Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
ba damuna tayi ba nayi akan lokaci!.
Sai tara na safe wata masifaffiyar yunwa ta tasheni, idan banyi kuskure ba rabona da abinci tun shekaran jiya da dare da na sha tea sai kuma wata makociyata a asibiti ta sammin abinci, ganin banada mai zuwa dubani, bayerabiya ce amma kuma tana jin Hausa sosai, ita ta dinga taimaka min da abinci idan Khalil bai kawo min ba, da za’a sallameni ta kwatanta min layin da take saman layinmu ne kuma ta bani lambar wayarta akan wai zamuyi zumunci, ina karɓar takardar lambar na saka a rigata.
Ina tashi na jawo takeaway din da ya kawo min jiya na fara ci hannu baka hannu ƙwarya, Saida na gama ci na koshi sannan na lura da abinda ya kawo min cewa ashe shinkafa da miya ce da salad da tumatur da kayan hadi dai sai nama guda daya.
Ina gama ci na fito neman ruwa a kitchen, a falo na sameshi yana bacci na wuce shi ban sake kallonsa ba naje na dauko ruwa na dawo daki na sha nasha magani na sake kwanciya ina saƙe-saƙe a raina.
Idan akace min shalele zai iya min wannan dukan bazan taba yarda ba! Nasan dai mari yana min wanda nasan kishi ne yasa yake min hakan, sannan kuma da sona da yake, amma yanzu ya Khalil ne da dukana harda belt ?
Anya kuwa ya Khalil Dina ne ? Anya kuwa ba canja min shi akayi ba a Lagos dinnan ?
Wata zuciyar kuma tace maybe waccan Yar iskar ce ta sauya miki shi amma ya Khalil ai yana sonki har yanzu.
To idan yana Sona kenan meyesa yake kula wata a waje ?
Abinda yasa kike kula wasu a waje mana! Wata zuciyar ta sake bata amsa. Da sauri ta kauda wannan tunanin,
To amma ai Ni saboda kuɗi ne kuma shi ya fara nuna min, sannan kuma ni ai kafin muyi aure ne!
Haka zuciyata ta dinga sake sake ta kawo min wannan ta kwance ta kawo wannan, har daga ƙarshe na amince zanje na bashi hakuri ina wannan tunanin bacci barawo ya daukeni!.
Sai Wajen la’asar na tashi ina tashi na fito falo ban ganshi ba na shiga dakinsa naji yana wanka.
Zaman jiransa nayi saidai kusan 30mnts bai fito ba, nace bari naje nayi wanka Nima kafin ya fito!
Ban jima da shiga ba na jiyo ana kulle gidan, alamun ya fita kenan.
Da sauri na watsa ruwa kafin na gama, na dauko zani na fito ina fitowa nayi turus dan kuwa ya fice, cike da takaicin rashin samun damar bashi hakuri na koma banɗaki na karasa wankana.
******** ********* ********
Addu’a da kuma tsayuwar best da ya Ahmad ne yasa mama ta ɗan fara warwarewa, gida ya fara komawa kamar da amma dai mama har yanzu tana nan da damuwar halin da nake ciki dankare a ranta, tana dannewa ne saboda su best.
Little SUMAYYA kuma sai wayo takeyi, mamanta kuwa kullum cikin trying na numberta ko zata shiga, wanda kuwa kullum ana fada mata cewa wayar nan a kashe take, amma bata hakura ba, kullum saita yiwa yaya haneep kuka akaina, a rashin hankalinta har da cewa zata zo Lagos nemana.
Dariya yayi yace “love anya kuwa kin san Lagos kuwa ? Lagos fa ba unguwarku bace da zaki ce kin san ko ina! Zaki gama rayuwarki a Lagos ma batare da kin shiga wani wajen ba, ko namiji ma bazai ce yaje Lagos neman wani ba bare ke mace!
Kiyi hakuri mu cigaba da Binta da addu’a in Sha Allah ko a ina take muna mata fatan kasancewa cikin aminci! Da wannan yake samu yake lallabata har tayi shiru!
