Chapter 21 Reading RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt Arewa Novels

RUDANI COMPLETE HAUSA NOVELS BY LASHMINZY.txt

Author :  LASHMINZY Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 27

60K to 63K   out of 79.1K words

tsaye tana kai kawo, "ita dai ganin komai take kamar a mafarki, "ashe da dalili nakejin duk yanayi na ya sauya??hmmm ashe ƙaruwa na samu?? Taɓɓ waya ga Amatullahi da baby?😍ita kaɗai fa take maganar ta.

"Tana cikin hakane taji motsin su Ameerah, da sauri ta koma bakin gado ta kwanta harda sa bargo ta rufe jikinta, Abdulrahman shine kan gaba, yana isowar wurinta ya zauna saman drowan dake jikin gadon gami da da yaye bargon cike da kulawa yana tattaɓa jikinta yace baby na ya jikinki, "kuma me waccen matar tazo ta maki?? Kamar wacce ta daɗe tana ciwo harda cewa washh sannan ta ɗago kanta ta jingina da gadon tana kallon shi tace lafiya ƙalau nake kawai jikina ne ba daɗi shine ammie ta kira Dr ta duba ni.

   "Ɓata rai yayi yace toh ni miye amfani na a matsayina na likita kuma mijinki, hahaha kuji shi fah sai kace wani likitan gaske 😍. Abdulraheem dake tsaye shida Ameerah suna kallon ikon Allah saura kaɗan dariya ta suɓuce masa sai ya danne ta.

    Ameerah ta ɗan matso kusa da Amatu tace besty tunda mijinki kawai kika sani ni nayi nan, ta juya da niyar fita, Amatu tayi saurin saukowa daga kan gadon tace "haba my meerah sorry dawo mu zauna, ta ƙarasa faɗar maganar haɗe da jan hannuntu suka zauna saman gado. Abdulraheem yace nikam na fita Allah ya baku lafiya. Batare daya saurari amsar su ba ya fice daga ɗakin, ameerah kuma cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace Amatu cikine dake ko? Itama amatu tayi ƙasa-ƙasa da murya tace hmmm waya faɗa maki?

 
    Uhmmm babu wanda ya faɗamun nidai kawai naga alamu ne, ta ƙara da cewa da gaske cikin ne dake? dan naga harda likita aka kira ta dubaki ameerah ta faɗa. Amatu tace eh insha Allah shine amma karki faɗawa kowa kinji, ameerah ta amsa da toh sannan ta fice daga ɗakin.

Maida duban ta tayi kan Abdulrahaman dake latsar wayan shi tace yaya yadai naji kayi shuru? Ɗago da kanshi yayi ya watsa idanunshi cikin nata yana kallonta ba ƙaƙƙautawa, ƙasa tayi da idonta dan bazata iya jurar irin wannan kallon da yake mata ba.

    Cikin sanyin murya yace baby ciki ne dake ko? Shuru tayi masa dan tana tsoron karta ce shine likita tace ba shi bane kuma haka tana tsoron tace ba ciki bane likita tace cikin ne, shima shurun   yayi na ƴan sakanni kan yace "baby ki faɗamun mana nifah nasan kina ɗauke da juna biyu kawai nayi shuru ne saboda ina son saina tabbatar ne kafin na sanar dake dan naga alamar ke baki ko sani ba.

    Murmushi tayi taja bargo ta rufe harda kanta tace nima bansani ba sakamakon Dr muke ji...........sai ga ammie ta shigo da murnar ta tace tau Alhamdulillah Allah mungode maka da kyautar daka bamu Allah ya saukar ki lafiya Amatullahi.


   """Wayyo zo kuga murna wurin Abdulrahman, saboda tsabar farinciki bai san sadda ya ɗaga ammie ba, dan tayi mashi babban albishir ɗin da bazai taɓa mantawa dashi ba. Ture shi ammie tayi daga jikinta, "yana dariya ya nupi wurin amatu, ba kunya ya wani haye saman gado, "aiko ammie dataga haka ƙafarta kawai taja tana murmushi tana kuma mamakin yadda akayi abdulrahman ya fitsare haka ko kuma daman hake yake tun yana yaro idan abun farinciki ya sameshi oho?? Ita dai tasan cewar tun haɗuwar ta dashi ba haka yake ba.

