Chapter 1 Reading ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx Arewa Novels

ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 40

1 to 3K   out of 117.2K words

❣️

💫

ICEN DAMUNA❣️

💫

By

Rabi’atu ( Fulani )

🤍

Young Telented Writers Association (YOTA)

Alhamdillah dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin talikai Wanda ya bani Ikon fara wannan labarin nawa, yadda na fara lafiya ubangiji ya sa na gama lafiya.

A Har kullum Ina jinjina a gare ki mahaifiyata Abar alfaharina





Gaba ɗaya kacakon book ɗin Sadaukarwa ne ga Aminiyata ɗaya tilo

Amina Muhammad ( Maman Zahra)

TRUE LIFE STORY......

Page 01

Yau tun safe na ke tunanin rayuwata da yadda na ɗorawa kaina ɗawainiyar kula da mahaifiyata.

Can kamar me mafarki na jiyo muryar mahaifiyata tana ƙwalamin kira “ Sumayya! Sumayya” kafin ta sake kiran na uku na mike da hanzarina na dauki wani siririn ɗankwali na ɗora saman rigar jikina na fita.

“Mama gani...!!

Kallo na tayi cike da nazari kafin tace “ me yasami idonki ??”

Babu komai mekika gani”?

Na bata amsa tare da jefa mata wata tambayar...

“Banasan shaashanci me yasameki” ??

Ta sake jefa min wata tambayar cikin tsare Gida!!.

“Kaina ke ciwo kuma na kwanta na kasa bacci!” Na faɗa ina narai narai da idanu!!!

Kinsha magani ? Mama ta sake tambayata.

Baki natura gaba dan bana shiri da Shi,

“Zansha anjima” nace kawai a takaice.

Gyaɗa kai kawai mama tayi bata ce komai ba ta shiga wata maganar

“Kije wajen babanku yana shago kice masa babu abinci...!!!

Tsayawa kawai nayi ni ban tafi ba kuma ban ce komai ba!

Magana nake Miki kina jina fa!!” Mama ta sake maimaita wa dan ganin nayi jimm.

“Toh” kawai nace najuya.

Itama dai mama ta Riga tasan amsar, toh meye na wahalar da Kai kuma...!

Ina tafiya ina Mita ni kadai a cikin raina!.

Kaman yanda nayi tunani yana kwance.

“Assalamu Alaikum baffa ina wuni..??

Saida ya hade rai sannan ya amsa da “lafiya”

Nima na hade rai nace mama tace babu abinci!.

Bai saki fuska ba ya maida min amsa da cewa “Kice Mata banida kudi wata yayi nisa kuma banje aiki ba!.

Bance masa komai ba kawai na juya don daman na riga da na san amsar!.

Tafiya kawai nake amman tunanina yana kan inda zan samu kudi a yau ɗinnan.

Kafin na karasa gida na na samarwa kaina mafita wacce nake ganin zata fishsheni.

Ina shiga gidan na wuce ɗaki dan nasan acan zan samu mama,

Ina shiga na ganta nace: “mama yace bashida kudi.

Batace komai ba!

Najuya na koma ɗaki

Wayata kawai na ɗauko batare da dogon tunani ba nayi searching lambarta! Akan wata lamba na tsaya wacce aka rubuta

“Boss lady” na aika mata da kira, tana fara ringing na lumshe idona!

Ringing biyu ta ɗauka duk da Naji ta ɗaga ban buɗe idona ba.

“Besty Baki da kirki wallahi” ta fada bayan ta daga wayar batare da ta tsaya mun gaisa ba.

Nima ban damu ba na amsa mata da : “Ayyah besty Allah ba haka bane kina rainah!!!

Ykk!?

Ta amsa da “Alhamdulillah yau antuna dani kenan ? Ta ƙare da tambayata.

Nace : ba haka bane Besty kinata ine yanzu ??

Ina ni’ima hotel zaki shigo ne!? Besty ta bani amsa itama ba tare da ta ja doguwar magana ba.

Na ja ajiyar zuciya na ajiye “Eh” zan zo kudi nake so faka faka” na faɗa cikin yanayin da yake nuna lallai ina bukatar kuɗin.

Okay! BA matsala ki shigo kawai, Kuma Allah kika shanyani sai munyi faɗa dan ba ruwana da wani dodonki” tace min cikin kaushin murya dan tasan Sarai zan iya shanyata ɗin.

Dan murmushi nayi iyakacinsa baki kawai nace : Baki da dama bara na shirya just 1 hour kawai zaki ganni in sha Allah.

Ok sai kin ƙaraso...

Okay!!! Na amsa mata tare da ajiye waya.

Koda ta kashe shiru kawai nayi ina tunani jikina babu ƙwari.

Tashi nayi tare da shiga wanka, na saka hijab har kasa, na dau facemask da wayana na fito.

