Author : LASHMINZY Category : Romantic Hausa Novels
haye saman gado.
Kunna wayarta tayi ta fara dialing number Abdul amma kusan kira biyar tayi mishi be dauka ba. Daman kamar ta sani dan ya hanata kashe waya kuma gashi yazo gidansu har sau biyu aikuwa yau ta shiga uku.
Wayar ta dauko zata sake dialing sai gashi ya kira, cikin dan marairaicewa ta amsa kamar wadda zatayi kuka ta fara bashi hakuri tana kashe mashi jiki da kalamai masu dadi saboda karya farayi mata fada.
Ba karamin tasiri kalaman sukayi a kanshi ba dan yama bar batun kashe wayarta datayi suka fara hira, suna cikin hirar take fada mashi ai dazu ta ganshi kuma taso tayi mashi magana sai kuma ya wuce. Murmushi yayi yace my baby ina kuma kika ganni haka??
My Abdul kusa da round about din shigowa shagon mu na ganka" shafo fuskar shi yayi yace ohh namanta, naje siyawa ammie fruits neh lokacin.
Shagwaba ta farayi mashi tana wani narke murya tana suburbudo mashi kalaman soyayya. Shi kuma jiyake ina ma ace tare suke" haka sukayi ta hira suna fayyace wa junan su sirrin zuciyar su
***********
Tsaye yake a daki sai kai kawo yake tayi kwata kwata ya kasa samun nutsuwa, gashi ya canza layi bale ya samu number ta. Laptop dinshi ya jawo yana dan wasu bincike daga karshe yayi addu'a ya kwanta amma sam ya kasa bacci sai tunaninta yakeyi.
'''washe gari'''
Abdul ne a asibiti acikin dakin marasa lafiyan da aka kawo kwana biyu da suka wuce. Su biyar neh, yammata guda biyu da maza uku sai baban su a gefe suna hira da Abdul dan har sun saba dan kwana biyun nan da sukayi.
Wani namiji daga cikin su wanda duk sun fishi samun rauni da yawa yace yaya wai yaushe zaka kawo mana amatullahi din ne mu ganta naga kullum in muna hira sai kayi mana maganar ta.
Murmushi Abdul yayi yace karka damu ai zaku ganta da zarar na sallameku har gida zan kawo muku ita. "Cikin zumudi fiddausi (kanwar shi) tace Allah yaya da gaske? Girgiza mata kai yayi alamar eh.
Baba kuma sai kallon su yake yana jindadin yadda Abdul ya saki jiki dasu kamar wani dan uwansu na jini.
Bangaren Abdul kuma kamar yadda yaci kwalliya jiya yazo gidansu Amatu haka yauma "amma wannan karon a farfajiyar gidansu ya paka motar shi dan kuwa megadi ya bude mashi gate.
Tsaye yake ya jingina da motar shi ya nade hannuwan shi a kirjin shi yana kallon daidai saitin kofar da zata fito dan kuwa ya aika megadi yayi mashi sallama da ita.....
................
Plsss comments
And share
[2/11, 5:46 PM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Page 27-28
Fitowar ta kenan ta hangi motarshi ta wuce sakamakon kiran gaggawa da daddyn shi yayi mishi shiyasa ya wuce zuwa anjima ya dawo.
Itako wayarta ta dauko tasa kiran Abdul taji ko lafiya ya wuce " sai kuma akayi rashin sa'a bai dauki kiran ba dan yana can asibiti a dakin tiyata.
Abdulrahman direct office din daddyn shi ya nupa inda ya mika mashi wasu takardu na samun gurbin zama lecturer anan BASE UNIVERSITY dake cikin garin abuja.
Karbar takardar yayi ya zauna daya daga cikin kujerun da'aka tanadar wa baki" kafin yasa hannu acikin takardar sannan ya mikawa daddy yana mai gode mashi kafin ya bar office din.
Abdulraheem kuma sai yanxu ya fito daga dakin tiyata inda ya tarara da missed call din amatu kusan guda goma harda kuma sakonni dan ita a tunanin ko yagaji da jiranta ne yayi tafiyar sa shiyasa tayi ta kiransa harda tura masa sakon yayi hakuri.
