Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
"dan kullum idan sukayi waya cewa take abdul yaƙi kawota gida.
Mommy kam murmushi kawai takeyi tana cewa tayi haƙuri ai bada daɗewa ba zai kawota. Nan suka ɗan taɓa hira daga bisani ameerah ta katse kiran sakamakon abincin ta dake kan wuta tana gudun karya fara ƙauri.
Saukewa tayi ta kwashe cikin kula, sannan ta wanke pots ɗin da sauran kayan data ɓata sannan ta gyara kitchen ɗin komai ta mayar dashi mazaunin shi. Bayan ta gama ne ta wuce ɗaki danta watsa ruwa. Bada daɗewa ba ta shiga toilet tai wanka sannan ta fito ta isa gaban dressing mirror tayi ƴar simple make-up wa fuskarta sannan ta ɗauko wata atamfa kirar swiss kalar ja tasaka. Masha Allah kayan sunyi mata kyau sosai.
Flat shoes tasaka kafin ta fito daga ɗakin ta shiga kitchen, kulolin abinci ta ɗauka tasa a wani ɗan madaidai cin basket ta fito tayi hanyar fita waje. Tana buɗe kofa ta ganshi a tsaye riƙe da rigar shi irin na likitoci." Murmushi ne ya bayyana a fuskar su ita kuma har dana mamakin ganin shi dan duka duka yanzu sha biyu ne da rabi.
Hannuwan shi ya waro mata alamar tazo, aikuwa aje basket ɗin tayi ta faɗa jikinshi tana mai sakin murmushi kamar yadda shima murmushin yakeyi.......
[3/5, 8:08 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Wannan shafin sadaukarwa ne ga Ruɗani fans grp 1,2&3 ina yinku sosai da sosai, Allah yabar kauna ❤
Page 81-82
Bayan ya cika ta neh tace zataje takaiwa Amatu abinci, "nan ya shige ita kuma ta isa part ɗinsu Amatu. A daidai ƙofar shiga ta tsaya ta fara knocking, "su amatu kuma lokacin suna bacci. Ƙara buga ƙofar tayi sai Amatu dake lafe jikin Abdulrahman cikin baccinta takejin kamar ana buga ƙofa.
"""Da sauri ta buɗe idonta sai kawai ta zuba su akan Abdulrahman da yayi nisa a bacci, "ƙoƙarin tashi tayi sai yasa hannun shi ya ƙara jawota ya riƙe ta gam. Tsayawa kallon shi tayi taga ya ɗan sassauta riƙon da yayi mata sannan a hankali ta zare jikinta daga nashi sai tasa mashi pillow makwahinta.
"Ɗankwalinta daya faɗi a ƙasa wurin bacci ta ɗauka ta ɗoro sannan ta nupi bakin ƙofar, "tana buɗewa taga ameerah, "aikuwa rungumar junan su sukayi kafin suka ƙaraso ciki. Ameerah tace lallai yarinyar nan kina jindaɗin ki, waton ma bacci kike ko? Amatu tayi murmushi tace kedai bari wallahi banjin daɗi ne shiyasa na ɗan kwanta.
"Ameerah tace lallai kam. Ni kinga tashi mu shiga ɗaki karmu dami mijinki, ta faɗa haɗe dayin murmushi, "amatu kuma kallon basket ɗin dake hannun ameerah tayi gami da taɓa shi tace besty yau wani irin delicious kikayi mana? Ameerah tace favorite ɗinƙu keda mijinki. Amatullahi cike da murna ta ɗauki basket ɗin tace ameerah mu shiga daga ciki.
"Nan suka shiga kitchen amatu ta aje basket ɗin kafin suka shiga ɗaki, "ɗan hira kaɗan suka taɓa ameerah tace zata wuce saboda abdul na nan. Sallama tayi mata ta wuce.
""Bayan ta tafi ne Amatu ta fito palour inda Abdulrahman haryanzu baccin sa kawai yake shirgawa, gashi lokacin sallar azahar yayi. Ƙarasawa wurin shi tayi haɗe da cire pillon data ɗora mashi, "aikuwa dajin ta cire yayi saurin jawo pillon haɗe da janyo hannunta data riƙe pillon. Sunkuyawa tayi ta ƙara zare pillon da hannunta a karo na biyu kenan, sedai a yanzu ya buɗe idonshi.
