Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
taja hannun Ameerah zuwa ɗakinta.
""""""""Su Abdulraheem na fita direct gidansu mummy suka nupa, dan sun san halin ammie balle datayi musu kashedin akan idan daga baya komai ya kwaɓe musu karsu kuskura suzo wurinta, dan sai datace karsuyi haka amma sukaƙi ji. Bayan sun isa palon mummy suka shiga daidai tana fitowa daga kitchen, tana ganin su tayi saurin Zuwa wurinsu, cikin rikicewa tace Abdul meya sameku na ganku haka? shuru dukansu sukayi sai da suka kusan kwashe minti biyar babu wanda yayi magana cikinsu, harta juya zata wuce Abdulraheem yayi ƙarfin halin cewa mummy tamu ta ƙare.
Duk da damuwar data tsinci kanta sai dataji kamar tayi dariya saboda maganar dariya ta bata, amma tana juyowa sai ta mayar da fuskarta fuskar tausayi tace ya akayi ne, Abdul yace mummy zauna, ba musu ta samu wuri ta zauna, Abulrahman kuwa jiyake kamar wurin bazai iya ɗaukar shi ba saboda tsananin damuwar datayi mashi yawa, fita kawai yayi batare dayace musu ƙala ba. Dukansu kallonshi sukayi harya fita, sedai fitar shi keda wuya suka jiyo tarin shi, a ruɗe suka fito waje Abdul ya riƙeshi haɗe da fesa mashi iskan bakinshi daga kanshi zuwa goshin shi wanda a hankali tarin ya fara tsayawa, cikin galabaita haɗe da dafe zuciyar shi yana nishi kaɗan kaɗan yace mummy, Abdul mutuwa zanyi dan Allah kuje ku bata haƙuri kuce karta zubar mun da ajiyata, yana faɗar haka ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya fara tari babu sassauci wanda harya fara fitar da baƙin jini.
"Cikin hanzari Abdul da mummy suka kamashi suka sashi a mota, Abdul ya wuce dasu asibitin su, mummy sai hawaye takeyi tana sharewa wasu na zubowa har suka iso asibitin, suna isa Abdul yayi saurin fitowa yaje ya kira wasu likitoci guda biyu, ciki harda usman, ba ɓata lokaci aka kaishi emergency room, taimakon gaggawa suka bashi, daƙyar aka samu tarin ya tsaya, sannan sukayi mashi allurar bacci haɗe da ɗora mashi drip, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon agaba dashi.
Abdulraheem na fitowa mummy ta tareshi, cikin tsantsar damuwa tace Abdul ya yake, saboda ya kwantar mata da hankali dan yaga duk a rikice take, yaja hannunta suka shiga ɗakin, ganin Abdulrahman a kwance yasata saki ajiyar zuciya da hamdala, zama tayi gefen gadon tana kallonshi, Abdulraheem kuma ya fita dan akwai wasu magungunan da yake son ya ɗorashi akai shine yakeson yaje ya siyo.
"Bayan Abdul ya dawo ne mummy ta tashi zataje gida ta girko mashi abinci saboda samha na gidansu hanan dan ta mayar da gidan tamkar gidansu, da ita zatace ta dafo mashi abinci. Abdul yace toh sannan mummy ta fice.
Da musalin ƙarfe shida na yamma mummy ta dawo, lokacin Abdulrahman harya farka sedai damuwar dake kwance a zuciyar shi yasa ya lumshe ido kamar mai yin bacci, yana sauraron hirar mummy da Abdul, wanda duk akan abunda ya faru ne. Mummy tace su kwantar da hankalin su insha Allah da kanta zataje tayi magana da mummyn Amatu ta bata haƙuri a wuce wurin.
