Chapter 9 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 27

24K to 27K   out of 79.1K words

itace ke tsawatar musu toh bata nan nikuma konayi magana baji sukeyi ba kuma a lokacin bani da kudi balle mu kebe daga garesu.

Haka rayuwar mu ke tafiya cikin gidan, idan har bana nan to fah aisha tana cikin kunci da damuwa, idan har kaga tana murmushi toh tana tare dani. nikuma ban fiye zama gida ba dan ina zuwa cikin garin kano ina dan kasuwanci na na saye da sayarwa shiyasa suke samun damar musguna mata.

Akwai lokacin dana tsaya dakin daka nace duk wadda ta kara koda taka takalmin aisha sai nayi karar shi, amma duk a banza dan da zarar nasa kafa na fita zasu fara zaginta suna mata gori wai bata haihuwa.

Kullum da sabon wulakancin da suke bullo mata, itakuma aisha akwai hakuri duk zagin da zasuyi mata bata taba ramawa sedai tabisu da Allah ya shirya. amma da suka kaita bango garinsu taje ba tare da sani na ba. ko dana dawo gida bata nan sai nayi tunnin kota shiga makwafata "sai ji nayi aisha shuru, su kuma yan gidan dake sun san abunda suka aikata babu wanda yace mun kala

Haka na gaji da nemanta washe gari naje garinsu dake garinmu ba daya ba amma kusa muke. nan na tarar da ita sai kawunta yayi ta fada akan bazai bani ita ba dan baze bari yana ji yana gani a wulakanta amanar da aka bashi ba. dan aisha tun tasowarta batasan iyayenta ba ita da kanwarta maryam. a hannun kanin baban su suka taso kuma bai laifi yana kula dasu yadda ya kamata.

Dakyar kawunta ya bani ita muka koma.

Bayan wata daya da faruwar Haka sai aisha ta kamu da rashin lafiyar da har takai mu ga zuwa asibiti. nan aka tabbatar mun da cewa aisha nada biyu.

Ba karamin farinciki mukayi ba dani da ita amma wani abun mamaki shine duk yan uwana babu wanda ya nuna jindadin shi. nikuma abun bai dameni ba daman tun tasowar mu sun tsaneni, bansani ba kodan ba uwa daya ta haifemu ba oho. Shine kiyayyar da suke mun ta shafi matata da kuma abunda ke cikin ta.

Haka rayuwar mu ta kasance inda nake bawa aisha kulawa fiye dana da har Allah ya sauketa lafiya, inda Allah ya azurta ta da yara maza guda biyu. duk wani abu da mejego zata bukata nayi kokari wurin ganin na samar mata shi amma yan uwana komai basu bani ba hasalima ranar da ake suna basu ko gidan yan dangin aisha ne dakuma makwaftan mu suka halarci bikin.



************
Haihuwar su abdul ta zama kamar wata kofa ce ta kunno masifa dan kuwa duk wani wahala da aisha ta fuskanta a baya bekai na wanda take fuskanta a yanxu ba dan bata da ikon zama a tsakar gida, duk wani abu da aisha zatayi indai baya zame mata dole ba ko fitowa batayi saboda gudun matsalar su.

Amma duk da wannan kaucewar da hakurin nata bata tsira ba dan kuwa yanxu kiri-kiri suke nuna mata bakincikin su.

Akwai wata rana aisha bata nan ta shiga bandaki, sai tabar yaranta nan cikin daki ta rufesu saboda karsu fito suyi musu barna dan Allah ya azo ma yaran rashin ji da barna. Tana cikin wanka sai taji kamar abdulraheem na kuka, nan ta fito da sauri amma abunda ta gani ne yasata firgita, da sauri ta dauko muciya ta kwala matar yayana mai suna saude, bayan ta kwala mata ne ta dauke abdulraheem da take shirin jefawa cikin rijiya ta shige daki tana kuka.

Ina dawowa aisha ta sanar dani, nan na shiga bata hakuri amma abunda aisha bata taba yimun ba shine musu amma a ranar saidata mun musu tace wallahi ta gaji hakurinta ya kare in sallameta ta wuce gidansu.