     Amatullahi cike da jin kunya ta ƙara shigewa cikin bargo dan gabaɗaya kunyar ammie ta rufe mata ido, musamman ma da Abdulrahman ya ɗagata, "jitayi kamar ta nutse cikin ƙasa, "amma wani ɓangare ɓa zuciyarta daɗi takeji. Fincike bargon yayi ya tura shi gefe sannan ya janyota jikinshi ya rungumeta kamar zai mayar da ita cikinsa.

Ita dai mutsu-mutsu kawai take tana jin tsoron kar ammie ta dawo dan taga fitar ta, Abdulrahman ko a jikinsa wai mahaukaciya ta faɗa rigiya tace wanka ta shiga yi. Sumbatar ta kawai yake yana sa mata albarka haɗe dayi mata addu'a Allah ya sauketa lafiya.

  "Kusan mintin su ashirin a haka dan harya fara fita hayyacinsa, "Amatu da taga yana shirin wuce gona da iri tace plsss yaya abdul ka bari muna gidan ammie ne fah, "ko ƙala baice mata ba yaci gaba da sarrafata dan  Abdulrahman akwai iya sarrafa mace duk yadda yakai ga romancing ɗinki ko bakiso ba dole ki biye masa dan in wurin kwanciya ne kam Abdulrahman saidai ya koya maka.😎

   Wani ƙarfi ne yazo mata, tasa duka hannuwanta biyu ta tureshi sannan ta mike zaune ta gyara ɗankwalinta daya faɗi saboda jarabar shi kan ta sauka daga kan gado, "shi kuma jinginewa yayi da kan gado haɗe da lumshe ido na ɗan wani lokaci kafin ya sauko daga kan gadon ya iso wurinta. Gabanta ya tsaya yana gyara mata rigarta data juya gefe, "komi batace ba harya gyara mata sannan ta kalleshi tace kaga abunda kaja ko? Duba fa kaga yadda rigarka tayi squeeze yanxu idan ammie ta gani ko su ameerah me zakace??

     "Ince naji ɗumin mata ta mana, "ko akwai laifi, ya faɗi maganar haɗe da ɗage girar sa sama, "tunkuɗe shi tayi ta fice daga ɗakin ta barshi nan tsaye, "murmushi kawai yayi ya gyarawa ammie gadonta kan ya isa wurin madubi ya gyara rigar shi sannan ya fito palour. Cikin haɗe rai ya fito palour dan bayason wani yaga alamun wasa a tattare dashi bale har akai ga tsokanar shi. "Zama yayi kan one seater yana latsar wayan shi, Abdulraheem yace toh ko baka faɗamana ba munji, abdulrahman ya ɗago kanshi ya kalleshi baice ƙala ba yaci gaba da latsar wayan shi dan yasan neman magana kawai yake

Ammie da yanzu ta shigo palon tace ahh har kin fito keda nace kiyi xamanki ki huta? "Cike da shagwaɓa tace ammie naji sauƙi ne kuma babu daɗi ina zaune ni kaɗai shiyasa na fito. Ammie tace tau bari in kawo maki abincin dana dafa maki ko?

   Amatu tace a'a ammie bana jin yunwa, ammie tace "toh bari insa maki a kula kije dashi gida, "toh kawai tace ammie ta shige kitchen, "Abdulraheem yace tau ku tashi mutafi idan kun shirya, Amatu da ameerah suka tattashi ko wacce ta ɗauki mayafinta da jakarta Abdulrahman kuma yana nan zaune yana jinsu amma bai tanka ba balle harya tashi sai da ammie ta fito daga kitchen gansu a tsatsaye tace ahhh badai tafiya zakuyi ba?

   Abdulrahman yace eh ammie tafiya zamuyi. "Ammie da takejin kamar karsu wuce tace tau bari ina zuwa, ta haura sama, bada daɗewa ba sai gata ta sauko riƙe da wasu ledoji guda biyu, ta miƙawa Amatu da Ameerah, Abdulrahman ya ansa na Amatu wai baya son ta wahala, shima Abdulraheem ansar na ameerah yayi ya riƙe. Ammie tayi murmushi tace tau su sai su ɗauki wannan tayi musu nuni da wasu kuloli guda biyu.

    Ba abun suyi godiya ba ammie tace sunyi laifi dan ammie ko kaɗan batason idan tayi kyauta ayi nata godiya sai kawai kowaccen su ta rungumeta haɗe dayi mata sallama. Nan suka fito farfajiyar gidan inda suka tarar da samha da hanan sun shigo gidan dan ammie ta aikesu sai yanzu suka dawo. "Da gudun su suka ƙaraso wurin su suna musu bankwana kan suka wuce.


