Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.
Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.
Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!
Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.
Chan dai ya kira sunan ta:
“Only!
“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?
Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.
Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.
“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!
Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.
Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.
Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.
“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”
“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.
Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.
Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.
Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.
Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.
******** ******* *******
Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:
“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.
Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.
Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.
This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!
Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.
“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.
Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.
“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!
Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.
Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......
Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??
Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??
Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??
Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?
Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??
Shin waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 31
Sosai gaba na yake faduwa, meya kawo sa, me yazo yamin, Allah ya gani ban shirya fuskantar sa ba, saboda har yanzu bansan ta yadda zan sauya masa matsayi daga yayana zuwa mijina ba.
“Ango, ango, kaga angon buzuwa bada kanka a sare kaje gida kace wa mamy ya faɗi.”
Wannan kirarin dole na bada tukuici best ɗin mu, hannu yasaka a aljihu ya ɗebo kuɗi ya miƙa mata.
Haɗe rai nayi sosai na zagaye su na wuce.
“Ke ina zaki ? bazaki tsaya ba ina miki magana ? Wajen ki fa yazo, sashi na!”
Banza na mata ko juyowa banyi ba na wuce da sauri.
“Bara naje na tawo maka da ita doctor.”
“A’a kyaleta leemah ai naganta hakan ma ya wadatar dani.”
“Dan Allah kayi hakuri doctor.”
“Karki damu barta nima ina buƙatar ganin ainayin buzuwa a tare da ita, ina son ta dawo yanda take kafin bikin mu”
Shiru tamasa kawai amman harga Allah bata jin dadin abinda sashin ta tayi ba.
Sallama ya mata ya juya ya tafi.
Tana shigowa zata fara bala’i, ta ganni a ɗakin mamah dole ta haɗiye rigimar ta a ranta.
Ni kuma daman da biyu na shigo ɗakin, nasan bazata taɓa faɗar abinda nayi a gaban mamah ba.
Ganin yanda take cika tana batsewa da yanda nima na haɗe rai se mama tayi tunanin faɗa mukayi a hanya.
Ku baza ku taɓa hankali ba ko ? yanzu a hanya kukayi faɗa ?
Gaba ɗaya an rasa me magana a cikin mu.
Humairah ce tace aunty haleemah tun ɗazu little take kuka fa.
Gaba ɗayan mu muka maida hankali kan ta.
Karɓar ta tayi tana rarrashin ta.
Abinci taje ta kawo mana, haka muka zauna muna cin abincin babu me magana a cikin mu.
Se yamma liss sannan duk suka tafi gida gaba ɗayan su, duk senaji gidan babu daɗi.
Daddare ina jin waya ta na ringing namata banza dan nasan waye me kiran.
Tashi nayi ma nashiga wanka, na ɗakko kayana na wajen *momma’s zhara* nayi amfani dasu sannan na kwanta.
********** ********** *********
A hankali ranakun suka fara juyawa zuwa kwanaki, yau gashi munci wata ɗaya da engagement ɗin mu nida doctor, amman har lokacin bana masa magana, idan yazo wajen mamah ko ta kira ni hakan zauna, shima baya cemin ci kanki nima haka, wayar ma dayake min ya dena.
A hankali nake ƙare wa jiki na kallo na, na maida ƙiba ta sosai, koma ince fiye da da, fata ta se wani sheƙi take, nida kaina nasan na canza ba’a ma magana.
Doguwar riga nasaka nayi rolling na fito.
“Mama zan tafi”
Saida ta gama kallona sannan tace “Ki gaisheta karkiyi dare kuma.
Toh insha Allah.
A hankali nake tafiya hannu na riƙe da na angel.
Napep muka hau ya kaimu har kofar gidan.
Waya na mata tazo ta buɗe min.
Angel taja tana mata wasa.
Nima ban kula ta har muka shiga gidan.
Bobo da biscuit ta ɗebowa angel.
Sannan ta juyo tana kallona, tagumi tayi da hannu biyu, “oh ni sadiya! Ke kam baiwar Allah me kike ci ko kuma duk aikin *momma’s zhara ne*?”
Murmushi nayi kawai naƙi ce mata komai.
“Gaskiya doctor yana cikin Alkhairi dumu_dumu”
Take kuwa na haɗiye murmushi na.
