ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 40

30K to 33K   out of 117.2K words

Koda mama tazo har lokacin bacci nake duk ta damu anya baccin nan na lafiya ? ta tambayi best wacce itama ta fara gyangyadi a zaune.

Mama lafiya amma Bara na kira doctor muji.

A hanya suka haɗu, daman wajenka zani.

Lafiya dai ?

Har yanzu bacci take fa ta faɗa tana bata fuska.

Muje toh.

Bayan sun gaisa da mama take tambayar sa wani irin bacci ne haka nake.

Mama ni nayi mata alluran baccine, ina so ta samu hutu sosai.

Yau da yamma zan sallameta Insha Allah.

Murmushi mama ta saki, masha Allah.

Yawwa doctor Wallahi kaman Kasan daman nagaji da zaman asibitin nan best ta faɗa cike da farin ciki.

Cikin yanayin zolaya doc yace: Mama gaskiya anma fasa sallamar se bayan sati biyu.

Haba mana yaya doctor ta faɗa tana marairaice wa.

Dariya yayi yace lallai ma haleemah yau kuma nine yayan ? ( Saboda bata kiransa da yaya saidai tace likita bokan Turai )

Shikenan idan ta tashi kizo ki kirani.

Yawwa ko kaipa yaya likita. Ta faɗa tana rufe baki tana dariya.

Kansa kawai ya girgiza ya juya ya tafi.

******* ******* *******

A ranar aka sallame mu, muka koma gida, shi ya kaimu gida da kansa a motar sa.

Mama tayi, tayi da shi ya shigo, yace a’a ana jiran sa a asibiti, amman zai dawo gaishe da mama.

A hankali na juya ina kallon sa.

Matsowa yayi kusa dani dan Allah kibi komai a hankali kinji kanwata.

Kaina kawai na gyada masa, Yaushe zaka dawo ?

Zan zo insha Allah.

Seda yaga shigarmu gida sannan ya juya ya tafi.



“Tunda nadawo gida ban haɗu da baffa ba, bansan ina yake zuwa ba, saboda kafin ya dawo nayi bacci.

Yau muna zaune da yamma se gashi ya dawo.

Kallon tsantsan mamaki kawai nake masa, Kayan gareji ne a jikin sa, alamun yanzu aikin kanikanci ya koma, yaushe ya koma gareji shi kuma ? Nayiwa kaina tambayar da bani da amsarta.

Bai min magana ba nima ban masa Sema kaina dana dauke.

“Wani irin tattalina mama take, da ammie, kullum best tana gidanmu.

Zan iya cewa alhamdullah, dan zumuncinmu ya dawo kaman da, nida ita.

Bayan sati biyu da sallama ta asibiti sega doctor.

Bayan sun gaisa da su mamah da humaira.. suka fita suka barsa.

Ta kawo masa abinci, babu kunya ya zage yaci abincinsa, yana ta santi.

Kanwata ba magana ?

Murmushi kawai nayi masa

Bayan ya kammala yace muje na baki sako.

Toh kawai nace masa, ya rigani fita saboda haka da na fito na ganshi a jikin motarsa yana kallona.

A hankali nake tafiya, saboda na rame sosai, fuskata babu komai, se ido da hanci.

Tunda na tawo yake kare min kallo.

Da sallama na ƙaraso wajen,

Bazaki dena tunanin nan ba ko ? Tambayar da ya jefa min kenan batare da ya amsa sallamar da nayi masa ba.

Shagwabe fuska nayi kafin nace haba yaya dr ka fara amsa sallamata mana.

Oops! To yi hakuri wa’alaiki-ssalam. Ya faɗa yana murmushi kafin ya dora daga inda ya tsaya, Kinga yanda kika koma, haba dan Allah, gaskiya ni bama zan kara zuwa ba.

Kayi hakuri nadena.

Idan kika sake me zanyi Miki to ?

Na yarda ka zaneni amma karkace bazaka kulani ba!!

Nooo saidai na daina kulaki tunda baki jin magana Ni kuma bana shiri da mara jin magana.

Tura baki nayi kafin nayi kokarin kauda maganar ta hanyar cewa:

Bani aron wayar ka dan Allah....

Me zakiyi da ita ?

Khaleel zan kirawo.

Shiru yayi ya na kallo na, yana nazari a ransa,

Ganin yayi shiru yasa nace: Shikenan tunda bazaka bani ba.

Mezakice masa ? Ya faɗa yana tsareni da ido

Sallama kawai zan masa fa.

Kin tabbata?

Kaina kawai na gyada masa.

