Chapter 5 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 27

12K to 15K   out of 79.1K words

sai yaji mutumin ya bashi tausayi ace duka yaranka sunyi hatsari aiko kana cikin tashin hankali da '''rudani''' dan ma Allah ya takaita babu wanda ya rasu.

Mikewa yayi ya fara bin dakunan marasa lafiya yana duba su wasu kuma sallamar su yakeyi wasu kuma kawosu ma akeyi.

Haka ya zauna nan asibitin har kusan karfe biyu na rana gashi yau yakeson ya kai amatu wurin ammie amma ga abunda ya gitto masa. Dakin marasa lafiyan nan ya koma yaga duk sun farfado kowa sai kallon dan uwanshi yakeyi.

Sannu yayi musu ya juya zai fita sai dattijon ya dawo da kulolin abinci da kuma magungunan da aka rubuta mashi. Karba Abdul yayi yace ya basu abinci shi zaije ya rubuto yadda zasu sha maganin.

Daga nan ya fita ya koma office dinshi, wata nurse ya kira yace ta kula dasu kafin ya dawo. Amsawa da toh nurse din tayi kafin ta fita. Shima tashi yayi ya fita yana sauri ya koma gida ya shirya dan har uku ta gota.

Bude motar shi yayi zai shiga sai ga Abokin shi Usman shima likita neh acikin asibitin yake aiki. gaisawa sukayi Abdul ya fada mishi akwai wasu patients ya kula dasu kafin ya dawo.

Motar shi ya shige ya bata wuta sai gida, da Isar sa kayan jikinshi ya cire ya shiga toilet ya watsa ruwa. Daya fito gaban dressing mirror ya isa ya shafa mai ya fece gashin kanshi dayake walkiya kamar anyi barin maiπŸ˜€

Wardrobe ya bude ya fiddo wani hadadden yadi kalar navy blue da ratsin sky blue ya saka" ya saka bakin agogo da bakin takalmi sai hula mai kalar kayan abun gwanin sha'awa dan gaskiya ya hadu sosai.

Fitowa yayi ya nupi part din ammie sai zuba kamshi yakeyi kamar wani sabon ango. Haka harya karaso part din ammie lokacin tana zaune a palour tana kallo.

Tunda ta ganshi take sakar mishi murmushi dan tasan wannan wankan da wala kin. Zuwa yayi ya mata peck a goshi yace ammie ki shirya nan da 30 minutes zan dawo. Beko tsaya jin abunda zata fada ba ya fice da sauri.

Wayar shi ya dauko yayi dialing number Amatu sai data kutsan katsewa kafin ta dauka, cikin muryar ta na shagwaba tace my Abdul dazu ina ta kira baka dauka ba duk hankalina ya tashi... Katseta yayi dacewa sorry baby kinji amma ki shirya gani nan zuwa yanzu.

Ko amsawa batayi ba ya katse wayar, bayan minti goma sai gashi a farfajiyar gidan su.

Ita kuma tana can sai kyalle kyalle take tayi har mummy sai datayi mata fada akan tayi sauri ta fito dan tana daga palour tana jin wayanta na ringing kuma data leka ta window taga Abdul neh.

Fitowa tayi cikin wani dakakken leshi me tsada da daukar hankali kalar ruwan kwai da digo digon ja" sai tasa jan gele da handbag ja ta fito sosai kamar a toilet. Mummy sai kallonta takeyi tana sakar mata murmushi dan ba karya yar'ta ta hadu sosai.

Sallama tayi wa mummy kafin ta fita" tsaye ta ganshi a jikin mota ya nade hannuwan shi a kirjin shi, fuskar nan tashi kamar gonar auduga dan gaskiya yana cike da farinciki.

Kura mata ido yayi har sai data karaso gaban shi kafin ya farfado daga duniyar kallonta ya bude dayan side din yace ta shiga.

Ba musu ta shiga shima ya zagaya ya shiga ya tayar suka fita. Kallonta yayi yace Baby wallahi kin hadu kinfi kowace mace kyau. Murmushi tayi tace my Abdul ai ka fini kyau so dubu.

Hmmm baby banason zolaya fah Kinsan dai duk inda akaje kin fini kyau shiyasa nake addu'a Allah yasa yaran da zamu Haifa duk suyi kama dake.

Dariya tayi ta rufe fuskanta da gyalenta wai ala dole taji kunya. Murmushi yayi bece komai ba har suka iso gida.

