ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 40

45K to 48K   out of 117.2K words

ta rikoni bayan na fito da shirin tafiya batare da nayi sallama da kowa ba.

Karki tafi kinji sumayya, ta faɗa hawaye nabin fuskarta.

Hawaye ne a Idona Nima saboda idan nace inason rabuwa da mama nayi Ƙarya, soyayya ce kawai take rudata.

Sashi na, karkiyi Wannan kuskuren.

Da sauri na juya dan bansan zuwanta ba.

Murmushi nayi “Karki damu ina nan ina lissafi da lokacin haihuwar ki yayi zanzo Kano.

“Dan Allah karki tafi aunty sumayya!

Humaira ya zama dole tunda an riga an daura ki tayani da addu’a in Sha Allah idan na tashi zuwa ganin gida zan taho miki da English wears tunda naga kina sonsu.

Kuka ta fashe dashi batare da tace komai ba ta rungumeni tsam a jikinta.

Saida muka gama kuka dukanmu sannan A hankali na zame jiki na daga wajensu na juya.



Nabar Ahalina! Dangina! Aminiyata! Mutanen arziki!

Duk na hakura dasu!

Saboda namiji!!!

Na zabeshi akan kowa nawa!!!!

Mu hadu a page 19 in Sha Allah Gobe, yau saboda gajartar pages din yasa nayi guda biyu.

Taku har kullum Rabi’atu Fulani.

Nagode.

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 19



******* ******** ********

A kofar gida na samesu, suna jirana domin rakani tasha.

Abokinsa da motarsa yazo domin a kaini tasha a ciki ina shiga motar ya fara ja na waigo da niyyar yiwa gidanmu kallon karshe dan yanda basa sona ji nake zan iya kara shekara goma sha wani abun ban kawo musu ziyara ba.

Mun zo fita daga layinmu naga Bappa a bakin layin kallo daya yayiwa motar ya ɗauke kai.

Jikina ne yayi sanyi na fara jin kewar gida da yan gidanmu.

A hankali na haɗe kaina da jikin glass, na lumshe idona!

******** ******** *********

Bayan tafiyata mama ashe faduwa tayi hawan jini ne mai ƙarfi ya kamata, motarmu tana tafiya humairah ta koma gida taga mama ta fadi, ihu ta saka ita da best, da sauri sukayi kanta,

Best tana ƙoƙarin kiran haneep ita humairah tana ƙoƙarin kiran Ahmad a Sa’a sai ahmad ya daga, Cikin kuka ta sanar dashi abinda yake faruwa, lokacin yana asibiti, ai da sauri ya hawo motarsa ya yo gida bai lura ma da bappa da yake bakin layi ba har lokacin.

Yana karasawa gida da sauri ya shiga ba ko sallama ya shiga saboda yanda yaji humaurah tana kuka, yana zuwa yacewa humairah da best su kamata a saka a mota,

Ana sakata a mota yaja da sauri ya dauki hanyar titi, yana zuwa bakin layin ne humairah tace ga baba can, tsayawa yayi suka daukeshi sannan ya dauki hanyar asibiti.

An dauki tsawon minti arba’in kafin a samu mama ta dawo hayyacinta, tana dawowa daidai yayi mata allurar bacci,

Sai bayan isha sannan ta farfaɗo, lokacin humairah tana tare da ita, tana daga can gefe a zaune tayi tagumi taji mama tana kiran SUMAYYA, da sauri ta tashi taje gareta, riƙe hannunta tayi tace: humairah amma dai SUMAYYA bata tafi ba ko ? Tana ina ? Ta dawo ? Haka ta dinga jera mata tambayoyi.

Hawaye ne a idon humairah kawai tana girgiza mata kai.

Ganin tana girgiza mata kai ne yasa ta rufe idonta bata sake budewa ba sai hawaye, takaici take ji a ranta sosai da kuma taurin kai irin na sumayya tunani take wannan ce irin soyayya ce haka ? Wannan soyayya ce ko hauka ?

Sai Wajen tara sannan yaya Ahmad ya shigo tare da bappa ya kara duba mama ya bata magunguna suka tattauna da bappa sannan yayi musu sallama ya tafi.

Sai dare sannan haneep yazo ya duba mama sannan ya dauki best suka tafi gida.

