Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
suma b'angaren amare zasuyi wankin amarya.
Duk ji nayi gidan babu dadi saboda ba casu sai wani hayaniya da mutane suke tayi. "Shiyasa kawai na fice daga part d'in na wuce part d'in Abdulraheem sedai kuma baya nan. Haka na jawo kafata nama fice daga gidan ina murmushi dan tunowa da nayi ko suna gidan mummy.
"Nan na tari taxi, nayi mashi kwatancen gidan da zai kaini. Bayan mun isa gidan ne, na nemi kudi na rasa, nace toh fah masu hali sun nuna mun nasu halin, dan duk inda ake biki toh fah barawo yana nan.
"Mai mota ko tsaye yayi mun wai sai na bashi kudin shi nikuma ina ta rokon shi amma fur yaki, muna nan sai ga Abdulrahman da Abdul sun, ganin kamar ana cecekuce yasa suka karaso wurin. Da fara'a ta tun kafin su nemi sanin ba'asi na fad'a musu, nan Abdul ya ciro 2k ya mikawa mai motar, duk da kudin shi beko kai rabin kudin ba.
"Bayan me motar ya wuce ne, nima ya zaro 10k ya bani, "Abdulrahman kuwa ko murmushi baeyi mun ba, nikuma ko ajiki na daman Abdul nakeson gani kuma na ganshi.
"Daga nan suka wuce nikuma na shige cikin gidan, "nan ma kodana shiga babu wani alamun akwai casu sedai cikin farfajiyar gidan nasu dana gaan fara decoration d'in wankin angon da za'ayi gobe.
Dake gidan bekai cikar gidan ammie ba, a free na wuce, "ina tafiya had'e da yin yan kalle-kalle na har bansan sadda na bugi wani abu kamar mutum ba.
Dagowar da zanyi inga ko mena buge keda wuya naji saukan mari a fuska ta. "Me zanyi inba dafe k'unci na ba. Bude idona nayi inga ko wace yar iskan ce ta mareni. Karaf idona ya sauka akan lubna da kwata-kwata fuskar nan tata babu annuri, "cike da haushin ta, cikin raina nace toh meya kawota??
Ina cikin wannan tunanin ne naji an bangajeni an wuce, "firgigit na dawo daga duniyar tunanin dana Lula, kafin na buga mata tsuki na shige gidan dan inga abunda ke faruwa a ciki.
Bayan na shiga ne na tarar da umma sai fada take kamar zata tashi sama, "mummy kuma na gefe tayi tagumi. Tsaye nake har na tsawon minti goma umma na fad'a daga bisani ta sarara, mummy kuma ta shige dakin ta.
Tsaye nayi ina rarraba ido, dan bansan ko wa zan tunkara inji dalilin fad'an ba. Haka na gaji da tsayuwa na juya zan wuce sai mummy data fito daga d'aki ta kirani. "Kafa ta na rawa na isa gabanta. Wata farar leda ta miko mun wanda bansan ko menene a ciki ba tace inkai wa umma.
"Wani daki dana ga umma ta shiga nan nima na shiga, "a bakin kofar na tsaya dan ji danayi umma nata kuka ina tsoron karna shiga fad'an ya dawo kaina. Sai dana ga kukan nata ya lafa ne kafin naja kafata, jiki a mace na isa wurinta, hannu na rawa na mika mata.
Ansa tayi ta ajiye nikuma na fice da sauri.
Readers mu had'u a next page insha Allah dan jin yadda wannan al'amarin zai kasance.
Plsss share
[2/26, 6:49 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Readers plsss kuyi hakuri da rashin jina da zakuyi na kwana biyu sbd ina d'an da wani biki ne, kuma bazan iya cewa ga ranar da zaku jini ba amma Insha Allah da mun gama hidimar mu zaku jini. I love all my fans ❤❤
Page 69-70
Mummy ce ta shigo d'akin da umma take dan ta gaji da jin kukan nata, zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta dafa ta, cikin sanyin murya tace, umma wai dan Allah yaushe zaki bar kukan nan ne? Duba fa ki gani tun da la'asar kike a haka kuma kinsan akwai baki masu shigowa ko so kike su fahimci akwai wani abu?
