Chapter 8 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 27

21K to 24K   out of 79.1K words

lemi yayi "Cikin magiya daddy yace haba Alhaji wallahi dana yana iya mutuwa a kan akan haka kuma fah kasani a dalilin sonda yake wa yar'ka ne fa har samu wannan ciwon, "plsss kayi hakuri na roke ka da girman Allah ka daga auren nan har zuwa wani lokaci.

Jikin Alhaji lemi ne yayi sanyi dan Allah yayi shi da tausayi, kallon daddy yayi fuska cike da damuwa dan har ga Allah beso fasa wannan auren ba, yace Alhaji na amince zan daga wannan auren har sai danka yaji sauki.

Wani irin farinciki ne ya ziyarci daddy har besan sadda ya rungume Alhaji lemi ba yana murmushi.
Ko hira basu tsaya yi ba daddy yayi mishi sallama dan zai koma asibiti yaga lafiyar danshi sannan kuma ya fada mashi wannan albishir din.

Lokacin da daddy ya isa asibiti har Abdulrahman ya  dawo hayyacin shi, amma fah kuka yakeyi sosai, likita kuma saida yayi ta ma mummy fada akan su dinga kiyaye bacin ranshi idan ba haka ba zasu iya rasa shi.

Bayan likita ya fita mummy sai rarrashin shi take, suna cikin haka sai ga daddy ya shigo da fara'a fuskarshi. Tunda mummy taga yanayin daddy ta tabbatar da sun samu nasara. Karasowa daddy yayi ya zauna kusa dashi ya dafa shi yace son ka kwantar da hankalinka wannan auren an fasa shi.

Waro ido yayi yana murmushi yace daddy da gaske kakeyi?? Dukan wasa daddy yakai mishi yace toh da ina wasa dakai neh??

Murmushi yayi ya rungume pillow. Mummy ma taji dadin haka harda darinyan ta ta fara tsokanar shi.

Bayan daddy ya fita, Alhaji lemi ya kira number mummy yace ta sameshi a palon baki yanzu yanzu.

Bada dadewa ba sai gata tazo, wuri ya nuna mata da hannun shi yace ta zauna.

Cikin yanayi na babu wasa yace rukayyatu ina son ki kasa kunnuwanki ki saurareni dakyau kuma kiyi aiki da basirar da Allah ya baki ki fahimceni "kina jina??

Cikin fargaba tace eh eh alhaji ina ji.

To wannan auren na Amatullahi na daga shi saboda wani dalili nawa.

A firgice ta mike tsaye tace Alhaji saboda me zaka daga wannan auren?? Duba fa kaga yadda gidan nan ya cika da mutane?? Me kakeson na fada musu?? Haba Alhaji ka canza tunani Dan Allah.

Cikin fada fada yace rukayyatu ba nace ki fahimceni ina da dalilin yin hakan ba? Dan haka ba shawara na tambaye ki ba umarni nake baki a matsayina na mijinki kije ki sanarwa bakin gidan nan an dage wannan auren har zuwa wani lokaci.

Amsawa tayi da toh sannan ta fita, da sauri ta nupi part dinta, dakinta ta shiga ta zauna tayi tagumi hawaye na zuba a fuskarta, kanwarta salma ce ta shigo dakin, ganin mummy na kuka da sauri ta karasa wurinta ta ta dafata tace aunty meya faru kike kuka haka??

Cikin muryar kuka tace salma an daga auren Amatullahi har zuwa wani lokaci! Cikin zaro ido salma tace injiwa yace miki haka??

Inji me gidan ta fada a takaice.

Tagumi salma tayi tana dan tasan wannan ba karamin kalubale bane, dan yadda ma zasu tunkari bakin dake cikin gidan nan ma aiki ne. Cikin lallashi salma tace kiyi hakuri Allah ne bai kaddari za'ayi wannan auren jibi ba dan haka sai mu dauki kaddara kuma yanzu zanje na fara  sanar ma mutane.

Nan ta fita ta nupi dakin su Amatullahi inda suke ta hira ita da kawayenta, kallonta salma tayi taga fuskar nan tata cike take da annashuwa ga kuma kawayenta da wasu tun fara biki suka dawo gidan da zama.

