Chapter 12 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 27

33K to 36K   out of 79.1K words

rai kamar yadda shima ya b'ata mashi rai sai ya dan yalwata fuskar shi da murmushi yace "my baby tunda yaki bani babbar hanya in shiga bari mubi ta k'aramar k'ofa ko,"ya fad'a had'e da d'age girar sa sama".

"Murmushin itama tayi suka jero zasu shiga ciki". aikuwa babu shiri Abdulraheem ya fito da hanzarin shi yasha gaban su gami da "shaqo kwalar rigar Abdulraheem ".

" yana huci kamar wani zaki yakai hannu zai naushi Abdulraheem, abdulraheem ya kauce masa had'e da cire hannun da Abdulrahman ya shaqo kwalar rigan shi da k'arfi".

"Yace what d hell are u? Waye kai dahar zaka shiga gona ta? To bari kaji kaja wa kafafunka kunne akan karsu kuskura su sake h'aduwa da nawa a k'ofar gidan". Idan kuma ba haka ba, " u shall see it. Abdulraheem ya fad'a a tsawace.

"Tunkaro shi Abdulrahman yayi rai b'ace yace gidan ubanka ne da zaka gindaya  mun sharud'ad'a ko kuma kai uba na ne da zaka bani umarni in bi?? Toh let me tell u, "wallahi baka isa ba"..... Abdulraheem ya katse shi, yace karka kuskura kamun rashin kunya yanxu in fasa ma bakin nan.

"Abdulrahman ya waro ido a zuciyar shi yace ya fasa mun baki? Shi a su wa?? Sai shed'an ya dunguza shi aikuwa ya kusanto shi har suna jin saukar numfashin junan su yace fasa mun bakin mana? Yana kara shigewa jikin shi had'e da cewa ai bansan ka cika ba sai naga baki na yana jini".

"Yadda ya wani shige jikin shi ne ya kara bashi haushi", aikuwa yakai mashi naushi a gefen kuncinshi" Abdulrahman da yaji zafi sai kawai ya rama" nan suka fara kokawa Amatullahi na ihu tana ture Abdulrahman da dake faman kai ma Abdulraheem naushi duk da shima din ba baya ba.

"Ganin fad'an yaki tsayawa ne yasa Amatullahi ta fasa wata irin "razananniyar kara" wanda ni kaina sai da biro na fad'i kasa.

"Cikin rud'ewa kowannensu yayo kanta Abdulrahman yana haki kamar wanda yasha gudu yace baby meya faru?? Banza tayi mishi ta amsa Abdulraheem da yake kokarin jan hannunta su shiga cikin gida".

Abdulrahman ya shawo gaban su yace ka saketa nace? Wata yar murmushi yayi saki wadda a iya leb'on shi kawai ta tsaya zai yi magana Amatullahi ta riga shi".

" tace bazai sakeni ba! Wai kai Abdul yaushe zakayi zuciya ne iyee "to wallahi daga yau ka k'ara zuwa gidan mu sai nayi karar ka", ta karasar maganar a yayinda hawaye ke zuba a kumatun ta wanda batasan dalilin zubansa ba.

"Abdulrahman yace Amatullahi ni zakiyi kara? Ni d'in yana magana ne tare da nuna kanshi yace baby yanzu akan wannan abun zakiyi karata?? Murmushin da bekai zuci ba ya saki yace hmmmm Amatullahi sedai ko kiyi karata amma kisani zuwa gidanku tamkar zuwa wurin kiwo ne.

"Sannan ya juyo kan Abdulraheem yace kai kuma zamu sake had'uwa. Yana kai nan ya shige motar shi ya fece a tsiyace. Dariya Abdulraheem yayi yace banza kawai mara zuciya ai ina nan akan bakata. 

Amatullahi ma Murmushin tayi tace su shiga cikin gida, " hannun su na sarke dana juna suka nupi kofar shiga cikin gidan, daidai lokacin ameerah ta fito daga cikin gidan zata wuce gida.

"Wani kolo abu taji ya tsaya mata a makoshi wanda take jinshi tamkar an dasa mata karfen darma mai dan karan zafi. " dafe zuciyar ta tayi tana shirin komawa ciki dan  bazata iya jurar ganin su haka ba.

"Amatullahi kuma ganin ameerah yasa tayi saurin zare hannunta daga na Abdul tana kiran sunan ameerah dat shige gida a guje. Batare data damu ba sukaci gaba da hirar su.

