ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 40

57K to 60K   out of 117.2K words

yayi, yana rikeni na fizge hannuna na juya cikin gidan da gudu da niyyar na karasa toilet nayi aman acan, saidai inaaa kafin na shiga cikin gidan aman ya sameni a bakin kofar shiga cikin gidan, anan na duƙe na fara kwarara aman ba ji ba gani.

Duk taliyar da naci dazu Saida na amayar da ita, sannan na fara mayar da numfashi, ina daga kaina na ganshi a tsaye a kaina yana min wani kallo mai cike da zargi da kuma raini.

Tsugunnowa yayi kusa dani yace “ke wai wane irin iskanci kika tsiro ne ? Meye wannan aman da kike daga jiya zuwa yau ? Bakida lafiya ne ko rainani kikayi ?

Girgiza kaina nayi nace lafiyata kalau kawai jiya ne naji wani kamshi a jikinka kuma naji bana sonsa shi ya sakani amai, yanzu kuma wannan warin tabar ne ya sakani amai, amma Ni lafiya kalau nake.

Kallona yayi cike da zargi kafin yace “cikine dake ??

Da sauri na girgiza kaina nace ah ah ba ciki bane kawai warin tabar ne bana so.

Tashi yayi ya juya zai koma wajen abokin nasa nace “shalele dama kana shan wiwi....!!!!??

Cakk ya tsaya sannan ya juyo ya kalleni da idanunsa da sukayi ja saboda shaye shayen da yayi, Ni idanun nasa ma tsoro suka bani “eh! Akwai wani abu ne ?

Girgiza masa kai nayi nace bakomai!

Cigaba da tafiya yayi ya koma suka cigaba da shaye shayensu, na tashi na shiga ciki na debo ruwa a banɗaki na dauko dankwalina na kulle fuskata da hancina saboda kar na sake jin warin, wanke wajen nayi sannan na koma cikin gidan na dauki ragowar abincina na karasa cinyewa!.

Sai can yamma ya shigo gidan ya kalleni yace “koma me kike ji ki rikeshi a Ranki amma karki sake ki ɗauki ciki a gidannan Wallahi, dan na fuskanci take-takenki, ban shirya haihuwa yanzu ba, idan kuma kika ɗauka zaki gane Annabi Isa ba ɗan Allah bane!!!

Ƙasa ƙasa nace “ai dama nasan ba dan Allah bane, tunda baka ji ana kirana Ngozi ba!

“Me kike cewa ? Ya fada yana kallona da jajayen idanunsa da sukayi tatul.

“Cewa nayi to Ranka ya daɗe! Ban ɗauka ya ji abinda nace ba shiyasa nayi sauri na kare kaina da naga yana tuhumata!

Bai ce komai ba yayi ƙwafa ya shige daki ya kwanta a gado ya fara bacci! Nima a wajen bacci ya daukeni.

******** ******** ********

Mama ce ta kirawo humairah dakinta ta bata kuɗi Naira dubu biyar tace ta kaiwa malam Hamza mai almajirai ta fada masa yayiwa SUMAYYA addu’a a duk inda take kuma Allah ya dawo da hankalinta gida.

“Toh mama bari na dauko hijab dina! Fita tayi zuwa dakinsu ta dauko hijab din ta fita taje ta samu malam Hamza ta bashi sakon mama tayi masa bayanin komai, ta kuma ɗauki abun sadakar ta bashi, yace in sha Allah za’ayi addu’a.

Daga nan gidan best ta wuce suka zauna suna ta tattaunawa, maganar dai daya ce idan an hadu baza’a tashi ba sai anyi maganata, sai bayan magriba ta fito ta koma gida wanda dama ta sanar da mama cewa zata gidan best.

Little sai wayo take yi, amma kuma akwai ƙuiya daga mamanta sai abbanta take amincewa sai kuma zuwa gidanmu yau da gobe yasa ta fara sakewa da mama amma har yanzu bata sakewa da Humairah!.

******* ******** *******

Wata yunwa ce ta ta kuma tashina wajen 9 na dare, ina tashi na samu har lokacin ya Khalil yana bacci na wuce kitchen na sake hada wani abincin na zauna naci.

Sai Wajen 11 na dare sannan ya farka, kai tsaye banɗaki yaje yayi wanka sannan ya fito yayi sallar la’asar magriba da isha ya saka ƙananun Kaya ya dau jakarsa, Saida yazo dab dani sannan yace “ya jikin naki ?

Idona a lumshe na amsa da da sauki!

Allah ya kara sauki” abinda yace kenan ya juya ya fita daga gidan! Saida ya fita sannan na maida kaina na sake kwanciya dan ban gaji da baccin ba!

Sai Wajen 3 na dare sannan ya dawo ya kwanta bacci sai kuma 11 ya tashi sallah ya sake kwanciya!