,,,,,,A hankali ya saukesu akan Amatu, "murmushi ya sakar mata ya tashi zaune yana miƙa. Ita kuma miƙewa tsaye tayi ta zauna kusa dashi, cikin sweet voice ɗinta tace ummm kasha bacci gashi yanzu har ɗaya ta buga. Waro ido yayi ya duba agogon dake maƙale a hannunshi yaga ɗaya ma harta wuce, "aikuwa da sauri ya miƙe yaja hannunta suka haura sama. Direct ɗakin shi ya shiga da ita ya zaunar da ita saman gado sannan ya shige toilet. Ita kuwa binshi da kallo kawai take taga abunda zaiyi.
"Bada daɗewa ba sai gashi ya fito fusrkar shi da danshin ruwa, da alama dai alawla yayi. Kusa da ita yazo yaja hannunta ya shigar da ita toilet, "sannan a hankali yace kiyi alawla kiyi sallah anan kafin na dawo, "yana faɗar haka ya fice daga ɗakin. Ita kuma murmushi kawai tayi tace hmmmm Abdul kenan. Nan itama ta ɗoro alawla ta fito gami da shimfiɗa sallaya ta tada sallah.
Tsawon minti goma ta kwashe kafin ta sallame tayi ƴan addu'ointa sannan ta naɗe sallayar ta fita palon ƙasa. Direct kitchen ta shiga ta ɗauko su plates da cups da kuma basket ɗin abincin da Ameerah ta kawo musu. Dinning area takai ta jera su sannan ta shige nan ɗakin ƙasa ta cire kayanta da niyar watsa ruwa sai ga Abdulrahman ya shigo.
"Aikuwa kamar wacce taga kwarto harda ƴar ƙara tayi haɗe da arcewa da gudu ta shige toilet, "murmushi yayi ya bita har bakin ƙofar. "Hannu ɗaya kawai yasa ya turo ƙofar a lokacin da ita kuma take kiciniyar sa key, sedai shi ya rigata. Cusa kanshi yayi ya shiga toilet ɗin. "mutuwar tsaye yayi a lokacin da idanunshi sukayi arba da kyakyawar surar ta, sanye take da towel wanda ko cinyarta bai ida rufewa ba. Hannuwanta tasa ta rungume kirjinta dashi wai duk dan karya gani. batasan kuwa hakan da tayi shiyasa nashanunta tasowa sama ba, har ana kallon burtsowar su ta saman towel ɗin.
Shi gabaɗaya hankalin shi ya tashi, dan ba ƙaramin sha'awar ta yaji ba musamman ma nashanunta da suke a waje. A tsorace ta fara ja da baya ganin yana kusanto ta. A hankali yake ƙara matsota har ta isa wurin bathtub wanda saura kaɗan ta faɗa ciki yayi saurin riƙo kugunta.
Ruƙo ƙugunta da yayi kuwa kamar ance towel kunce ne, towel ɗin ya suɓuce mata, "da sauri tasa hannunta ta gyara tana wani sunne kai ƙasa. Shi kuma duƙ ya wani susuce dan yadda ya gansu uwa an hura baloon, "ƙara matsowa yayi daf da ita yasa hannuwan shi duka biyu ya ɗago kanta.
Ƙura mata ido yayi yaga idanunta sun cicciko da ƙwalla, "Cikin tashin hankali ya tambaye ta yace baby kukan me kikeyi haka? Hannunta tasa tana goge ƙwallar data zubo mata muryar ta na rawa tanason tayi magana amma ta kasa saboda kukan da yaci ƙarfinta.
?Cikin tashin hankali, ya rungumota jikinshi, cikin lallashi ya fara bubbuga bayanta at d sametime yana hura mata iska a kunne wanda hakan ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba. A hankali ya zareta daga jikinsa jin tayi shuru yace baby waton gudu na kikeyi ko?
Cikin sigar shagwaɓa da jan hankali tace toh ba wanka zanyi ba shine ka biyoni. Dariya maganarta tabasa yace toh shine abun kuka? Ta girgiza kai alamar a'a yace toh menene, "shuru tayi masa yace tau koma dai menene ya wuce yanzu dai bari in rage kayan jikina sai nazo na miki ko??