******* ********* ********

Da safe ammie da Daddy suka zo duba mama saboda a daren jiya best ta kirasu ta sanar dasu tana kuka, aikuwa suka bugo sammako suka zo asibitin basuyi minti talatin ba sai ga best nan tazo da haneep, zuwa safiya makota, yan uwa, da abokan arziki suka dinga zuwa duba mama, ba yanda ta iya haka ta ajiye damuwar da take cinta ta fara tarbar mutane duk da bata son magana daga angaisa saita rufe ido ta cigaba da tunani sai taji shigowar wasu bakin take bude ido, saidai ta bar su best da tattaunawa da mutane bayan angama gaisawa.

Ahmad tun safe da yazo duba mama yake tunanin meyesa bai ganni ba jiya kuma yau ma bai ganni ba ?

Lafiya kuwa ? Yana son tambayar best amma bai samu dama ba saboda shima aiki yasha kansa su best kuma yan dubiya sai zuwa dubiya suke.

Mamaki yake to ko har ta sake wani auren ? To idan ta sake wani auren meyesa bata zo ba ? Dan tana gidan miji ai hakan bazai hana tazo duba mahaifiyarta ba”. Tunanuka ne makil a ransa.

Da dare yazo bada magani lokacin best ta tafi sai humairah kawai kowa yayi ya tafi yan dubiya su Daddy ma sun koma gida baba ne kawai a masallaci sai humairah tana jinyar mama.

Bayan ya gama duba mama yaga jininta dai yana nan har a lokacin bai koma daidai ba, nan ya zauna yana lallashinta da karfafa mata gwaiwa da kuma nuna mata illar da damuwar zata yi mata, daga karshe dai ya samu ya shawo kanta da kyar akan cewa zata rage in Sha Allah tayi masa alkawari.

Sallama yayiwa mama sannan yace humairah tazo yana son magana da ita,

A waje suka tsaya shi da ita, yana tambayarta damuwar mama meye ya jawo mata wannan mummunan hawan jinin ? Sannan kuma ina yayarki ? Ya kare yana tambayarta ni.

Hawaye humairah ta share sannan tace: yaya Ahmad duk akan SUMAYYA ne wannan abun ya samu mama, sumayya tayi aure batare da saka albarkar su mama ba, sannan kuma tayi aure ta bar garin Kafin auren kuma........ Nan dai ta kwashe komai da yake faruwa tun ranar da na samu su mama da maganar aurena da Khalil har zuwa jiya da mama ta yanke jiki ta fadi bayan SUMAYYA ta tafi Lagos wajen mijinta.

Ji yayi kafafunsa suna kokarin kadashi, yaji kansa yayi wani iri, damuwa, takaici, mamaki da kuma bakin ciki duk suka tarar masa, me yarinyar nan take nufi ne ? Meye a kanta ne ? Me ta dauki soyayya ? Ita kadai take soyayya ne ? Meyesa batada hankali ? Tambayoyi ne a ransa makil ya rasa mai amsa masa sai wacce yake da tambayar a kanta.

“Shikenan kawai ya iya cewa, ya juya ya nufi office dinsa, ita kuma humairah ta juya daki wajen mama.

******** ******** ********



Kwanan mama uku a asibiti yaya Ahmad yaga jikinta yayi sauki sosai dan haka ya sallameta tare da bata wasu shawarwari wanda zai taimaki lafiyarta.

Yaso ya maidasu gida amma aiki yasha kansa saboda haka haneep ne ya maidasu gida.

********* ******** *******

Washe gari yaya Ahmad yazo duba mama ya jima a gidan suna hira yana lallashinta, yana kwantar mata da hankali akaina da kuma aurena.

“Hmmm! Ahmad yaron ba alkhairi bane a rayuwar ta, zata sha wahala a hannun sa, duk yanda akayi kokarin fahimtar da ita taki fahimta amman zan bita da addu’a insha Allah”. Abinda mama tace kenan.

Bai ce komai ba ya shiga wata hirar kuma har zuwa bappa ya dawo ya sameshi aka zauna aka cigaba da hira gaba daya, sai Wajen 9 yayi musu sallama ya tafi gida.

Tun ranar da mama ta farfaɗo humairah taso kiran SUMAYYA ta sanar da ita abinda ya faru best ta hanata, kuma bappa ma ya goyi bayan kar a fada min, wannan dalilin yasa banada sani akan abunda ya faru.