Mamah! Mamah!! Mamah!!! Na cigaba da kwalawa mama kira.

“Wai lpy kike ta kwalamin Kira kamar sabuwar makauniya” ?? Mama ta amsa min da faɗa_faɗa jin kiran da nake mata ya ƙi ƙarewa.

“kwari zani yanzun zan dawo” na faɗa ina tunkarar ƙofa.

Me zaki je yi a kwari ?” Mama ta jefo min tambaya.

“wajen yayanmu zani yanzun zan dawo zan karɓo saƙo”

Jim tayi kafin tace shikenan:

“karki Daɗe”

“Toh nace ina karasa fita.

Ina fita titi drop kawai na ɗauka ya sauke ni a bakin gate ɗin Ni’ima hotel,

Waya nayi mata ta fito ta sallami mai napep din muka shiga ciki.

Ba yau na fara Shiga hotel ba amman duk sanda zan shiga gabana yayita faɗuwa kenan, fuskata cike da tsoro.!

Juyowa tayi tana kallona tare da cewa:” wai bazaki dena tsoron mutuminnan ba ?

Bazaki gane bane bawai tsoronsa nakeji ba ina sonsa kuma har yanzun ban shirya rasa Shi a cikin rayuwata ba,”

Na faɗa fuskata cike da gaskiyar abinda nake cewa.

“Toh ai gashi nan a bayanki yana kallonki” cewar bestyna.

Jikina ne kawai ya dauki rawa sai ji kake dif diff difff ƙirjina yana dukan uku uku, cakk na tsaya a wajen na kasa juyawa kamar wacce aka dasa, ina jiyo takunsa yana nufomu bugun zuciyata yana ƙaruwa da ƙarfi.

Wata wawuyar ajiyar xuciya nasauke!! Jin maganar sa a bayana.

Yar buzuwa ce yau a gidan namu.

Juyawa nayi jikina babu kwari, na ƙaƙalo murmushin dole! Ƙasa ƙasa nace “barka manager kana lpy” ?

Alhamdulillah kepa ? Ya fada yana bina da wani mayen kallo kamar kura taga akuya.

“Lafiya nake” na fada idona yana kallon wani sashi dabam batare da na kalleshi ba.

Amma dai yau Ni aka kawowa ziyara ko ? Ya fada yana kallon Boss lady, dan yasan idan nice bazai ji bakina ba.

Uhm! Naga alamun idan kaga yarinyar nan har wani rawar ƙafa kake,” besty ta fada tana harararsa ƙasa ƙasa.

Ƴar dariya yayi mai sauti kafin yace:

“To Yanxun dai ba wannan ba fatan xaki bani aronta” ?

Idan nabaka menene tukwuicina? Boss lady ta tambayeshi tana karkaɗa idanu cike da bariki!

Karki damu ai kema kin san muna tare!.

“gaskiya to mun Gama magana da wani tun dazu ka bari tafito!” Boss ta kama hannuna muka juya zamu nufi cikin hotel din.

Da sauri manager ya sha gabanmu ya marairaice yace:

“Ina babbar yarinya baza’ayi haka dani ba, kinfi kowa sanin halinta, zata iya canza shawara yanzun nan.”

Kafin Boss lady tayi magana na tari numfashinta da cewa “ba fa daɗewa zanyi ba na cewa mama ba jimawa zanyi ba!.

Bai bari nakarasa ba yace “ahaff kinga halin nata ko”?

Dariya Boss lady tayi kafin tace “Kyaleta kawai yanzun dai muje shaf shaf”.

Juyawa kawai mukayi muka nufi office dinsa batare da wani ya Kara magana a cikin muba.

Ruwa ya kawo mana da lemo, nikam ko ta kansu ban bi ba.

Dan Allah kadai yasan tunanin danake adaidai lokacin....!!!

Ya dage yana ta Jana da hira, amman nakasa sakewa dashi duk da ba wannan ne haduwarmu ta farko ba.

Maganar Boss lady ce ta katse min tunani.

“Besty Bara naje reception na jiraki, Dan Allah karku Dade Dan nasan halinka.

Ban ce mata komai ba.

Tana fita ya matso kusa dani na Kara matsawa, dariya yayi kawai yace “Allah ya nuna min ranar da zaki dena haka yar buzuwa, ke kullum kaman bakuwa a harkar ?

“Nidai shiru nayi bance masa komai ba, Da ya cikani da surutu nace masa “nipah tafiya zanyi sauri nake”.

Da sauri yace “Ah ah kiyi hakuri Dan Allah taso mushiga ciki”.

Saida nagama Shan kamshina sannan natashi na bishi.

Ya Riga yasan halina, duk nacin da zai mun bazan cire kayana ba sai dai muyi haka.