Kayan tiyata ya cire kafin ya bude dan karamin fridge din dake office din ya kwankwadi ruwa. Sai dayaji baya jin kishi sannan ya ajiye ragowar ruwan saman teburin shi ya zauna.
Ammie ya fara kira dan itama tayi mashi kira biyu. Bayan ya kirata ne sai ya kira Amatu,"cikin yanayi na mamaki yace Amatu lafiya kuwa naga missed call dinki har goma ga kuma wani sakon hakuri duk na menene???
Shuru tayi kamar me tunani dan ta kasa fahimtar sa" toh miye yake nupi da hakan?? Katseta yayi da cewa baby ki daina damuwar kanki mana nasan dai akan jiya kin kashe wayarki ne kuma ai wannan ya wuce.
My Abdul ba... Yace no stop it koma me kikayi mun na yafe saboda nasan bazaki bata mun rai da gangan ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace nagode my Abdul Allah yabar mu tare.
Amsawa yayi da ameen daga bisani yayi mata sallama akan yana aiki zuwa anjima idan ya fito daga asibiti zai zo gidan su.
Yana gama waya da ita ya tashi ya nupi dakin su fiddausi, baba ya tarar yana hada kayan su dan an basu katin sallama. Da fara'a a fuskar baba yace dana harka shigo kenan??
Eh baba ai tun dazu naso in shigo sai aka kawo wata mara lafiya yanxu haka tana dakin tiyata.
Tagumi baba yayi yace Allah sarki kudai kuna ganin abubuwa iri iri "Allah ya saka muku da alkhairi akan taimakon jama'a da kukeyi, amsawa yayi da ameen kafin baba yace kaga waccen yarinyar burina ta zama likita amma rashin jinta ya hanata zama tayi karatu" baba ya fadi maganar yana nuna fiddausi da dan yatsar shi.
Murmushi kawai Abdul yayi yana kallon fiddausi data wani tamke fuska jin baba yace bata jin magana. Sauran yan uwanta ko sai dariya suke mata.
Baba na gama shiryawa suka fito zasu wuce, daya daga cikin su wanda ke dingishi kadan yace baba wai yanxu ina zamuje?? Ina fatan dai ba gidan mahaukaciyar matan nan zamu koma ba?? Wani irin kallo da baba ya gefeshi dashi neh yasa yin shuru be kara magana ba har suka iso inda baba ya paka yar 406 dinshi.
Abdulraheem kuma yana biye dasu sai dai hankalin shi bekai kan maganar da sukeyi ba. Sallama yayi musu harda karban number baba yayi saboda sun rika gaisawa.
Bayan sun wuce ne Abdulraheem ya koma office ya fara hada yan tarkacen shi dan dama baya dutyn dare sedai in wani abun gaggawa ya samu neh yake zuwa amma shi a asibiti baya wuce six yake dawowa gida sai kuma da safe.
Yana gamawa yayi sallama da abokan aikin shi ya wuce gida " kodaya koma gida a gajiye yake shiyasa ya kira Amatu yace tayi hakuri bazai samu zuwa ba sai gobe. Ita kuwa bata damu ba saboda tasan yanayin aikin likita ako wani lokaci aiki kan iya gitto musu.
Basu dade suna waya ba ya katse kiran sannan ya shiga bandaki ya watsa ruwa. Bayan ya fito ya sanya wasu kananan kaya masu kyau sannan ya nupi part din ammie.
Palour ya sameta ita da hanan suna cin abinci, gaishe da ammie yayi sannan shima ya samu wuri ya zauna yasa hannu suna cin abincin tare kuma suna dan taba hira.
'''Bayan sati biyu'''
Abdulraheem neh tare da auntyn shi wato kanwar mahaifiyar shi maryam, suna tattaunawa neh akan bikin shi dan yanxu saura wata daya da sati biyu ayi bikinsu.
Maryam kasuwanci takeyi inda take dauko kaya tsadaddi daga dubai" kama daga less, atampa, shadda, takalma da dai sauran su. Shine ammie ta kirata suna son ta hado musu kayan lefe masu kyau da tsada yadda duk wanda ya gani sai ya burge shi.
Abdulraheem dake kusa da maryam yana fadar kalar kayakin da amatu tafi sawa da kuma kalolin su tace kai malam ya isa haka mana " ta fada a dan tsawace. Murmushi yayi yace haba aunty nifa sonake in bata mamaki" bakiga gidan da za'a kaita bama penti kalar da tafi so nasa akayi mata ba??