******** ******** *******

LAGOS

Kwananmu biyu a hanya muka isa Lagos, duk gajiya ta gama wahalar dani.

Muna sauka na ganshi yana jirana a tasha, murmushi yayi min ganin fitowata daga mota.

Murmushin kadai yasa naji duk gajiyar da nake ji tana bajewa, daukar jakata yayi ya saka a mota, na shiga gaba muka nufi gidanmu.

Muna karasawa gida na tambayeshi banɗaki ya nuna min, na cire kayana na shiga wanka, ina fitowa ko kaya ban saka ba na kwanta sai bacci.

Bacci nake me nauyi sosai.

Koda na tashi tsoro ne ya kamani ganin gidan duhu sosai babu motsin kowa.

Khaleel na fara kiran sa cikin tsoro!

“Khaleel! Khaleel!! Khalil!!!

A haka na lallaba na fito daga bedroom din zuwa parlo.

Lokaci daya haske ya mamaye dakin.

Suman tsaye kawai nayi saboda tsabar mamakin abinda na gani!!!!!!

Ayi min afuwa yau page daya zaku samu sannan zaku ga page din bashida tsayi, in Sha Allah next time zaku jini da page me tsayi.

Mu hadu a page na gaba domin jin abinda SUMAYYA ta gani.

Nagode.

Taku har kullum ( Rabi’atu Fulani ).

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 20

Mamakine ya hanani na motsa.

Lokaci daya nake hawaye da dariya.

Bansan sanda na tafi a guje ba na rungumeshi.

*HAPPY MARRIAGE LIFE MY HAPPINESS*

Ya maimaita min a cikin kunne na, kara ƙanƙameshi nayi a jikina.

Duk yaushe ka shirya abin nan ? Na tambayeshi cike da shagwaba wacce shi ya sabar min da ita.

“Kina can kina bacci mana sweetheart”.

Ɗagowa nayi ina karewa dakin kallo.

Decoration din yayi min kyau sosai.

Komai baby pink ne harda cake din.

Hannuna ya rike muka matsa wajen cake din.

Farin ciki yama hanani magana gaba daya.

Bara na shirya mu yanka cake din shaleleh, na fada ina juyawa daki.

Maza toh ammatana! Ya fada yana murmushi.

Shaf shaf nayi wanka.

Ina neman kayan sawa kawai naga yar jaka ta shopping a kan gado na.

Da hanzari na buɗe.

Wowww!!!!!!

Doguwar riga ce baby pink, ta gaji da haduwa. ( This is my Fav color ).

Shigowa dakin yayi yanata zuba kamshi shima cikin shadda milk tasha aiki ga hula.

Ina ganin sa na kara washe baki! Nace “Kayi sosai shaleleh.

Na kaiki kyau ne lollipop!? Ya faɗa yana jan hanci na.

Tare muka yanka cake din ya bani a baki, nima na basa, sannan muka sha hotuna.

A daren ranar na tabbatar da gaske khaleel yana sona.

Ya nunamin soyayya, soyayyar da zan iya cewa beta nunamin irin taba tsawon shekara 4.

Naga kauna, naga gata.

Naji babu wta mace data kaini Sa’a a fadin duniya.



******** ******** ********

Ga baki daya mama tasaka kanta damuwa, takasa cire sumayya a ranta, duk yanda baffa yake mata faɗa ta kasa.

Kusan kullum ya Ahmad se yazo gidan, ya mata labarai masu dadi da sanyaya rai, amman ta kasa cire damuwa a ranta.

Angel Tunda ta dawo take zuba rigima ina masoyiya, humairah da yaya Ahmad ne suke aikin lallashinta.

Dagiya da kulawa da kuma addu’ar yaya Ahmad yasa mama ta fara kwantar da hankalinta yana nuna mata in Sha Allah addu’arta ce zata zame min garkuwa daga kaidin Khalil.

Haka kuwa ta dukufa da yi min addu’a da fatan Allah ya karkato da hankalina gida, Allah ya ganar dani gaskiya, ba dare ba rana kullum cikin addu’a.

******** ******** ********

Wani irin tattalina khaleel yake, a halin yanzu gaba ki daya bani da wata damuwa.

Dama matsalata a rayuwa rashin Khalil ne, kuma gashi kullum muna tare manne da juna.

Gaba daya na manta da gida.