Haka rayuwa ta cigaba da turawa, kullum kara cin abinci nake da kuma yawan bacci, Ni kaina mamakin baccina da cin abincina nake saboda sun ninka da ya kai sau uku! Hutun da na samu yasa fatata ta washe sannan na fara cika, yanzu banada wata damuwa ta ya Khalil ko ta wani abun.

Nasan dai yanzu time to time Yana yawan gayyato abokansa inyamurai gida su zo su chake da kayan shaye shaye sannan ya kwanta yayita bacci, sai dare ya shirya ya fita aiki.

Na tambayeshi abu biyu ban samu amsarsu ba kuma yace kar na sake tambayarsa, na farko nayi masa magana akan shaye shayen da yake da kuma gayyato maza gidansa ya nuna min kar na sake masa maganar nan idan ba haka daiina zai ɓaci, na biyu nayi masa magana akan aikinsa ya akayi ya koma na dare bayan da safe nasan yana tafiya farkon fara tarewata a garinnan ? Yace min aikin da ya koma yanzu ya koma na dare ne anyi changing duty!.

Nace wane aiki ne haka ?

Karki sake min irin tambayar nan ba abinda ya shafeki da aikina! Tunda dai ina baki ci da sha a gidannan karki sake saka min ido, dan ba Ni nake zaune a ƙarƙashinki ba kece kike ƙarƙashina! Sannan Ni ba yaronki bane!.

Tun daga lokacin na bashi hakuri ban sake masa maganar ba, saboda ina tattala dan zaman lafiyar da muke wasu lokutan! Ko ba komai ina samun jusantarsa idan muna cikin dadi, kuma muna iya kasancewa a shimfida daya!.

Saidai duk sanda suka zo suna shaye shayensu shida abokansa saina kulle kaina a daki na kunna turaren wuta, na kwanta nayita bacci, dan idan ba haka ba amai ne zanyi ta yinsa ba kakkautawa!.

Rayuwa ta fara canjawa yanzu sosai dan yanzu kusan watana bakwai a Lagos, nayi magiyar kiran gidan har na cire rai.

Ba da wanda na saba a garin saboda ya hanani mu’amala da maƙota, Nima ba wani so nake na saba dasu ba saboda ba jin yarensu nake ba, broken din ma ba iyawa nayi ba, saidai kuma wannan matar da muka zauna da ita a asibiti mai suna Maman Uche itace kadai ta taba zuwa gidana sau daya! Nima na taɓa satar hanya naje naga gidanta! Lokacin naje yo refilling na gas a karshen layinmu!.

******** ******** ********

Bacci nake yi wajen karfe daya na dare na jiyo warin da har yanzu na kasa sabawa dashi! Warin wiwi.

Kulle hancina nayi na fito falo, ya Khalil na gani a zaune a falo da faranti a gabansa da guntattakin taba a cikin farantin wanda ya kashe sannan ga kwalba a gabansa da kuma glass cup a ciki, ina shigowa falon na fara tari kamar zan mutu!.

Karasowa ciki nayi ina rufe hancina nazo kusa da ya Khalil still bakina a rufe!.

Miƙo min hannu yayi alamun naje gareshi, ba musu na matsa kusa dashi, “me ya tasheki a darennan ammatana ? Ya tambayeni da Muryar mashaya da kuma idanunsa da suka kada sukayi jaa!.

Buɗe bakina nayi da niyyar magana, amma inaaa! Aman da nake rikewa ne ya jikeshi gaba daya, na bata miki jiki na bata masa abun shan sa.

Wancakalar dani gefe yayi na fadi a kasa na dauje baki! Ball yayi dani a wajen Saida kaina ya bugi kujera, kwalbar hannunsa ya dauka ya buga a kasa yayo kaina da gudu na tashi nayi cikin daki, na saka key.

Ina jiyoshi yana zage zage can kuma naji shiru, sai munshari kuma, bude kofar nayi a hankali na fito, ganinsa nayi ya fadi a bakin kofar dakin yana bacci, da sauri na koma daki na kwanta bayan na saka key.

Daga nan na fara wasan yar buya dashi, saboda naga alamun so yake sai ya kassarani, so yake ya kasheni!.

Wata ranar Monday ina zaune a falo bayan naji fitarsa lokacin ina daki!.

Zaune nake daga ni sai daurin kirji na saka taliya da manja a gaba inaci! Leda daya na dafa amma tashi daya na sakata a gaba na kusa cinyewa saura kadan.

Banji shigowarsa ba sai daga kai kawai nayi naga mutum a kaina yana kallona, da gudu na tashi zan gudu yace ke dawo nan!

Jikina Yana rawa na dawo gabansa na tsaya.

Saida ya gama kare min kallo sannan ya matso kusa dani, ji nake kamar nayi fitsari a wando saboda yanda nake tsoronsa yanzu, gaba daya na tsorota tun ranar da ya dau kwalba zai kasheni na samu na gudu, bamu sake haduwa ba kusan wata daya kenan yanzu da kwana huɗu.