Hararan shi maryam tayi tace tau naji nidai yanxu ma wucewa zanyi dan ina ganin gobe ma zan wuce, duk wani abu daka tuna kayi mun waya kaji ko?? Amsawa yayi da toh sannan ya tashi ya basu wuri.
Bayan ya fita ne ammie ta kalli kanwar tata tace maryam ki fita harkar yaron nan nidai duk wani kaya da kikasani na kece raini ki siyo sannan kuma akwatuna ki turo hotunan su a waya sai na zaba mashi, kinaji na ko?? Eh aunty.
Haka sukaci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da mijin maryam yazo daukarta suka wuce.
A bangaren Abdulrahman kuma ji yake kamar zuciyar shi zata fashe, gabadaya kwana biyun nan duk ya shiga damuwa saboda rashin ganinta. Kusan kullum sai yaje gidansu sai ya tarar da bata nan, wani sa'in kuma sai ya kama hanyar zuwa gidansu wani uzuri ya gitto mashi.
Ga kuma wannan jarababbiyar yarinyar data like mashi kamar cingum. Ita kota ganshi cikin damuwa bata iya tabuka komai sedai ma ta nemi kara bata mashi rai.
Yauma zaune yake a gaban mirror sai kace wata mace, yana shiryawa da niyar zuwa gidansu Amatu dan yau ya kudurta wa ranshi duk yadda za'ayi sai ya ganta dan kuwa cewa yayi koda yaje gidansu bata nan zama zeyi har sai ta dawo tunda ta zama me kafar kaza.
Niko nace a wurinka dai ta zama mai kafar agwagwa, dan rainin sense kawai😏😏
Lubna ce ta shigo dakin da fara'a a fuskarta, kusan minti biyar ta kwashe tana kallonshi dan ba karamin kyau ya mata ba, shi kuma gogan ko ajikin shi dan ya saba da halinta. Wani lokaci haka kawai sai tazo dakinshi tayi tsaye kamar wata gunki tana murmushi tana kallon shi yana kai kawo shi kadai.
Kuma ko kala baya ce mata sai dai ta gaji ta wuce ko kuma shi yabar mata dakin. Yanxu ko zuwa tayi zata zauna bakin gadonshi ya daka mata tsawa sai data razana.
Cikin huce takaici yace wai ke wace kalar yarinya ce?? Sau nawa zance karki kuskura ki kara taba wani abu daya shafeni??? Iyee dake nake.
Shuru tayi batace komai ba dan tasaba da irin wannan wulakancin. Tsuki kawai yaja yadau key din motar shi zai bace ya fice ya barta a wurin.
Ita kuma kuka tasa ta daura hannuwa saman kai 🙆 ta rasa ko wace irin narkakkiyar zuciya gareta ko tayi kokarin ta cire shi a ranta sai taji bazata iya ba. Kuka tayi sosai kafin ta shiga toilet dinshi ta wanke fuskar ta ta fito.
Abdulraheem kuma yana wani mall yana ma Amatu shopping, kayan kwalama kawai ya siya mata kafin ya biya kudi ya fito. Wani Abokin shi ya gani a daidai shiga malla din, nan suka tsaya suka gaisa daga bisani kuma ya shige motarsa ya bata wuta
Amatu kuma tana can gida tana hadawa Abdul dinta delious, bayan ta gama ne tayi wanka tayi kwalliya tasa wata doguwar riga mekyau kafin ta fito palour.
Zama tayi saman kujera tana jiran isowar Abdul, aikuwa bada dadewa ba sai gashi ya kirata, yace ta fito kuma dai dai lokacin megadi yazo kiranta.
Murmushi Amatu tayi dan taga Abdul ya kirata kuma abun ma be isa ba sai daya aiko megadi. Mayafinta ta dauko kafin ta fito sannan ta sanarwa mummy Abdul yazo.
Gyara gyalenta tayi da murmushi a fuskarta ta nupi hanyar fita waje.................................