“Hmm gulma yarinya kwana nawa ne, Ni gaskiya ma bazan ga abin arzikin nan ni kaɗai ba”
Wayar ta ta ɗakko tana dannawa, bansan me take ba yanda naga tana murmushi da chije baki kawai naji ban yadda da ita.
“Ke ina little?”
Bacci take na taso miki ita? “A’a kyale ta”
Hira muka ci gaba dayi.
Waya naji ana mata, kafin naga me kiran ta ɗauke da sauri ta fita harabar gidan, tana amsawa.
Da Dr tayi waya ba jimawa sai Gashi ya bayyana a gidan nata.
“Meyasa Meta haleema ?” Yake tambayarta (da yake bata fada masa komai ba kawai cewa tayi yazo gidanta tana tare dani )
“Kwantar da hankalin ka doctor, kawai dai yau ɗin so nake na haɗa ku muyi maganar biki da nasan halin kayata, da kyar idan kuna shirya wani abin arziki.”
Ajiyar zuciya ya sauke.
“Kin ɗagamin hankali wallahi ya faɗa yana mata hararar wasa.”
“Nidai muje”
Tsaya nifa wannan kawar taki haleemah halin ta se ita, dan kamar ma tsoron ta nake ji yanzu.”
Dariya ce ta kubce mata.
“Haba doctor yada karaya haka tun yanzu, ai kura tayi lafiya, amman dai muje komai ze wuce.”
Ina kallo naji sallamar sa, duk da yanda naji zuciya ta na bugawa ban ɗago na kalle sa ba.
Yana zama na miƙe zan fita.
“Koma ki zauna Malama.”
Yanda yamin magana a dake kuma babu alamun wasa a muryan sa yasa na zauna babu musu.
Ajiyar zuciya best ta sauke dan dama tana ta tunanin yanda zata kasance.
Kitchen ta shiga ta kawo masa snacks da lemo.
Sannan taja hannun angel suka hau sama.
“Baki iya gaisuwa ba ?”
Ciki ciki na gaishe sa ko amsa min bai yi ba ya fara danna wayarsa.
Wasa nake da zoben hannuna.
Jin yanda idon sa yake yawo a jiki nane yasa na ɗago nima ina kallon sa.
Taff idona ya ciko da hawaye, kuma har lokacin ban ɗauke idona a kansa ba.
Shine yayi ƙasa danasa idon.
Kaina na ɗora a cinyata kawai na fashe masa da kuka, kukan dako yankani za’ayi bansan meyasa ka ni kukan ba.
“Duk ƙiyayyar tawa ce yasa kike kukan nan buzuwa?”
Da sauri na ɗago jin maganar sa a kaina kuma bansan sanda yazo kusa dani ba.
“Bakya sona ko?”
Ƙasa nayi da kaina dan rasa mezan ce masa nayi, betaɓa cewa yana sona ba amman ya titsiye ni wai bana son sa.
Wani kukan kawai naƙara sakar masa.
“Ki kwantar da hankalin ki kome kike tunani ki ajiye sa a gefe.”
“Magana zamuyi yanzu.”
Da bayan hannuna na goge hawayen.
“Ki sakko madam”
Da little a hannun ta tasakko.
Tana ganina tafara miko min hannu, murmushi nayi natashi na karbe ta.
Zama tayi kusa dani.
“Me kuke shiryawa na biki?”
“Kai muke sauraro doctor.”
“Abokaina sun haɗa doctor’s day.
Shi kaɗai ne abinda zanyi se reception ranar ɗaurin aure.”
“ Kufa ?”
“Waleemah zamuyi muma ranar ɗaurin auren.”
“Duka kinga event biyu kenan a ƙawayen ku mutum nawa ne zasu wajen taron?”
Shiru tayi alamun tunani.
“Karki damu kada dai su wuce mutum 15.”
Toh insha Allah doctor.
Ranar Friday za’a kawo lefen, ki faɗawa mamah.
“Allah ya kaimu da rai da lafiya”
“Ke baki da abin cewa ne?”
“Bazani wajen event ɗin ba gaskiya..”
Sakin baki kawai best tayi tana kallona.
Zatayi magana ya girgiza mata kai, alamun tayi shiru.
