Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
ya rasu?? Ta ƙarasa maganar kamar zatayi kuka. "Cikin tausaya mata Ameerah tace besty ba mutuwa akayi ba, mune nan ta faɗi tana nuna kanta dasu Abdul, Amatu duk ta rikice sun sata cikin RUƊANI tace kune me? Me kuka aikata?? dan Allah ameerah ki faɗa mun idan su bazasu faɗa mun ba plssss na roƙeki, ta ƙarasa maganar a yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta, wanda ba ƙaramin zafi Abdulrahman yakeji ba aduk lokacin da hawayen nata ya zuba.
"Cikin dakewa da dauriya Abdulrahman yace Amatullahi dan Allah ki yafe mana abunda muka aikata miki, kinji dan Allah, wallahi duk abunda muka aikata bawai munyi ne da niyar cutar dake ba sai dan ceto rayuwata da ɗan uwana yayi. "Cikin zaro ido tace kamar ya nifa bangane ba kunsani a cikin duhu fah, plssss ku fito fili ku faɗamun yadda zan fahimta.
Tsoro ne sosai ya shiga jikin Ameeerah dan gani take kamar idan amatu taji wannan lamarin shikenan zata cire ta daga matsayin ƙawarta zuwa maciya amana. kuka ne ya kufce mata da danasanin amincewa datayi ta auri wanda ƙawarta keso. Abdul kuwa yama rasa ta ina zai fara gashi amatu sai faman roƙonsu take dasu faɗa mata, "yace da kinsan abunda zamu faɗa maki da bakiso zama a wurinnan ba ya faɗi can ƙasan zuciyar shi.
Tashi tayi ta duƙa gaban Abdulrahman ta riƙe hannuwan shi duka biyu tace plsss mijina idan su bazasu iya faɗamun ba kai ka taimaka ka faɗamun kaji?? Shuru yayi mata ayayin da yakejin zuciyar shi na wani irin suya dan a gaskiya bazai iya kallon ƙwayar idonta yace mata ga abunda ya aikata mata ba. Cike da ɓacin rai dajin haushin su dukansu ta miƙe zata bar palon, abdul ya tsayar da ita, be tsaya wata-wata ba ""yace Amatullahi BANI ABDULRAHEEM KIKE AURE BA ABDULRAHMAN KIKE AUREEE...
Hmmmmm rikici kenan, readers wai ya kuke tunanin Amatu zatayi? Shin zata ɗauki ƙaddara ko bazata ɗauka ba?? Wani matsayi zata aje ƙawarta Ameerah data auri wanda takeso???
Hmmmm duk ku biyoni dan jin yadda lamarin zai kasance
[3/17, 8:56 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 97-98
"A firgice ta juyo cikin wani irin yanayi ta fara pointing ɗin Abdulraheem gami da sakin wani ɗan guntun murmushi tana girgiza kai tace plssss ya Abdulrahman (tana magana ne da Abdulraheem) ka daina banason irin wannan wasan plsss. "Ameera da duk hawaye ya cika mata fuska daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta datayi mata nauyi ta ƙaraso wurin Amatu ta dafata, tace besty wallahi ba wasa bane abunda Abdulraheem ya faɗa gaskiya ne, "cikin rikicewa tace Ameerah harda ke cikin wannan mafarkin? Dan Allah ki watsa mun in farka daga wannan mummunan mafarkin, ta ƙarasa maganar da ƙwalla taf a idonta.
"Cikin dauriya da jarumtaka, Abdulrahman ya ɗago idanunwanshi da suka canza launi zuwa ja kamar gwarwashi ya watsa su akan Amatu kan ya kira sunanta cikin murya mai ban tausayi yace Amatullahi ba mafarki kike ba dan Allah ki buɗe idonki ki kalle mu ki kuma fahimce mu da basirar da Allah ya baki kinji ma.......Girgiza kai ta farayi tana ja da baya, "Wai da gaske ba mafarki nakeyi ba? Na shiga uku ni Amatullahi wani irin RUƊANI ne ya shige ni wanda yasa na kasa banbance ku? Wallahi kun cuceni kunci amanata, ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya, da sauri Ameerah ta ƙaraso wurinta da niyar dafata, Amatu ta dakatar da ita ta kalleta ido cikin ido tace wallahi kin bani mamaki, yanzu harda ke za'a haɗa baki a cuceni? Ameerah kinfi kowa sanin yadda nakeson Abdulraheem amma har kika yarda sheɗan yaci galaba akanki kika auri masoyina?? Ameerah wai kece kuwa wacce nasani mai son farincikina? Wacce ko abu tagani tanaso idan na nuna inaso take barmun?