'''cyprus'''
Wani hadadden matashi neh fari dogo wanda dagani bazai wuce shekaru ashirin da bakwai zuwa da takwas ba " sanye yake da kana nan kaya bakin wando da farar Riga daga gabanta an rubuta I'm cool.

Kayan shi yake shiryawa cikin trolley, da ganin yadda yake shirya kayan kasan ya matsu bebar wurin ba kenan. Bayan ya gama shiryawa ya dauki agogo fari kal yasa da bakin hula sannan ya jawo trolley dinshi ya fito.

Bodyguards dinshi dake bakin kofa sukayi saurin ansar trolley din suka nupi mota inda dayan guard din ya bude mashi gidan baya ya shiga, direct airport suka nupa inda guards din basu bar wurin ba sai da sukaga tashin shi.

Da misalin karfe biyar na yamma ya iso ainihin kasar shi ta haihuwa waton nigeria, saukowa yake daga matakalan jirgi amma sai ka rantse ba kasa yake takawa ba saboda yanayin tafiyar shi a nutse yake yinta cikin kwanciyar hankali harya sauko ya karaso wurin.................






πŸ‘‰πŸΏπŸ‘‰πŸΏπŸ‘‰πŸΏ
[2/9, 5:30 PM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŽΓ’Γ‘πŸ’₯

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Page 23-24

Karasowa yayi wurin Abokin shi ya bashi hannu suka gaisa sannan shiga mota suka wuce" Abokin shi me suna kabeer yace guy dinnan kana hutawa fah, jika kamar wani balarabe.

Tabe baki yayi yace kabeer banson iskanci fah, kai kullum baka da aikin daya wuce zolaya? Murmushi Kabeer yayi yace babu wani zolaya ai gaskiya na fada. Banza dan saurayin yayi mishi har suka iso gida.

A daidai kofar shiga Palo Kabeer ya ajiye wa saurayin trolley dinshi dan yana sauri shiyasa be shiga ba. Kwankwasa kofar yayi kafin wata kyakkyawar yarinya ta bude mashi kofar, ihu murna tasa tana kiran sauran yan uwanta.

Suma da hanzarin su sukazo suka rungume shi, daya daga cikin su me suna lubna wadda bata karaso ba cikin tsananin mamaki take kallonshi dan ita kallon gizo takeyi mishi shiyasa batayi gaggawar zuwa ta rungume shi ba.

Sai da Yar uwarta samha tazo kusa da ita tace aunty bakiga yaya Abdul bane?? Sai a sannan ta sheqo da gudu ta rungume shi tana cewa yaya abdul Kaine kuwa naga ka kara girma da kyau.

Murmushin dole ya kirkiro yayi mata danshi har yanzu haushinta yakeji " duk wani abu da zatayi danya burgeshi baya taba burgeshi sai dai ma ya bashi haushi.

Ganin taki cika shi ne sai ya janye ta daga jikinshi ya karasa wurin ammie da yanzu ta iso wurin dan jin hayaniya, zuwa yayi ya rungumeta yana murmushi.

Kallonshi tayi tace son meyasa baka fada mana yau zaka dawo ba? Dan sosa kanshi yayi yace mummy wallahi na matsu ban dawo bane kuma nayi missing dinki shiyasa nace bari inyi muku zuwan bazata.

Dariya mummy tayi tace aikam kayi zuwan bazata saidai kuma dakin naka ba share yake ba amma ka shiga dakinsu Umar ka watsa ruwa kafin a gyara naka.

Amsawa yayi da toh sannan ya shige wani daki dake cikin palon, lubna kuma taja trolley dinshi zuwa dakin.

*********
Tunda suka shiga gidan amatu taki sakin jikinta kamar irin ma bata saba da ammie ba, Abdul kuma sai faman tsokanarta yake tayi shiyasa ammie ta koreshi.

Hanan kuma yanzu ta shigo gidan dan bata nan kuma batasan da zuwan Amatu ba shiyasa tana ganinta taje ta rungume ta tana cewa aunty yaushe kikazo?? Sai Amatu tace ban dade da zuwa ba.

Murmushi hanan tayi tace aunty baki ci abinci ba? Ko baiyi dadi bane? Waro idanunta amatu tayi tace laaaa rufa min asiri nidai bance ba. Bari ma kigani in fara ci karki cewa ammie naki ci saboda beyi dadi ba.