Ameerah kuma cin karo tayi da mommy data fito daga daki" mummy tayi saurin tsayar da ita tace ameerah meya sameki kike kuka? Kuka kuma" ta shafo kumatunta taji eh lallai tabbas ga hawaye a fuskarta.

Cikin son boye damuwarta tace mummy ba kuka nake ba ruwa ne. Mummy tace shine zuciyar ki ke bugawa haka da sauri? Ameera tace eh" mummy tace ameerah wai meke damunki ne, kinga yadda yanayin ki ya sauya kuwa? Kodai wani abun ne ya sameki da kika fita?

Tuni ta fara tuno yadda taga hannuwan su sarke dana juna, take taji wani irin kishin Abdulraheem ya shige ta, "tama manta da mummy na wurin sai kawai ta fashe da kuka gami da dafe zuciyar ta dake faman zugi.

"Rikon da mummy tayi mata ne yasa tayi saurin share hawayenta murya na rawa tace wallahi mummy babu abunda ke daa........... Bata karasa fad'a ba sakamakon tarin daya sarke ta, lokaci guda ta fad'i a kasa.

Da sauri mummy ta sunkuya kasa tana bubbuga ta amma bata tashi ba, ruwa ta dauko ta yayyafa mata amma bata tashi ba. " nan mummy ta rude ta fita waje tana neman agaji" nan tarar da Abdul da Amatullahi a tsaye.

"Suma babu shiri sukayo kan mummy dan yadda ta fito a rikice yasa suka gane babu lafiya". Batare da tayi magana ba tayi musu nuni da hanyar palour. Nan suka shiga palon inda suka tarar da ameerah kwance bata motsi. Abdul ne ya dauke ta da sauri yayi hanyar waje da ita. Nan suma suka bishi yasa ta a mota Amatullahi ta shiga gaban mota.

"Mummy kuma ta zauna gidan baya tare da daura kan ameerah saman cinyarta. Direct asibitin su ya wuce dan yafi kusa daga inda suke.

A harabar asibitin su ya paka mota sannan ya fita da sauri ya kirawo wasu nurses guda biyu. Da sauri suka iso suka ansa ameera suka shiga da ita emergency room.

"Taimakon gaggawa suka fara bata "cikin ikon Allah sai gata ta farfado, ganin kanta a gadon asibiti ne kuma ga drip ansa mata yasa ta kwalla ihu.

"Abdulraheem dake bakin kofar dakin yana magana da wata nurse sai jin ihunta yayi. Da sauri ya bude kofar ya shiga inda ya tarar da ameera na kokarin cire drip din da aka sama ta.

Cikin kuzari ya isa gareta ya rike hannunta, yana kokarin........


Plsss share
[2/21, 9:38 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

     Page 53-54

"Cikin kuzari ya isa gareta ya rike hannunta yana kokarin mayar da drip din a hannunta, ita kuma sai turjewa take tana nema ta fincike ta sauka daga gadon.

"cikin yan dabaru irin nasu na likita yayi mata allurar bacci" sannan ya zare drip din ya gyara shi yadda ya kamata. Kare wa fuskarta kallo yayi sai yaji ta bashi tausayi "duk da cewar besan abunda ke damunta amma a iya gwajin da yayi mata ya gane damuwa ce tayi wa zuciyarta yawa".

" kawar da fuskar shi yayi daga kallon da yake mata, ya kwashi wasu files daya shigo dasu ya fice daga dakin. "Yana fita sukaci karo da mummy da Amatullahi"

"Cike da damuwa Amatu tace Abdul ya jikin ameera? "Abdul yace alhamdulillah yanzu haka ma ta samu bacci". Mummy dake tsaye a wurin cikin godewa Allah tace zan iya ganinta kuwa? Abdul ya amsa da eh.

Nan suka shiga dakin, "Amatu tayi saurin karasawa wurin gadon da ameerah ke kwance" hawaye na zuba a fuskarta tace my ameera ki bude idonki ki kalleni......mummy tayi saurin katseta ta hanyar fad'in amatu miye haka? Keda zaki mata addu'ar samun sauki shine zaki wani tasata a gaba kina kuka, "miye amfanin kukan naki?