Baya san ɓacin raina shiyasa kawai ya bani wayar.

Tana fara ringing ya daga.

Kauna! Na faɗa a hankali, idona na cikowa da hawaye.

Ykk!

Bani da lafiya.

Allah ya baki lafiya amarya.

Kukan da nake dannewa kawai nasaki.

Kittt!!! Ya kashe wayar sa.

Ganin yanda nake kuka ne yasa kawai ya buɗe min gaban motar sa.

Banyi musu ba, nashiga na zauna, kaina kawai na hade kai da gwiwa ina kuka.

Kuka nake wanda duk wanda ya jishi, zai fahimci zafi da radadin da yake damun zuciya ta. Kuka nake tun daga kasan zuciya ta.

Gaba daya ya rasa da wata kalma, ze rarrashe ni ganinta cikin damuwa yana daga masa hankali.

Sai bayan da na gama kukan sannan ya mika min Handkerchief dinsa domin na share hawayena

Kiyi hakuri mana! Ya faɗa a hankali.

Ya Ahmad! Wallahi ina sonsa, ya zanyi da kaunar sa a raina, bana iya juran fushinsa a kaina, kana gani fushi yake dani, amman dan Allah ai kaima Kasan bana son auren nan ko ?

Na tambaye sa cikin zubar da hawaye.

Ki nutsu mana!

Kansa kawai ya hade da sitiyarin motar, yazeyi ?

Wannan wace kalan soyayya ce Dame gayen nan yake takama ne ?

Kije gida zamuyi magana.

Toh na faɗa a hankali tare da buɗe motar na fita.

Ko sallama ban ba, na shiga gidan, na zauna.

Tagumi kawai nayi hawaye na bin fuskata.

Mama bata tambaye niba, dan tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta Koki.

Tun daga ranar damuwa ta, ta dawo sabuwa narasa inda zan samu waya na kira Khalil.

Mamah bata ajiye wayar ta inda zan ganta yau na riga na yankewa kai na hukuncin da nake ganin shine daidai.



****** ******* *******

“Da yamma mamah ta shiga wanka, na dauki hijabina da face mask na fice daga gidan.

Ban tsaya a ko ina ba sai majalisarsu.

Tun daga nesa na hangoshi Sai kuma gaba na ya fara faduwa wata irin tarba zemin ? Har na kara so wajen ban lura ba ina tunani.

Sumayya! Ya kira sunana cike da mamaki.

Ganin ina niyar rike masa hannu yaja baya, muje kawai yace yana gaba.

Me ya kawoki waje na ? Kina matar aure ?

Zubewa kawai nayi akan kafata, na hade hannayena

Dan Allah khaleel! Bazan iya ba, bazan juri rashinka a tare dani ba, zuciya ta bazata taɓa dauka ba, kamin rai, na roke ka!!!

Dagoni yayi kawai ya rungume.

Zan iya cewa na dade banga soyayyata da tausayina a idon khaleel ba, se a wannan ranar.

Na miki alkawarin zan aureki idan har auren ki ya mutu! Ya faɗa yana rike fuskata, idonsa cikin

Nawa, ina sonki sosai only!!

Ya faɗa yana sumbatar goshina.

Nasan zaka rabu dani ai yanzu!

Mutuwa kadai zata saka na rabu dake!!!

Cike da son tabbatar maganarsa nace: Kamin alkawari ?

Nayi miki yammatana!!!

Kara rungumeshi nayi ina hawayen farin ciki.

Yaushe rabon da nasamu wannan kulawar a wajen sa?

Bazan iya tunawa.

Kije gida, amman kidena zuwa nan. Duk sanda kike son ganina kiyi min waya.

Kaina kawai nake gyada masa kaman kadangare.

Shi ya rakoni har titi Sannan ya koma.

Har nazo gida banji ko dar ba dan wani irin kwarin gwiwa nake ji atare dani, cikin zuciyata nace WELCOME BACK YAMMATAN ƘAUNARTA......!!!



****** ****** *******

A daren ina zaune, humaira tazo ta sameni tace kije inji baffa.

Gani nan

Babu sallama babu komai, a tsaye na tsaya gani.

Dan ubanki mu zaki tsayawa a ka ? Cewar mama da ranta ya gama baci ganin irin shigowar da nayi musu da kuma tsaya musu da nayi aka.

Zama nayi banyi magana ba sai hararan gefe da nake.

Shima be jira cewata ba ya dora da fadin

Mun tsaida tariyar ki nan da sati biyu, masu zuwa insha Allah.