"Waro ido tayi haɗe da marairaice fuska tace plzzz yaya Abdul kayi haƙuri zanyi da kaina. Dariya yasa harda dafe ciki yace laaaa yaushe na zama yayanki?? Ƙafafunta ta fara bubbugawa a ƙasa tana cewa uhmmmm nikam ka fita da kaina zanyi. Murmushi yayi batare daya bata amsa ba ya fita.
Yana fita tasa key ta rufe ƙofar sannan ta zare towel ɗinta ta shige bathub ta fara waka, "fita nayi na bata wuri dan yadda naga ta ɓallo mun harara. Abdulrahman kuma fita yai daga ɗakin ya nupi ɗakinta ya ɗauko mata wasu riga da wando da hular su me kyau. Sannan ya rufe ya buɗe ɗaya side ɗin ɗrowan ya ɗauko mata underwears kalar kayan waton pink colour ya aje saman gadon sannan ya fita.
Yana fita ɗakin ƙasa ya shiga ya zauna bakin gado yana jiran fitowarta, "bada daɗewa ba sai gata nan ta fito, aikuwa tana ganin shi tai saurin komawa dan kunyar fitowa take ya ganta babu kaya. Shi kuma ɓata rai yayi ya tashi a fusace yaje toilet ɗin, "tsaye ya ganta ta takure kanta. Batare da yayi tunanin komai ba ya isa wurinta ya jawo hannunta ya fito da ita ya zaunar da ita saman gado yace baby wai wannan kunyar fah?? Ni fah gaskiya wannan kunyar a daina ta saboda tana shiga hakki na.
Kuma ma daga yau tare zamu dinga wanka. A zabure ta ɗago idanunta ta watsa su akan nashi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa zatayi magana ya dakatar da ita.... Yace a'a baby banason musu, yana faɗa ya fice daga ɗakin.
Cike da zulumi ta miƙe tsaye tana tunanin ko yayi fushi ne ya fita? Ganin bata da amsar da zataba kanta ta kawar da tunanin akan idan ta gama shiryawa zataje ta sameshi. Haka ko tayi bayan ta gama shafa mai tayi simple make-up ta haura sama zuwa ɗakinta.
Da shigarta ta hango kayan daya aje mata, murmushi tayi ta ƙarasa wurin ta ɗauki kayan ta fara sawa dan tasan shine ya fitar mata dasu. Woww kunga yadda kayan sukayi mata kyau kuwa?? Musamman rigar dan ita ta ƙara fito mata da surar ta waton kiran coca cola. Isa tayi bakin madubi ta ƙarewa kanta kallo tana ɗan jujjuyawa dan ita karan kanta tasan kayan sun amshe ta.
""""Yalwata fuskarta tayi da ƙayataccen murmushi ta fito daga ɗakinta ta nupi ɗakin shi. Tsaye ta hango shi a gaban madubi sedai da alama tsuwa kawai yayi. Ƙarasawa tayi inda yake ta tsaya ta bayan shi ta kira sunan shi, "shuru yai mata kuma yana jinta har tayi masa kira uku amma bai amsata ba.
Kukan shagoɓa tasa haɗe faɗawa bayan shi ta rungumo ta baya, a yayinda shi kuma wani irin yarrrr yaji sedai be nuna hakan ba sai ya juyo da ita ta gabanshi yana fuskantar ta yace baby rigimar ki tayi yawa, "nifa bakiyi mun laifin komai ba kawai nayi shuru ne inga yadda zakiyi. Sake shi tayi ta matsa baya tana share ɗan guntun hawayen data farayi ta nupi hanyar fita.
Da sauri yabita yasha gabanta, ya riƙe ƙugunta da hannuwan shi cikin salon nuna soyayya da jan hankali haɗe ka kashe murya yace "baby wannan...
[3/7, 5:22 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 83-84
Yace "baby wannan irin yanga haka fah, ai sai notin kaina ya kunce, ya faɗa yana murmushi. Da bataso kulashi ba amma maganar shi dariya ta bata kuma ita harga Allah tasan ba yanga tayi masa ba. Ɗan shan toka tayi ta cire hannunshi dake riƙe da ƙugunta ta fice daga ɗakin, "murmushi yayi ya bi bayanta har suka isa dinning area, nan ta zuba mashi abinci a plate ta tura gaban shi.