'Amatu ta juyo ta kalli mummy "tace mummy kukan tausayinta nakeji, bakiji abunda abdul yace ba wai damuwa ce tayi mata yawa, kuma mummy kin fa san halin ameerah da zurfin ciki" abu bekai abu ba zata iya mayar dashi abun damuwa and mummy ni nasan cewa akwai abunda ke damun ameera, "sau tari nasha jinta tana wasu yan maganganu ko kuma kiji tayi shuru tana tunani kuma kona tambaye ta sai tace babu komai".

" idan baki manta ba watannin baya datayi ciwo dakyar da iya bud'ar baki ta fad'a mun abunda ke damunta"

Ajiyar zuciya mummy ta sauke "tace hakane Amatullahi amma abunda nakeso dake shine kiyi mata addu'a Allah ya yaye mata damuwarta kinji ko? "Tau Amatullahi ta amsa dashi".

"Kallonta mummy tayi tace ta zauna ita zataje gida ta sanar wa aunty hajara abunda ke faruwa" Amatullahi tace toh" daga nan tayi mata sallama ta wuce.

"Bayan ta fita ne Abdulraheem ya shigo dakin lokacin amatullahi na shirin yin sallar magariba, shi kuma har yayi nashi sallar, ganin zata tada sallah ne yasa shi komawa.

"Bayan yan mintuna kalilan sai ga mummy tare da aunty hajara da kuma mijinta. "Aunty hajara a kage take dataga halin da ameerah ke ciki dan hankalinta a tashe yake shiyasa bayan sun shigo asibitin ta rigasu shiga da sauri", wata nurse ce ta nuna mata dakin da a kwantar da ameerah.

"Da hanzarinta ta shiga, cikin tashin hankali ta karasa wurin da ameera ke kwance. Kwallace taf a idonta tace ameerah sannu ya jikin ki?

Ameerah da yanzu ta farka daga bacci, cikin kasalalliyar murya tace aunty lafiya ta kalau ki daina kuka."Cikin tausaya mata tace ameerah na daina kuka, ta fad'a gami da share hawayen daya zubo mata.

Usman (mijin hajara) dake coge a bayan hajara yace ameerah ya jikin naki? Ameerah tace alhamdulillah naji sauki yaya. Tau Allah ya kara sauki, ameera ta amsa da ameen.

Nan suka dan soma hira suna jan ameerah da hira dan su kawar mata da duk wata damuwa dake tare da ita. suna nan har kusan karfe goma na dare daga bisani suka mik'e zasu wuce, mummy tace ita zata kwana, aunty hajara tace a'a ita ya dace ta kwana. Sai Amatullahi tasa kukan shagwaba ala dole wai ita zata kwana.

"Abdul da yanzu ya shigo nan yasa baki akan abar amatu ta kwana da ita tunda ma ameeran taji sauki ko zuwa gobe ana iya sallamar ta Kuma ma akwai nurse masu kwanan dare koda wani abu ya faru".

Mummy "tace tau ai bakomai", nan suka fita har harabar asibitin sukayi musu rakiya, Abdulraheem ma wucewa yayi amma sai daya had'a amatullahi da wasu nurse guda biyu kafin ya wuce.

"Bayan amatu ta dawo dakin ne ta tarar da ameera kan sallaya tana rama sallolin da suka wuceta, "bayan ta idar ne ta dawo bakin gado inda amatu ke zaune tana murmushi tace my amatu daman ina Allah Allah in idar da sallah in tambaye ki waya kawoni asibitin nan?

Amatullahi tace Abdulraheem ne ya kawoki, Kinsan lokacin da abun ya faru muna cikin gidan shine mummy ta fada mana yayi sauri ya kawoki wannan asibitin.

Murmushi ne ya bayyana a fuskar ameera tace Allah sarki gaskiya Abdul nada tausayi.

"Cikin ranta ko jindadi take Abdul ya ceci ranta, "wani taci daji a lokacin data tuna cewar shi fa baiko san tanayi ba ita kadai ce ke haukarta, sai nan danan taji irin kololon dazu na shirin tokare mata makoshi, "da sauri ta kawar da tunanin saboda kar amatu ta gane.

"Amatullahi kuma harta dan fara fuskantar wani abu sai ameerah ta katse ta da cewa suje kwanta dare yayi. Amatullahi batace komai ba illah fatan Allah yasa su wayi gari lafiya. Daga nan kowa ya kwanta makwancin shi.