“Ba shawarar ki na nema ba ai, umarni ne.
Ɗagowa nayi ina kallon sa, da mamaki gaba ɗaya yanzu ya sauya min, yadena lallaɓani.
Ɗauke kai yayi tamkar besan kallon me nake masa ba.
“Zanje haleemah duk yanda ake ciki zan miki waya, zan tura miki kaya seki zabar mata.”
“Toh doctor muna godiya.”
Tashi yayi ya fita.
Ki tashi ki raka shi.
Banza kawai na mata.
“Wai sumayya nufin ki a haka za’ayi auren nan me kike nufi, aikam indai wannan halin zaki je ki masa wallahi bazaki taɓa jin dadin zama da shi ba duk kuwa son da yake miki, ance miki ana yiwa namiji haka ne.”
“Ni karki kara cewa yana sona dan ba sona yake ba tunda be taɓa faɗamin ba”
Tsaki kawai tayi ai sekiyi tayi.
Seda yamma na tafi gida.
********* ********** **********
Koda nadawo sosai mukayi hira da mamah amman nakasa faɗa mata saƙon ta, koda yake daman ai bani Ya faɗawa ba.
Ranar laraba best tazo da ruwa da lemo da fulawa.
Ke kuma mezakiyi da waɗan nan kayan mamah take tambayar ta.
“A’a mamah na karɓar lefen ne mana, gobe humaira zata zo munyi waya, se muyi aikin kayan snacks ɗin.”
“Wane lefe kike magana ne haleemah?”
Juyowa tayi tana kallona fuskar ta cike da ɓacin rai.
“Baki faɗa mata ba daman?”
Ɗauke kai nayi tamkar badani take ba.
“Mamah tun ranar da taje Ahmad yace ranar juma’a za’a kawo lefe bansan bata faɗa miki ba dana faɗa miki tun tuni.”
Rasa ma me zata cemin tayi gaba ɗaya.
Hannu na taja, banyi musu ba nabita har ɗakin.
“Ke bakyason gaskiya a rayuwar ki ko sashina?
Ki sani Allah ya baki dama ne, amman kina wasa da damar ki, wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Har kika bari doctor ya juya miki baya sekin danasanin da baki taɓayi ba a rayuwar ki.”
“Allah ya baki doctor ne, ba tare da dabarar ki ba, idan har baki godewa ni’imar sa ba, tabbas zaki godewa azabar sa, kuma a wannan lokacin karki zargi kowa ki zargi kanki, haka kuma karki kuka da kowa kiyi da kanki.”
Tunda ta fara magana nake kuka, zuwa sanda ta kai karshen maganar ta kukana ya kara tsananta.
“Cikin kuka nace best bawai ina gudun doctor bane, a’a be dace dani ba, mace kamila ce ta dace da shi bawai niba, ina ganin idan na aure sa tamkar banyi masa adalci ba, best ya Ahmad yafi karfina.”
Na karasa faɗa ina kuka me tsuma zuciya.
Ajiye little tayi kawai ta rungume ni.
Baya na take bubbugawa alamun rarrashi.
Ki cire komai a ranki doctor yana miki son da baze taɓa bari wani ya wulaƙantaki ba bare kuma shi da kansa.
A hankali mamah ta juya tabar kofar ɗakin.
A zuciyarta albarka kawai take sakawa haleemah, tabbas koda itace ta tsugunna ta haifi haleemah soyayyar dazata na nuna wa sumayya kenan.
Seda ta tabbatar nayi shiru sannan muka fito tsakar gida.
Ita ma mamah nunawa tayi tamkar bata ga komai ba.
“Mah zamuje gidan ammie.” Cewar best.
“Agaishe ta”
********** ********* **********
A hanya take tambaya ta ko kayana na wajen *momma’s zhara* sun ƙare.
“Chab ai inaga har can sena je dasu”
“Kinyi sharr dake sashi na har na fara tausaya miki billah”
Bance mata komai ba se fuskata dana marairaice mata.
Dariya tayi “yarinya bani zakiwa ba ki ajiye shagwaɓar ki zata miki amfani.”
Hararar ta kawai nayi.
Sosai ammie tayi farin ciki da