Karasa shigowa tayi, ta tsaya a jikin wardrobe murya a sanyaye tace Amatullahi mummy na kiran ki amma kije tare da ameerah, nan suka tashi suka fita, salma kuma dakyar ta bude baki ta fada musu an daga auren.

Aikuwa nan aka fara cece kuce ana Allah yasa shi yafi zama alkhairi

Amatullahi kuwa tunda taga yanayin mummy tasan wani abu ya faru ga kuma aunty hajara dake zaune kusa da mummy da itama din yanayin ta ya sauya.

Aunty hajara ce ta jawo hannun amatu ta zauna kusa da ita tace my amatu  dole mummy ta shiga wani hali amma dan Allah ke idan kikaji karki dauki abun da zafi, komai da kikaga gani mukaddari ne daga Allah dan haka ki dauki kaddara kinji ko??

Amsawa tayi da toh sannan aunty hajara tace daddyn ki ya daga bikin har zuwa wani lokaci.

Amatullahi abun tausayi ko hawaye batayi ba tace Allah yasa shi yafi zama alkhairi. Suka amsa da ameen

Cikin zuciyarta kuwa Allah ne kadai yasan irin damuwar data shiga amma daurewa kawai tayi saboda karta tada hankalinta ta kuma tada na mummy. Karasawa tayi kusa da mummynta tace mummy shine kike kuka?? Plsss ki daina kuka mu rungumi kaddara ai nasan ba karamin abu bane yasa da daddy ya daga wannan auren ba kuma mummy ai ba abun tada hankali bane tunda ba fasawa akayi ba dagawa akayi.

Rungume ta mummy tayi tace Allah yayi miki albarka Amatullahi Insha Allah kina tare da cigaba a rayuwar ki.

Ameerah kuma tana gefe tarasa farinciki take ko bakinciki. tana cikin wannan tunanin Amatu taja hannunta suka fita daga dakin.

Suna fita sai ga mutane sun fara shigowa dakin mummy suna mata naje, wasu daman ba zuwan tsakani da Allah sukayi ba wasu ko harga Allah basuji dadi ba. Nan wa'yanda ke kusa suka fara shirye-shiryen tafiya wanda ke nesa kuma sai gobe dan yanzu yamma ta gabato.

Haka Amatu ta tarar da kawayen ta suna shirin tafiya wasu kuma sai gobe, nan ta sallame su suka wuce, masu kidin kwaryar da aka gayyata suma an fada musu an daga bikin, hatta da malamar da zatayi wa'azi ranar daurin aure an fada mata an dage bikin.

Zuwa wasu yan mintoci har an fara watsewa ba tare da wani fada ba amma fa masu bakinciki suna nan suna na zuci.

A bangaren daddy kuma yanzu ya isa gidan Abba, amma basu tsaya maganar ba sai da sukayi sallar magariba dan yana isa ana kiran sallah. Bayan sun dawo daga masallaci part din abba suka nupa.

Bayan sun zauna ne ya kwashe komai tun daga zuwan daddyn Abdul na farko zuwa na biyu ya fada mashi.

Abba beji dadin daga auren da za'ayi ba amma tunda yaji dalilin haka sai  yace toh babu komai Allah yasa shi yafi zama alkhairi a garesu kuma ma yace zasuje asibiti dubiyar Abdulrahman.

Nan suka dan taba hira kadan daga bisani kuma ya wuce.

Abdulraheem kuma yana wani wuri inda zai kama hall din da za'ayi dinner sai ga abba ya kirashi, nan ya tafi ba tare da bata lokaci ba dan besan kiran da Abba keyi mashi ba.

A part dinshi ya sameshi tare da ammie, da yanzu yake fadamata, haka nan taji babu dadi amma ya ta iya dole tayi hakuri. Shi kuma uban gayya yana zuwa ya wani fada jikin ammie yana shagwabe mata, a ranta tace hmmm yaro yaro ne da kasan abunda za'a fada maka da baka kwanto jikina kana shagwaba ba.

Abba ne ya dubeshi yace Abdulraheem an dan samu wata matsala wanda a dalilin hakan yasa aka daga bikin ka har zuwa wani lokaci.

Tashin hankali ba'a sa mashi rana😟

A firgice ya taso daga jikin mummy murya na rawa yace.......................



