Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
jindadin amincewar abba. Wayar shi ya dauko ya fita sai part din ammie, da shigarsa hanan taje da gudu ta rungume shi tana kukan shagwaba wai yaje wurin Amatu be fada mata ba.
Murmushi yayi yace my hanan kukan me kikeyi haka. Dan hararar sa tayi tace ba kai bane kaje wurin aunty Amatu baka fada mun ba. Waro ido yayi yace injiwa? Tana dariya tace inji ammie mana bakai ka fada mata ba.
Ammie dake shigowa cikin palo tace ke yar nan yaushe nace yaje wurinta nida nace miki yaje wani wuri? Dariya Abdul yayi yace toh dai ammie fada mata ni babu wata da nake zuwa wurin ta. Kura mishi ido hanan tayi tace aunty Amatu fah ko ita wurin ta ba wuri bane??
Dan shafo keyar shi yayi yaje wurin ammie ya zaune gami da dora kanshi saman cinyarta. Aikuwa kamar jira take ya hau tayi magana tace laaa dagani karka karyani ban shirya ba. Cikin sigar shagwaba yace ammie waton kinfi son hanan fiye dani ko? Toh miji ma zan samo mata ayi mata aure kowa ma ya huta.
A million hanan ta dauko piloluwa guda biyu ta jefeshi dasu duk kuma a lokaci daya tace Allah yaya ban is aure ba sai na girma kuma kuma....Sai hawaye shar ta fada jikin ammie tace cewa ni ammie bazanyi aure ba ina nan tare dake kuma ji yaya ma daya fini girma sau goma ba'ace za'ayi mishi aure ba sai ni toh wallahi sai na fadawa Abba idan ya dawo.
Kyalkyalewa yayi da dariya ita kuma taci gaba da kuka ammie kuma tasa bakinta tace baby na rabu dashi ai kwanan nan zamu koreshi duk ya cika mana gida da kashi. Dariya hanan tasa harda rike ciki. Aikuwa ya taso zaiyo cikinta ya bugeta ammie ta dakatar dashi.
Bata rai yayi ya ficewarsa daga palon ma baki daya. Part dinshi ya shiga ya watsa ruwa kafin ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta.
Bangaren amatu kuma kwance take tana jiran kiranshi ga wani matsiyacin bacci da takeji dan yau tayi aiki da yawa kuma yanxu idan ya kira bai sameta ba ya hau wani shan kanshi shiyasa ta dauko wani littafi tana karantawa saboda hasken waya da daddare bacci yake sata shiyasa ma batayi yunkurin dauka wayar ba.
Babu dadewa ya kirata daman jira take babu wani jan naji ta dauka. Cikin sassanyar muryarshi yace baby na ya kike? A hankali tace yadda kake. Murmushi yayi yace kinsan yadda nake neh kuma kinsan yadda nakeji neh? Girgiza kai tayi kamar yana kallonta tace a'a. Dan jim kafin yace toh kinason kiji yadda nake? Saurin amsa da eh tayi.
Yace baby na lafiya kalau nake kamar yadda kike amma kuma soyayyar ki tayi mun illah ta hanani sukuni banaji bana gani indai akan soyayyar ki neh. AMATULLAH sonda nake maki baya misaltuwa bana samun nutsuwa idan har ban saurari muryarki ba kuma ki sani bazan iya rayuwa batare dake ba.
Shuru tayi bata ceh komai sai wani abu da takeji yana mata yawo a jiki wanda ita kanta bazata iya fadin ko menene ba. Ganin shurun yayi yawa neh sai yace baby ina jinki nima ki fadamun yadda kikeji game da soyayyata. Aikuwa kashe wayar tayi dan batasan abunda da zata fada ba duk cewar itama tana jin wasu feelings a kanshi.
Zaro wayar yayi daga kunnen shi yaga ta kashe sai ya fara kiranta amma bata dauka ba. Zai kara kira kenan yaga sakonta ya shigo. Karantawa yayi yana murmushi ya rungume wayar a kirjin shi a haka bacci barawo ya sace shi. Itama haka da tunanin shi tayi bacci.
Washe gari tunda safe ta shirya zata shago sai wasu kawayenta na makaranta sukazo sunzo kawo invitation na auren daya daga cikin su mai suna maryam. Nan ta zauna sunata hira saboda an dade ba'a hadu ba. Kuma basu suka wuce ba sai da yamma.