     Bayan sun isa gida kowa ɗakin shi ya shiga ya watso ruwa haɗe da ɗauro alawla dan lokacin magariba yayi, "jallabiya kawai Abdulrahman ya zura ya wuce masallaci, amatu kuma bayan ta idar da tata sallar ɗakinshi ta shiga bata ganshi ba sai kawai ta dawo palon ƙasa ta zauna tana jiran ya dawo suci abinci, shuru har aka kira sallar isha'i, tashi tayi taje tayi sallar sannan ta sake fitowa palour, ta zauna kenan sai gashi ya shigo.

   Murmushi ya sakar mata haɗe da buɗe hannuwanshi alamar tazo, ba musu taje da gudu ta rungumeshi, ya ɗagata sama yana juyi da ita kafin ya direta ƙasa yace baby kinga na daɗe ko? Na tsaya sallar isha ne, murmushi tayi mashi tace "ai bakayi laifi ba, shima murmushin yayi mata haɗe da jan hancinta yaja hannunta suka zauna ƙasa wurinda yaga ta jera musu abinci, "tana zaune saman cinyarshi ya fara bata a baki itama tana bashi.



*******
Zaune yake a bakin gado da waya a kunneshi, gabaɗaya ya mayar da hankalunshi kan wayar da yakeyi, "da alama dai wayar nada mahimmanci dan baiko san lokacin data shigo ɗakin ba, adaidai lokacin yake faɗin "toh abba dan Allah ka ƙara haƙuri kasan idan ka fito fili ka faɗamashi cewar kai kasa aka sace yarrrrrrr.....

Sai kawai ya hangeta ta madubi, "da sauri ya katse wayara haɗe da miƙewa tsaye suna kallon kallo, cikin ruɗu ta fara ja da baya tana cewa.........






Comment
       Share
[3/12, 10:02 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
           *RUDANI*
       💫🌞💫🌞💫🌞

Story & written by
    Lashminzy

💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
        ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥

'''vote me on wattpad @lashminzy'''

       Page 91-92

""""Cikin ruɗu ta fara ja da baya tana cewa Abdul wa aka sace ne? Dawa kake waya?duk a lokaci ɗaya ta jero masa waƴannan tambayoyin wanda cikinsu babu wanda ya iya amsa ta saboda wata irin nannauyar ajiyar zuciyar daya sauke, dan ya ɗauka ko ta gane inda maganar ta dosa, shuru sukayi na yan mintuna ta juya zata fice daga ɗakin dan taga alamaun baida niyar amsata.

   "Da sauri yasha gabanta, ya janyo hannunta suka zauna gefe gado, yace my ameerah ki kwantar da hankalin ki, am..dam..daman ƙanwar abokina ce aka sace amma yanzu an gano wanda ya saceta shine nake faɗawa abba yayi musu jaje sabida yasan mahaifin yaron. Ajiyar zuciya tayi tace wai Alhamdulillah har hankalina ya kwanta, daman nazo dubawa ne ko ka fito daga toilet in kawo maka lunch ɗinka? Duk da cewar yanajin yunwa amma baya jin zai iya cin abincin kuma ba abun yace ya ƙoshi bane ta tisa sa agaba kamar uwarshi tana jero mashi tambayoyin da a halin yanzu bai shirya amsa mata su ba, sai kawai yace taje ta kawo.

  Tashi tayi ta shiga kitchen ta zubo mashi sauran farfesun kayan ciki da jollop ɗin taliyar da Amatu ta aiko mata dashi, dan taci nata shi kuma cewa yayi sai ya fito daga toilet, shine ma dalilin dayasa ta tarar dashi yana waya. Da sauri ta haɗa komai takai mashi, batare data zauna ba tace mashi yaci zataje ta watso ruwa, toh kawai yace mata ta fice daga ɗakin.

     Tana shiga ɗakinta ta fara kaikawo haɗe da game tafukan hannuwanta wuri ɗaya tana bubbuga su, girgiza kai tayi tace inaaa ya za'ayi in yarda da maganar ka bayan naji kana cewa idan aka fito fili aka faɗamashi cewar kai kasa aka sace ta?? Toh me hakan yake nufi? Wa aka sace?? Waye ya sace ta?Abba? Da ƙarfi tace noooo ya za'ayi abban Abdul yayi sata? Wannan ba halinshi bane tayi maganar a lokacin data sassauta murya.