Ba yadda ya iya haka ya biyemin Dan wani mugun lallabani Yake baya son abunda zai yi min nayi masa bore.

Yana tabani ina kaucewa, dan ji nake kaman yana zuba min garwashi a jikina.

Shi kuwa Ya dage sai sumbatu yake zubawa.

Nikam hawaye nake, na rufe fuskata cike da tunani da takaicin Ni rayuwata kenan a haka zata ƙare....???

Jin ya gama na tureshi a jikina natashi na fada toilet.

Banyi wanka ba Dan nasan da ƙyar idan wasan ya kare fuskata kawai na wanke da jikina.

Ina fitowa nasa hijabi nace masa “tafiya zanyi..!!

Marairaice min yayi kafin yace “Dan Allah kibari ayi second round, ko nawa kike so zan Baki........!!!!

Ganin kallon danake masa, da yanda na hade Rai tamkar ban taba dariya ba yasa bai karasa ba.

Sai kawai yace “Bani account dinki ??

Bani dashi sedai kabani cash...

Ba yanda ya iya haka yabani, na juya ko sallama ban masa ba, don wani mugun haushinsa nake ji, tamkar dole yamin bani na kawo kaina ba!.

Tana zaune tana Danna waya nace “Salma!

Dagowa tayi tana kallona haɗi da tambayata “har kin fito”?

Uhm! Gida zan zo na wuce.

Haba ya zaki min haka?

“kina min waya fa na Kira wani Gaye ya turamin kudi nakama daki yanzun ma haka yana can yana jiranmu..!

Harararta nayi kafin nace: Babu inda zani ni gida zan tafi... Kar mama tamin fada....

Naci da magiyar datakemin yasa nabita badan nayi niyyaba. Amman da sharadin minti 30 zanyi na tafi, tace ta yadda.

Muna zuwa ɗakin mukayi knocking.

Ya taso ya Bude saurayi ne. Kai da ganinsa basai ance maka wannan yaci ya tada Kai ba.

Ina tsaye yayi hugging nata, yayo kaina nayi sauri na kauce.

“Masha Allah..! boss lady! Wai a ina kike Samo kalan kyawawan ƴan matan nan ne” ? Ya fada yana kallona yana lashe baki kamar tsohon maye....!!!

Dariya kawai tayi, tace masa sauri take a hanya take ayi me yiwuwa ta wuce, bara najira Ku a reception.

Bata Jira cewar muba ta fita ta jawo mana ƙofa.

“Ƴammata ya sunan ki!!!.

Sunan Daya faɗane yasamun faduwar gaba na ɗago daga Danna wayar danake batare Dana shirya ba ina kallonsa.

Ganin kallon danake masa ne yasa ya Kara maimaitawa, bansan sanda nace karka Kara kirana da sunan nan bana so...! na fada da sigar kashedi...

Shiru kawai yayi ya tsaya kallona.

Malam sauri fa nake na katse masa tunanin dayake!

“Owk” kawai yacemin ya kashe light na dakin.

Shima duk yanda yayi na cire kayana naƙi, kuma nace masa baxan iya sex ba dan Bana da lpy.

Babu yanda ya iya haka ya biyemin da romance har yayi releasing natashi. Na shiga toilet da sauri nayi wanka,

Dan wlh hankalina gaba Daya yana gida.

Ina fitowa Naganshi shida salma ( Boss lady ) a haɗe da juna a kan gado, suna kissing ɗin juna da shafe_shafe,

Tsaki kawai nayi nace tafiya zanyi.

Duk yanda yayi Dani akan na bari yayi wanka yasaukeni, naƙi amincewa dan nasan idan aka ga ya saukeni yau raina idan yayi duba sai ya ɓaci.

Haka ya dakko kudi yabani, na juya ko sallama ban Bari munyi da itaba.

Ina tafiya ina tunanin waya aikeni hawa mota a saukeni a unguwar mu mazan gidan mu su ganni, ko suji labari nashiga uku..

Ina fita nasamu napep na hau drop yasaukeni na karasa gida da kafa.

Saida nazo gida kuma gaba na ya fara faɗuwa, da tunanin me zan cewa mama idan tace na daɗe.?

Sallama kawai nayi nashiga da shahada, sallah take Dan haka humaira ce ta amsamin. Tare da jefo min tambayar ina naje ?

Nace “inda kika aikeni uwata”

Shiru tayi bata ƙara Jan zancen ba, na dau buta nima nayo alwala nazo natada sallah.

Ina idarwa ban Bari mama tayi magana ba, nace mama yunwa nakeji” Na marairaice fuska, kuma dagaske yunwar nakejin...

Inda kikaje Basu Baki abinci ba”?? Ta jefeni da tambaya tana hararata.