Nikuma abun ya kona mun rai sosai ya za'ayi su takurawa mata ta tunda ba zamansu take ba ina ruwansu. nan na fito tsakar gida suna cin abinci na fara musu fada ina zaginsu, ta inda nake shiga ba tanan nake fita ba. haka na karaci babatu na babu wanda yace dani ko kala, abun ya bani haushi sai kawai na dauko wani icce na kwadawa auwal kanina dake zaune, nan jini ya fara zuba a goshinshi yan ihu haka na tafi na barshi.

Washe gari bayan na fita ne matan gidan suka kama aisha suka kulle a daki suka mata dukan tsiya, kodana dawo gida na tarar duk sun kumbura mata jiki, na tashi zan fita inje wurin megari inyi kararsu ayi mana iyaka dasu dan lokacin raina yakai kololuwar baci, aisha tasha gabana.

Tana kuka harda majina tace wallahi saina saketa kota kashe kanta dan ta gaji da zama cikin wahala dan itama tanada gata dan haka in sake ta, nan na shiga bata hakuri ina mata magiya amma kamar kara zugata nakeyi.

Munyi kusan awa daya muna jayayya da ita, dana ga cewar da gaske takeyi sai na yanke shawarar inyi mata saki daya inyaso ta dan huta na kwana biyu kafinnan sai in samo mana wani gida koda na haya ne mu zauna.

Haka na furta kalmar saki batare da zuciyata da gangar jikina sunso ba. ina kallonta ta shirya kayanta dana yaranta ta fito zasu wuce, sai nace mata nipa bazan bari taje da yaran ba tabar munsu in rike.

Fur taki wai bazata barsu a dinga gana musu azaba ba, tun muna saisa saisa har abun ya dawo mana fada. ta fadi in fadi, daga karshe dai ta dauki abdulraheem ta wuce dashi. nikuma na rike abdulrahman yana ta kwalla ihu amma haka nayi ta rarrashin shi.

Bayan kwana biyu da faruwar hakane sai na shirya zuwa garinsu aisha dan in kaimata abdulrahman ta rikesu har zuwa wani lokaci.

Nan na tarar da mummunan labari, dan ba karamin firgita nayi ba dajin su aisha sunyi gobara kuma babu wanda aka fitar da rai.

Haka na kwashi jiki na koma garin mu nan ma kamar wani hadin baki na tarar da gobara ta tashi kuma duk yan uwana sun kone saude ce kawai ta fita da rai amma itama ko sati batayi ba ta rasu.

Na shiga damuwa da danasanin rabuwa da aisha danayi. kullum kuna ne sana'ata, abdulrahman kuma lokacin yana da shekara uku babu ruwanshi da abunda ke faruwa tunda ba wayo ke garesa ba.


***********
Gidan wani abokina na koma da zama nida abdulrahman har zuwa wani lokaci da nayi ta fafutukan samun aiki, dakyar nasamu wani alhaji ya taimaka mun muna aiki tare dashi, inda har yaga na burgeshi ya hadani da yar'shi aure. A lokacin ban musa mashi ba dan ya zama kamar uba a gareni kuma ga abdulrahman yana fama da maraicin uwa shiyasa kawai na amince na aureta kuma Allah yasa muka fahimci juna da ita.

Daga nan rayuwar mu taci gaba da tafiya inda kasuwancin alhaji yakara yelwaita, nima kuma yabani babban jari wanda shine silar zamana mai kudi.


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalli ammie yace aishatu ina kika shiga ne a tsawon wannan lokacin kuma ma ya akayi kika kubuta daga gobarar data cinno muku??


ıŊAŦƐŘMıŞŞıƠŊ




[2/16, 4:59 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

I love u so much ummu arpat, ngd da irin soyayyar da kike nuna mun amma karki manta nima fah ina kaunarki din kuma ina yinki 💯💘

     Page 41-42

Kwalla ce ta zubo mata kafin ta share tace "bayan na koma gida washe gari gobara ta tashi a gidan mu a lokacin kuma nida maryam kanwata munje gidan halima matar kawunmu, toh muna can ne mukaji labarin gobara ta kama a gidan mu.

