Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.
Seda ya sauke ajiyar zuciya.
Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!
Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.
Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.
Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!
Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.
Chan dai ya kira sunan ta:
“Only!
“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?
Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.
Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.
“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!
Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.
Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.
Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.
“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”
“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.
Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.
Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.
Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.
Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.
******** ******* *******
Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:
“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.
Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.
Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.
This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!
Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.
“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.
Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.
“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!
Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.
Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......
Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??
Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??
Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??
Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?
Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??
Shin waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 29
Kuka nake irin silent kukan nan daba ka bukatar kowa ya ji sanda kake yinsa.
Nida kaina bansan kukan menake ba, nasan dai ban tsani ya doctor ba amman kuma bansan menake ji a kan sa ba.
Babban tashin hankali na da wace fuskar zan kalle sa ? Wane irin zama zamuyi dashi meye ne be sani a kai na ba ?
Babu na bawa kaina amsa.
Idan shima a ranar auren ya dawo yace ya fasa fa ?
Kirjina na dafe jin yanda ya amsa min da karfi.
Bansan sanda bacci ya dauke ni ba.
********* ********** **********
Zaune yake gaban mamyn sa, kansa a ƙasa.
Ahmad kasani a gaba ka ƙi magana, meyake faruwa ne?
“Mamy daman akan maganar auren da kike min ne..”
Wani kayataccen murmushi ta sakar masa, masha Allah! Yau kai da kanka, wacece haka.
Mamy ai kin santa ma.
Kallon ƙarin bayani ta masa.
Sumayya mamy!
Sumayya ta faɗa tana nazari, sumayya dai data sani matar aure ce amman bata sani ba ko wata sumayyar ya samo.
Mamy sumayya fa, ya katse mata tunanin datake.
Auren ta ya mutu da daɗewa.
Bazan hana ka abinda kake so ba ahmad, tunda bani zan zauna maka da ita ba.
Yanzu yaushe zaka tura manyan ?
Ajiyar zuciya ya sauke daman yasan mamyn sa bata da matsala ko kaɗan.
Mamy duk sanda kika ce.
Shikenan zanyi magana da su insha Allah.
********* ********** **********
Da safe sukuku na tashi kaman mara laka.
Mama ce tazo ta kawo min abinci.
Amman nakasa ci se jujjuyashi nake.
Lura mama tayi da na kasa cin abincin yasa tace “Sumayya!
Na’am mah!
Meyake faruwa ? Bakyason Ahmad ɗin ne?
Mahmah Ni yanzu har ina da zaɓin wanda zan so?
Duk da magana ta, ta sanyayar mata da jiki, bata fasa maganar da tayi niyya ba.
“Sumayya Ahmad yana sonki, kuma yayi miki halacci sosai a rayuwa sumayya, dan Allah ki rarrashi zuciyar ki insha Allah komai zeyi daidai, ina jin a jiki na zaki farin ciki da auren sa insha Allah sumayya”
Mah kina farin ciki da auren nan da zanyi ?
Sosai sumayya.
“Insha Allah zamu zauna lafiya mama na miki alkawari.”
Sosai farin ciki ya bayyana a fuskar mahmah.
Ganin farin ciki a fuskar mahaifiyata yasa kawai na amince da shi da dukkanin zuciyata.
“Bansan wane kalan zama zamu yi, kuma bansan a wane matsayi zan ajiye auren ba, amman dan farin cikin mamah zanyi komai kaman yanda ita ma take abubuwa daya a kaina.!!!
********* ********** **********
A zaune muke muna kallo, ni kuma ina wasa da little.
Best kin san wani abu?
A’a sashi na, meyafaru ta juyo gaba ɗaya tana bani hankalin ta.
Ƙasa nayi da kaina, sannan na faɗa mata duk abinda ya faru tun daga farko har ƙarshe.
Tsawon lokaci batace komai ba se kuma ta miƙe kaman wadda aka tsikara.
Ƙatuwar speaker ta kunna kawai ta fara tiƙar rawa kaman mahaukaciya.
Baƙin ciki ne kawai yasa na fara kuka.
Hannuna take janyo wa muyi rawar tare na zare na cigaba da kuka na.
Seda ta gaji dan kanta sannan yya kashe ta dawo ta zauna tana maida numfashi.
Toh yanzu dai kin kusa zama matar doctor kenan ?
Bansaniba! Na bata amsa ina harar ta.
Yanzu meye abin kuka bakya son sa ne?
Bansaniba nima.
Dogon tsaki kawai taja.
“A wannan karan ne zamuyi biki sashina, a wannan lokacin ne zaki san kinyi aure, abubuwan bama ɗaya ba, wallah nafi kowa farin ciki da wannan auren sashina.”
Sosai take tamin zuba amman narasa mezan ce mata haka na haƙura na kyaleta kawai.
Da ƙyar ta barni na tafi gida.
********* ********** **********
Ina kwance da daddare naji waya ta na ringing.
Ɗagowa nayi ina duba me kiran.
“YAYANA!
Ido kawai ka na zuba wayar har ta yanke banyi picking ba, sema zuciya ta datake bugawa, har ta tsinke banyi picking ba, haka yaci gaba da kira beyi zuciya ba, ni kuma na kasa ɗagawa.
Massage ne ya shigo, ban ma buɗe ba akan screen na karanta.
“Ki fadawa baffa ranar Friday za’a kawo kuɗin auren”
Shikenam abinda massage ɗin ya kunsa.
Ido na kawai na lumshe.
A haka mama ta shigo ta same ni.
Zo kici abinci sumayya.
“Mah na koshi, ya Ahmad yace ranar Friday za’a kawo kuɗin zance ki faɗawa baffa.