Plsss share
[2/15, 8:17 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

May Allah honour your knees when you bow in prayer and recognize your voice when you call upon Him,may you receive response from Him each time you asked.May the peace,blessing and mercies of Almighty Allah be upon you and your entire family. ᎪᎷᎬᎬΝ...
JႮᎷᎷᎪ'ᎪͲ ᎷႮᏴᎪᎡᎪᏦ

     Page 37-38

Abba...sab..boda me za'a daga bikin nan?? Abba yace Abdul bani nace a daga ba mahaifin yarinyar ne yace a daga kuma shima ba haka kawai ya daga ba yana da dalili.

Batare da wani boye-boye ba Abba ya fayyace mishi komai, Abdulraheem kam wani haushi ne ya kamashi  yace Abba yanxu akan wanann abun za'a daga aurena?? Abba yace Abdulraheem dan Allah kayi hakuri, insha Allah komai zai daidai ta.

Yanzu abunda nakeso dakai shine kaje ka huta Kuma banace kaje kayi ta sake sake bane ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai wuce kaji ko??

Amsawa yayi da toh kafin ya tashi ya fita.

Dakinshi ya nufa, da shigar sa ya fada saman gado, yana tunanin maganganun Abba da yace saboda wani za'a daga bikinshi. Nan take yanayin shi ya sauya, fuskar shi ta koma kalar ja, idanunwanshi kamar garwashi suka koma saboda bacin rai.

Wata irin zazzafar iska ya feso yace wallahi sai naga ko waye yake nema ya rabani da masoyiyata. Kuma ma idan har yana tunanin wannan ciwon nashi zaisa in hakura da Amatullahi toh ya farka dan mafarki yakeyi.

Shi waye? A ina yake? Na rantse da Allah bazan taba bar maka ita ba, yadda kakejin zaka iya mutuwa akan sonta nima haka zan iya bada rayuwata saboda ita.

Wani dogon tsuki yaja, ya zaro wayar shi daga cikin aljihu ya kira number ta akashe,. Wurgi yayi da wayar saman gado saboda haushi, "yana tunanin idan ya kirata zaiji dan sanyi a ranshi sai gashi tama kara bata mashi rai ta kashe wayar.

Tashi yayi ya gyara kwanciyar sa yana mai jin bakin cikin faruwar wannan al'amarin, shi matsalar shi daya ma kar ace an fasa auren gabadaya saboda bakin mutumin nan da kuwa ya shiga cikin tashin hankali.

Juye-juye kawai yake tayi saman gado yana surutu shi kadai kamar wani zautacce, wayar shi ce ta hau kuka amma saboda baya cikin jin dadi sai ya kashe wayar baki daya ba tare da yasan wanda ke kira ba.

Saboda tsananin bacin rai ko kayan jikinshi be cire balle ma yayi tunanin wanka, haka bacci ya sace shi da niyar gobe zaije gidan su Amatu.

Ammie kuma tana gaban Abba tana mashi mita akan cewa an tauye wa Abdulraheem "har a cewar ta wai bataga amfanin daga bikin da akayi ba tunda ko yaji sauki auren ba fasa shi za'ayi ba.

Abba hakuri kawai yake bata yana cewa ta yadda da kaddara.

Washe gari da misalin karfe goma sha daya na safe Abdulraheem yaje gidansu Amatu, koda megadi ya ganshi sai da hanjin shi suka kada, Abdul kuma beko bi ta kanshi ba ya paka motar shi bayan ya bude masa gate.

Be jima da zuwa ba sai gata nan ta iso, kura ma juna ido sukayi, sai yaga ita kamar ma bata damu da daga bikin nan da akayi ba. Itakuma sai gani tayi duk idanuwan shi sun fada kuma ga fuskar shi ta nuna yana cikin damuwa.

Kawar da idanunta tayi daga kallonshi ta gaishe shi, cikin dan sakin fuska ya amsa mata. Sai yace baby kinji abunda ya faru ko??

Eh wallahi jiya da daddare daddy keyi mun bayani "amma ni na shiga cikin ᎡႮᎠᎪΝᏆ fah saboda a iya sani na babu wani wanda nake soyayya dashi bayan kai amma daddy yace wai nima nace masa ina sonsa ji fa? Anya ba rabamu akeson yi ba?