Kuma duk mutanen gari sun aza harda mu dan tunda mukaji labarin haka bamu dawo ba sai mukayi zaman mu can daman kuma kawunmu kadai muke dashi shiyasa bayan wannan gobarar bamu dawo ba.

Bayan sati d'aya da faruwar haka sai kawu bala wato mahaifin halima yace ni tunda mijina na nan kuma ga abunda ya samemu inyi mishi kwatancan garinsu yaje ya sameshi dan a mayar da auren mu. "batare da nayi wata jayayya ba na amince saboda ko nan da muke zama ba wani dadi mukeji ba danshi ma baida hali sosai.

Bayan yaje garin ya dawo ne yake fada mana wai kun samu gobara kuma duk kun rasu wasu kuma sukace kabar gari. Daga nan nikuma na shiga damuwa, nayi kuka harna gaji daga karshe na dangana ga Allah.

Bayan wasu lokaci da faruwar haka ne Allah ya hadani da Ibrahim waton mijina na yanzu, a lokacin ina yin panke ina kaiwa wani shago ana siyarwa sai Allah ya hadani dashi kuma tun daga lokacin daya bayyana mun yana sona na amince. Ba'a dauki lokaci me tsawo ba aka daura mana aure inda yace maryam ta dawo gidan mu da zama, dan yana da hali sosai dan ko lokacin bikin mu ya dauki nauyin abubuwa da dama.

Haka rayuwar mu ta kasance inda muka dawo nan abuja da zama dan nan yake aiki, maryam kuma yasata a makaranta taci gaba da karatu nikuma yana kula dani yadda ya kamata. Abdulraheem kuma ko sau daya be taba nuna mashi bashi ya haifeshi ba dan haryanzu Abdulraheem besan Ibrahim bashi ya haife shi ba sai yanxu da wannan al'amarin ya faru.

Ajiyar zuciya ta sauke tace Aliyu kaji yadda akayi muka tsira. Hamdala yayi ya kalli Abdulraheem yace dana zo kusa mana. A hankali Abdulraheem ya tako har zuwa inda yake ya zauna.

Abba yace toh alhamdulillah munji dadi da Allah ya bayyana wannan lamarin, yanxu sai kowa ya gode ma Allah. Daddyn Amatu yace kwarai kuwa ai yanzu matsalar data kunno yanzu zamu kasheta tunda abun ya zama haka.

Daddyn Abdulraheem yace eh kwarai kuwa amma yanxu wannan ya rage a tsakanin su tunda yan uwan juna ne yanzu sai daya yabar ma daya ko??

Gaban su ya fadi rassss a tare suka juyo suna kallon juna. "Cikin zuciyar  abdulraheem ko cewa yake lallai akwai chakwaki, amma nifa bazan taba bar mashi ita ba. Abdulrahman kuma dadi yakeji dan yasan duk yadda za'ayi shi za'a barma Amatu.

Suna cikin zancen zucin su mummy ta katse su ta hanyar marairaicewa tana kallon ammie tace Aisha nasan cewa kina bukar duka ya'yanki a kusa dake amma dan Allah kiyi mun alfarma kibar Abdulrahman a wurina saboda na shaku dashi banason yayi nesa dani Dan Allah...... Ammie ta katse ta tace haba ke kuwa ai bazan rabaki dashi ba tunda haihuwar shi kawai nayi amma ke kika kula dashi tuna yana karami har zuwa girmanshi kinga ai kema danki ne dan haka kici gaba da zama dashi kuma kici gaba da bashi matsayin shi na danki.

Murmushin jindadi mummy tayi ta karaso wurin ammie tana zuba mata godiya dan ba karamin dadi taji ba. Saboda ko ya'yan data haifa bata musu irin sonda takewa Abdulrahman ba" wani sa'in samha har kuka take tana shagwaba wai mummy tafi son Abdul.

**********
Lubna ce ta shigo yanzu tare da samha dan duk abunda ke faruwa basu sani ba sai yanxu kuma dalilin zuwan su shine basu ga ammie da Umar ba kuma sunga motar daddy dana wasu shiyasa suka nupi part din ko suna ciki.