Dan haka suna fita itama ta wuce shago kuma dake ameerah ta tafi shiyasa kai tsaye ta nupi shagon.
Bayan ta shiga neh suka fara gaisawa da mutanen dake cikin shagon. Ameerah tace Amatu sai yanzu kinsa mutane sai faman jiranki suke tayi, wata ma cewa tayi a fada miki sai gobe zatazo tunda bakya nan. Murmushi amatu tayi tace toh ayi afuwa gashi nan dai na iso yanzu waye akan layi.
Wata cutomanta me suna hajiya Aisha tace amatu nice mana bakiga ma kujerar dana zauna ba? Murmushi Amatu tayi tace mummy kiyi hakuri na bata miki lokaci wallahi wani uzuri neh ya kamani.
Murmushi hajiya Aisha tayi tace ai babu komai yanxu dai mu fara naga yamma tayi. Amsawa da toh tayi sannan ta kashe wayarta saboda kar Abdul ya kirata danshi ko aiki yakeyi haka yake kiranta suna hira kuma idan tayi magana yaga laifinta yace bata sonshi shiyasa bata damuwa ko bataji muryar shi ba.
Nan ta fara da ita sunayi suna hira dan sun saba sosai shiyasa ma take kiranta da mummy kuma ba karamin dadi hajiya Aisha keji ba, dan tana matukar son yaro mai girmama na gaba dashi. Basu dade sunayi ba suka gama saboda ba wani abu me yawa akayi mata ba kawai wanke mata kai akayi da stretching.
Bayan ta gama mata neh sai ga wata yarinya ta shigo wai ana sallama da amatu. Sai da gabanta ya fadi dan tasan Abdul neh haka yake idan ya kira wayarta a kashe sai yazo yagani ko lafiya ta kashe wayarta.
Hajiya Aisha kuma zaune take tana kiran number driver amma switch off shiyasa kawai ta fara kiran number Abdul yazo ya mayar da ita gida.
Daidai lokacin da amatu ta isa wurin shi wayar shi ta fara kara, dubawa yayi yaga ammie ce ke kiranshi sai yayi saurin dagawa. Daga cikin wayar naji ana cewa Abdul idan baka aikin komai kazo ka mayar dani gida na kira number musa ban sameshi ba.
Har ga Allah beji dadin katse hirar su da ammie zatayi ba amma saboda ganin girma da darajar mahaifiya yace ammie kina wani wuri neh??
Ina maitama federal housing kusa da maitama store zakaga wani saloon a bakin titin nan nake. Amsawa yayi da toh kafin ya katse wayan. Kallon wurin da ammie tayi mishi kwatance yayi yaga ai shagon amatu take nupi.
Ras gabanshi ya fadi dan bayason ammie ta fahimci wani abu tsakanin shi da amatu danshi yaso yakai mata ita har gida dasu hadu saman hanya, kuma ma akwai kunya tunda yanxu idan ta fito ta tarar dasu me zasu ceh?
Amatu kuma satar kallon Abdul take a ranta tana cewa toh ko lafiya naga dazu yana murmushi yanzu kuma kamar me tunani. Ji tayi yace ki koma cikin shago anjima zan dawo ammie ce ta kirani. Zatayi magana ya daga mata hannu alamar ta tafi kawai.
Juyawa tayi zata koma daidai kuma lokacin ammie ta fito..................
Yawan comment yawan typing๐
[2/8, 8:57 PM] Lashminzy๐: ๐ซ๐๐ซ๐๐ซ๐๐ซ
*RUDANI*
๐ซ๐๐ซ๐๐ซ๐
Story & written by
Lashminzy
๐ฅGรLDรร"S WRรTรRS
รSSรรรรTรรร๐ฅ
Masoyana gsky babu kamar yau dan naji dadin comments dinku sosai, ina yinku irin ehh dinnan ku biyoni muci gaba da gashi
Muje zuwa
Page 19-20
Ammie na fitowa taci karo da amatu Wanda daga gani ko ba'a fada maka ba kasan daga wurin Abdul take. Amatu kuma zuwa tayi ta karbi jakanta tace mummy har kin fito kenan? Murmushi ammie tayi tace eh ga dana ma can ku gaisa.