Abdulrahman ya ɗan buɗe idonshi kaɗan yace mummy Allah bazasu haƙura ba saboda harda korata fa sukayi kuma ni abunda ke damuna shine karsu zubar mun da ajiyata "wallahi mummy komai zai iya faruwa idan aka taɓa lafiyar matata da ajiyata.......Abdul dake gefen shi ya dafashi yace plssss calm down ɗan uwa komai zai wuce ka daina sa damuwa a ranka kaga abunda ya faru dakai yanzu ko? Shuru yayi ya jinginar da kanshi jikin gadon. Cike dajin tausayin shi mummy tace son tashi kaci abinci
"""""Shuru yayi mata wanda ko bai faɗamata ba tasan baida niyar ci dan hakanan halayyarshi take idan bayason abu kace yayi shuru yake maka,,, cikin lallashin shi ta samu yaci spoon biyar shima daƙyar danta bashi a baki ne yaci. "Bayan ya gamaci yasha magani sannan aka cire mashi drip danya ƙare. Bayan an cire ya shiga toilet ya ɗauro alawla sannan ya fara gabatar da sallar azahar da la'asar ɗin data wuce shi, yana idarwa aka kira magariba nan yayi harda ita ya zauna a wurin yana lazumi har akayi isha'i yayi ta, mummy tata sallar tayi daga gefe, Abdulraheem kuma masallacin dake cikin asibitin yaje yaje yabi jam'i.
Da misalin ƙarfe tara suka karɓi takardan sallama, dan Abdulrahman cewa yayi bazai kwana ba yaji sauƙi, mummy ta aza ko wasa yakeyi sai dataga yana shirin fita tukunna tasa aka karɓar musu takardan sallama suka wuce. Bayan sun isa gida mummy ta wuce part ɗinta Abdulraheem kuma part ɗin Abdulrahman ya wuce dan nan zai kwana saboda bazai iya kwana shi kaɗai a gida ba kuma ba abun yaje gidan ammie ba ta tisasa agaba da tambayoyi.
"Wanka Abdulraheem yayi yasa wata jallabiyar Abdulrahman ya kwanta haɗe da jawo wayar shi ya fara dialing number sedai wannan karon a kashe take saɓanin ɗazu da yayi ta kira ana rejecting, tsaki yaja ya tura wayar gefe yaja blanket, ya rufe jikinshi.
Abdulrahman shima kwance take ya kasa bacci sai kiran Amatu yake amma ba'a picking daga ƙarshe ma rejecting akayi aka kashe wayar baki ɗaya...
"""Duk ji yayi babu daɗi kuma daya rufe idonshi ita kaɗai yake gani tana mashi yawo, tashi yayi ya shiga toilet ya ɗauro alawla ya fara nafilfili, wanda bashi ya gama ba sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan Ya kwanta.
Ɓangaren su Amatu kuwa damuwace fal ranta wanda hakan ya hanata samun cikakke bacci ga kuma ciwon kan daya isheta wanda kukan datayi ne ɗazu ya jaza mata ciwon,,,,, haka ma Ameerah kuka kawai takeyi ƙasa-ƙasa dan ɗakin mummy take kuma mummy taja mata kunne akan kadata kuskura taji kukan ta kuma kukan yaƙi tsayawa shine takeyinsa a hankali.
A taƙaice dai wannan daren a daddafe suka ganshi harda aunty hajara da mummy, su ammie kuwa dasu samha kam basu kosan wainar da ake toyawa ba.
Bayan kwana biyu..........
share
🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
```vote me on wattpad @lashminzy```
Page 109-110
"Idonta dake kulle ta buɗesu a hankali jin ba'a ƙasa ta faɗi ba, kallonshi tayi ta wani yatsine fuska haɗe da cewa tnx ta zame jikinta daga nashi ta wuce palour,,,,hijabinta ta ɗauko batare data kalli inda yake ba ta haura sama. Shiko tsaye yayi kamar wani gunki yana kallonta harta ɓace wa ganinsa.
"Fasa shiga kitchen ɗin yayi ya haura sama ya shiga ɗakin shi ya sauya kaya zuwa jallabiya ya wuce masallaci, bayan ya dawo ne ya shiga kitchen ya ɗauko plate da cup ya hauro dasu sama, a bakin ƙofarta ya tsaya ya yafara bugawa a hankali, sedai har kusan minti biyar beji alamar mutum ba balle kuma yasa ran za'a buɗe dan ƙofar gamƙe take da makulli, maƙe kafaɗa yayi irin ko a jikin shi ɗinnan, ya shiga ɗaki, bada jimawa ba sai gashi ya fito da wani makulli a hannun shi.