Toh Allah ya kai mu da rai da lafiya na faɗa cikin murmushi.

Gabaki dayan su da kallon mamaki suka bini

Babu wanda ya tsammaci haka a cikin su, dan ita mama har tunanin ta yanda zan karbi maganar take.

Se kuma taga babu wani tashin hankali a tare dani.

Shi kansa baffa kasa shiru yayi.

Me kike shirya wa ? Ya tambaye ni yana tsare ni da idon sa.

Bakomai, na faɗa har lokacin da murmushi a fuskata.

Ganin duk sunyi shiru se aikin kallona Da suke ne yasa nace zan iya tafiya ?

Jeki kawai yace.

Ban yarda da yarinyar nam ba, baffa ya fada yana kallon mamah.

Bansan mezan ce ba a halin yanzu.

Ki saka ido sosai akanta

To Insha Allah.



******* ******** *******

“Da safe ina tashi, nace mama dan Allah ara min wayarki na kira ya Ahmad.

Me zaiyi miki ? Kin manta akwai auren wani a kanki ko ?

Ah ah fa mama kaikayi nake ji jikina yana yi Shiyasa zan tambayeshi maganin da zanyi amfani dashi domin Naji daidai.

Ungo kirawo shi a gabana yanzu.

“Mamancy tawa” na faɗa ina dariya, ganin yanda mama ta dage tana tsarona sai yake bani dariya.

Assalamu alaikum mamana!

Dan mama Toh ba ita bace kanwarka ce, na faɗa ina turo baki.

Me muka samu haka kanwata ?

Bari sai kazo zan baka labari Yanzu Kasan me nake so ??

A’a sekin faɗa.

Kaga jikina ne duk tabo gashi nayi baƙi ba kyawun gani dan Allah abinda zai komar min da fatata kamar da nake so idan ka sani ? Sannan wannan ramar ta fara damuna itama.

Wai lafiyar ki kuwa ƙanwata ? Wannan shirin fa ? Ko duk na tariya ne ?

Tura baki nayi kafin nace Shikenan tunda bazaka fada min ba.

Karki kashe pls zan hado na kawo miki da kaina rama kuma maganinta yana wajenki dagewa zakiyi ki cire tunani a ranki sannan ki rage saka damuwa da kuka duk a ranki.

To in Sha Allah yaya yanzu yaushe zaka zo ?

Ɗan Anjima kaɗan.

To sai Allah ya kawo ka, ina jiranka.

Ganin kallon da mama take min ne yasa nace mama wannan kallon fa ?

Hararata tayi sannan tace Ina fatan ba wani mugun abun kike shirya wa ba ?

Matsawa nayi jikin ta, ki kwantar da hankalin ki uwa ta gari Komai daidai.

Na faɗa ina kiran best.

Hello mama nah! Ta faɗa da alamun bacci a idon ta.

Ke dallah ni ki tashi daga Wannan baccin asarar.

Wayar ta ciro ta kara dubawa dan tabbatar da waye ya kiran ta.

Best! Na faɗa da karfi.

Wani irin ihu ta fara.

Babu shiri na cire wayan daga kunne na.

Welcome back sumayya Abubakar mai nasara!!!

Gani nan zuwa yanzu.

Bata jira cewa ta ba, ta kashe wayar ta.

Ni kaina dariya nake.

“Zan iya cewa rabon da naji ni a farin ciki irin wannan, nida kaina na manta.

Kawai wani irin nashadi nake ji, tun daga kasan zuciya ta.

Da ihu ta shigo gidan kaman mahaukaciya.

Tashi nayi, nima na biye mata muka dinga tsalle da ihu.

Humaira na gefe se kyalkyala dariya take.

Ita kanta mama ta nason dakatar damu, sedai farin cikin data gani akan fuskata bata son yanke min shi.

Seda muka gaji dan kanmu sannan, muka zauna maida numfashi.

Fadamin meyafaru ? Ta faɗa tana rike hannuna.

Babu komai Aminiyas nima kawai a haka na tashi yau.

Duk da har ranta take jin ba haka bane kallon da take min ya nuna bata yarda da abinda nace ba Amma bata ce komai ba.

“Daki muka shige muna hiran yaushe gamo, dan gaba daya bamu samu lokacin magana da juna ba se yau.

Anan take bani labarin Yusuf.

A hankali nayi murmushi toh fadamin wani irin so kike masa.

Nima bansaniba ta faɗa tana dariya.

Tun yaushe kuka haɗu

Mun kusa shekara daya.

Amman kince min bazakiyi doguwar soyayya ba zakiyi aure.