"Amatullahi dan Allah kiyi haƙuri munsan bamu kyauta ba amma dan Allah ki sauraremu kiji abunda zamu faɗa maki, Abdulraheem ya faɗa cikin marairaicewa, "Cike da ɓacin rai da kuma jin haushin kalamanshi cikin faɗa da gunjin kuka tace ashe duk sonda kake mun na banza ne? Abdul me zaka faɗamun? Kana tunanin akwai wasu kalamai ne da zakayi amfani dasu wurin fahimtar dani ne?? Ɗan guntun murmushi ta saki wanda yafu kuka ciwo tace "kunyi amfani da damar ku na zama ƴan biyu kun cutar dani, wallahi Allah sai ya sakamun, ta ƙarasa faɗar maganar a yayinda hawaye ke zubo mata.
Sharewa tayi, ta juya wurin Abdulrahman dake zaune kamar wani gunki tace kai kuma maye natacce burinka ya cika ka aureni amma kasani daga rana irin ta yau niba matarka bace dan wallahi sai ka sakeni idan ba haka ba kotu ce zata rabani dakai kuma wannan ƙazantar tana magana tana pointing ɗin ɗan ƙaramin cikin dake jikinta, daka ƙunsamun wanda acikin rashin sani hakan ta faru toh ka ɗauka tamkar ba'ayi shi bane dan yau ba gobe ba zan zubar shi. "Tana faɗar haka bata ko jira amsar su ba ta haura sama da gudu.
Gabaɗayan su daskarewa sukayi a wurin, Abdulrahman ya tashi da niyar yabi bayan ta Abdulraheem ya dakatar dashi, Ameerah naganin haka itama ta haura sama a guje dan batasan abunda Amatu zatayi ba dan yadda taga ta haura sama kamar wacce zata tashi sama, "daidai bakin ƙofar ɗakin sukaci karo, kafin Ameerah tace wani abu Amatu ta bangajeta ta sauka ƙasa. "Ko kallon inda su Abdul batayi ba ta fice daga palon.
"A tsorace Abdulrahman ya tashi ya fito waje jin ƙarar tashin mota, sedai kafin ya iso harta wuce amatsiyacin gudu wanda indai ba ikon Allah ba daƙyar ta iya kai gida lafiya. Da sauri ya koma palon ya ɗauko makullin mota danya take mata baya, Abdulraheem ya dakatar shi yace karka bita, Abdulrahman ya banko mashi wata uwar hararara cike dajin takaici yace what are u saying? Matata na cikin wannan yanayin zan barta a haka?, idan na rasata fa?? Iyeee kodan ba matarka bace?? Tsuki yaja haɗe dayin kwafa ya nupi parking space, ba ɓata lokaci ya tayar da motar ya fice a guje.
"Abdul ka sakeni wallahi bazan iya zama dakai Amatu na cikin wannan halin ba, plsss ka sauwwaƙe mun kaje ka auri Amat....bata ƙarasa ba sakamakon marin daya yayi mata cikin ƙunar rai yace kina da hankali kuwa? Dame zanji ne wai? Ko Kin taɓa ganin yaya ya saki mata ƙani ya aura alhalin yayan na nan da ranshi? Gabaɗaya duk a rikice take danko maganar da take faɗi batasan tayi ba, kuka ta fashe dashi ta shige part ɗinsu ta ɗauko gyalenta ta nupi hanyar fita, da sauri ya sha gabanta yace ina zaki? Cikin ko in kula tace gida zani, agadarance yace babu inda zaki.
Kallon uku saura ta aika mashi sannan tace wallahi sai naje ƙafarka ko ƙafata? tana faɗar haka ta raɓa ta gefenshi ta wuce, aikuwa kamar leda haka ya fincikota yace Ameerah dani kike musayan yawu? nine fah mijinki Abdulraheem? Cike dajin zafin riƙon dayayi mata tace me kake nupi? Me kake tunani? Yanzu baka tuanin halin da Amatu zata shiga? Baka duba girman laifin da muka aikata mata ne? Kodan baka damu da halin da ɗan uwanka zai shiga bane shine ni zaka hanani zuwa ganin halin da ƴar uwata zata shiga? Abdul miye ke damun ƙwaƙwalwarka ne? Mu muka aikata mata laifi ba ita bafa?