"Gaban Amatu neh yake dukan tara tara tana mamakin daman Abdul yaron mummy neh? "Katse ta ammie tayi da cewa tau amatu sai wani lokacin. "Itakuma ta lula duniyar tunanin sai da ammie tayi magana kafin ta tuno da cewar bata gaida Abdul ba kuma harya shige mota" Sallama tayi wa ammie ta koma shagon.
''Ammie kuma suna cikin mota take tambayar shi ko yasan amatu neh? Cikin rashin gaskiya yace am daman nazo neh sai na ganta shine nake tambayar ta ko kina ciki. Murmushi ammie tayi danta gano karya yakeyi sai tace owk ai na dauka akwai wani abu a tsakanin ku ne.
Saurin girgiza kanshi yayi yace a'a ammie babu komai fah. Satar kallonshi ammie tayi taga kamar me wani nazari sai can tace gaskiya son yarinyar nan ta shiga raina ina ma ace zaka sota. "Jan burki yayi wanda sai da ammie ta danji tsoro tace Abdul miye haka? Ko dan nace haka shine zaka nemi ka shekeni"
''Dariya yayi harda dafe kai yace sorry ammie na ba haka bane kawai dai banyi zaton zaki ce haka bane. "Hmmm tau Abdul nidai gaskiya tayi mun dan tana da kirki sosai kuma kaga Har yanzu baka kawon yarinyar danaji kuna magana kaida hanan ba. Plsss son ka nemo mata kayi aure nima in samu yan jikoki na"
Murmushi yayi yace karki damu ammie nah kiban nan da sati daya zan baki mamaki.
Tau Allah ya kaimu son.
*******
Bayan ta koma shago jan ameerah tayi suka koma gefe "cikin rada tace ke kinsam wani abu kuwa? Kallon ameerah tayi tace a'a sai kin fada. "Hmmm Ashe mummy itace mahaifiyar abdul bansani ba. Dan waro ido ameerah tayi tace wai da gaske kina nupin abdul dinki dan gidan hajiya Aisha neh?? Kwarai mai kuwa gaskiya nidai naji dadi" zan samu suruka mai mutunci.
"Murmushi ameerah tayi tace gaskiya nima naji maki dadi Allah ya sanya alkhairi muma Allah yasa mu a sawun ku. Amsawa da ameen Amatu tayi kafin suka koma sukaci gaba da aikin su"
Kusan magariba suka bar shagon suka nupi gida. Direct gidansu suka nupa, "bayan sun shiga ciki neh suka gaida mummy sannan sukayi sallah suka fita. Gidan aunty hajara suka shiga.
Da shigar su aunty hajara dake wasa da danta mubaraka tace yauwa daman ku nake jira. Dazu abban mubarak yake fada mun wai an fara registration din JAMB shine nace sai ku shirya ku tafi ko zuwa gobe ne ko?
Tau aunty nima dazu wata ta fada mun aza nayi karya ma takeyi shiyasa ban fadawa ameera ba amma yanxu zan fadawa daddy idan na koma gida.
Dake ameerah ma tayi bataci ba shiyasa ma ta dawo gidan aunty hajara da zama " fatan samun nasara sukayi wa junan su kafin suka nemi wuri suka zauna.
Amatu kam kitchen ta shiga dan jin yadda cikinta ke kugi kuma sai da mummy tace su tsaya suci abinci sukace a koshe suke. Kulolin dake kitchen din ta fara budewa tana dubawa ko zata ga abinci amma bataga komai ba. Nan ta fito ta wuce dinning inda ta tarar da best food dinta wato jollop din cous cous. Kamshi neh kawai ke tashi gashi yasha kayan lambu.
''aikuwa nan ta zauna tanawa ameerah gwalo dake ameerah batacin kifi kuma ansa kifi a ciki. Aunty hajara ko goyon bayan amatu take tana cewa "my amatu kici iya cinki sai kin koshi" Murmushi amatu tayi tace andai bar wata a baya. Shuru ameerah tayi mata dan tasan da ita takeyi.
Tashi ma ameerah tayi ta sulala indomie, daidai lokacin kuma amatu harta gama cin abinci tana shirin zuga gida. Tsayar da ita ameerah tayi tace taje tayi sallah kafin ta gama cin abinci sai ta rakata.