Bayan sun shigane lubna taga Abdulraheem kusa da daddyn su duk a tunanin ta Abdulrahman ne, samha kuma gaishe dasu tayi kafin ta nemi wuri kusa da mummy zata zauna mummy ta kwabeta tace bakiga dan uwan Abdul bane?? Sai a sannan ta hango Abdulraheem dake zaune kusa da daddyn su.

Lubna kuma jin maganar mummy ne yasata dawo daga duniyar tunanin data shiga dan ita kallon Abdulraheem kawai take ba kakkautawa sai yanxu ta kalli gefen gado, can ta hango Abdulrahman ya jingina da kan gado.

Aikuwa cikin rudewa ta fara ja da baya, mummy ta taso ta jawota ta zauna tace lubna kwantar da hankalinki mana anjima zamuyi magana kinji ko?

Gyada kai kawai tayi tana me kallon Abdulrahman da Abdulraheem dan babu wani banbanci a tsakanin su, hatta da yanayin askin Kansu yazo daya, "kayan da sukasa ne kawai ya banbanta dan Abdulraheem manyan kaya yasaka Abdulrahman kuma T-shirt ce baka da blue din jeans.

Samha ma na daga gefen mummy tana kallon Abdulraheem, take sai taji ya shiga ranta dan yadda ya saki fuska sai taji ya burgeta ba kaman Abdulrahman daya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da manzon mutuwa.

Daddyn Abdulrahman ne yafara magana cikin nutsuwa yace toh alhamdulillah komai yazo yadda ya kamata sedai wani hanzari ba gudu ba.

Abdulrahman tunda ya kasance Abdulraheem dan uwanka ne ni a matsayina na mahaifin ku bazan iya cewa kai ko shi wanin ku ya hakura ba dan yin hakan ya zama tamkar tauye muku hakki ne amma shawara ta guda daya shine kuje ku sasanta kanku dan magance wannan matsalar.

A tare suka kalli junan su

Sai ammie ta karbe zancen da cewa alhaji kana ganin shawarar ka tayi kuwa? Bawai kar ace na nuna banbanci ba da sai ince Abdulrahman ya hakura tunda har anyi komai da sunan Abdulraheem kuma nake ganin kamar Amatullahi bazata amince da haka baa........

Sai daddyn amatu yace a'a hajiya shawarar shi tayi daidai dan kuwa Abdulrahman ya tabbatar ma Ibrahim da sun taba soyayya can a baya.

Cikin dan mamaki ammie ta zaro ido tace kenan ta rigamu sanin shi?? Toh amma ya akayi tabar mu cikin RUDANI bata fada mana ba??

Sai Abdulraheem yace ammie itama bata sani ba dan a lokacin dana hadu da ita ta nuna ta sanni kuma harda cewa tayi munyi kusan shekara biyu muna soyayya da ita nikuma ban dauki maganar ta da gaskiya ba dan na dauka shirmenta ne kawai dai ina mata kama da wani ne Ashe da gaskiyar ta.

Ammie tace tau Allah me iko🤔 indai kuwa hakane nima na yadda da shawarar daddyn ku, Allah ya baku sa'a

Murmushi samha tayi dan ammie tace Allah ya basu sa'a sai kace wani jarabawa.

Daddyn amatu ne yayi musu sallama musu yace duk shawarar da suka yanke a sanar dashi.

Ammie da Abba suma tashi sukayi zasu wuce, sai Abdulraheem ya mike zai bisu, aikuwa ammie ta banka mashi harara tace toh bazaka tsaya ku gana da dan uwan naka ba! Bata rai yayi ya koma ya zauna.

mummy da daddya kuma kallon juna sukayi kafin sukayi murmushi suka basu wuri, lubna kuma rai bace tabi bayan mummy tana yan sake sakenta dan a zuciyar ta cewa take tunda Abdul yan biyu ne ya zama dole ta samu daya daga cikin su.