"Dafe kanta tayi da sauri a lokacin da zuciyar ta ke raya mata cewar ko Abdul kidnapper neh? Girgiza kai tayi da ƙarfi kamar wadda zata cire kan dan bata yadda da abunda zuciyarta ta rayo mata ba dan ta yadda da Abdul mutumin kirki ne kuma ko a mafarki aka faɗamata cewar Abdul kidnapper ne bazata taɓa yadda ba.

"Gaskiya ya zama dole insan abunda ke faruwa da mijina. "Zuciyar ta tace toh ina ruwanki da bibiyar lammuransa?shuru tayi tana wani ɗan nazari sai kuma ta yamutse fuska alamar tunanin datayi baiyi mata daɗi ba. Wata zuciyar tace ai mijinki ne kuma da ikon yin bincike akan shi, yess kawai ta faɗa ayayinda murmushi ya bayyana a fuskarta, sedai bansan kona menene ba.

  Da sauri ta shige toilet, agurguje ta watso ruwa ta fito, ta shafa jikinta da mai, sannan ta saka daguwar rigan baccin ta tasaka hula kan ta fice daga ɗakin, ɗakinshi ta shiga ta tarar dashi kwance saman gado da alama ma harya gama cin abincin dan bataga kulolin abincin data kawo mashi ba.

Saman gadon ta haura tana mai tambayar ina abincin data kawo mashi, yace ai tun ɗazu ya gama yakai su kitchen, "murmushi tayi tace owk my Abdul ka hutashsheni ta faɗa gami da cusa kanta cikin faɗeɗen kirjinsa. A hankali ya rungumo abar sa yaja blanket ya rufe su

  Nima na rufe babin su 😎


         Bayan kwana biyu
   Abdulraheem ne zaune a palour shida daddyn Amatullahi, cikin girmamawa Abdul ya gaishe shi, haka ma daddy da fara'arshi ta amsa mashi yana mai tambayar shi iyalin nashi, Abdul yace lafiya ƙalau take. Daddy  yace masha Allah haka akeso, yanzu ya maganar mu?Abdul ya duƙar da kanshi ƙasa dan ji dayayi gabaɗaya daddy yai mishi wani irin kwarjini har yakejin ina ma ace baizo ba daya fasa faɗar maganar har zuwa wani lokaci, sedai kuma hausawa kance idan dama tazo maka kayi amfani da ita akan lokaci karta wuce kuma duk jinkirin da zasuyi watarana dole zasu faɗa toh miye amfanin jinkirtawa.....

"Tsinkayo muryar daddy yai yana cewa Abdul yaya dai naji kayi shuru, kawai ka faɗi maganarka babu komai kasan dani dakai an zama ɗaya yanzu na ɗauke ka tamkar ɗan dana haifa a cikina, karkaji tsoron komai ina sauraronka.

     "Abdul ya gyara zama haɗe saita kanshi ya saci kallon daddy yaga shima kallon nashi yake sai ya sadda kanshi ƙasa, a hankali ya fara magana kamar.....
Amm daddy daman kan maganar sace Amatullahi da akayi ne shine nakeson in faɗamaka ko waye.

Murmushi daddy yai irin nasu na manyan mutane yace Allah sarki aini harna manta dan koma wanene nabarshi da Allah, amma gaskiya zanso insan ko waye. "Abdul da yanayin sa ya sauya wanda na kasa gane daɗin maganar daddy yaji ko akasin haka?              Sai Abdul yace Eh toh daddy zan faɗamaka amma wani hanzari ba gudu ba, yanzu daddy idan wani ne na kusa dakai ya aikata maka hakan ya zakayi??

"Jin irin tambayar dayayi mishi yasa daddy ruɗewa yana saƙe-saƙe, dan yama rasa amsar da zai bashi sai yake tunanin kodai shine? "bazato kawai Abdul yaji yace toh ko kaine? Gaban Abdul ya shiga dukan uku uku, gashi ba halin yace "eh kuma su samu matsala dashi idan kuma yace "a'a yayi ƙarya. Duk ji yayi ya burkice, kwanyar shi taɗau zafi, ya shiga cikin "RUƊANI" sabida tsananin tunane-tunanen da yakeyi.