Kallonta yayi yace baby makiya sunyi mana yawa na tabbata bakin ciki kawai yakeyi dan yaga mun dace shine ya biyo ta wannan hanyar dan ya rabamu toh wallahi yayi karya, "Abdul ya karasa maganar a dan tsawace.

Amatu tace my Abdul toh wai ma waye wannan yake son shiga tsakani na dakai neh?? Shuru yayi na yan muntuna yana yan sake-sake. Haka itama tunani takeyi, ita dai tasan babu wani wanda take soyayya dashi bayan Abdul dan ita shaf ma ta mance da wancan Abdul din dan har yanzu a tunanin ta shine Abdul dinta tun na farko shiyasa bata kawo komai a ranta ba.

" haka shima beyi wannan tunanin ba dan ko lokacin data nuna shine Abdul dinta ba yadda yayi ba saboda a iya sanin shi shi kadai ammie ta haifa kuma be taba jin tace su biyu bane ko wani abu makamancin haka ba.

Abdulraheem ne ya dawo daga duniyar tunanin daya fada yace baby ki kwantar da hankalinki idan har yayi nasara wurin ganin an daga bikin nan toh ya sani auren nan kamar an daura shine da izinin Allah kuma yau dinnan ba gobe ba zanbi abbana asibiti inga ko waye shi dan yanxu haka yana can asibiti yana ciwon zuciyar karya.

Baby na shirya abubuwa da dama, na tanadi abubuwa masu tarin yawa, na tsara yadda bikin mu zai kasance amma wannan bakin azzalumin bawan Allah ya ruguza mana "toh ta Allah ba tashi ba.

Amatullahi ko shuru tayi dan tana jinsa yana fadan shi, sai daya gama kafin ya dan yi kasa da muryar shi yace sorry na dameki da fada ko? Kiyi hakuri wallahi ina tsananin sonki da kishin ki ne shiyasa.

Dan murmushi tayi batace komai ba sai yace baby zan tafi anjima zamuyi waya kinji?

Amsawa tayi da toh shi kuma yayi mata sallama ya wuce.

Ya fita kenan sai ga merry, da titi, da bola (ma'aikatan saloon dinta) sunzo, ko cikin palour bata kai ba ta tsinkayo muryar titi, dan kuwa titi muryar ta sama-sama take kamar na namiji, har gwanda ma in tana yarensu muryar tafi dadi.

Iso tayi musu suka zauna a nan palour suna mata jaje dan sunji labarin a daga bikin ta. Daga nan suka fara hira sai ga ameerah ta fito daga dakin amatu, daman tana ciki.

Zuwa tayi suka gaisa itama ta zauna ana hira da ita. Sai kusan la'asar suka ansa makullin shago suka wuce, daman tun lokacin da aka fara events din Amatu tasa aka rufe shagon tace kowa yaje hutu,. Toh shine yanxu da aka daga bikin sukazo ansa makullin dan suci gaba da aiki kafin Amatu ta dawo.

Bayan sun wuce ne sai ga daddyn Amatullahi ya fito, nan yake fada musu zaije ganin Mara lafiya waton Abdulrahman.

Gidan su Abdulraheem ya nupa dan tare zasuje, Abdulraheem ma yace zaije amma shi da biyu zaije dan yanason yaga ko waye, dan haka shike driving har suka iso asibitin.

Da suka shiga ne ake sanar musu yanzu aka sallame su. Basuyi wata-wata ba daddy ya kira abban Abdulrahman ya fada mashi gasu sun iso asibiti wai an sallame su.

Nan daddy ya fara basu hakuri kuma yayi musu kwatancen gidan shi.

Basu sha wahala ba suka gano gidan dan gidan beda wuyar ganuwa. Koda suka shigo gidan Umar ne yazo yayi musu jagora zuwa part din Abdulrahman dan can aka kaishi amma shi hankalinshi bekai ga ganin Abdulraheem ba.

Bayan sun shiga ne idon Abdulraheem ya sarke cikin idon Abdulrahman, cikin tsantsar tsoro da mamaki ya shiga ja da baya yana nuna Abdulrahman da shima ya mike tsaye yana nuna Abdulraheem.

Nan yan dakin suka juyo suna ganin ikon Allah, Abba yace wai mafarki nake gani ko gizo?