"Shuru yayi duk jikinshi yayi sanyi, sai kawai ya juya batare dayace mata komai ba ya shige gida, ya ɗauko makullin mota ya fito, lokacin har ameerah ta wuce, da sauri ya tayar da motar ya fita waje, yana tafiya yana waige-waige ko zai ganta, cikin sa'a kuwa ya ganta zata shiga taxi, da sauri ya fito ya ƙaraso wurinta yace plss my Ameerah kiyi haƙuri muje in kaiki duk inda zaki wallahi da gaske nake, jin yayi rantsuwa ne yasa ta bawa mai taxin haƙuri sannan tabi bayan shi suka shiga mota suka wuce.
"""Tuƙi take harna fitar hankali, bata ji bata gani kawai da sunan tana tuƙin ne amma bata san inda take saita kan motar ba, duk inda ta gitta sai an bita da kallo, wasu ko sai zagi suke ɗura mata suna cewa wannan mahaukacin direba dan yadda take tsala gudu babu mai gani yace macece ke tuƙin.
Gudu take sosai harta kawo daidai traffic light dake ba cikin hayyacinta take ba yasa bata lura ba tawuce da gudu sai ji kake ƙiiiii................
Share
[3/27, 10:08 PM] +234 816 787 6616: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
```vote me on wattpad @lashminzy```
Page 99-100
"""Sai ji kake ƙiiiiiiii taja wani irin wawan burgi wanda duk da irin burkin data ja saida motar ta bugi paul (pal waya) ɗin kafin ta tsaya, da sauri mutanen dake kan titin suka taso sukayi gaggawar zuwa inda take, kowa abun mamaki yake bashi ganin macece, "wasu ko marasa imanin tsuki kawai sukeyi su wuce abun su, "mashi imanin kuma tsayawa sukayi suna mata barka dan basu ɗauka abun zai tsaya a iya haka ba. Wasu ƴan matasa ne guda biyar, maza uku mata biyu, suka iso wurin, ɗaya daga cikinsu me suna fauziya, a ɗan rikice ta juyo tana kallon ƴan uwanta tace wannan ba Amatullahi bace matar Dr Abdulraheem? Ta faɗa tana pointing ɗin Amatu data daskare a wurin ta kasa ko magana.
Babban yayansu yace ƙwarai kuwa itace amma meya faru da ita hakane? Fauziya tace yaya abunda ya faru da ita ba shine ya kamata mu sani ba, taimakonta ya kamata muyi dan naga kamar bata cikin hayyacinta, ummi yayar fauziya tace Eh wallahi yaya mu taimaketa kasan fah muma mijinta shine wanda ya ceto rayuwarmu dan haka muma mu taimaka mata. Daga nan suka kutsa cikin mutanen suka iso gabanta, fauziya ta kamata tace aunty sannu, kowa ya maida kallon shi zuwa garesu, cikin mutanen dake wurin wani yace ke malama lafiya? Ummi tace ƴar uwarmu ce gida zamu kaita. Cikin rashin yadda mutumin ya tambayi Amatu, duk da cewar bata ganesu ba amma taga kamar ta taɓa ganin su a wani wuri sai kawai ta girgiza kai alamun tasan su.
"Daga nan kowa ya fara watsewa, daman kuma bataji ciwo ba illah gaban motar ta data lotsa da kuma ƙwayaƙwan motar duk sun dagargaje. Jan hannunta fauziya tayi takaita cikin motar su, sannan ummi da babban yayan su suka shiga, motar Amatu kuma sauran maza biyun ne suka shiga, basu zarce ko'ina ba sai gidan su Amatu, da shigar su Amatu ta fita daga motar a guje ta shige palon su inda ta tarar da mummy na cin abinci, da sauri mummy ta ajiye plate ɗin abincin tayo kan Amatu cikin rikicewa take tambayarta lafiya ta ganta a haka? Kuka ta fashe dashi ta faɗa jikin mummy tana cewa wallahi mummy sun cuceni.
