Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
ba tace naji ta anshi Afrah suka shige ɗaki dan za'a sake musu wanka ne duk da cewar yamma yayi amam haka kullum ake musu wanka biyu harda Amatu.
Da misalin ƙarfe takwas na dare lokacin kowa ya watse se wasu yan dangi da ba'a rasa ba, zaune Amatu take tana ba Afrah nono sai wani cije leɓo take danjin zafin yadda afrah ta kama nonon sai zuƙa take, tana gama ba Afrah, Amrah tasa kuka itama haka ta bata sai wani yatsine fuska take Ameerah kuwa sai dariya take tana cewa ashe shayarwa da wuya mudai Allah yayi mana da sauƙi, Cikin wasa Amatu tace ba ameen ba.
Ameerah kuwa murmushu tayi tace daɗin abun dai kowa dai nason sauƙin😏 Amatu batace komai ba taci gaba da shayar da ƴan biyunta.
Bayan wata bakwai
Zaune take a palour tana wasa da Afrah fitinanniya dan Allah ya ɗauro mata rigima da koke-koke in dare yayi, dan ma yanzu tayi sauƙi amma fa bata jin magana, da an kwantar da ita zata nemi ta tashi ko wasa kake mata tayi ta maka dariya, in aka kunna tv haka zata ƙura mashi ido kamar wacce tasan ma'anar shi.
Amrah kuwa tamkar mahaifinta take dan babu ruwanta ko irin kukan nan na yara batayi kai ko wasa kake mata bata fiye dariya ba, sumi-sumi takae kamar wata mara lafiya, sau dayawa mutane kance ko bata da lafiya ne basu san haka yanayinta yake ba.
Ameerah ta haihu lafiya ƙalau dan bata daɗe tana naƙuda ba ta haihu, ta haifi ɗa namiji ansa mashi sunan abba waton ibrahim khalil suna kiranshi da khalil, fari ne tas tamkar mahaifin shi, shima anci ansha a bikin shi, kowa ya nuna farincikin shi.
"Wani ɗan abun wasa ta riƙe tana mata wasa dashi, sai tayi kamar zata bata sai kuma ta ɗaga sama, ita kuwa afrah sai washe baki take tana dariya, Abdulrahman ne ya shigo palon cikin sanɗa, ta bayan Amatu yaje daidai ta ɗaga abun wasan sama ya anshe, aikuwa cikin tsoro ta juyo.
"Tana ganinshi tayi murmushi tace shine zaka ban tsoro ko? Sorry maman ƴan biyu ya ɗafa ayayinda yake ɗaukar Afrah da tun ganin shi take mashi dariya. Zama yayi saman kujera yana mata wasa Amatu kuma ta shiga kitchen kawo mashi abinci dan daga masallaci yake kuma shi take jira ya dawo suci tare kamar yadda suka saba.
Bayan shekara goma
Su Amatu an ƙara girma an ƙara sanin abubuwa da dama game da zaman aure, yanzu haka ta gama degree ita da Ameerah suna aiki a wani sabon company da Daddyn Amatu ya buɗe na teaching techniques and computers, kampanine na ƙera computoci da kuma sarrafasu da koyar da yadda ake amfani dasu da sauran su, kampani ne babba, duk wani abu daya shafi computer anayi a wurin, kuma ko wani aiki da ɓangaren da ake yinshi.
Kullum sai sun fita saturday and sunday ne kawai ba'a zuwa, amma duk aikin da suke zuwa bai hanasu kuƙa da ƴaƴansu da mijin su ba, suna matuƙar ƙoƙari wurin basu kulawa haka ma mazajen.
*************
Wasu kyawawan ƴammata na gani guda uku da wasu maza guda biyu suna wasa a wani haɗaɗɗen garden, ƙaramin namijin mai suna Affan shine ya daki Waleedah akai saboda ta ɓata mashi motocin roban shi daya jera su yana turawa, kuka tasa ƙafin tayi daka tsalle ta cijeshi a hannun ta arce a guje.