  Daddy da gabaɗaya ya shiga cikin damuwa da kuma "RUƊANI" dan ya kasa gane ma Abdulraheem ɗin "yace wai Abdul lafiyan ka ƙalau kuwa, naga duk yanayinka ya sauya. "Abdul ya ɗago idonshi da suka koma kalar ja danya shiga cikin danasanin dalilin dayasa ya amince wa abba suka sato Amatu, "runtse idonshi yayi da ƙarfi ayayinda yake tunanin lallai ya zama wajibi ya sanar ma daddy komai tunkan lokaci ya ƙure musu. "Buɗesu yayi ya ɗora kanna daddy "yace daddy dan Allah ka dubi girman Allah ka yafe mana laifin da muka aikata maka nida abbana, "wallahi sharrin sheɗan ne da kuma rashin haƙuri irin namu, dan Allah ka yaf.......

A razane daddy ya miƙe tsaye kalli Abdul da idonshi suka canza launi, cikin dakiya yake magana, "yace Abdul yanzu kanason kace mun harda abbanka aka haɗa baki wurin sace ƴata? To akan wani dalili?  Abdul ya katse shi ya fara bashi labarin abunda ya faru. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace lallai biri yayi kama da wando. A ɗan tsawace yace yanzu Alhaji ibrahim saboda kuɗi zai sace mun ƴata?? "Wallahi naji mamakin haka kuma kaima ka bani mamaki, "shi idan kuɗi sun rufe mashi ido ai kai bai kamata su rufe maka ido ba.

"Girgiza kai daddy ya shiga yi haɗe da cewa babu komai kawai ka tashi ka wuce. "ko alamar tashi Abdul beyi ba illah kamo ƙafar daddy da yayi yana roƙon shi dayayi haƙuri, cike da jin takaicin Alhaji ibrahim wanda ya harya shafi Abdul tunda shine ma ya sato Amatu da kanshi ya fisge ƙafar shi daya riƙe yace Abdul ka tashi ka wuce nace ko? Ya faɗa da babbar murya.

"Ƙwallah ce taf a idon Abdul wanda su basu zuba ba kuma basu koma ba balle ya rage jin haushin kansa dayake ji a yanzu, "ɗago kanshi yayi da niyar magana sai yaga wayam, daddy baya palon, "duƙewa yayi a wurin kusan tsawon minti talatin kafin ya tashi daƙyar dan yadda ƙafar shi tamai nauyi ya fice daga palon "A farfajiyar gidan ya tsaya yana kallon ko'ina sedai babu alamar motar daddy da alama dai yabar gidan, shima jan jikinsa yayi ya shige motarsa da tunanin halin da abba zai shiga idan yaji yadda sukayi da daddy gashi yayi mishi alƙawarin duk yadda za'ayi bazai taɓa bari abokantakar su ta samu matsala ba, amma ga yadda lamarin ya kasance.


******* ******* *********
""""Keeeee" dakata ya faɗA da sauri haɗe da ƙarasawa wurinta ya riƙeta yace haba baby ya kikeson kisani asara biyu? Gaskiya karki kuma hakan. "Tsuke bakinta tayi ta turo shi gaba wanda ba ƙaramin sha'awa suka ba Abdulrahman ba tace toh toh niba ɗaukowa zanyi ba? Abdulrahman yace to bagani ba tunda tsawonki baze kai ba basai kice in ɗauko maki ko?

   "Ɓata rai tayi ta wani juya mashi baya da niyar sake hawa kan kujerar, Cike da jin haushi ya wani fusgota da ƙarfi ta faɗo jikinshi, cikin faɗa yace, wai meyasa bakya jin magana ne, sau nawa zan faɗamaki kibar wannan haye-hayen tunda ba abun dole bane, kuma kina ganin yanzu bake kaɗai kike ba ammai sai kiyi ta wani abu ƙaramar yarinya, yanzu idan wani abu ya sami babyn mu me zakice iyeee??

  "Kuka tasa mashi ta fice da gudu daga kitchen ɗin, shi kuma kallonta kawai yayi harta wuce sannan yasa dogayen hannun shi saman drower ya buɗe ya ɗauko wata farar roba mekyau me ɗauke da zuma, kan ya fito daga kitchen ɗin da niyar haurawa sama dan ya ɗauka ko ɗaki ta wuce ashe tana palour hakimce saman kujera. Murmushi yayi ya isa wurinta ya duƙa agabanta yace sorry baby na nayi laifi ayi mun afuwa, ya faɗa cikin marairaicewa at d same tym kuma yana miƙa mata zumar.

Murmushin itama tayi ta karɓi roban ta

21 / 27