan kwana uku baisa ameerah a idonshi ba, shiyasa yau ya shirya ya nupi gidan su. Bayan yaje ne ya kirata sai gata ta fito. Tun daga nesa ya fara aika mata da sakon daya saba, waton kallonta. Haka yaci gaba da kallonta har ta karaso wurin shi bai sani ba. Sai data huro mashi iskan bakinta a fuskar shi.

Firgigit, ya dawo daga duniyar daya shiga yana mai sakar mata lallausan murmushin shi. Yace sweetheart yawo nazo muje. Ita kuma cikin shagwaba tace nikam ba inda zani, duba fa kaga kwanan ka nawa bakazo wuri na ba??

Cikin marairaicewa yace haba my sweet ameerah ayi mun hakuri kinji plsss ya karasa fad'a tare da kama kunnuwan shi. Murmushi tayi ganin yadda ya kama kunnuwan shi tace owk na hakura amma ba bazan je yawo ba.

Nan ma ya sake bata hakuri yana rokonta kafin ya amince tace bari taje ta sanar da aunty hajara. Babu jimawa sai gata ta dawo. Nan ya bude mata gaban mota ta shiga sannan ya zagayo ta b'angaren direba ya zauna.

Bayan ya shiga ne har sun fara tafiya tace sweet Abdul ina zamuje ne?? Yana kallon waje ta gefen windon shi yace zanje in sayar dake ne. Sai data kyalkyace da dariya mai isarta sannan tace sweet Abdul ai ko a mafarki kaga wani zai sayar dani bazaka bari ba ballantana kai da kanka ko??

D'an yatsine fuska yayi had'e da cewa inji waya fad'a maki?? Bata rai tayi ta banka mashi harara had'e murgud'a mashi baki ta juya kanta ta gefen window tana cewa Allah sai na fad'awa ammie.

Kallon d'an karamin bakinta yayi wanda a duk lokacin da take shagwaba yake burge sa yayi nuni da kanshi yace ni kikei murgud'awa baki ko, qyatt Allah nayi kusan maganin bakin nan mai tsiwa da murgud'e murgud'e.

Ita kuma ko kallon shi batayi ba taci gaba da lekenta ta window har suka iso "A CLASS PARK".
Kud'in gate pass ya biya musu kafin suka nupi wurin parking ya paka motar sannan ya fito. Ita kuma sarauniya tana ciki tana jiran sai yazo ya fitar da ita saboda tsabar Jan aji irin nata.

Shi kuma ko a jikinshi ya nupi inda take ya bude mata ta fito tana wani shan toka, wai a dole fushi take dashi akan maganar dazu. Murmushi yayi ya dawo gefenta yadda zasu samu damar tafiya tare, yana kallonta yana murmushi dan yadda take wani shan kanshi ma dariya take basa.

Haka suka jera suna tafiya gwanin sha'awa sedai babu mai magana cikin su. Tsayawa Abdul yayi dan ya gaji da shurun nata yace sweet ameerah plsss kiyi magana mana, ai Kinsan wasa nake maki ko? Ta wani kawar da kai gefe, yace Allah idan bakiyi mun magana ba zan kurma maki ihu a wurin nan. Waro ido tayi tace a'a yi hakuri ka rufamin asiri.

Yaso yayi dariya gudun kar asake komawa gidan jiya, yace toh, sannan suka fara hirar su na soyayya, ameerah sai kalle-kalle take, duk wani abu data gani wanda ya burgeta sai tayi magana a kanshi, ko kuma tace sai sunje ta gani. Haka sukayi ta zagaye a park d'in dan akwai shi da girma sosai kuma akwai kayan burgewa wanda zai sa ko baka cikin jindadi kaji shi.

Wurin da ake sayar da ice-cream suka nupa, nan suka zauna saman kujerun dake wurin suna fuskantar juna yasa a kawo musu kayan mota baki. Babu bata lokaci sai gashi an kawo musu ice cream da pizza. Nan ta fara sha shi kuma sai kallonta kawai yake yana jin ina ma ace shike bata da kanshi.