Dago fuskata yayi yace “ke har yanzu kina yin aman ?

Da sauri na girgiza masa kai alamun ah ah!

Ƙirjina yakai hannu yanda yanzu suka cika suka kara girma, matsasu yayi, ya saka hannu a cikin rigata yana shafasu, na fara wani nishin daɗi. Saboda ni kaina nasan nayi kewarsa!.

Hannu yasa yana shafa cikina, yanda yayi tauri yasa Saida ya dan dinga latsa cikin.

A kunne yayi min raɗa “Ammatana yaushe rabonki da period ??

Hankali kwance nace wata uku!!!

Sakin jakar hannunsa yayi Nima ya sakeni, yace dauko hijab ɗinki kizo muje.

“Shalele ina zamu ??

Wani kallo yayi min wanda yasa dole na juya na koma daki na dauki hijab dina nazo muka fita!

Mashin naga mun hau mai kafa biyu, to yaushe ya Khalil ya siyi mashin ba labari ?

Asibitin rannan muka sake zuwa, Saida muka ɗan jima saboda munyi rana akwai layi, can muka samu ganin likita muka shiga, shi yayi masa bayanin abinda nake ji, saidai ba likitan rannan bane, wancan bayerabe ne wannan kuma inyamuri ne.

Tambayoyi yayi min sannan yasa aka ɗauki fitsarina akaje akayi gwaji!.

Jira muka yi kusan thirty minutes kafin a kawo sakamakon, dan ya Khalil yace bazamu je mu dawo ba mu tsaya mu karba yanzu ba sai munyi zuwa biyu ba.

Nidai yunwa nake ji, kamar naci babu, nuna masa mai mangoro nayi da nufin ya siya min, wata hararar ya sake min dole nayi shiru.

Likita ne yayiwa ya Khalil congratulation akan cewa inada juna biyu, ya ɗauka zaiga yayi murna saidai fuskar nan a haɗe take ba alamar rahama.

Ina waje ban san wace wainar ake toyawa ba a ciki, Yana fitowa daga office ɗin likitan ya kama hannuna ya jani muka tafi gida.

Muna shiga gida ya Khalil ya daukeni da mari har biyu Saida naga taurari.

Nace “ya Khalil me nayi kuma ?

Uban waye yace ki dau ciki ? Me nace miki akan ciki a gidannan ? To wallahi ki jini da kyau sai kin zubar da cikinnan.

Sai a lokacin nasan akan me yake fushin kuma akan me ya mareni!

Kallonsa nayi nace shalele naga ai kai kayi min cikin, akan me kake tuhumata ?

“Meye tabbacinki na cewar Ni nayi miki ciki ? Na sani ko har yanzu kina kula yan iskan mazan wajen kamar yanda kika saba kina budurwa !?

Ke impact idan ma cikina ne nace bana sonsa ba dole ai, saboda haka dole ki zubar dashi.

Murmushi nayi nace “KHALIL!!! Idan ma ina bin wasu mazan kai ka fara koya min, dan idan baka manta ba kaine ka fara fasa budurcina, duk wani hakkin zina da na ɗauka kaima kana dashi, kuma wannan cikin dan sunna ne tunda ɗanka ne, kuma bari kaji WALLAHI TALLAHI ba wanda ya isa ya sakani na zubar da cikinnan....!!!!

Ina fadar haka na juya na shige daki da gudu ina kokarin danne kukana, Saida na shiga na saka sakata na wuce toilet na saki kuka mai nauyi.

Na kudurce a raina ko me Khalil zaiyi min bazan zubar da cikinnan ba, kuma zan jure cin zarafi zagi da duka duk akan wannan cikin, na daura damarar yaki da Khalil ko ta halin yaya ne domin kare cikin jikina.......!!!!!!

Topah, yanzu littafin ICEN DAMUNA ya dauko fire

🔥

🔥

🔥

shin ko ya zata kasance ?

Shin SUMAYYA zata yarda ta zubar da cikin jikinta ko zata haifeshi ??

Mu hadu a cikin littafin ICEN DAMUNA page 24.

Taku har kullum Rabi’atu Fulani.

Sashin talla

Talla!

💫

Talla!!

💫

Talla!!!

💫

💫

ALIYU HAIDAR ( THE LION

🦁

)

💫

Paid Book...

By

Rabi’atu Fulani....

&

Ubeera.....

Happy New Year Update......

A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.

Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.

Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.

Seda ya sauke ajiyar zuciya.

Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!

Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.

Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.

Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!

Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.

Chan dai ya kira sunan ta:

“Only!

“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.

“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?

Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.

Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.

“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!

Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.

Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.

Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.

“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”

“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.

Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.

Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.

Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.

Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.

******** ******* *******

Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:

“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.

Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.

Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.

This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!

Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.

“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.

Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.

“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai!

20 / 40