Nan ta wuce daki tayi sallar isha'i kafin tayi wa aunty hajara sallama suka fita. Wayarta ceh ta hau ruri, tana dubawa taga Abdul ne ke kiranta. Sai da taja aji kafin ta amsa kiran. "Cikin zazzakar muryar shi yace baby gani nan kofar gidanku kiyi sauri plsss akwai inda zani.
Katse wayar tayi tana murmushi sannan tace my meerah ki koma gida ga Abdul can yazo. Harara ameerah ta banka mata tace to ina ruwana nidai har gida zan rakaki. Amatu dai batace komai ba sukaci gaba da tafiya. Bayan sun iso neh ameerah ta gaishe shi kafin ta koma gida.
Ita kuma amatu tsaye tayi tana kallonshi kamar yadda shima kallon nata yakeyi. Kusan minti uku suka kwashe suna aikawa junan su sakon soyayya ta cikin ido daga bisani kuma yace my baby me matar nan tace miki dazu? Duk da ta gane wacce yake magana a kanta sai ta basar tace wace mata kenan??
Ina nupin wadda nakai gida dazu mana! Ohh ai sai kace mun mummy dan nafi ganewa ta haka. Murmushi yayi a ranshi yana cewa lallai sun saba da juna tunda naji tana ce mata mummy " amma a fili sai yace ina jinki me tace miki??
Dan murmusawa Amatu tayi tace kawai cewa tayi ga danta nan in gaida shi shine kaina ya kulle a lokacin bakaga banko gaishe ka ba? Murmushi yayi yace owk yayi kyau daman ita ta aikoni tace wai inzo in nemeki.
Kallonshi tayi tace ni din? Eh mana kinsan fa batasan kece amatun danake fada mata ba ni kuma sai nayi mata wayo irin namu na yan zamani nace mata karta damu zan bada surprise a cikin satin nan. "murmushi amatu tayi naji dadi wanda sai da dimpul dinta suka lotsa tace naji dadi sosai my Abdul amma wane irin surprise zaka bata?
"Hmmm ke zankai a matsayin surprise din nasan zataji dadi sosai idan kuma tace ina waccen amatun sai ince zabin mahaifiyata nakeso kinga zatayi farinciki da hakan"
Murmushi amatu tayi na jindadi tace Allah sarki ammie (kamar yadda taji yace) tana sonka sosai nima gaskiya ina sonta saboda tana sona kuma naji dadi da zan zama surukarta fatana Allah ya kara mana son junan mu? "Amsawa da ameen yayi kafin ya bude motar shi ya miko mata wata leda yace gashi daga dan gidan ammien shi.
Hararar wasa tayi mishi tana dariya tace hmmm wai dan gidan ammien shi toh nikuma fa?
Hmmm kema yar'ta ceh ai kuma... Sai ga daddy yayi horn a bakin kofar gidan.
Sai da daddy ya shiga kafin ya kalli amatu yace muje na gaida daddy nah. Bata ce komai ba suka shiga cikin gidan inda suka tarar da daddy har yayi pakin ya fito daga cikin mota.
Karasawa yayi shi kadai dan amatu ta shige gida. Gaisawa sukayi har daddy ke fada mashi ai ya hadu da abban shi kuma yaso suyi magana saboda babu lokaci yace sai gobe zai zo har gida suyi maganar.
Abdul ba karamin dadi yaji ba yace toh daddy nagode Allah ya saka da alkhairi ni natafi." Sallama sukayi wa juna kafin daddy ya shige cikin gida Abdul kuma ya wuce.
Bayan daddy ya shiga ciki yaci abinci ya huta sai yasa mummy ta kira masa amatu dan akwai maganar da yakeson yayi da ita.
Babu bata lokaci sai ga mummy tazo tare da amatu. Kallon daddynta tayi taga yadda ya nutsu yana kallonta alamar maganar nada mahimmanci kenan.
Amatullah yaron nan dake zuwa wurinki kina sonshi?? Cikin jin kunya tace eh daddy. " tau masha Allah gobe za'a zo neman aurenki ina fatan kin amince dashi dan kinsan duk abunda kikeso shi nakeso bazan yi maki dole ba.
Dan sunna da kanta kasa tayi tace daddy na amince. Tau naji dadi sosai Allah ya tabbatar da alkhairi, "amsawa da ameen sukayi dukansu har da mummy dan itama tana son abunda yar'ta keso.