"'"""Mummy ta ɗago kanta tace Amatu su waye suka cuceki? Mummy daman ba Abdulraheem nake aure ba? Mummy tace kamar ya ban fahimceki ba? Kuka ta fashe dashi tace mummy ina nupin ba Abdulraheem ne mijina ba Abdulrahman ne mijina!!!
"Tsaki mummy taja tace inji wani mahaukacin? Toh ƙarya ne kawai dai ana son a shiga tsakanin ku ne amma wannan ba gaskiya bane, "wasu hawaye masu zafi suƙa zubo mata tace mummy ba jinayi a waje ba su dakansu suka faɗa mun, nan ta kwashe komai ta faɗamata. kuma mummy wai harda Ameerah aka haɗa baki aka cuceni? Mummy yanzu kin taɓa tunanin Ameerah zata iya auran wanda nakeso? Innalillahi wa'inna ilaihirraj'iun kawai mummy ke maimaitawa sannan ta kalleta tace yanzu maganar nan da kike faɗamun gaskiya ne?Amatu ta girgiza kai alamar eh.
"Hmmmm lallai biri yayi kama da wando,,, waton sunyi amfani da damar su ta kamanceceniyar su sukaci amanar mu ko?Toh kwantar da hankalinki wallahi dani suke zancen mummy ta faɗa ayayin da take shafa bayan Amatu. Tana cikin shafata ne idonta yakai ga su fauziya, sakin Amatu tayi ta kallesu tace sannun ku dan sai yanzu ta lura dasu duk kuwa irin gaishetan da suka dingayi amma ina hankalinta naga kan ƴarta.
Gaisheta suka ƙarayi ta amsa haɗe da sakar musu fuska, su kuma ganin gidan ba lafiya ba yasa basu tsaya wani dogon zance ba suka wuce akan nan da kwana biyu zasu dawo, mummy ta amsa da toh sannan suka wuce, "wurin Amatu ta koma ta zauna tana facing ɗinta tace daughter wannan kukan da suka saki nayi maki alƙawarin suma sai sun zubar da fiye dashi.
Su fauziya na fita sukaci karo da Abdulrahman a farfajiyar gidan, ya ƙurawa motar Amatu data lanƙwashe ido, fitowar su fauziya ya dawo dashi cikin hayyacin shi, cikin tsoro da wani irin murɗawan ciki yake binsu da kallo dan duk a tunanin shi ƴan gaisuwa ne 🙈😂 su kuma dake basu san cewar Abdulraheem ɗin ƴan biyu bane sai fauziya ta ƙarasa wurin shi tace Dr Abdul ina wuni, suma duk suka gaishe shi amma shuru bai amsa su ba sai ma wuce su dayayi ya shige cikin gida.
"Da kallo suka bishi harya shige cikin palon, fauziya tace wannan gidan kam ba lafiya yake ba, ummi tace ina lafiya kuwa mudai mu wuce gida kar baba yace mun daɗe, ɗan autan su yace toh da dai yafi, amma nifa nan da kwana biyu sai na dawo inji takamaiman abunda ya faru, sai babban yayan su yace kai wallahi wurin jin ƙwaƙwafinka zaka malgaya lokacinka baiyi ba, dukan su suka sa dariya gami da shige wa mota.
""Abdulrahman na shiga palour ƙamshin turaren shi ya daki hancinta,,, ɗagowa tayi ta kalleshi tun daga kan ƴan yatsun ƙafar shi har zuwa kan fuskar shi, sai tayi saurin tashi tsaye tace karka kuskura ka shigo mana gida, "mummy dake fitowa daga ɗaki tayi saurin ƙarasowa wurin Amatu ta zaunar da ita sannan ta kalli Abdulrahman da jiyake kamar yayi kuka ko zasu saurareshi, tace waton kai mara kunya ko? Duk abunda kukayi kaida ɗan uwanka bai isheka ba sai kun biyota har gida kun ƙarasata ko, toh ta Allah ba taku ba, kuma bari kaji kamar yadda ta faɗa wannan cikin dake jikinta sai nasa an cire shi saboda nasan shiya baka ƙarfin gwiwar zuwa har cikin gidan nan...