      Washe gari
Tunda safe Abdul yayi saukon zuwa asibitin, dan harya rigasu mummy zuwa amma suma bada dadewa ba suka iso.

Gaida junan su sukayi suna mai tambayar amatu yamai jiki, amatu "tace tau da dama dan jiya ameerah batayi wani baccin kirki ba, in banda sake-sake da tunani datayi tayi wanda a cikin daren ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani.

"Koda asuba tayi Amatu hankali a tashe taje ta kirawo nurse din da Abdul ya hadata dasu, nan suka danyi mata allurori sannan jikin nata ya dan lafa.

Abdulraheem kuma Amatullahi na fada mashi yayi saurin shiryawa yazo asibitin shiyasa ma ya riga su mummy zuwa.

Abdulraheem dake kusa da Usman, cikin yanayi na damuwa yake tambayar kanshi toh wai meke damun ameerah ne?? Cikin son nemo mafita ya dubi dukan su dake cikin dakin yaga kowa damuwa ce shimfide a fuskar shi musamman ma hajara da Amatu.

"Mummy ce tayi magana tacewa Abdul ko za'a iya bata abinci? Abdul yace eh, "nan mummy tasa Amatu ta zuba mata hadaddiyar jollof din taliya   da alayyahu da sauran kayan lambu.

Bayan tasa ne mummy ta ansa plate din taje bakin gadon da "ameera ke kwance ta tayar da ita zaune ta mik'a mata ruwan gora tace taje ta wanke bakinta" Sukuku ameerah ta tashi dan babu wani k'arfi a tattare da ita, haka ta shiga dan karamin toilet din dake cikin dakin ta wanko bakinta ta dawo.

"Zama tayi tana mai fuskantar mummy data debi abinci a spoon tana mika mata. "Bude bakinta tayi ta karba dan tasan halin mummy batason musu.

Haka mummy ta dinga dura mata abinci sai da "ameerah ta fara rigima tana cewa cikinta zai fashe sannan mummy ta kyaleta".

"Aunty hajara kuwa hararanta ameerah tayi tace ai gwara da kikayi mata dure, dan inba dan ke da bazata ci ba. Murmushi kawai mummy tayi batace komai ba.

"Amatullahi dake gefen aunty hajara tasata tayi a gaba wai sai taci abinci, dan tun jiya bataci komai ba.

"Usman ne yace shi zai wuce karya makara, sai aunty hajara tace ya jirata ya sauke su tare da Amatullahi. "Amatu tayi saurin dagowa ta kalli aunty hajara tace nidai aunty bazan je ba ina tare da ameerah. "Sai aunty tace a'a ki tashi muje kiyi wanka zuwa da rana sai mu dawo, "kinga yanzu ga mummy nan zata zauna da ita.

Bata rai tayi,"ta fara bubbuga kafa a kasa" sai mummy ta harare ta had'e da cewa ta tashi su tafi. "saida Abdul ma yasa baki yace sannan ta hakura badan taso ba suka wuce.

Tare suka fito Abdul na gefen Usman, suna magana, a haka har suka kai harabar asibitin, daga nan sukayi sallama suka wuce. "Abdulraheem ma kiranshi akayi a waya , sai dai banji abunda akace ba naga ya shige mota.

"Gidan su ya nupa, inda daga fitowar shi wani abokin shi ya kirashi, "nan ya amsa wayar suna ta hira, sai dariyar Abdul kawai kakeji, rufe motar shi yayi ya nufi part din ammie still da wayar a kunnen shi.

"Haka ya shiga cikin palon yana waya gami da dariya harya isa saman kujera "two seater yana ta wayar shi, kusan minti biyar yana waya kafin ya datse kiran".

"Ajiye wayar yayi yana murmushi, ya mike kenan sukayi ido biyu da Abdulrahman dake zaune saman kujera. Aikawa junan su harara sukayi, kafin Abdulraheem ya mike zai haura sama sai yaji kamar motsin ammie a kitchen".

"Fasa haurawa yayi ya dawo ya nufi kitchen din. Ta bayan ammie yaje da niyar ya bata "tsoro sai tun kafin ya bata tsoron" tayi saurin juyowa da taji kamar motsin tafiyar mutum.