******* ******** ********
Ina zaune har wajen 12 na dare amma ya Khalil bai dawo ba.
Sai Wajen 1am na dare sannan ya dawo, sai a lokacin naga dressing din dake jikinsa tunda dazu ina wanka ya fita!
Ƙananun Kaya ne a jikinsa sai kuma hula p-cap akansa kayan blue Black ne sunyi masa kyau sosai.
Bai kalleni ba ya wuce zuwa dakinsa ya fara kwabe kayan jikinsa, da sauri naje ta bayansa na rungumeshi na fara dan marayan kuka ina shafa ƙirjinsa wanda nasan shine weakpoint nasa!
Juyo dani yayi muna kallon juna! Ya akayi ne ?? Abinda yace kenan.
Cikin hawaye nace “dan Allah shalelenah kayi hakuri! Wallahi bazan sake ba, wannan ma da ya faru kishinka ne yasa Idona ya rufe amma ba halina bane ka sani! Kuka na fara sosai na kwantar da kaina a ƙirjinsa wanda har a lokacin bai ce komai ba! Saidai zuciyarsa da take bugawa a hankali.
Hakuri na cigaba da bashi da kuma nuna masa yanda nayi kewarsa har Saida na tabbata ya sauko.
“Shikenan amma kafin na karbi ban hakurinki akwai abinda zaki kiyaye guda uku!!
In Sha Allah ko mene naji na yarda! Na bika nabi Allah mijina! Na fara ina shafa ƙirjinsa.
“Na farko babu ke babu wayata!
Na biyu babu ke ba saka min ido akan abinda kika ga inayi ko kuma yawan tambaya, duk bana so!!
Na uku babu ke ba maganar zuwa gida har sai sanda na gamsu cewar zaki je ɗin!
Duk da sharudan sunyi min tsauri amma ba yanda na iya sulhu nake nema, more especially ma maganar zuwa gida da yace sai sanda yaso, magana ta gaskiya inason yin magana da gida ko zuwa ganin gida.
Na amince in sha Allah shalele, amma maganar zuwa gida ko a waya ne ka haɗani dasu muyi magana dan Allah.
Kauda kai yayi yace “shima sai sanda na gamsu da hankalinki sannan zan hadaki dasu, karki daga musu hankali da kuka su ɗauka wani abun nake miki.
Wallahi bazanyi kuka b......
Haɗe bakina da nasa yayi wanda ya tilasta min yin shiru, karbarsa nayi dan kuwa nima nayi kewarsa over.
Sai kace wacce aka kawo yau haka Khalil ya darjeni, Saida ya tabbatar da cewa ya darjeni zuwa wajen 2 na dare sannan muka je mukayi wanka muka kwanta, wannan farin cikin da na samu a daren yau da har na ɗauka na rasashi kenan......
******* ******** ********
Yanzu rayuwarmu ta dawo nrml duk da yanzu ya Khalil ya tsiri yin dare wani lokacin sai ya kai 12 bai dawo ba wata ran ma kwana yake acan, idan nayi magana sai yace wajen aiki, yanzu aiki yana musu yawa shiyasaa, ban taba tambayarsa aikin da yake ba amma dai inason wata ran na tambayeshi.
Yau ma dai kamar kullum ina zaune a falo ina jiran dawowarsa har wajen 12 bai dawo ba, ban san lokacin da bacci ya daukeni ba, motsi naji a falon, na bude Idona na ganshi ya shigo ya jefar da takalmansa yayi daki, kaina na daga na kalli agogo naga 3:15am na dare, tashi nayi na bishi daki, ɗakin na sameshi yana kokarin cire riga.
Rungumeshi nayi ta baya, ina tayashi bude botiran rigar.
Shalele ya aiki ? Yau ma aikin ne ya rikeka ?
Da wata iriyar murya yace min Eh!!
Juyoshi nayi da niyyar na zame masa wandon, saidai wani wari da naji ya daki hancina yasa ba shiri nayi cikin banɗakin da yake dakin.