*********
Bayan kwana biyar, kwance yake yana waya da ita sai faman zuba love sukeyi. Duk wani kalaman soyayya sun sanshi, wani kalamin ma kai kace basu suka fada ba.
Suna cikin hirar neh yace mata ta shirya gobe zai zo ya kaita ta gaida ammie. Cikin farinciki ta amsa masa da toh sannan sukaci gaba da hira.
Yana gama waya da ita kiran abban shi ya shigo. Katsewa yayi ya nupi part din abba inda ya tarar dashi yana cin abinci.
Gaida shi yayi kafin ya samu wuri kusa dashi ya zaune yace..............
Muje zuwa๐๐ฟ
[2/9, 10:36 AM] Lashminzy๐: ๐ซ๐๐ซ๐๐ซ๐๐ซ
*RUDANI*
๐ซ๐๐ซ๐๐ซ๐
Story & written by
Lashminzy
๐ฅGรLDรร"S WRรTรRS
รSSรรรรTรรร๐ฅ
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 21-22
Gaida shi yayi kafin ya samu wuri kusa dashi ya zauna yace abba gani. Kallonshi Abba yayi sannan ya rufe abincin da yakeci yasha ruwa sannan yayi hamdala.
Maida dubanshi yayi ga Abdul yace yauwa son daman maganar ka ce kuma an tsayar da magana dan kwana hudu da suka wuce naje mun tattauna da aminina Muhammad kuma ya amince da batun ka sai dai yace da sharadin zaka bari taci gaba da makaranta kuma nace mashi wannan ba matsala bane ina fatan ka amince??
Eh Abba na amince.
Tau tau yayi kyau sai ka fara shirye dan mun tsayar da lokaci nan da wata uku. Murmushi neh ya bayayyana a fuskar Abdul yace Allah ya nuna mana lokacin "amsawa da ameen abba yayi
Tashi yayi zai fita sai kuma ya dawo yace Abba ka fadawa ammie neh? "Girgiza kai Abba yayi alamar a'a" sai Abdul yace owk plsss Abba karka fada mata ka bari sai gobe da daddare."murmushi kawai Abba yayi batare da yace komai ba.
Fita yayi ya koma part dinshi ya kwanta dan dare yayi kuma ya kira Amatu bata dauka ba dan yana son ya tambayeta ko meyasa bata fada mishi ansa lokacin auren su ba" sai wata zuciyar shi tace kila itama bata sani ba.
"Wata duniyar tunani ya lula yana ayyana irin rayuwar da zasuyi shi da amatu.
Niko nace Allah ya nuna mana lokaci musha biki๐
Washe gari tunda safe ya shirya zuwa asibiti dan ana neman shi da gaggawa shiyasa bayan ya shirya part din ammie ya shiga ya gaisheta sannan ya shige motar sa ya tafi.
Bayan ya isa neh ya tarar da wasu mutane guda biyar wanda sukayi accident a daren jiya" abun dai ba'a cewa komai dan sunji ciwo sosai amma babu wanda ya rasu.
Cikin tausayawa Abdul yace ya fara fada meyasa baza'ayi treaating dinsu ba har sai yazo? Nan yaci gaba da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba.
Sai daya gama fadan neh yasa aka kaisu wani special room, nan ya fara basu agajin gaggawa shida wasu nurses din. Bayan sun gama neh suka fita suka basu wuri dan anyi musu allurar bacci.
Wani dan dattijo ne ya shigo office din abdul da kukan shi da komai yana rokon Abdul akan Dan Allah ya taimake shi karya bari su mutu. Kallonshi Abdul yayi yace baba kayi hakuri insha Allah zasu samu sauki amma kai miye hadin ka dasu??
Cikin muryar kuka yace wallahi dukan su yarana neh sai dana ceh karsu dawo su bari a yau amma sukaki yanzu kaga kaddarar data riske su ko??
Lallashin shi Abdul ya shiga yi yana bashi baki akan yayi hakuri nan bada dadewa ba zasu warke. Wata takarda ya mika mashi wacce ke dauke da sunayen magunguna yace yaje siyo ya kawo. Karban takarda dattijon yayi ya fice yana sharar kwalla.
Abdul zugum yayi