''''''Yatsine fuska yayi kamar wanda yaga kashi kafin ya kalleta yace bazan ci ba! Waro ido tayi ta kalleshi suka haɗa ido taga duk ya murtuƙe fuskar nan tashi tace ayyah my Abdul plsss kayi haƙuri kaci, "idan bakaci ba nima fah bazan ci ba. Batare daya kalleta ba yace ya zanyi inci abinci bayan kina fushi dani?
"Ni fah ba fushi nake dakai ba ta faɗa a shagwaɓe, sai yace toh idan ba fushi kike dani ba miye neh? Babu komai ta bashi amsa a takaice. Komi baice mata ba ya tura plate ɗin gaban ta yace naji indai ba fushi kike dani ba toh ki bani a baki. Murmushi tayi wanda a iya laɓɓanta suka tsaya tasa spoon cikin couscous ɗin sai data cika cokali taf har yayi soro kafin ta ɗago ta kalle shi tace buɗe baki?
Waro ido yayi yace zaki kashe mijinki neh??? Cike da shagwaɓa ta cunno bakinta gaba tace toh ni ban iya bama wani abinci a baki ba, "sai a naki bakin ko, ya ƙarasa faɗar maganar". Murmushi tayi tace uhmmm, "sai yace toh daga yau zaki fara kuma kullum a baki zaki dinga bani.
Kallonshi tayi har tana ɗan bubbuga kafarta dake sarƙe cikin nashi tace toh nifa ban iya ba, "murmushi yayi yace hmmm zaki iya ne ai ya faɗa haɗe da miƙewa tsaye ya isa wurin kujerar ta, "ta bayanta ya tsaya ya saƙalo hannuwan shi saman kafaɗunta ya saita bakin shi daidai kunnenta yace baby yaushe zamu maimaita ne ya ƙarashe maganar haɗe da shafo nashanunta??
""""Yi tayi kamar bata fahimce shi ba tace mene?? Shi kuma yasan sarai ta gane kawai jan magana ne sai yace toh bari in nuna maki ko, ya faɗa yana murmushin ƙeta. Aiko tayi saurin girgiza kanta, tace a'a nagane, dan tasan baƙar azabar datasha jiya kuma bata buƙatar sake jinta.
Ajiyar zuciya ya sauke ya koma mazaunin shi haɗe da janyota saman cinyar sa yace bari in koya maki yadda zaki dinga ciyar da mijinki. Ita dai komi batace ba sai gani tayi ya ɗebo abinci a spoon yafara bata, ba musu ta ƙarɓa.
Bayan ya bata spoon ɗaya ne ya juyota tana fuskantar shi yace saura ni, "cike da kunya ita ma ta bashi, haka sukayi tayi tana bashi yana bata and dsame time suna hirar su ta soyayya.
"After three weeks"
Abubuwa da dama sun faru, Abdulrahman ya koma bakin aikin shi waton lecturing sedai kullum taka tsantsan yake da Amatu dan bayason ta fahimci wani abu dan shekaran jiya saura kaɗan ta gano shi dan mantawa yayi ya fito palour yana waya yana cewa shi bazai samu damar attending lecture.... Bai ida faɗa ba sai ya hangeta tafe, "aiko da sauri ya katse kiran. Shiyasa yanzu daya zo da takardun shi ɗakin shi yake kaiwa yasa cikin drower ya kulle, ko aiki zaiyi sai ya faketa yakeyi, "wani sa'in kuma sai tayi bacci yakeyi".
A ɓangaren soyayyar su kuwa sai abunda ya ƙaru, "kullum cikin kula da junan su suke, babu maison ɓata ma wani rai. Abdulrahman hatta da aikin gida indai yana nan tare sukeyi. Duk wani abu da amatullahi takeso shi yakeyi, ko kaɗan baya son ganin ɓacin ranta, inda itama hakane, duk wani hakki nashi bata taɓa tauye mashi, "a taƙaice dai zaune suke cikin zaman amana da kwanciyar hankali kullum suna liƙe da juna kamar cingum zuwa office ne kawai ke rabasu. Wannan tattalin da tarairayar da shagwaɓar da abdulrahman ke nuna wa amatu ba ƙaramin tasiri yayi a jikinta ba dan yanzu ta koma tamkar ƴar autar mata, "duk wata hanya ta shagwaɓa da kissa da kisisina babu wanda bata sani ba.