Na kai minti goma ina amai, kamar zan amayar da kayan cikina, Saida naga na nutsu sannan na fito.
Har yanzu yana tsaye bai bar inda yake ba, miƙo min hannu yayi da niyyar naje gareshi.
Saidai ina karasawa wajen nasa wani aman ya sake zuwa min, ba shiri na sake komawa toilet da sauri ina rufe bakina.......!!!!!!!!
Toooo..... Jama’a anya kuwa bazamu bi Khalil wajen aikin nan nasa ba kuwa ?
Anan na kawo karshen page 22 sai mun hadu a page 23 in Sha Allah.
Nice taku har kullum Rabi’atu Fulani.
Sashen talla.
Talla!
💫
Talla!!
💫
Talla!!!
💫
💫
ALIYU HAIDAR ( THE LION
🦁
)
💫
Paid Book...
By
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.
Seda ya sauke ajiyar zuciya.
Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!
Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.
Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.
Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!
Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.
Chan dai ya kira sunan ta:
“Only!
“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?
Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.
Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.
“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!
Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.
Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.
Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.
“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”
“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.
Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.
Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.
Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.
Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.
******** ******* *******
Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:
“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.
Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.
Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.
This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!
Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.
“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.
Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.
“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!
Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.
Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......
Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??
Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??
Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??
Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?
Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??
Shin waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 23
Kakarin aman nake yi amma yaƙi fitowa saboda na gama amayar da duk abinda yake cikina, na kai minti goma ina kakari amma ba abunda ya zubo, haka dan dole na fito daga toilet din.
Ina fitowa na rufe fuskata da tafin hannuna, saboda idan na toshe hancina kai tsaye nasan zan hadu da bala’in ya Khalil!!!
Wuceshi nayi na fita daga ɗakin na tafi dakina na kwanta, har bacci ya daukeni bai shigo ba.
Saida safe sannan na tashi naji inajin wata wahalalliyar yunwa, ina tashi ko wanke baki banyi ba na wuce kitchen na fara ƙoƙarin haɗa abun kari, cikin minti sha biyar na gama hada taliya jollof komai da komai na dauko na dawo falo na zauna, sai a lokacin na fara tunanin ko ya Khalil ya fita ne ? Domin ban ganshi ba!.
Tashi nayi na shiga dakinsa ban ganshi ba na duba banɗaki ban ganshi ba, a raina nace to watakila ya fita ina bacci.
Zama nayi na fara cin abincin nawa hankali kwance, Saida naji nayi nakk sannan na rufe ragowar nace wannan kuma sai anjima, ina zaune a wajen na fara hamma, kafin a jima bacci ya daukeni anan inda nake, can cikin baccin na dinga jiyo wani ƙauri yana tashi, ji nayi numfashina zai ɗauke, ba shiri na tashi daga baccin a firgice.
Nasan dai na kashe gas da nayi girki dazu, kuma ba wuta a gidan to wannan kaurin fa ? Tashi nayi naje kitchen domin nayi confirming, tabbas ba wani gas da yake ci a kitchen din, ta tagar da take kitchen din naji kaurin yana tashi, zura kaina nayi na leƙa ta taga banga kowa ba, saboda tagar tayi tsawo da yawa, saboda haka na fita na zagaya inga me yake kauri a gidan!
Ina zagayawa naga ya Khalil da wani bayerabe suna zaune akan wani tudu da yake bayan kitchen dina, suna shan wiwi, mamaki ne ya matuƙar kamani, to me ya Khalil yake nufi ne ? Wannan sauyin da yayi duk na mene ? Wannan shaye shayen fa ? Dama ya Khalil yana shaye shaye ?
Abokin nasa ne ya nuna masa a tsaye a bayansa tunda shi ya juya baya abokinsa kuma yana iya kalloni saboda sunyi facing ɗin juna ne, waigowa yayi ya ganni a tsaye a bayansa ina hawaye na toshe bakina saboda aman da nake ji, tasowa yayi ya nufo inda nake da wiwin a hannunsa dai, warin da naji yana kusantoni yasa yunkurin aman nawa ya karu.
Rike hannuna