Taya kike tunanin zan iya aure bakya wajen sashi na ? an dai kawo kudin aure Rana ce kawai ba’a saka ba, amma shi ko yau aka ce masa a shirye yake ai.

Hannun ta na rike, ido na na cikowa da hawaye.

Dan Allah kiyi hakuri.

Da sauri ta rufe min baki da hannunta.

Ba bukata,

Yau ranar farin ciki ce, dan haka ki manta da duk abinda ya faru.

A hankali na kwantar da kaina a jikinta.

Toh kiramin haneep a waya muyi magana.

Babu musu, ta kirashi, tana fara ringing ta mikomin.

“Hello ta musamman”

Ba ita bace na faɗa ina murmushi.

Shiru da farko se kuma yace sashinmu ?

Ka canka daidai.

Toh yakk ?

Alhamdullah ya jikin ki ?

Na warke.

Ka shirya auren best nan da sati biyu ?

Idonta ta zare kaman zasu fado kasa.

Banbi ta kanta nasaki dariya.

Jin yama kasa Magana se inda Inda yake.

Shikenan tunda baka shirya ba.

Tsaya dan Allah.

Kinga dai wannan ba maganar wasa bane!

Ka shirya ko baka shirya ba ? Na tambayeshi har lokacin da dariya a muryata.

Ko yanzu kika ce a shirye nake wallahi. Ya faɗa cike da zumudi.

Shikenan zan tare nan da sati biyu, Idan ka shirya ka aiko a hada da nawa bikin.

Wayyo Allahna! Gaskiya nama rasa bakin da zan miki godiya.

Base ka gode min ba.

Ka sota tsakaninka da Allah! Ka kaunace ta da zuciya daya Ka kulamin da ita karka barta ta zubda hawaye, Shine kawai abinda zakamin.

Namiki alkawari insha Allah!!!

Nagode.

Ganin ta kasa Magana se motsa baki take.

Yasa na dungure mata kai dallah wai meye ?

Sannu baffa ko daddy, ai su kadai ne zasu zartar da aurena lokaci daya bake ba Ta faɗa tana rarraba ido.

Zamu gani toh! Na faɗa ina mata gwalo.

Mamah! Mamah!! Mamah!!!

Wai yaushe zaki dena min kiran mafarauta ? Ta faɗa tana harararta.

Ki rabani da wannan matar, ta faɗa kaman zatayi kuka

Meta miki ?

Haneep ta kira wai idan ya shirya bikinmu nan da sati biyu shi kuma ya yarda.

Toh meye zaman me kuke mana a gida bayan duk kunada masu sonku ? Ai gwara dukanku mu miƙaku mu huta da wannan haukan naku.

Ganin kaman mama ta goyi baya na, yasa tace ita gida zata tafi.

Dallah ki bari yayana yazo, se mu tafi tare.

Bazan iya jira ba gaskiya.

Ganin na hade rai tace toh shikenan

******** ******* *******

Se yamma likis Sannan yazo, lokacin best ta cika tayi fammm saboda yanda na sakata a gaba da tsokana.

Bayan an gama gaishe gaishe.

Ya mikomin leda ta.

Kallona yake, yana sakin murmushi kamar yau ya fara ganina,

A ta bangarensa kuwa ji ya ke tamkar be taba ganina ba, wannan buzuwar, ba kalar waccan bace, wannan fuskar ta cike yake da annuri da farin ciki.

Ganin kallon yayi yawa ne yasa na bata rai nace lafiya ?

Dariya ta na yi miki kyau! Abinda kawai yace kenan.

Kamar so kuwa nakara sakar masa dariyar.

Best dan Allah batafi kyau a haka ba ?

Ganin yanda take galla masa harara ne, Yasa yace toh ni kuma menayi.

Tun dazu ina son tafiya gida an hanani dole seka zo, awana nawa ina jiran ka ?

Toh kiyi hakuri bara ayi Sallah sena ajiyeku na wuce gida.

Bata ce komai ba se hararar wasa da ta sake masa.

Kyaleta dan uwa, Kasan lallaba amarya ake.

Amarya kuma ? ya faɗa da mamaki.

Insha Allah nab da sati biyu ma kuwa.

Masha Allah Abu yayi kyau ya faɗa yana murmushi, sai kuma muka juya kanta da tsokana.

Ganin yanda muka sata a gaba da tsokana, kawai ta fara kuka.

Seda naga dagaske kuka take Sannan na dena.

Yanzu dan Allah Ni yar tsana ce da za’a

11 / 40