Nan birona ya fadi saboda bansan yadda haduwar tasu zata kasance ba🤷🏻♀
Plsss share
[2/12, 1:27 AM] Lashminzy😎: 💫🌞💫🌞💫🌞💫
*RUDANI*
💫🌞💫🌞💫🌞
Story & written by
Lashminzy
💥GÕLDÊÑ"S WRÌTÊRS
ÀSSÔÇÎÃTÎÒÑ💥
'''vote me on wattpad @lashminzy'''
Ina matukar jin dadin comments dinku, kamar yadda kuke bibiyar book dinnan haka nima nake bibiyar ku a cikin raina.
I love u all gabadaya ❤
Page 29-30
Tun kafin ta karasa ta hangeshi jingine da motarsa, sai wani murmushi yake faman zuba mata, itama haka dan kuwa duk tunanin ta Abdulraheem neh.
A hankali ta fara tafiya harta karaso kusa dashi. Ko kala bata ce mashi tayi mashi nuni da hannunta akan ya biyota. Shi kuwa sai mamakin yadda ta tarbeshi yakeyi dan kuwa beyi tsammanin zaiga koda murmushin ta ba balle har takai ga bashi masauki.
Tana gaba yana biye da ita a baya har suka iso palon baki. Kujera ta nuna mashi ya zauna kafin ta fita, "bata jima ba ta dawo dauke da katon paranti a hannunta.
Gabanshi takai ta ajiye sannan ta dauki ruwa ta zuba mashi a kofi ta mika mashi, kamar mazari haka ya karba da sauri ya fara shan ruwan, sai daya shanye ruwan tas ya ajiye kofi.
Wani farinciki ne mara misaltuwa ya dabaibaye shi, daya bangaren zuciyar shi kuwa tausayinta yakeji yadda ko kala bata ce mashi ba saima sakin fuska daya gani daga gareta" hakan kuwa sai yasa yaji jikinshi yayi sanyi gashi yanason yayi mata bayani amma kuma ya gaza yana tsoron karya bata mata rai tunda yaga alamar tana cikin farinciki.
Kawar da tunanin yayi ya mayar da kallonshi zuwa gareta yace my Amatu kina burgeni saboda ke mace dayace tamkar dubu, kina da hankali da tarbiya ga kuma tunani, na bata maki rai a wasu yan lokuta da suka wuce, na sakaki a damuwa sai gashi ke daga karshe kin sanya ni a inuwar ki.
My Amatu duk abunda zanyi maki bazai iya goge laifin dana aikata maki ba, amma kisani ni Abdul na dauki alkawarin yi maki duk wani abu da kike bukata a rayuwa kuma insha Allah zan kasance mai faranta maki har abada.
Lumshe idanunta tayi ta kuma budesu ta dora akan nasa tace my Abdul plsss abunda ya wuce ya wuce mudai kawai mu roki Allah ya shige mana gaba duk wata maganar laifi kuma be taso ba" rayuwar mu kawai zamu fuskanta.
Duk fa a tunanin ta saceta da Abdul yayi neh yake kara bata hakuri fah dan daman wani sa'in idan suna hira sai ya dinga bata hakuri yana cewa kaddara ce tasa ya satota, toh shine fah take cewa ya wuce.
Amatu sai wani jindadi take gata ga Abdul dinta shima hakan ce ta kasance a wurin shi shiyasa yake ta wani kodata yana kashe mata jiki da kalamai masu dadi.
Abdulraheem bawon Allah yana can asibiti an kirashi, yarinyar da akayi wa tiyata ta rasu shine ya koma asibitin da gaggawa. Kuma harya iso gidansu Amatu aka kirashi amma dake yana da son taimako da tausayi da kuma kula da aikin shi sai ya juya ya koma asibitin.
Yanxu haka yana cikin asibiti tare da yan uwan yarinyar data rasu ana aunata kafin su bayar da ita.
Su Amatu kam ana can ana soyewa da Abdulrahman "yanxu haka a tsaye suke bakin motar shi wanda sunyi kusan minti talatin a hakan kuma wai sallama zasuyi ya wuce amma shine sukaci gaba da soyewar su.
Suna nan tsaye sai ga ameerah ta shigo, tunda taga Abdul ta fara danasanin shigowarta gidan, dan a cewarta datasan yana nan da bata shigo ba. Kuma ba abun ta koma ba tunda har sun ganta.