Shiru kawai nayi ban Kara magana ba, “sai can nace wlh mama shagon mutane, bansamu nayi magana dashi ba, seda zasu tafi sallah kinga ma da kyar yabani 3k. “?

Na ɗauko ina nuna Mata, batacemin uffan ba” hakan yasa nace ina Salim ? yazo yasiyomin taliya nadafa!!!.

Yana jina ya taso nabasa kudin ya tafi da sauri.

Kallon humairah nayi nace : ina angel take ??

Tace “Tafita wasa”. Ban Kara magana ba naja bakina nayi shiru.

Ba jimawa salim ya shigo daga aiken da nayi masa, cikin abinda bai wuce 15mnts ba na kammala na zuba mana muka ci.

Dare yana yi boss lady ta kirani: ke wlh kinyi sa’a.

Nace Sa’ar me ?

“ Abdool fa yace min sonki yake!!!

Waye Abdul kuma ? Na fadi haka duk da na gane wa take so tace.

Kefa kinji matsalan ki wulakanci...! Ta fada cike da jin haushin ko in kula ɗin da na nuna mata.

Hmm..!!

Kawai nace Mata naja bakina nayi shiru.

Shikenan yanzu yaushe zaku hadu ?

Babu Rana! Nabata amsa Kai tsaye..!

“Dan Allah kibari wlh xaki samu kudi nima haka”.

Ki haɗashi da wata, amman bazai ƙara ganin me kama dani ba..!

Ganin xata faramin halin nata na magiya kawai na kashe wayata na kwanta..!

“Haka nayita lallaba kudin nan muna amfani dashi.

Gefe Daya ga nacin boss lady da abdool, Dan haka ba yadda na iya haka na tsaida mana ranar haduwa.

Ranar asabar da wuri nayi Shirin islamiyya, nasaka extra hijab a jakata nayi sallama da mama.

Dama munyi dashi a gidansu zamu haɗu babu kowa, gidan yana ƙofar nasarawa.

Ina fita! Nashiga bayan layin mu nacire hijabin makaranta nasaka na gida.

Na karasa titi na tari napep na fada masa inda zai ajiyeni, tun kafin nakarasa yana wajen yana jirana.

Ina zuwa yabawa me napep kuɗinsa na koma motarsa nidai gabana nata faduwa..!

Dan duk abuna bana zuwa gidan su saurayi saidai mu hadu a hotels...

Muka gaisa Sama Sama.

Muna zuwa ya saukeni a bakin layi yayi min kwatancen gidannasu da zan shiga... Bamu tafi tare ba saboda tsaro.

Matsalan da aka samu, nafarko namanta kwatancen, saida na kirasa a waya ya ƙara min kwatance,

Gashi layin da mutane a haka dai na dake na Shiga gidan...

Ina Shiga Naga maza wajen uku a zaune, na tsaya na kasa gaba, na kasa Baya,

Sai Gashi ya shigo yace na hau Sama hawa nayi kawai bawai dan ina ganewa ba, Dan wlh fadar irin tsoron Daya dirar min a lokacin ɓata Baki ne...

“Ya kawomin abinci da ruwa da lemo nace masa na koshi...

Ya zauna munkai 15 minute a zaune kawai mukaji wani mahaukacin bugun kofa...

Mikewa nayi tun kafin ya Mike ina tambayar sa waye haka ???

Ki kwantar da hankalinki, bara naje na dubo,ya fita wajen 30 minutes naji shiru, kawai message dinsa nagani ya shigo wayata “kisamu waje ki buya!! Yan hisbah ne!!!!

Hisbah! Hisbah!!!! Nakara maimaitawa innalillahi wa inna ilaihir raji’un................!!!!!!!!!

Mu hadu a page 02 idan Allah ya kaimu.

Taku har kullum

𝑅𝑎𝑏𝑖’𝑎𝑡𝑢 𝐹𝑢𝑙𝑎𝑛𝑖.

[28/09, 10:39 pm] Fulani: ❣️ICEN DAMUNA❣️

By

RABIATU (FULANI)

Young Telented Writers Association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





TRUE LIFE STORY.....

PAGE 02

Shikenam nashiga uku Na lalace!!

Yanzu me zance masa ya kawoni gidan saurayi ?

Da wane ido zan kalleshi ?

Da wace kalma xan kare kaina a wajensa ?? shikenan zan rasa sa ? yaxanyi da soyayyar sa ? Tayaya xan iya rayuwa babu Shi ? Tambayoyi ne fal cikina nake yiwa kaina wanda banada amsar su a yanzu....

Bansan sanda nakara raushewa da kuka ba!!

“Ko kadan tunani ni baya gida yana kan kaunata”

Da zarar na tuno yana sani shikenan mun rabu zan Kara fashewa da kuka!!!

Kuka nake sosai ina “wayyo

1 / 40