Dariya maganarta tabata ta mike tsaye gami dacewa bari in shiga ciki in dawo, amsawa da toh amatu tayi kafin ta fara cin abincin. Tana cikin ci sai ga Abdul ya shigo, tunda yaga an jere mata abinci yaji yanason," zuwa yayi ya zauna yasa hannu wai suci tare.

Ita kuma kunya takeji kar ammie tazo taga suna cin abinci tare tace har rashin kunyar tasu takai suci abinci tare a gidanta kuma ma ba'a koyi auren ba?

Nima dai nace wayaga zumudiπŸ˜‹

Mikewa tayi zata zauna saman kujera ya wani daure fuska yace karki kuskura ki zauna kuma kisa hannu muci. Zaro ido Amatu tayi cikin magiya tace plsss my Abdul ka rufa mun asiri yanzu kanason ammie tazo ta ganmu a haka?

Eh mana to miye a ciki?

Yatsine fuska tayi kamar wadda taga abun kyama tace nikam bazan iya ba nama koshi. Bata rai yayi ya mike zai wuce ita kuma da tsokana sai ta jawo pillow ta wullah mashi.

Aikuwa cikin rashin sani ya fadi timmmmm a kasa. Cikin firgici tayo kanshi dan bata zaton zai iya faduwa ba shiko da gangan ya wani kara lafewa a kasa harda wani kukan karya yana kiran sunan ammie kasa kasa.

A hankali ta furta mishi a daidai kunnenshi tace sorry my Abdul plsss ka tashi kaji? Cikin ranta sai faman dariya takeyi amma a zahiri sannu takeyi mashi harya mike tsaye.

Daukan pillon tayi zata mayar gunda yake sai yayi saurin fisgewa yace ai kuwa baki isa ba dan sai na rama. Marairaicewa tayi tana bashi hakuri amma ina sai daya jefeta amma bai sameta ba dan kaucewa tayi sai pillon ya fada cikin plate din abincin da takeci.

Salati kawai ta farayi tana kallonshi da shi dinma ita yake kallo tace Abdul kaga abunda kayi ko? "Allah babu ruwana idan ammie ta gani.

Cire pillon tayi daga cikin abincin ta dora mishi a hannu sannan ta koma mazaunin ta ta zauna. Abdul kuma tsaye yayi yana kallonta. " jin kamar motsin ammie sai yayi sauri ya fice waje da pillon.

Ammie kuma karasowa wurin amatu tayi tace amatu har yanzu dai banga kinci abinci da yawa ba kodai ta bakin hanan baiyi miki dadi ba. Saurin girgiza kanta tayi tace a'a wallahi ammie yayi dadi sosai kawai dai naci abinci neh kafin in fito.

Murmushi ammie tayi ta fara kwashe plate din zata kai kitchen sai Amatu ma ta dauka zata tayata, aikuwa ammie ta hanata tace tayi zamaninta. Haka ko ta zauna badan ranta yaso ba.

Abdul kuma part dinshi ya nupa ya wanke inda pillon ya baci sannan ya aza saman gadonshi dan ya bushe kafin zuwa anjima.
Fitowa yayi ya dawo part din ammie inda ya tarar da bakowa palon.

Haurawa sama yayi zuwa dakin ammie, "nan ya tarar dasu ammie tace ya koma gasu nan fitowa. Murmushi kawai yayi ya koma palour yana jiransu. Kusan minti goma sai gasu nan sun sauko harda hanan.

Tasowa yayi ya ansa ledar dake hannun amatu yace bari in rike maki karki wahala" kunya taji ta wani sunna da kanta kasa hanan kuma murmushi tayi ganin yadda yayanta ke tarairayar mace.

Har wajan mota sukayi mata rakiya daga bisani sukayi sallama suka wuce.

Bangaren Abdul kuma wanka yayi ya shirya tsaf cikin yan kanti, fitowa palour yayi inda ya tarar an jera mashi abinci saman dinning. Zama yayi ya fara ci lubna kuma sai zuba mashi surutu takeyi shiko in bada eh da a'a su kadai neh abunda yake fada.

Bayan ya gama cin abincin ko kallonta beyi ba ya tashi ya fita. Wurin Abokin shi Kabeer ya tafi, " be dawo gida ba sai wuraren tara na dare.