Ita kuma ko a jikinta dan ta mayar da hankalinta kan ice cream saboda ba karamin sonshi take ba. Bayan ta gama sha ne ta dubi robar shi taga ko alamun fara sha ba'ayi ba tace sweet Abdul ya baka sha ba? Sai yace a'a bana shan abu mai sanyi sosai. Mak'e kafad'a tayi irin ko ohon nan tajawo nashi zata sha, daidai shima yasa hannun shi zai d'auka.

Wani irin yarrrrrrrr, sukaji a lokaci d'aya kuma a tare sukayi saurin janye hannuwan su suna kallon cikin kwayar idon junan su.  Ameerah ce ta fara kawar da kanta, cikin jin kunya ta rusunar da kanta kasa. Shima cikin jin kunya yace shida yace bazai sha ba kuma miye na d'auka, ya fad'a a cikin zuciyar shi?? Sai kawai ya tura mata gabanta yace gashi.

Kallon junan su sukayi yayi mata sigina da girar shi a kan tasha, wani iri taji sai duk taji yama fita a ranta.  Sai tace su wuce gida ta gaji. Batare daya tambayi dalili ba yace su tafi, nan ta d'auki handbag d'inta ta rataya kafin suka jera a tare suna tafiya. Sun kawo wurin da sukayi parking kenan Abdul yaga motar Abdulrahman sedai bai gasgata ba sai daya hango shi tafe shi da Amatullahi.

Cike da mamaki kallonsu yake kamar yadda suma da suke nesa suka hango shi. Cike da zumudi Amatu tafara sauri har tana d'an had'awa da gudu dan tayi saurin zuwa wurin da ameerah ke tsaye ta basu baya tana waya.

Gama wayarta kenan ta juya cikin rashin sani wani mai mota da yazo da baya saura kad'an bugeta, Amatu data hango haka ta  kurma ihu, Abdul kuma dake can hankalin shi ya d'auke yana kallon Abdulrahman dake watso mashi hararan da besan ko na menene ba. Yayi saurin juyawa yaga saura kad'an motar ta buge ameera, da hanzarin shi yasa duka hannuwanshi biyu ya rikota kamar wata yar baby.

Mai motar a tsorace ya fito dan ya aza koya bugeta ne. Hakuri ya fara basu akan bai lura da ita ba. Amatu kuwa har hanjin cikin ta sun kad'a.

Abdul kuwa sai b'ab'atu yake tayi yana zagin shi wai da gangan ne, hhhhh kuji fa shirmen Abdulraheem. Abdulrahman yazo ya bashi hakuri yacewa mai motar yayi tafiyar sa. Bayan mai motar ya tafi ne Abdulrahman ya kalli ameerah datayi lamo a jikin Abdul tana faman haki kamar wacce tayi gudu.

Abdulrahman yana dariya yace dalla malam cika ta, sai a sannan ya lura da rungume ta dayayi, yayi saurin sakinta, cikin jin kunyar su ameerah ta sunnar dakai kasa, shi kuma ko damuwa baiyi ba.

Amatullahi ta karaso wurinta tana mata barka. Daga nan suka fara hira, Abdul yace subari har su koma gida saci gaba. Nan kowannensu ya d'auki tashi suka wuce, daman suma gidan zasu wuce.



      Bayan wani lokaci
Abubuwa da dama sun faru, ciki harda sa ranar auren su amatu da ameerah dan yanzu komai ya zama normal, iyayen ameerah sun amince data auri Abdulraheem, sai aka had'e bikin nasu lokaci daya. Amatullahi da ameerah sun samu admission a BASE UNIVERSITY sedai basu fara zuwa ba sai bayan auren su dan wani sati za'ayi bikin su.

Yanzu haka duk gidajen nasu shirye-shirye kawai suke tayi, su amatu kamar wancan karon mummy ta d'auko me gyara na musamman dan a gyara amatu da ameera. Aunty hajara kam itama daginta dake kaduna wasun su sun fara zuwa.

Su Abdulraheem kuma suma shirye-shiryen sukeyi, kamar yadda mummy itama ba'a barta a baya ba, dan itama shiri na musamman takeyi.

Yau ta kama.......