Hamdala kawai take yi har ta juya ta fita.
Bansan ya sukayi da baffa ba.
********* ********** **********
Ya Ahmad bayan ya ajiye wayar tunani yayi inaga akan cewa bazan fadi sakonsa ba tunda ban daga masa waya ba ma, saboda haka kawai ya yanke shawarar kiran best ya bata sakon.
Bayan ta daga wayar yace “Hello!
Hello doctor!
Haleemah ya gida ya little da abbanta.
Kowa lafiya alhamdullah.
Pls ki faɗawa baffa ranar Friday za’a kawo kuɗin zancen buzuwa.
Murmushi kawai tayi cike da zolaya kuma tace
“Ah masha Allah doctor ka ƙara samo mata ango kenan??
Ke meyasa kin fiya neman magana ne?
Ni dan Allah ki kulamin da ita, kar ki barta a damuwa kuma karki takurawa amaryata yawwa...
Ah lallai doctor kasami kan ka ta faɗa cikin dariya.
Shima dariya yayi sannan yayi mata sallama.
********** ********** *********
Ranar Alhamis humaira tazo gida ita da best.
Gaba ɗayan su murna suke sosai.
Ni kam kallon ta kawai nake ta ƙara girma tayi fresh abunta, dan a yanzu zan iya cewa tama fini ƙiba sosai, wanda bana raba ɗayan biyu ciki gare ta.
“Mamah dame za’a sauki baƙin ? Best ce take tambayar mama.
“Kaman dai yanda aka saba haleemah” itama tabata amsa.
Nikam daman yau ina nan bazan koma gida ba se gobe.
Da sauri mama ta katse ta kibar haneep ɗin da wa a gida?
Ayya mamah ai gobe aiki zamuyi ko humairah?
Haka ne fa mamah dan nima se gobe zan koma gida.
Babu wadda zata kwanar min a gida ko waccen ku seta koma gidan mijin ta.
Babu wanda ya ƙara magana a cikin su.
Taso muje sashi na.
Banyi musu ba nabita muka shiga ɗakin mu.
Sumayya ina son ki bani hankalin ki, ki ajiye komai a gefe ki tsaya ki fuskanci gaba, ki manta da doctor yasan wacece ke, eh yasan wacece ke amman ai besan ya kike ba.
Dan haka zamuyi shirin da doctor seya shiga cikin kokonta anya kin taɓa aure?
Bansan sanda dariya ta kusa kwace min ba, daɗi na dake haleemah wani lokacin baki da hankali.
“Mtssss ni kitsaya mu ƙarasa magana, nasan mamakin furucina ne ya sakaki dariya haka ne?”
“Sosai ma”
Kinsan *momma’s zhara*?
“A’a wacece? Na mayar mata da tambayar ta.
*Momma’s zhara me supplement ce taken ta maida tsohuwa yarinya*
“Babu kalar supplement ɗin dabata siyar wa, idan har matsalar ki zubewar breast ne ko rashin hips da bom_bom, haka kuma idan har matsalan ki rama lokacin jeki wajen momma’s zhara (09129969795)
Kin tsaya kallona sashi na ba a iya nan ta tsaya bafa.
Matsalar ki fatar ki na yamushe wa ko bushewa maza ki garzaya wajen momma’s zhara (09129969795) zata haɗa miki mai da shower gel harda supplement shiyasa kika ji ana mata take da *maida tsohuwa yarinya* tana siyar da maganin ni’ima da sanyi duk yanda gaban ki ya kai ga buɗewa zata baki maganin da ɗan ya tsanki baze iya shiga jikin ki ba..
*Anan kano take birget kasuwar murtala* (091292996975)
Ajiyar zuciya kawai na sauke.
Dan haka gobe zamuje zama be gan muba.
Bana son muta jan zance shiyasa na kyaleta.
Amman wane gyara zanyi Allah na tuba auren da bashi da tabbas.
********* ********** **********
Ranar juma’a aka kawo kuɗin zance da saka rana, wata biyu aka saka.
Zoka ga murna wajen best da humaira.
Mamah kanta farin cikinta yakasa ɓoyuwa.
Karfe uku muka shirya muka tafi gidan momma’s zhara.
Akace shimfidar fuska tafi ta tabarma, sosai ta karɓe mu hannu bibbiyu, munga karamci.
Bayan angana gaisawa best tayi mata bayanin abinda ya kawo mu.
Kallona tayi tace ahaka kuma kaman bata taɓa aure ba.
Murmushi kawai nayi.
Babu bata lokaci ta haɗa min duk abinda ya dace best ta mata transfer.
Buzuwa juyowa nayi na kalleta karki wani damu fa zaki chanji sosai insha Allah.
Godiya muka mata sannan muka mata sallama muka tafi.
A hanya nake cewa best amman tana da kirki.
Ke kaɗan kika gani baki ji yanda ake yabon ta, ga kayan ta sauki.
Da irin hirar nan har muka ƙarasa gida.
Chak na tsaya na kasa gaba kuma na kasa baya ganin wanda ban taɓa tunanin gani ba a Kofar gidan a tsaye.........
Ayi hakuri a bisa gajartar wannan page din, in Sha Allah next page zanyi kokarin na fadadashi.
Nagode taku har kullum Rabi’atu Fulani
Talla!
💫
Talla!!
💫
Talla!!!
💫
💫
ALIYU HAIDAR ( THE LION
🦁
)
💫
Paid Book...
By
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.
Seda ya sauke ajiyar zuciya.
Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!
Murmushi ta masa, “ka kwantar da