Kodaya dawo har an gyara part dinshi dan haka can ya shiga, zama yayi gefen gadon shi yana ayyana yadda zasu kwashe da ita "wata zuciyar na cewa idan tayi aure kuma fah??tsuki yaja ya kawar da tunani ya tunanin yadda zai shawo kanta da ba abu mai sauki bane yayi tafiya tsawon shekaru biyu basu hadu ba

Daga karshe dai ya yanke shawarar zuwa wurinta gobe dan yasan Amatullah da hakuri tunda tana tana matukar sonshi zata fahimce shi.

'''waye abdul'''

Asalin sunan shi............


πŸ‘‰πŸΏπŸ‘‰πŸΏπŸ‘‰πŸΏ
[2/10, 10:07 PM] Lashminzy😎: πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«
*RUDANI*
πŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒžπŸ’«πŸŒž

Story & written by
Lashminzy

πŸ’₯GΓ•LDΓŠΓ‘"S WRÌTÊRS
Γ€SSΓ”Γ‡ΓŽΓƒTΓŽΓ’Γ‘πŸ’₯

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Page 25_26

Asalin sunan shi "ABDULRAHMAN "da neh ga Alhaji Aliyu. Abdul yaro ne mai hankali da nutsuwa ga ilimin addini dana boko, tun yana karami yake sha'awar zama malamin makaranta shiyasa bayan ya girma yaci gaba da jajircewa akan sai ya cika burin shi.

cikin ikon Allah ya samu abunda yakeso, dan yanxu haka ya gama degree dinsa a ABU Zaria inda ya karanci education computer daga bisani ya wuce Cyprus dan yayi masters kuma alhamdulillah yanzu ya kammala ya zama cikakken lecturer

Abdul su uku neh a wurin iyayenshi, Abdul shine babba sai umar sai kuma autar su samha, lubna kuma Yar uwarsu ce tana mugun son abdul shiyasa ta dawo gidansu da zama

Abdul kuma baya sonta ko sau daya be taba jin sonta ya darsu a ranshi ba, hasali ma ya tsane ta. Dan duk wani sakin fuska da take gani a wurin shi taci albarkacin mummy neh dan ita ke tsawartar masa saboda ta lura da yadda yake mata wulakanci" ita kuma ba abun ta tursasa masa sai ya sota dole ba.

Cigaban labari

Tsaye yake a bakin wardrobe dinshi yana duba irin kayan da zai saka, can ya hango wani yadi me shegen kyau kalar ruwan kasa. Daukowa yayi ya aje saman gadon shi.

Murmushi yayi na jindadin tunowa da yayi Amatu tafi son ya sanya manyan kaya, rufe wardrobe din yayi ya dawo gefen gadon ya fara sanya tufafin. Sai daya gama shiryawa tsaf kafin ya dauki wayan shi da makullin motar shi ya fice daga dakin.

Beko leka part din mummy ba yasa kai ya fice daga gidan. Direct gidansu amatu ya nupa, a hanya sai addu'a yake Allah yasa ta fahimce shi "harya iso daidai gate din gidansu addu'a yakeyi dan shima yasan be kyauta ba.

Horn yayi a bakin kofar sai ga megadi ya fito dan ba kowa yake budewa gate kai tsaye ba. Tun kafin ya karaso Abdul ya sauke glashin motar shi. Hannu Abdul ya bashi suka gaisa shi kuma megadi sai wani wangale baki yakeyi duk a tunanin shi waccen Abdul dinne dan suna matukar kama da juna sosai.

Abdul kuma ganin yadda megadin ya sakar mishi fuska bai kawo komai a ranshi ba, sai ma cewa yayi ya kira mashi Amatu.

Dan murmushi megadi yayi yace yallabai ai hajiya yanxu ta fita amma gaskiya bansan inda taje ba. Haushi kamar ya kashe Abdul dan baiyi tunanin baza'a sameta a gida ba.

Kallon megadi yayi ya zaro dubu biyu daga aljihun shi ya mika mashi. Godiya megadi ya shiga yi kafin ya tada mota yabar wajan.

Bangaren Amatu kuwa yanzu ta iso shago dan kuwa yau ita kadai ta fita ameerah na gida wai bata da lafiya. Tun shekaran jiya aunty hajara ta fara ganin sauyi atattare da ita amma tayi tayi ta fada mata abunda ke damunta fur taki.

Koda Amatu tazo gidan haka itama tayi ta tambayar ta tana lallaminta amma haka tayi burus taki fada mata. Ita kuwa ameerah tun lokacin da taga Abdul taji ya shiga ranta, tun tana ganin abun kamar wasa har ta fara gazgata kanta da cewa tanason Abdul.