Aikuwa kullum cikin rarrashinta yake, "da zarar yayi mata abu kaɗan zata sa masa kuka, hatta da fita zaiyi kuka take sa mishi wai bata son ya fita ya barta ita kaɗai shi kuma haka zaiyi ta lallashinta harya samu yai mata wayo ya fita.
''''''Yanzu abunda ma ke damun sa shine yadda gabaɗaya ta sauya, batason yana kusantar ta, "hatta da turare yasa cewa take ya daina sawa bata so, "ko abinci ba kowani iri takeci ba a yanxu, "sai kayan maƙu lashe wanda sune suka zama abincinta.
Ɓangaren ameera da abdul suma hakance ta kasance dan kuwa kullum cikin kyautatawa junan su sukeyi, kuma soyayyar su ƙaruwa kawai take.
,,,,,Kamar kullum, zaune suke suna hira Amatu na saman cinyar abdulrahman, dan yanzu indai suna tare nan ne mazaunin ta, "wani film suke kallo suna hira akan film ɗin. Sai wayar amatu tayi ringing, dubawa tayi taga mummy ce ke kiranta, da murmushi a fuskarta ta amsa kiran tana cewa "hello"
Daga can ɓangaren mummy ta amsa mata, bayan sun gaisa ne, mummy ke faɗa mata ai daddy yace su shirya ita da Ameerah ran monday zasu fara zuwa school, Cike da jindaɗi ko katse wayar batayi ba ta fice a guje, "daidai lokacin data isa bakin ƙofar part ɗin ameerah yayi daidai da lokacin da Abdulraheemk ke shirin fitowa cikin shirin su na likitoci, "harya sa hannu zai murɗa handle ɗin ƙofar sai ya tuna daya manta da wani abu.
Sakin ƙofar yayi ya haura sama har yana ɗan haɗawa da gudu, ameerah dake bayanshi kuma ko ƙala batace ba dan yadda taga yanayinsa yasa ta gane cewar yayi mantuwa ne. Zaman ta keda wuya amatu tayi knocking, nan ta tashi taje ta buɗe ƙofar lokacin amatu na tsaye riƙe da waya a hannunta. Murmushi suka sakarwa junan su amatu tace besty monday zamu fara zuwa school.
"""Ameera tayi mata wani kallon up and down haɗe da yatsine fuska tace toh wa zaki faɗawa? Nida har ma na kira daddy nayi mashi godiyar kyautar motar daya bamu kuma Abdul yace cikin weekend ɗinnan zai fara koya mun mota. Amatu ta waro ido cike da mamaki tace mota? Yaushe? Wallahi jiya kuwa ina sa ran ma yau za'a kawo su harda naki. Amatullahi ta daka tsalle tana dariya tace wayyo Allah daddy, Allah ya saka maka da alkhairi, "ameera ta amsa ameen".
Abdulrahman daya biyo sahun amatu dan yaga abunda takewa murna, yayi saurin ƙarasowa wurinta ya riƙeta, yace baby miye haka? Ko so kike ki zubar mun da ajiya ta ne?? Sheƙeƙe take kallonsa ga kuma ƙunyar ameerah dataji sai ta kawar da zancen tace Abdul daddy ne ya siya mana mota nida ameerah kuma monday zamu fara zuwa school shiyasa nake jindaɗi.
Dan murna kam ya tayasu sedai tunanin shi ɗaya yadda ƴan mazan jami'a zasu dinga kalle mishi mata, ga kuma cu ɗanya tsakanin maza da mata, take yaji wani irin kishinta ya dabaibaye masa zuciya kuma a take ya yanke hukuncin da zai ɗauka.......
Murmushi yayi yace gaskiya na tayaku murna Allah ya sanya alkhairi kuma Allah ya baku sa'a, duk suka amsa da ameen. Nan amatu ta koma part ɗinta ita da abdulrahman, ameerah kuma ɗaki ta wuce dan taga abunda ya tsayar da abdul dan kome ya manta yaci ace ya ɗauko shi.
[3/8, 8:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''