Cikin shash'sheqar kuka umma tace "dole inyi kuka, wannan abun kunyar da yar isakan yarinyar nan tayi mun ai ya isa yasa nayi kuka. Kuma fisabilillahi yanzu ta kyauta mun kenan?
Mummy da duk bataji dadi ba tace "umma kiyi shuru mana, wallahi nasan wannan d'anyan aikin da lubna tayi ba bayin kanta bane, kuma ai kuruciya ce ke damunta, plsss kiyi hakuri ki cire komai a ranki, kinsan banason kowa yaji wannan abun ko.
"Umma tace nasani amma wallahi yarinyar nan ba karamin bata mun rai tayi ba, ji yadda nake nuna maki cewa ko maganar yaronnan sam batason ayi mata, ashe munafunta ta takeyi.
Mummy tace umma, "kiyi hakuri mana, d'an yau fa ka haife shi ne baka haifi halin sa ba, "kuma tunda dai abunda taso ta aikata beyi ba ai sai mu gode ma Allah, "kinsan dai da ace Allah ya bata nasara ai da kashin mu ya bushe, daga ku har ni d'in.
Tau Alhamdulillah Allah ya takaita, "share kwalla umma tayi tace yaya nagode da Allah yasa kece ba wata ba kuma insha Allah wani abu makamancin haka bazai sake faruwa ba. "Mummy tayi murmushi tace yauwa ko ke fah, yanzu sai ki tashi kiyi sallah muci gaba da aikin mu ko. "Itama da murmushi a fuskarta ta amsa da toh sannan ta tashi ta shiga toilet. "Mummy ma fita tayi daga d'akin.
******** ******** ********
Lubna na fita daga gidan mummy, gidan wata kawarta dake aso drive ta nupa, bayan taje sun gama gaisawa ne kawarta ke tambayar ta lafiya ta ganta a haka? Nan lubna ta fara kuka tace wallahi Khadija na tafka b'arna da yawa, "cikin son jin abunda ta aikata tace lubna me kikayi ne haka?
Lubna ta share hawayenta tace "duk abunda na aikata zee ce ta zuga ni, Khadija tace wace zee kenan? Lubna tace zee auwal mana. Khadija tace ina kika had'u da ita, ita dake kano meya had'a ta dake da kike nan abuja??
Lubna tai ajiyar zuciya tace, "ai yanzu na koma garin mu da zama saboda Abdulrahman, tun bayan komawa ta umma ta tace mun tunda shi baya sona nima kawai na hakura dashi. Sai nace mata toh kuma ni kwata-kwata na rabu dashi, wallahi ko maganar shi banason ayi mun, kinga umma harda dad'i taji saboda na cire wa kaina damuwa.
"Wata rana na fita sai na had'u da zee, Kinsan kuma tasan ina son Abdul, data tambaye ni ina yake shine nake fad'a mata ai na rabu dashi, "shikenan fah ta fara cewa ai bai kamata in rabu dashi ba ai gashi gashi. Nan ta fara zugani harda cewa ai aure kamar anyi shi nw an gama.
"Nikuma lokacin akwai d'an sauran sonshi a zuciyata shiyasa kawai na biye mata tace kar in damu yaushe zanje gidan su dan akwai abunda take son ta bani, " nace mata bansan lokacin da zanje ba, "sai kwatsam kawai naji labarin zai yi aure, sai na fake da haka nace ta bani.
"Ni na d'auka wani abun ne zata bani sai gani nayi ta bani wani kullin magani, wai insa mashi a cikin abinci daya ci zai ce ya fasa auren waccen ni zai aura. "Da farin k'in ansa nayi saboda ina tsoro kar asiri na ya toni, "amma dake zee macuciya ce haka tayi ta Jana da dad'in baki har na yadda na amince.