Danne abun tayi a ranta dan tasan yadda kawarta ke mutuwar son Abdul kuma abun kunya ne a gareta ace duk yadda suke ta furta Kalmar so ga wanda Yar uwarta keso.

Abun haushi ma shine beko san tanayi ba shiyasa ta fara tunanin yadda zata cire shi acikin ranta ta karfi da yaji.

Amatu kuma kawai dai taje shagon ne amma babu wani karfi a tattare da ita saboda yanayin yadda taga ameerah shiyasa taji jikinta ya mutu, yanxu haka ma wata takeson ta karasawa gyaran kai ta koma gida dan hankalinta yaki kwanciya.

Abdul kuma tafiya yake yana yan sake sake dan yarasa abunda ke mashi dadi, Amatu kuma fitowar ta kenan daga shago ita da wata ma'aikaciyar shagon ta zata sauke ta saman hanya sai ta hango kamar Abdul ta cikin glass din motar ta.

Sauke glass din motar tayi ta kare mashi kallo, daga dai fa Abdul dinta neh. Murmushi tayi ta budewa titi mota ta fita sannan ta juyo ta gefen data hango shi amma wayam babu ko alamar motar shi.

Tsuki tayi taja motarta ta wuce, direct gidansu ameerah ta nupa, inda ta tarar da Aunty hajara a kitchen tana girki. Gaisawa sukayi kafin ta wuce dakin ameerah.

Kwance ta tarar da ameerah kamar wata mara lafiya" da gudu Amatu ta karasa wurin ta gami da zama ta gefen ta tana kallonta har kwalla sun cika mata ido ganin ameerah na kuka ga jikinta yayi zafi sosai kamar garwashi.

Hannunta tasa tana share mata hawayen da suka gangaro mata tace ameerah plsss na rokeki ki taimaka ki daina wannan kukan kuma ki dubi girman Allah ki fadamun abunda ke damunki.

Rass rass taji gabanta ya fadi da jin irin yadda amatu ke hadata da Allah akan abunda ita karan kanta bazata so wani yaji ba ballantana ita Amatu.

Share hawayenta tayi tasa hannuwan Amatu a cikin nata ta rike su gam tace my Amatu ki kwantar da hankalinki, duk wani abu da zai rusa maki farinciki bana fatan ya sameki kuma ki sani abunda ke damuna bazan taba bari ya hanaki sukuni ba shiyasa zan fada maki.

Amatu saurayina aure zeyi nan bada dadewa ba kuma ni kinga gidan mu basu tashi yimun aure ba shiyasa na shiga damuwa dan nasan na rasa shi kenan kuma amatu zeyi wuya in samu kamar shi,
" ta karasa maganar ne a yayin da hawaye ke kwaranya a idanunta.

Share mata hawayen
Amatu ta shiga yi tana lallashinta, dakyar ameerah tayi shuru dan kuwa tasan ta rasa Abdul ne da gaske. Haka Amatu tayi ta lallashinta inda daga karshe harta dan sake suna hira, da aunty hajara taga ameerah taji dadin yadda Amatu ta lallasheta amma tayi tambayar Amatu ta fada mata sai taki tace wai wannan sirri neh a tsakanin su

Haka dai sukayi ta hira har zuwa magariba kafin Amatu ta wuce gida, a farfajiyar gidansu tayi parking din motar ta sannan ta fito, megadi ne ya karaso wurinta bayan sun gaisa yake shaida mata ai Abdul yazo har sau biyu bata nan,

Dan waro idanunta tayi tace laaa yaushe kuma be kirani a waya ba?? Karasawa ciki tayi ta dauko wayarta sai a sannan taga wayar ta a kashe.

Mummy ceh ta shigo dakinta tace Amatu ina kika sa wayanki ne dazu nayi ta kiran wayarki a kashe? Marairaice fuska tayi tace mummy nima bansan wayan a kashe take ba sai yanxu kuma wai Abdul yazo gidan nan??

Eh yazo har cikin palour yazo ya gaida ni, dan murmushi kawai tayi ta cire hijab dinta ta shige toilet, mummy kuma fita tayi daga dakin.

Tana fitowa tayi sallar magariba, tana nan zaune har akayi isha'i, tana gama tasbihi ta linke sallayar ta maida ita ma'aji yinta sannan ta

5 / 27