Tunda na tambayi khaleel wayata, yace ba yanzu zanyi waya da yan gida ba, ban kara masa magana ba, saboda kada ransa ya ɓaci.

Yau tsawon wata na uku da aure, babu abinda zan cewa Allah se godiya.

Ban nemi komai na rasa ba a gidana.

Indai ba wai batan lissafi nayi ba yanzu muna cikin watan da best zata haihu, EDD dinta ya cika.

Tun kwana biyu da ya wuce nake son tambayar Khalil wayata domin nayi waya da best, saidai bana son nayi masa maganar ransa ya ɓaci duba da baya son maganar gida tana fitowa daga bakina.

Daurewa nayi na cije nace yau dai zan tambayeshi. Saida dare yayi muna zaune muna kallon wani Film na korean, na kalleshi nace:

Shalelenah dan Allah ka bani wayata na kira best yanzu tana cikin watan haihuwarta, inason naji yaushe zata haihu ? Ban sani ba ma ko ta haihu.

Shiru yayi bai ce min komai ba,

Saida na sake maimaitawa sannan ya kalleni yace, “ban san inda wayarki take ba! Ina tunanin ta fadi!!! Yana fadar haka ya tashi ya shige daki ya barni a wajen.

Ji nayi kamar na dora hannu aka na fashe da ihu!

******* ******** *******

Anan Kano kuwa tun wajen karfe ukun dare Best take nakuda, abu yaki yuyuwa, har karfe takwas na safe.

Gaba daya ta fita hayyacin ta.

Nurse sun sha zagi, shikam haneep ance an tsanesa ma ba’a son kara ganin sa.

Sashi na tasha kira kaman sunan ze kare.

Zuwa karfe tara, Allah ya sauke ta lafiya ta samu yarta mace.

Faɗin farin cikin da sukayi da samun yarinyar nan bata baki ne.

Ɗakin hutu aka wuce da maman baby.



******** ********* *******

Gajiya na da zaman kuka na tashi na nufi dakinsa.

Yana zaune yana danna waya amman ban bi ta kansa ba, na hau bincike a dakin.

Me kike nema?

“Waya ta!

Wai bana ce miki bata nan ba ? Ya faɗa cike da tsare gida.

Bansan meyasa fuskar sa ta bani tsoro ba, kodan na dade banga ya hade min rai ba.

Zama kawai nayi, na haɗe kai da gwiwa, ina rera masa kuka kaman marainiya.

Tun inayi a hankali har nafara da karfi.

Jin ya rungumeni ta baya kawai kukan nawa ya kara sauti.

Fadamin me kike so yanzu.

Ina cigaba da kukan nace “Gida!!!

Toh ya isa haka zan kaiki insha Allah, zan nemi izini a wajen aikina.

Kaina na gyada masa.

Amman yarinyar nan Allah ya shirya ki.

Menayi ? na faɗa ina tura masa baki.

Baki nemi mama ba, kin nemi best ɗin ki.

Murmushi nayi, nace ai ita mama ko yaushe muna tare.

Kaman ya, ya faɗa yana kallo na.

Best! Na tare da ita, nasan bazata barta cikin damuwa ba, sannan ga ya Ahmad.

Haɗe rai yayi kafin yace “Sau nawa zance miki kar na karajin sunan mutuminnan a bakin ki ?

Duk da zuciya ta babu daɗi seda nayi dariya.

Bakomai fa tsakanina da shi na faɗama.

Ganin yanda ya hade rai ne yasa nace Allah ka rage kishi kauna.

Bai ce komai ba ya koma kan gado ya zauna.

Dawowa nayi kusa dashi nace

Yanzu yaushe zamu tafi gidan ?

Zamu je soon ai.

****** ****** *****

Tunda ta tashi take kuka.

Yarinyar kawai take kalla, seta kara fashewa da kuka.

Anyi tambayar duniya kuma taƙi magana.

Koda doctor yazo dubata babu wata matsala sallama kawai ya basu.

Yarinyar yazo dauka.

Da sauri ta dauke ta, tana harararsa da kumburarrun idanuwan ta.

Wannan ɗin yar amana ce.

Kayi hakuri uwarta bata son allura, dan haka bazaka mata ba.

Shi doctor murmushi yayi kawai, yace dama zan kara ganin fine girl din ne, amman ba allura zan mata ba.

16 / 40