Karasowa tayi ta gaida Abdul kafin ta wuce ciki, Amatu kuwa sai cewa take ta jirata amma ko kallonta batayi ba ta shige cikin gida kamar ta fasa ihu dan jin yadda zuciyar ta ke mata zafi.
Basu dade ba yayi mata sallama ya wuce. Cikin gida ta dawo inda ta tarar da ameerah a dakinta, ameerah kuma duk damuwa ne fal ranta amma da jin shigowar Amatu sai ta kawar da duk wata damuwa dake fuskarta.
Murmushi Amatu tayi ta hauro saman gadon tana kallon ameerah tace nace ki jirani shine kika wani wuce ko?? Hararan wasa ameerah ta aika mata tace toh sai in tsaya kuna soyewa a gabana kome??
Dariya amatu tayi ganin yadda ameerah ta bata rai kamar masu fada, " nan kuwa batasan duk zafin kishi bane.
Kawar da hiran ameerah tayi suka shiga hirar abubuwan da za'ayi na bikin Amatu wanda duk ameerah ce ke fadin abunda za'ayi da kuma yadda za'ayi.
Bayan sallar isha'i Abdulraheem neh ya kira amatu yana bata hakuri akan rashin zuwan shi, dake dazu Abdulrahman yace ze dawo ya kawo mata wani abu sai kawae tace ya daina bata hakuri ai sun zama daya itama ai watarana tana iya bata mashi laifi.
Murmushi yayi yace baby na kenan ni wallahi na matsu ba'ayi auren nan ba nasan idan muna zaune a Inuwa daya komin daren dadewata a aiki kullum sai munga juna.
Um um tace, shiko yace miye um um badai dan na ambaci aure ba zakice kunyata kikeji?? Saurin girgiza kai tayi kamar tana kallonshi tace nidai bance haka ba.
Dariya yayi yace wallahi baby ji nake kamar a daura mana aure gobe.
Laaaaa hmmm nidai banaso ta fada cikin tsokana, shi kuma har yaji babu dadi yace waton daman ni kadai ke kidina ko?? Sai tace a'a my Abdul ai nima ina so kawai dai bana zumudi ne saboda kar mutane suce wannan amayar da hazonta take.
Dariya takeyi shi kuma ya bata rai yace waton ni ango ni nafi kowa zumudi ko?? Cikin dariya tace eh mana gashi sai wani murna kake kana jin kamar ma ace a kawo maka ni gobe!
Kyacci yayi mata yace zaki gane kurenki neh dake da bakin ki me iya zaro zance idan kin shigo hannu. Shuru tayi masa dan tasan inda maganar tasa ta dosa yanzu tana biye masa zai fara wuce gona da iri shiyasa ma ta dauko wani labarin.
************
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, yau saura sati daya bikin Amatu, gidansu harya fara cika da mutane sai shirye shirye ake tayi.
Haka ma bangaren Abdulraheem suma suna can suna nasu shirye shiryen dan jiya suka kai lefe akwati saiti biyu da dubu dari. Masu kaiwa ma ba'a barsu a baya ba dan tukuicin dubu dari biyu aka basu bancin kuma gagarumin tarbar da sukayi musu dan abinci kala biyar sukayi kuma ko wanne da irin hade haden da akayi mashi.
Abdulraheem harya buga invitation card ya aikawa Amatu danta rabawa kawayenta shima a nashi bangaren duk abokan shi sun sani "lokaci kawai suke jira.
**********
Abdulrahman tun lokacin daya zo gidansu Amatu washe gari ya wuce Cyprus saboda wasu yan uxura, a lokacin da daddy ke fada mishi maganar tafiyan ba karamin tashin hankali ya shiga ba.
Kuma wani abun haushi shine tun washe gari daddy yakai shi airport da kanshi, duk ranshi bace dan beso tafiyar ba amma haka ya wuce,
Kwanan shi uku yaji bazai iya zama ba sai ya dawo gida, kwatsam sai ga daddy yazo Cyprus din, harda dan karamin zazzabi yayi saboda damuwa da tunanin ta kuma gashi shiba number ta balle ya kirata.
Haka yayi hakuri har kusan wata daya, sai yau da Allah ya kaddari zai dawo. Duk wani abu me mahimmanci ko kuma wanda zai iya sashi ya dawo Cyprus sai daya dauko shi dan