Ƙara takowa yayi zuwa cikin palon cikin ɗaga murya mummy tace auww sai ka shigo kenan? Toh ka shigo tunda gidan kune?tana faɗin haka ya dakata haɗe da duƙawa cikin marairaicewa yace mummy dan Allah ki taimakeni kiyi haƙuri Wallahi ba da gangan muka aikata ba dan Allah ki saurareni kiji.
Cikin faɗa mummy ta katse shi" ka fita nace ko? Tashi yayi sum-sum ya wuce batare daya sake koda juyowa ba, "yana fita yaci karo dasu Ameerah, Ameerah kam ko kallon shi batayi ba ta shige cikin palour.
""Abdulraheem kam tunda yaga yanayin Abdulrahman yasan ba lafiya ba,,, ƙarasowa kusa dashi yayi yace ɗan uwa dan Allah kayi haƙuri insha Allah komai zai dawo normal, yana faɗar haka yasa kai zai shige cikin palon Abdulrahman ya riƙo hannun shi, cak ya tsaya haɗe da juyowa sai Abdulrahman ya juya mashi kai alamar karya shiga."Batare daya ce wani abu yaja hannun shi suka nupi wurin mota, take suka tayar da mota suka bar gidan.........
"Ameerah na shiga palon sai kuma ta dakata saboda ji datayi ƙafafunta sunyi mata nauyi a ɗaya ɓangaren zuciyarta ko tunani take da wani ido zata kalli mummy? Hawaye ne sukaci gaba da zubo mata, mummy kuwa tana ganinta tayi saurin isa wurinta, ta rungumeta tana cewa yi shuru Ameerah, Ameerah kuwa sai ƙara kuka take tana cewa mummy Amatu, plsss kic...tabarrr.. fushid...dani kinji, tayi maganar ne cikin shasheƙa sabida kukan dayaci ƙarfinta.
Cikin lallashi mummy ta zaunar da ita ta ɗauki wayarta ta kira number aunty hajara, tace mata tazo yanxu-yanzu, tana faɗar haka ta katse kiran taci gaba da lallashin Ameerah.
Amatu kam tunda taji Ameerah na kuka sosai ta shige ɗaki dan bazata iya jurar ganinta tana kuka haka ba........
Share
[3/27, 10:08 PM] +234 816 787 6616: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
```vote me on wattpad @lashminzy```
Masoyana dan Allah kuyi hkr da rashin jina da kukayi kwn biyu, wlh schl ne ya ɓoyeni. But never forget, one heart ❤
Page 101-102
"Ko minti biyar ba'ayi ba sai ga aunty hajara tazo, sallamar datayi a iya laɓɓanta kawai suka tsaya saboda halin da taga Ameerah ita tama ɗauka ko mijin nata ne ya rasu,,,, ƙarasa shigowa tayi ta samu wuri ta zauna saman kujerar dake facing ɗinsu, cikin son taji abunda ke faruwa tace mummy lafiya? Mummy tace ina kuwa lafiya, ta zayyana mata duk abunda ke faruwa, aikuwa a hasale aunty ta taso tayo kan Ameerah tana huci kamar wata zakanya, cikin canjin murya tace ""Ameerah kina da hankali kuwa? Me suka rageki dashi da zaki cucesu? Ko kin manta Amatullahi ƙawarki ce da zaki auri wanda takeso???
"Wallahi kin ban kunya,,,, Ameerah miye bayin Allahn nan basuyi mana ba,,, amma kirasa hanyar da zaki saka musu da ita sai wannan? "Toh wallahi umma zan kira in faɗamata abunda kikayi, ta ƙarasa maganar a yayinda take matsar wayarta. Da sauri Ameerah ta isa gabanta ta rusuna haɗe da riƙe mata ƙafafuwa tana bata haƙuri,,, mummy ta taso tazo wurinsu ta janye Ameerah dake duƙe a gaban aunty hajara tana bata haƙuri, cikin bada umarni mummy tace hajara kada ki kuskura ki kirata, kuma ko ba yanxu ba banason kowa yaji wannan maganar.
Dake ta ɗauki mummy a matsayin ƴar uwarta, dan kam mummy tayi mata abubuwa da dama kuma koba komai tana gaba da ita shiyasa takejin nauyin ta musa mata, sai kawai ta ajiye wayar kamar tayi kuka haka takeji,,, sedai kota kansu batabi ba ta wuce ɗakin Amatu.
Cikin ko'in kula da halin da aunty hajara ke ciki