Niko nace kidai bi a hankali 😏

Umar ma fita yayi sai ya rage daga samha sai Abdulrahman da Abdulraheem. Zaune suke babu wanda yayi magana cikin su sai samha data ga shurun yayi yawa sai ta karasa wurin Abdulraheem cikin zolaya tace gaskiya yaya kafi yaya Abdul kyau ta fada tana murmushi, shima murmushin ya mayar mata yana tambayar sunanta.

Cikin yanga tace baga yaya Abdul ba ka tambaye shi, " tana fadar haka ta fice. Dariya yayi a ranshi yana gani yanayin yarintar ta sak dana hanan dan itama haka take da surutu da shishigi.

Dake Abdulrahman haka yake jin kanshi kamar wani sarki dan Allah yayi shi da son girma gashi kuma baya daukar raini shiyasa ya wani sha toka yana latsar wayanshi dan ko kallon inda Abdulraheem yake bayayi.

Abdulraheem kuma gajiya yayi da zaman kuramen da sukeyi ya mike batare da yace kala ba ya ficewar sa daga dakin. Yana fita Abdulrahman ya ajiye wayar a fili yace wallahi baka isa kaso abunda nakeso ba gwara ma ka janye maganar baby ka dawo muyi zaman yan uwa.

Abdulraheem kuwa yana fita yaga wayam su ammie sun tafi gashi daman bada motar gidansu sukazo ba, ammie kuma da zasu wuce motar datazo da ita ta shiga ita da abba suka wuce.

Tsaye yayi yana yan kalle-kallenshi, yana kuma zancen zuci yace Abdulrahman kenan, bani ya kamata na hakura da Amatullahi ba kai ya kamata ka hakuri da ita dan haka idan ma kaki mun magana saboda ita ne to kayi gaggawar janye wannan hukuncin naka dan kuwa amatu kamar na aureta ne.

Ni kuwa toh 😳

Samha ce tazo wurin shi ta katse mashi zancen da yake tace mummy na kiran shi, juyowa yayi suka nupi hanyar shiga palo tana gaba yana baya har suka shigo palon..............


Plsss share
[2/17, 11:31 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Godiya mara iyaka, my fans ina sonku sosai da sosai, ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke

     Page 43-44

Mummy na zaune saman kujera tayi mishi nuni daya zauna, zama yayi kan two seater, mummy tace daman naga mummynka sun wuce da mota shine nace samha ta kira mun kai tunda magariba ta kusa kabari idan akayi sallah sai umar yakai ko?

Da kamar zaice a'a sai yace toh mummy nagode. cikin jindadi tace yauwa bari a kawo maka ruwa kasha, ta fada gami da mikewa ta shiga kitchen. Samha kuma na nan palon tana kallon shi sai faman latsar waya yakeyi.

Lubna dataji kamar magana sai ta fito palo, ganin abdulraheem yasa ta daskarewa a wurin tana kallon shi.

Mummy ce ta fito daga kitchen dauke da faranti a hannunta sai lubna tayi saurin karbar farantin takai gaban abdulraheem ta ajiye. murmushi mummy tayi tace dana abdul gashi amma kayi sauri kaci dan lokacin ya sallah ya gabato.

Da fara'ar shi ya amsa da toh sannan ya fara cin abincin dan dama yunwa yakeji, rabon da yaci abinci tun shayin safe, shiyasa yanzu ya mayar da hankalinshi kan abinci.

Lubna ko sai kai kawo take kamar wata mayya, shiko abdul beko san tanayi ba dan dadin girkin mummy ya tafi da tunanin shi. Sai dayaci ya koshi kafin ya kalli samha data mayar da hankalinta kan wani season film a tashar bollywood. yanason yamata amma yarasa ta ina zai fara dan besan sunanta ba.

Mikewa kawai yayi sai lubna ta taso ta karaso wurin shi tace yaya tafiya zakayi ne? kai ya gyada mata, sai tace tana zuwa bari ta sanar ma mummy. Bada jimawa ba sai ga mummy tazo, tana murmushi tace ahh har zaka tafi kenan? yace eh mummy.

Kallon inda samha take tayi tace baby jeki kira umar kice yayanku ya tashi kinji? amsawa tayi da toh ta fita. Lubna kuma sai wani noke-noke takeyi

9 / 27