Plsss share
[2/26, 8:46 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Wannan shafin nakune yan rudani fans grp 1&2 da beauty novels grp

        Page 67-68
Yau ta kama laraba yau ake mother's day, ko'ina na gidan cike yake da mutane, "duk inda ka kutsa mutane ne a wurin. "Palon mummy na shiga, nan ma cike yake da mutane, gaishe da mutanen nayi kafin na kutsa dakin amarya, dan ita nakeson gani.

Dak'yar na samu na shiga cikin d'akin, can karshen gado na hango amarya Amatullahi, fuskar nan tata sai sheqi takeyi, " sedai babu wata kwalliya a fuskarta, "da alama dai sai lokacin mother's day yayi za'ayi mata kwalliya.

"Nan na samu wuri na zauna, ina jiran lokaci yayi, dan alkawari na d'auka sai na kawo wa Rudani fans GRP rahoto. "Ina nan zaune aka kawo mun abinci mai  rai da lafiya, sai danaci iya ci na kafin nayi gyashi na godewa Allah daya kawo ci da sha.

"Bayan awa biyu akayi waje dani saboda za'a shirya amarya. Raina baiso ba amma haka na fita, da biro na da littafi na. Bayan awa biyu sai aka bud'e kofar, da sauri na shige gudun kar a rufe kofar.

"Ko dana shiga baki sake nake kallon amarya, "tasha make-up mekyau, sedai kalar ta bata canza ba, "dana dubi kayan dake jikinta sai dana rufe ido na kara bud'esu dan in tantance kowane kala ne, sanye take da riga da skirt, shiba pink ba, kuma shiba purple ba, a takaice dai bansan kalar kayan ba.  idan baka lura da kayan nata ba zaka d'auka ko gown ce.

Bayan an gama mata wanka da turare, "aka fito da ita waje, nan uwayen amarya suka bi layi suma sunsha anko, har cikin farfajiyar gidansu aka kaita. Inda shima yasha decoration d'in da sai ka rantse ba gida bane.

Wani d'an kujera me kamar ta sarauniya, aka ajeta akai, lokacin har an kawo ameera, itama kalar kayan da amatullahi tasa akasa mata sedai kowa da kalar gyalen shi da purse. "Sun wanku sosai kuma daka fuskar su kasan suna cikin farinciki. "daga gefensu kuma uwaye ne kowacce da nata kalar wankan, amma anko suka dukansu harda uwayen ameera. Masu DJ kuwa duk sun hallara a wurin, uwar amarya tana cikin gida itama ana shiryata.

Bayan kowa ya zauna ne aka fara jawabi, "bayan an gama aka kunna DJ, toh fah nan gidan ya dau wani irin duma wanda tun daga nesa zaka san ana wani abu a gidan. DJ ne ya umarci uwaye da su fito su nuna tasu farincikin, tunda dansu akayi taron. Nan kowacce ta fito da nata irin rangwadar suka sa amare a tsakiya suna zagaye su had'e dayi masu liki.

   "Su amare na tsaka suma suna d'an takawa kad'an, Bayan sun gama cashewa ne aka nemi uwayen amare dasu fito, dakyar mummy ta fito wai kunya takeji, ameerah kuma kanwar mahaifiyarta ce ta maye gurbin ta dan fur taki shiga, kai tunda taji ana neman uwayen amarya ta sulale ta wuce.

Nan mummy da aunty uwani suka fito suda su amare suna rawa suna liki, gabadaya gidan aka d'auki tafi dan ba karamin burgewa sukayi ba musamman aunty uwani data saki jiki tana rawa tana liki. DJ sai kara musu duma da katon kai yake su kuma suna dansewa.

Haka akayi ta cashewa, daga baya kuwa kowa ya shiga ana nuna farincikin, nima na kutsa cikin mutane ina rawa, sedai banda kudin liki, sai kawai na fara yanka littafi na ina liki dashi 😍.sai kusan magariba sannan taron ya watse, nan kowa ta kama gabanta.





Hmmmmm bari mu leko su Abdul mu gani😎



B'angaren su Abdul yau babu wani events da sukeyi, sedai suma ana ta shirye-shirye ammie duk ta rikice, ko magana kayi mata nan zata barshi ta wuce, dan kanta ya d'au zafi. Hanan uwayen biki tana gidan su samha suna nasu shirin dan gobe zasuyi wankin ango, inda

15 / 27