"Bayan munzo gidan su ne yau d'innan mummy tace in kaiwa Abdulrahman abinci can part d'inshi, "daman ina tunanin yadda zanyi ne sai kawai na amsa da fara'a ta na shiga kitchen na zuba mashi cikin plate sannan na d'auko kullin maganin zan zuba kenan sai ga umma da mummy sun shigo kawo kula.
"Nikuma saboda tsoro na yarda maganin a kasa, umma nagani ta karaso kusa dani, ta d'auki maganin tace miye wannan?? Cikin rashin gaskiya nayi mata shuru dan bansan abunda zance ba kuma taga lokacin da maganin ya fad'o a hannu na.
"Tayi ta tambaya ta miye wannan na fara inda, inda, mummy ta karaso wurin ta dafa ni tace miye wannan? Nan ma nayi shuru shine umma dataji haushin shurun danayi ta watsa mun mari, " nan da nan na fara zubar hawaye, still tana tambayata ko miye amma baki na yayi mun nauyi na kasa magana.
"Haka ta kara d'age hannu ta watsa mun mari, daga nan mummy ta rike ta tana cewa tabar mari na. Umma tace bazata bar marina ba Har sai na fad'a mata ko miye, "nan zuciyata ta raya mun kawai in fad'a mata dan nasan halin umma da zafi take, kuma tana da tsanani sosai.
Nan na fad'a mata ko miye, "aikuwa tun kafin in gama fad'a mata ta dinga mari na a ko'ina na jiki na, mummy na tareta amma sai turjewa take. Haka ta gama jibaga ta sannan ta fara fad'a tana zagi na tace in fice daga gidan batason gani na.
Mummy taja hannu na muka fito palour, inda mutane ke zazzaune sedai basu san taka maiman abunda ya faru ba amma suna iya jiyo fad'an da umma keyi. Daki mummy takai ni tace in wanke fuska in wuce koda gidan kawata ne tunda umma tace sai na bar gidan.
Nan na wanke fuskata cike da jin kunyar mummy dan nasan tana ita ne amma da wata ce bazata taba rufa mun asiri ba. "Nan na share guntun hawayen daya zubo mun, "na fito daga d'akin mummy na biyo ta palour sum sum na wuce ina jin umma ta fito palour tana fad'ace fad'acen ta.
Ajiyar zuciya Khadija ta sauke, "tace gaskiy lubna kinyi sakaci da kika bari zee taci galaba akan ki, "idan fa baki manta ba zee muguwa ce ajin karshe, yanxu gashi takai ki ta baro. Amma wallahi Allah ya wadar da mai hali irin na zee.
"Uhmm lubna tashi kije kiyi sallah ki dawo, "nan lubna ta wuce toilet ta d'auro alawla dan gabatar da sallar magariba.
Washe gari
Su amare na hango sanye da dogayen riguna masu kyau kalar ja da adon duwatsu agaban rigar su. Amatullahi na fara kare ma kallo naga iya wankuwa ta wanku, "dana leka mayafin ameerah naga itama ba karya ta wanku.
Nan na juya, "na kare ma wajen kallo, sai naga fili ne amma an kawata shi da kayan alatu masu Jan hankali, "mutane na fara kallo, ina ganin kowa da irin wanka daya d'auka, can na hango,
Habiba Usman, teema, hawwer, babyn MD, ummi baita, hassy, Ayeesha, swt aseeya da naima, sai faman kwasar rawa suke baji ba gani, dakyar na samu na tsayar da babyn MD nace ina sauran members suke?? Nan take fad'a mun wai sai gobe zasu zo dinner.
Gaba na kara ina ta kallon mutane kowa sai rawa yake yana raha, "nikuma kutsawa kawai nake cikin mutane ina d'auko rahoto.
Wurin wankin ango😎
Hmmm can na hango wasu kyawawan mazaje su biyu masu kama da juna. tsaye suke abokan su sun zagaye su suna musu liki, "kare musu kallo nayi naga Abdulrahman ne da Abdulraheem, sanye suke cikin yadi kalar brown mai masifar sheqi da d'aukan eyes.