"Soka ɗan makullin yayi ya buɗe yasa kai ya shige ɗakin sannan ya mayar ya rufe ya zare makullin yasa cikin aljihun jallabiyar shi, kayan dake hannun shi yakai saman ɗan center table ɗin dake tsakiyar ɗakin ya aje, sannan ya cire jallabiyar shi ya rage daga shi sai singlet da boxers, bakin ƙofar toilet ɗin ya isa yana jin yadda take wasa da ruwa wanda take yaji kamar ya shiga ya tayata, sedai beko gama tunanin da yake ba yaji motsin zata fito.
"Da sauri ya ɓuya bayan labule"
"Ita kuwa fitowa tayi da wani ɗan ƙaramin towel a jikinta wanda ko cinyarta bai gama rufewa ba, ƙarasawa tayi bakin madubi tana ɗan gwaggoge jikinta da wani ɗan karamin towel, sanin ita kaɗai ce a ɗakin yasa ta kwance towel ɗin ta gyara mashi zaman shi
"Aikuwa karaf idanun shi suka sauka a nashanun Amatu da suka ƙara cika kamar an hura baloons, kallon su da yayi ba ƙaramin tayar mashi da hankali sukayi ba, hakan yasa ya kasa daurewa kawai batare da yayi fargabar wani abu ba yaje ta bayanta ya rugumeta.
"Dake ta bashi baya tana kallon madubi dan shima ta cikin madubin ne ya kallesu. "A tsorace ta kurma ihu har towel ɗin dake jikin ya kwance ya faɗi ƙasa, Murmushi Abdulrahman yayi yace matsoraciya kawai toh nine mijinki, a ɗan zabure ta juyo suna facing juna cike da mamakin yadda akayi ya shigo mata ɗaki bayan tasan ta rufe harda makulli, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tayi saurin kallon direction ɗinda yake kallo, aikuwa taga jikinta yake bi da kallo ko ƙyaftawa bayayi.
Da sauri ta zame daga jikinta daga nashi taja towel ta ɗaura tana mai banka mashi hararar da beko san tanayi ba, dan zama yayi kamar wani gunki ya tsura mata ido har ta ɗaura towel ɗinta daya faɗi.
Wurin wardrope taje ta buɗe ta ɗauko wata night gown me shara-shara ƴar guntuwa da pant ta saka, ko brazier bata saba saboda yawan takura mata da takeyi, haka harta gama shiryawa yana tsaye yana kallon.
Niko nace kodai suma yayi mu yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo? 😂lolx
"Sai bayan ta gama shiryawa tazo zata fita taji ƙofar a rufe, murmushi yayi ya ƙaraso wurin ta yayi hugging ɗinta ta baya yace haba baby wannan irin rikitarwa haka ai sai a kwashi gawata, murmushi yaso ya suɓuce mata sai kanne ta wani ɓata rai ta juyo suna fuskantar juna tace ya Abdul leave me alone!
Duk da ya tsani amai tsawa amma saboda itace bai nuna komai ba sai ma Ƙara matseta dayayi ajikinshi har sai data saki ƴar ƙara yace saboda me zan ƙyaleki? Shuru tayi masa ta ƙwace kanta daga gareshi tace ka bani makulli na? Ya waro ido yace yaushe na ɗauki makullinki ni dana shigo ta sama! Kukan shagwaɓa tasa masa harda bubbuga ƙafa a ƙasa tana wani turjewa sai kace ƙaramin yaron da aka anshewa sweet😂
"Ni Allah ka bani makulli na? Tamke fuska yayi alamar babu wasa yace ina zaki je? Batayi wata gardama saboda irin yunwar da takeji tace am hungry zan shiga kitchen ne!
"Dariyar zuci yayi yaja hannunta zuwa wurin center table ya zaunar da ita a ƙasa, ya saukar da kayan ƙasa shima ya zauna haɗe da nannaɗe ƙafafun shi sannan ya buɗe ledar, kaza ce gasashiya da friedrice cikin take away da kuma hollandia yoghurt, zuba musu yayi cikin plate ya ƙara matsowa gap da ita yadda zaiji daɗin bata a baki.