"Murmushi suka sakarwa junan su ammie tace likitan turai kenan kace harka iso?? Yace eh ammie nah "kinsan duk abunda nakeyi idan kika kirani ya zama dole ne in barshi in amsa kiran mahaifiyata".

"Murmushin jindadi ammie tayi tana kallon Abdul tace ya jikin ameeran ne? "Abdul yace taji sauki sosai kila ma yau ya sallame ta. Ammie tace tau Allah ya kara sauki. "Ya amsa da ameen".

"Abdulrahman kuma Abdulraheem" na shiga kitchen, "yayi saurin tashi yaje ya dauki wayar Abdulraheem yana addu'ar Allah yasa batada security, "aikuwa yaci sa'a batada. Nan ya washe baki yana cewa idan kunsan wata baku san wata ba.

"Nan yayi sauri ya shiga contact dinshi yana dubawa, "can yagano wata number ansa my baby" take zuciyar ta bashi number amatu ne. Cikin gaggawa kwashe number, ya ajiye wayar yadda ya ganta sannan ya juya zai koma kujerar da yake zaune sai.....................





👇🏽👇🏽👇🏽
    Follow
    Vote
  Comment
@lashminzy (wattpad)
[2/21, 1:58 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

Яυ∂αиι fαиѕ gяρ 1&3 ιиα мιкα ѕαкσи gσ∂ιуαтα α gαяєкυ, α gαѕкιуα ιиα ʝιи∂α∂ιи ¢σммєитѕ ∂ιикυ, ιиα αℓfαнαяι ∂αкυ
❤❤❤❤

     Page 55-56

"Sai yaji motsin su, da sauri har yana dan hadawa da gudu ya koma ya zauna, yana latsar waya s kamar bashi ba".

"Fitowa sukayi ammie na rik'e da wata food flask mekyau. Bayan sun k'araso wurin shi ne ammie ta mik'a ma abdulrahman food flask din" tana cewa yayi sauri ya wuce karya makara. "Abdulraheem ya wani langab'ar da kanshi bisa kafad'ar ammie, cikin sigar shagwab'a "yace ammie waton shi kawai kika sani, shine harda wani sa mashi abinci ya tafi shi? "Ammie tace bakaga zai makara bane shiyasa nace ya tafi dashi yaci a can".

"Abdulraheem ya bata rai yace Allah ammie inda ni ne ko makara" zanyi sai kin rikeni kin bani amma shi kika bari ya tafi dashi ko? "Ammie tace tau ba shine babba ba"

"Gabadayan su suka kalli juna,"Abdulraheem ya kara shan toka, Abdulrahman kuma dadi yaji wai ance shine babba". Aiko da fara'ar shi yace cewa ammie sai ya dawo. "Ammie tace a dawo lafiya".

"Sai daya kai bakin kofa sannan ya juyo ya kalli Abdulraheem yace kani babu ko rakiya?? "Abdulraheem ya wani washe baki saboda duk abun nan da sukeyi babu wanda ya sani, "dan in suna gaban daddy ko abba ko ammie far far suke wa junan su. "Sai ya waske kawai yace kaje bana son kayi lattin shiga makaranta anjima zamu hadu."

Ficewa yayi batare da yace komai ba, Abdulraheem kuma da harara yayi mashi rakiya.

"Zama ammie tayi saman kujera "tana mai fuskantar Abdulraheem tace" yauwa son jiya abbanku yace wai yau ku hadu gidan daddyn ku akwai maganar da zakuyi kaji ko? Abdul ya amsa da toh, gami da tambayar ta "wace magana zasuyi".

"Ammie tace be fadamun ba amma nasan dai maganar bazata wuce akan naku ba, "dan jiya naji alhaji yana waya kuma da alama daddyn amatu ne dan naji sai hakuri yake ta bashi yana cewa "insha Allah yau zai jisu".

"Ajiyar heart Abdul ya sauke yana tunanin yadda zata kaye, danshi yasan dai bazai iya hakura da Amatullahi ba..... Ammie ta katse shi ta hanyar "cewa Allah yasa a kwashe lafiya dan dai ita bataga wata alamu na cewa daya daga cikin su ya saduda ba".

Abdul yace ameen ammie na insha Allah komai zai tafi yadda ake so.

"Tashi ammie tayi ta shiga kitchen ta zubo ma Abdul, breakfast, ta kawo mashi, lokacin shi kuma yana shirin tashi ya wuce, "ammie ta

12 / 27