Abdul rawa yake ba kunya ga uwaye nan da kannai suna kallon shi sai faman cashewa yake, "saboda jindadi da nuna farinciki yaje ya yawo hannun ammie da mummy yasu a tsakiyar su, "nan kowa ya basu fili ammie da yan biyun ta suna dansewa, "duk yadda taso kar tayi rawa amma saboda ta nuna farincikin ta ga ya'yan nata sai ta gyara mayafin ta had'e da ciro bandir d'in yan dubu dubu cikin purse ta fara musu liki tana takawa. "Mummy kam tuni ta fara rawa tana musu watsi da kud'i.
Inaaa DJ saboda rikid'ewa volume din wakar ya kure, MC kuwa sai wasa su yakeyi, "masu eyes kuwa kowa ya kara bud'e su yana kallo ana tafa musu had'e yin ihu, ammie kuwa ji take kamar ba ita ba, dan rawa ba damunta yayi ba, haka tayi ta rawa dasu har sai da wakar ta kare kafin suka tsaya.
Ammie na fitowa mutane suka shi ga rungume ta ana dariya, hanan da tunda take bata taba ganin ammie na rawa ba ta karasa wurin ta tana dariya dan taji dad'i sosai.
Su yan biyu kuwa ai duk farincikin mu bamu kaisu ba. Haka akayi ta raye raye har kusan magariba kafin taron ya watse.
Washe gari
Plss comments
And share
[3/1, 4:42 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون
May Allah shower his Rahma & Salama on you. Prevent any evil act from reaching you & decree you to end with the most pious & beautiful acts. And May Allah uplift your value, forgive your past, grant you and your Family manifest Victory Fid-duniya Wal-Akhirat. Ameen. '''Jumma'at Mubarak.'''
Page 71-72
Washe gari
Ko wane b'angare na gidajen yau babu wani hidima da ake illa shirye-shiryen zuwa dinner daga gefen amare har izuwa na ango.
Da misalin karfe takwas da rabi na dare.
"Sanye suke cikin wani dakakken shadda riga da wando da babbar riga kalar baki mai sheqi da walk'iya, "daga gaban rigar anyi musu aiki da golden d'in zare. Kowannensu yasa agogo golden had'e da hula da takalmi golden.
Wankan turare akayi musu a yayin da fuskar nan tasu cike take da annuri, "ga wani masifar kyau da haske da suka kara yi. "Domin kuwa kalar kayan ba karamin amsar jikinsu yayi ba. "abokan su kuma sanye suke da yadi milk mai sheqi. "Bayan an gama kammala shirya su ne aka fito dasu waje nan inda aka paka wasu sabbin motoci.
"Motoci ne a kalla zasu kai ashirin, jere, "tun daga farfajiyar gidan har zuwa can wajen gida, "sedai guda biyun nan a tsakiya suke, kuma an kawata su da flawoyi masu d'aukar hankali.
"Wasu daga cikin abokan ne suka ja hannuwan su Abdul suka sa kowanne cikin tashi motar. "Daga na suma suka shiga sauran motocin suka fice daga gida. Bayan fitar su direct gidan amare suka nupa.
A lokacin amare sun sha kwalliya, "har baka iya ganesu saboda tsabar kwalliyar da akayi wa fuskar su, "sanye suke da wasu irin kaya masu kama da Arabian gown fari kal.
Ko waccen su rik'e take da d'an karamin purse golden colour da d'an uban su takalmi mai tsini shima kalar purse, "sai mayafin da aka yafa musu mai raga-raga, "wanda ya rufe duka ilahirin jikinsu. Ga doguwar rigar da suka sa sai jan kasa take sosai, dan lokacin da za'a fito dasu sai da kawayen su suka rirrik'e musu shi ta baya.
"Haka aka fito dasu ana gud'a har akasa ko wacce cikin motar angonta, sauran kawaye dake sanye da dogayen riguna kalar ja da d'ankwali milk, suma suka take musu baya ta hanyar shiga sauran motocin da aka tana dar domin su.