"Ɗebowa yayi a spoon da niyar ya bata a baki ta kauce haɗe da rufe bakinta tana yatsine fuska cikin shagwaɓa tace ya Abdul plss ka matsar dashi a gaba na amai zanyi, ta ƙarasa faɗar maganar harda fiddo wasu ƙwallar ƙarya wanda daƙyar ta fakeshi ta matso su, cikin kulawa ya matsar da abincin a gabanta yace toh me kikeson kici, kinsan banason ki zauna da yunwa ko?
Toh, ni indomie nakeson naci kuma asa yaji da yawa, toh yace yana miƙewa saboda bayason duk wani abu dazai samu lafiyar matar da kuma babyn shi, yace bari inje in ɗauko key ɗin mota insiyo maki ko? Da sauri ta tashi tsaye tasa mashi kukan shagwaɓa, ni fa banason na waje kai nakeson ka dafa mun da kanka, ta faɗa haɗe da cuno ɗan ƙaramin bakinta mai bala'in burgeshi a duk lokacin da take shagwaɓa.
"Juyowa yayi wurinta suna fuskantar juna yace karki damu baby na farincikin ki o nawa dan haka duk abunda kike so shi za'ayi, just give me 15mins kawai, yana faɗa ya ciro makulli daga aljihun jallabiyar shi dake rataye jikin wardrope ya buɗe ya fita.
Yana fita taja tsuki haɗe da marin kanta tace oowoooo dama abunda baza'a iya samun shi kusa nace ba, wallahi na kwafsa, kwafa tayi ta haye saman gado ta kwanta tana jiran shi ya dawo, daga nan bacci yayi awon gaba da ita, wanda ba ita ta tashi ba sai lokacin data jita a jikin mutum, a hankali ta fara buɗe idonta har ta watsa su a kanshi, cike da jin bacci tace ya Abdul na ƙoshi fah.
Lallashinta ya farayi daƙyar kafin ya samu ta faraci, a hankali yake bata harta gama ci ya bata ruwa tasha sannan ya kwantar da ita saman gado, kwashe su plates ɗin yayi bayan ya cinye rogowar indomien data rage, su kaza kuwa yabar batun su saboda babyn shi bataci ba shima haka yaƙi ci yakai cikin fridge yasa dan karsu lalace.
Ɗakin ya dawo bayan ya kimtsa ko'ina, ya kashe ƙwan wutar ɗaki ya rage sai disco light dake haska ɗakin, can gefenta yaje ya kwanta a takure dan jiyake kamar yaje ya rungumeta sedai ganin yadda take wani sha mashi ƙanshi tana iya sai hankalin shi yakai ƙololuwar tashi ta hanashi aiwatar da abunda yakeso dan haka kawai yaja blanket yayi musu addu'a ya kwanta.
Washe gari...........
Share
[3/28, 6:52 PM] Lashminzy💞: AᏔᎬՏϴᎷᎬ ᏔᎡᏆͲᎬᎡ'Տ ᎪՏՏϴ...🏮
(Թαʆαɕε σƒ εXɕίtαtίση αηδ Թʆεαςαηt ϖɾίtεɾς)
💫🌞💫🌞💫🌞
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Տtơɾу Ꭺηɖ Ꮤɾίttεη Ᏼу
Ꮮasིhིmིiིnིzིyི
Page 111-112
"Washe gari"
Koda Amatu ta tashi rungume ta ganta a jikinshi wanda shi kanshi besan lokacin da yayi hakan ba, Karewa kyakyawar fuskar shi kallo tayi yadda yake bacci hankali kwance, a hankali yake fitar da numfashi, Cikin baccin shi yakejin kamar ana son akwace mashi wani abu, kara matseta yayi ya cigaba da baccin shi, itakuwa zuba mashi ido tayi taga yadda ya kara matsota jinkin shi.
Duba agogo dake makale a dakin tayi taga har lokacin sallar asuba ta wuce, da sauri ta zame jikinta daga nashi ta sauka saman gadon ta koma can gefen shi tasa lallausan hannunta ta fara bubbuga shi a hankali, Wata irin mika yayi hade da jawota jikin shi, a hankali ya bude eyes dinshi ya zuba mata, murmushi ya sakar mata yace baby har kin tashi? girgiza kai tayi alamar eh, Shi kuma wayan shi dake gefen shi ya duba yaga lokacin sallah ya wuce, da sauri ya dagata daga jikin shi ya sauka saman gadon gami da cewa baby shine baki tasheni naje masallaci ba?