Daddyn Amatullahi yace wai kuna ganin abunda nake gani kuwa??

Daddyn Abdulrahman da mummy kam kwata-kwata basu mamaki domin kuwa sunsan wata rana hakan zata iya faruwa.

Abdulraheem ya kalli abban shi yace abba kana ganin abunda nake gani kuwa?? Abba yace eh Abdul ina gani amma na shiga cikin ᎡႮᎠᎪΝᏆ dan ina bukatar a fitar dani daga cikin wannan ᎡႮᎠᎪΝᏆΝ

Abdulrahman ya kalli daddyn shi yace daddy daman mu yan biyu neh??? Kowa ya zuba ido yana kallon daddy yaji abunda zai fada sai daddy ya.......................




Plss comments
And share




Plss comments
And share
[2/15, 6:16 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

```vote me on wattpad @lashminzy```



Page 39-40

sai daddy yace tabbas ku yan biyu ne ya bashi amsa,

Kallon kallo suka shigayi a tsakanin su. abdulraheem kuma mamaki yakeyi yana cewa toh idan su yan biyu ne meyasa aka rabasu kuma ma abun tambayar anan itace be taba jin wani ko wata tace su yan biyu bane.

Anya kuwa badai kawai kamanceceniya bace.... sai ya tsinkayo muryar daddy na cewa eh kwarai ku yan biyu ne kuma ni na haifu dukan ku.

Kowa zaro ido yayi yana kallon daddyn abdulrahman. mummy kuma bataji dadin faruwar wannan lamarin ba dan gani take da zarar mahaifiyar su tazo tana iya tafiya dasu duka ita kuma ta shaku da abdulrahman bazata iya rabuwa dashi ba.

Abba ne ya kalli daddy yace daman kaine mahaifin abdulraheem?? girgiza kai daddy yayi yace eh nine, wallahi sai yanzu nake danasanin raba ya'ya na danayi dan gaskiya na hakince su amma koda yake bani kadai keda laifi ba harda sa hannun mahaifiyar su tunda ita ta tilasta mun na rabu da ita.

abba yace kana nupin aisha tana da hannu wurin raba yaran nan?? daddy yace wace aisha kenan? abba yace mahaifiyar abdulraheem mana. Cikin mamaki yace kana nupin aisha na raye?

Abba yace eh tana raye, nan ya yaro wayar shi yayi dialing number ammie yayi mata kwatance inda yake yace tayi sauri ta iso, babu wani bata lokaci ammie ta shirya ta fito, yan mintoci kalilan sai gata a cikin harabar gidan ita da musa danshi yayi driving dinta.

Tana nan tsaye sai ga umar nan yazo ya gaisheta sannan yayi mata jagora zuwa inda suke. koda ammie ta shiga gabanta ne yayi mummunar faduwa sakamakon abunda ta gani. Karasawa gaban abdulrahman dake tsaye kamar gunki ta dafashi hawaye na zuba a idanunta tace dana daman kana raye......

Abba ya katse da cewa daman abdulraheem yan biyu neh baki sanar dani ba?? juyowarta keda wuya zatayi magana da abba idanunta suka sarke cikin na daddyn abdulrahman.

Ja da baya ta farayi tana nuna shi da dan yatsa, cikin rawar murya tace Aliyu da..man. kan..a raye?? shuru yayi mata dan shima tambayar da zeyi mata kenan ta riga shi.

Alhaji lemi ne yayi magana yace dan Allah ku fitar damu daga cikin wannan ʀuɗɑɳiɳ. sai daddy yace alhaji mun tafka babban kuskure wallahi, amma ba'a son ranmu hakan ta faru ba kuma dalilin raba ya'yan mu da mukayi shine....

Shekarun baya da suka wuce aisha mata ta ce ina sonta tana sona dan auren soyayya mukayi, amma duk dangina basa kaunarta, mahaifiyata ce kawai ke sonta a cikin gidanmu sai kuma Allah ya dauki ranta.

Bayan rasuwar tane yan uwana suka dinga musgunawa aisha, duk wani abu da zaisa ta farinciki sai sun ruguza shi haka duk wani hanya da zasubi dansu sakata cikin kunci sai sun bi. Daman mahaifiyata

8 / 27