Kuka ya farayi ya bita a baya yana wallahi sai na rama har suka shigo palon Amatu, da sauri Amatu ta tare Affan dake shirin dukan Waleedah tace yi haƙuri affan kaji ƙyaleta, yana huci yace Allah mummy sai na rama jipa inda ta cije ni harya fashe.
"Afrah tace aikuwa, ta arce sai wurin Ameerah taje ta faɗa mata, tare sukazo Tace ina waleedan take? Bana hanaki cizo ba? Allaha saina sassaɓa maki da shegen kanta kamar na ƙwallo.
Waleedah dake bayan Amatu ta laɓe ta fashe da kuka dan ance mata me kan ƙwallo😁 yarinyar Ameerah kenan wacce aka haifeta bayan shekara biyu da haihuwar khalil. Sam bata jin magana ga baƙin tsokana da tsoro shiyasa tasu tazo ɗaya ita da Afrah dan itama haka take.
"Affan kuma ɗan Amatu ne shi kuma an haifeshi bayan shekara uku da haihuwar su Amrah, shima babu ruwanshi kamar Amrah sedai akwai son wasa dan aduk al'amuranshi sai ya haɗa da wasa.
Abunda ke haɗashi da daddyn shi kenan waton Abdulrahman. Suna cikin hakane Abdulrahman ya shigo wow wai kunga yadda ya dawo kuwa? Ya ƙara kyau da girma harda ɗan gemu ya tara, fuskarshi ta ƙara faɗi da kyau, yana cewa toh sun fara ko? Su kullum cikin rigima suke, Affan ne ya ƙarasa wurinshi yana nuna mashi wurin da waleedah ta cije shi dan har wurin yayi jini, Sorry yace mashi ya ɗauko tissue ya goge mashi.
"Bayan ya goge mashi Ameerah taja hannunshi suka fice daga palon, su Afrah suka take mata baya, Amatu kuma jan hannun waleedah tayi suka zauna tana lallashinta haɗe dayi mata nasiha cikin hikima akan ta daina cizo babu kyau mutum zai shiga wuta.
Tana cikin mata nasihar ne taji motsin su Amrah tana wasa, da gudu ta tashi ta fita, murmushi kawai Amatu tayi tana girgiza kai tace yarinta kenan, matsowa kusa da ita Abdulrahman yayi yace aikema haryanzu yarinta na cinki tunda haryanzu baki barmun rigima da shagwaɓa ba, ya faɗa yana mata dariya.
Hararar sa tayi tana tashi tace kai kuma da jaraba ba itama ta faɗa tana dariya,,,,, batyi aune ba taji ya biyota yasa hannu zai riƙota harya kamo ɗankwalinta ta cire ta ruga da gudu, ya fara binta suna ta zagaye palour, dake ta ɗanyi gwaɓi gwaɓi kuma ba'a haɗa gudun namiji da mace aikuwa ya kamota ta faɗo ƙirjinshi, rungumeta yayi yana faɗi wana kama??
"Murguɗa mashi baki tayi tace kai ɗin, yace ni ɗin?Tasa hannunta tayi pointing ɗinshi tace Eh kai ɗin, aikuwa ya sungumeta sai ɗakin shi can tsakiyar gado ya kwantar da ita kafin ya koma ya rufe ƙofar.
Kan gado yaje ya sameta batare da ɓata lokaci ba ya fara aika mata da wasu manyan saƙonnin da faɗan su ɓata lokaci ne, itma biye masa tayi suna ta jiyar junan su daɗin da basa taɓa gajiya dashi.
Da gudu na fito daga ɗakin ganin abun nasu na shirin makantar dani nace ALHAMDULILLAH!!!
ALLAH YA BAMU MAZAJE NAGARI DA MATAYE NAGARI MASU ƘAUNAR MU TSAKANI DA ALLAH
ALLAH abun godiya ALLAH nagode maka daka nunamun naga farkon littafin nan lafiya kuma naga ƙarshen shi lafiya, kurakuren dake ciki Allah ka yafe mun Abun amfanuwa kuma Allah kasa Ya amfanar damu.
Taku ce lashminzy