Cikin dan shagwaba tace toh nima ai yanzu na tashi, kallonta kawai yayi batare da yace wani abu ba ya shiga toilet ya dauro alawla ya fito ya zura jallabiya ya wuce masallaci, ita kuma bayan ya fito ne ta shiga tayo alawla ta fito ta daura zani da dogon hijab ta tayar da sallah, bayan ta idar ne ta zauna tana karatun Al Qur'ani, ko daya dawo tana nan zaune tana karatu, shima gefenta yaje ya zauna ya jawo Qur'ani ya fara karantawa, basu suka tsaya ba sai da gari ya washe sosai sannan suka rufe Qur'anin.
"Tashi tayi zata nade daddumar yace ta barshi da zai nade, komi batace ba ta cire katon hijabin data saka ta kafin ta fita daga dakin. Shima fita yayi ya wuce nashi dakin saboda yayi wanka saboda yau akwai class din da zai ma lecture by 10am.
"Toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin riga da wando na yadi wanda suka matukar karbar jikinshi, turare ya feshe jikinshi dashi sannan ya bude side drowan dake gefen gadonshi ya dauko wasu takaddu yasa cikin jakar shi, "Sannan ya rataya jakar ya fito, dakinta ya leka bai ganta ba, kasa ya sauko ya sameta a palour tana jera mashi breakfast, gabadaya palon ya cika da kanshin arish da ferfesun kayan ciki.
"Ji tayi kamar mutum a kanta, da sauri ta dago kanta suka hada ta sakar mashi murmushi hade da rungumar shi, cikin sweet voice dinta tace ya Abdul har zaka fita ga breakfast dinka na gama? Tabe baki yayi yace no nayi latti idan na fita zanci a restaurant, ai jitayi kamar an buga mata guduma a kahon zuciya, cike da tsananin jin kishin shi na addabar ta tace"
Plsss ya Abdul kayi hakuri da shareka danayi jiya nasan shiyasa bazaka ci abinci na ba, plsss am sorry wallahi bazan sake ba, ta karasa maganar hade da fiddo kwalla, cike dajin zafin hawayen nata dake zuba ya kara rungumota jikin shi yace nima wasa nake maki, ai idan ba matata Amatullahi ba bazan iya abincin wata ya mace ba sai ammie na da mummy, so ki kwantar da hankali yanzu zan zauna inci ko? Ya dage mata gira.
Kawar da ita yayi daga jikinshi ya aje jakar shi sannan ya zauna hade da tankwashe kafafun shi, itama haka zama tayi suna fuskantar juna kafin tayi serving dinsu,
"Cikin kwanciyar hankali suke cin abincin suna hira irin ta mata da miji masu matukar ji da junan su, haka har suka gama cin abincin, ya tayata kwashe komai suka kai kitchen, palour suka fito ta dauki jakar shi ta rataya a kafadarta, hannuwan su na sarke dana juna suka fita har farfajiyar gidan, can wurin parking space suka tsaya suna hira, suna jin kamar karsu rabu da juna, haka dai badan suna so ba sukayi ma juna sallama ya wuce a yayinda take daga mashi hannu harya fice daga gidan.
"Ameera dake gyaran palour tazo wurin window tana kakkabewa idonta ya sauka akan su Amatu dake jikin Abdulrahman har suka isa wurin mota, ido ta zuba musu har suka gama zancen su ya wuce, da sauri ta fito ta tari Amatu, harara ta watsa mata tace sannunku? Waton kince inja aji ke kina nan kina zuba love ko? Murmushi Amatu tayi tace injiwa kawai dai naje rakashi ne.
Dakuwa Ameerah ta kaiwa Amatu akai tace Allah bakida mutunci kuma sai na rama....Amatu tace kiyi hakuri wallahi naso injawa ya Abdul aji amma jiya yadda naga duk ya damu a kaina kuma koba haka ba bai dace ace ina wulakanta mijina ba shiyasa kawai yau da safen nan na nemi sulhu a wurin shi kuma daman ina da niyar in fadamaki mun