"Nan kowa ya tada tashi motar suka fara tafiya a Jere, "abun gwanin ban sha'awa. A cikin mota kuwa Abdul sai kallon ameerah yake tayi, "ji yake kamar ya rungume ta. Gashi duk yadda yaso su had'a ido taki ta bari.
Abdulrahman tun daya ga Amatullahi yayi mutuwar zaune, "dan ba karamin kyau tayi masa ba, haka itama sai taga yafi ko wace rana kyau. Ba laifi Amatu ta saki jikinta suna hira da Abdulrahman sakamakon ameerah da gabadaya kunyar abdul ta lullub'e ta. Haka sukayi ta hira har sadda suka iso shahararren hall d'in da za'ayi event d'in.
Koda suka iso mutane da dama sun hallara, a ciki, a bakin Hall d'in aka shirya yadda za'a shiga ciki. Samha da hanan dake sanye cikin dogayen riguna baki suma sun sha kyau su akasa a gaba a matsayin flower girls.
Daga su sai Abdulrahman da Amatullahi wanda suma sun jeru da juna suna takowa a nutse, bayan su kuma, abokan Abdulrahman ne da kawayen amarya kowa da partner d'inshi.
Daga su sai Abdulraheem da Amatullahi suma bayan su abokan shi ne da kawayen ameerah, "suna take musu baya. Tunda suka sa kai suka shigo hall d'in ya d'au wani irin duma, wanda ko a ina kaji shi, ko bakayi niyar rawa ba sai kayi. Haka sukaci gaba da tafiya masu d'aukar hoto sai haska su sukeyi da kuma masu wayoyi duk sun zageye su ana d'auka.
Bayan sun kai mazaunin su ne kowa ya nemi wuri ya zauna, nan MC ya fara su jawaban shi daga nan aka fara su programs wanda daga ciki aka buk'aci amarya da ango su fito su nuna nasu farincikin. Nan aka basu fili, "kowanne ya rikon tashi amaryar suna d'an takawa, Abdul kuma sai fama yake da ameera yana mata magana a kunne akan tayi rawa fur taki koda motsa jiki ne, tsaye tayi kamar wata gunki.
Abdul kuma ganin tana mishi taurin kai, "kawai baiyi wata, wata ba, ya saki hannuwan ta ya kama k'ugun ta yana girgiza wa a hankali, dan dole ta fara motsawa tana fakar mutane tana aika masa da harara.
Abdulrahman kam ba laifi shima yana d'an takawa dashi da Amatullahi. Mutane sai liki suke ta musu, can na hango readers ko wacce da wayarta a hannu tana jan selfie 😎 saura kuma kuce karya ne 😏😏
Sai kusan karfe d'aya na dare taron ya watse.
*************
Yau asabar wacce ta kama ranar da ake d'aurin auren ABDULRAHMAN ALIYU DA AMATULLAHI MUHAMMAD LEMI da kuma ABDULRAHEEM IBRAHIM DA AISHA USMAN (ameerah) akan sadaki duba dari, dari.
Inda aka d'aura aure anan central mosque dake garin abuja, "d'aruruwan mutane sun halarci d'aurin auren su domin taya su murna.
Bakin angwaye ko rufuwa bayayi saboda tsantsar farinciki, "haka ma su daddy suma sun matukar jin dadi da Allah ya nuna masu wannan rana, fatan su Allah ya nuna masu na y'an baya.
Bayan an dawo gida ne, ammie ta kawo musu ferfesun kayan ciki da jallof din shinkafa da drinks ta ajiye musu. Dake gidan ta suka sauka bayan an dawo daga d'aurin aure.
Saboda tasan ba lallai su samu wani isashen lokacin cin abinci ba yasa da aka kawo su ta rufe kofa ta kai musu abinci tace sai sun cinye duka. Kowannensu ya zaro ido yana kallonta, "Abdul yace ammie so kike cikin mu ya fashe ne?? Dan a kalla abinci data kawo ko mutum goma suna iya ci su koshi.
Hararar sa tayi ta