Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
Ahmad da taki wucewa a raina.
Sai bayan la’asar na bar gidan nata na tafi gida.
Har na koma gida gaba ɗaya na kasa sakewa, maganar da best tayi ta tsaye min a raina sosai.
Tayaya ma take tunanin aure tsakani na da ya doctor, mutumin da yasan ni gaba da baya, koda matan duniya sun kare babu abinda zeyi ni.
Kaman yanda khaleel yake faɗa ne bani da tarbiyyar da za’a haɗa zuri’a dani, dan haka nasan shima ya Ahmad hakan ne a wajen sa.
Da haka na samu na cire maganar a cikin raina.
********** ********** *********
Shirye-shiryen bikin humaira ya kankama, dan har mun fara karɓar baki.
Mutanen da suke zuwa bikin ko sunfi waɗan da suka zo nawa yawa babu ma haɗi.
Sedai wani abu da yake ɗaure min kai da sun gani za’a fara magana ƙasa ƙasa.
Ban kawo komai a raina ba.
Yau zamu fara event.
Duk yanda best taso nayi kunshi nakiya, harseda ta haɗa ni da mama sannan.
Sun ki ganewa Ni kwata kwata bani da sha’awar abubuwan nan a halin yanzu, ko burgeni ba sayi.
Yau akayi kamu, gobe walima, jibi a daura aure a miƙa ta gidan ta.
Wajen taron ya cika sosai.
Waje na fito neman best.
Kaman ance nabi wata hanyar.
Maganar danaji anayi ne yasa na kusan yanke jiki na faɗi.
Hmmm wallahi da auren ta biyu, na farkon ta kashesa ita da saurayin ta, Sannan ta auri saurayin ai kuwa yaci ubanta ya korota.
Bakuga yanda ta zama yanzu ba.
A hankali na fara ja da baya, ina hawaye, kenan daman duk kallo na kawai ake tayaya suka san meyafaru dani.
Koda na koma wajen taron, duk wanda naga yana kallo na, kawai senaji a jikina maganar da suke kenan.
Barin wajen nayi naje na samu waje ɗaya na zauna ina hawaye.
Wani sabon danasani ne ya ƙara rufe ni.
Har aka tashi a wajen ban koma ba.
Zamewa nayi Ni kadai na koma gida.
Gaba ɗaya na kasa bacci ganin yanda yan uwana na jini suke yada min magana abin ya ɗagamin hankali, kenan kowa kallo na yake kawai.
Amman tayaya suka san komai da yafaru.
A hankali zuciya ta tabani baba musa da matansa.
Idona kawai na lumshe hawaye na zubo min.
Yanzu ya zanyi ? Na tuba na koma ga Allah amman mutane sunƙi sun gane.
Koda safe da na tashi muka haɗu da mama kasa jurewa tayi ganin yanayin da nake ciki.
Hannu na taja har ɗakin baffa.
Meyafaru sumayya ?
Babu komai mah! Na fada ina sauke Idona ƙasa hawaye yana zubo min.
Hankalin mama ne ya tashi ta dinga tambayata me ya faru ?
Ganin duk yanda ta damune ya karyamin zuciya.
Rungumeta kawai nayi ina kuka sosai.
Mah ki yafemin kinji dan Allah!!!
Sau nawa zan faɗa miki na yafe miki sumayya.
Rarrashi na tayi sosai, sannan muka fito.
Gidan su best nake son tafiya sedai, bansan mezan tarar can ba.
Gashi har yanzu babu waya a hannu na.
Lafiya lau akayi biki a gama, amman Allah kaɗai yasan baƙin cikin dana ƙunsa a raina.
Mun kaita lafiya Alhamdullah.
Se fatan Allah ya basu zaman lafiya me dorewa.
********* ********** **********
Sosai nayi nisa a karatuna har gashi muna shirin sauka.
Masoya na fito min amman Allah ya gani nidai babu lissafin aure a tsarin rayuwa ta.
Ya Ahmad yana kula dani sosai.
Yanzu haka yanata kokarin baffa ya barni na rike waya, kuma be ƙiba.
Yace amman na kula.
Sosai muke shirin saukar Alkur’ani.
Baffa ya taka rawar gani sosai, haka aminiyar arziki.
Naga soyayya sosai lokacin saukar nan sosai.
A ranar da daddare baffa ya aiko a kira ni.
Batare da fargabar komai naje ba dan nasan ba wani lefi nake a yanzu ba.
Har kasa na tsugunna na gaishe sa.
Albarka yasamin akan karatuna Sannan yamin magana da ta gaba, da seda na nemi nutsuwa ta narasa.
Yanzu miji nake son ki fitar kiyi aure sumayya shine kawai abinda zaki min.
Duk da maganar tazo min a bazata haka na dake ban nuna masa ba.
Shirun da yaji ne yasa ya sake maimaita min maganar, Ni kuwa tuni na tsunduma kogin tunani.
“Toh baffa insha Allah! Abinda kawai nace kenan.
Sallamata yayi na tashi na fita.
Ina fita na kira ya Ahmad a waya dan Wallahi hankalina a tashe yake, yana ɗagawa nace “Ya Ahmad baffa yace na fito da mijin aure cike da tashin hankali nake magana.
Nan na labarta masa yanda muka yi da bappa, rarrashina ya fara yi yana kwantar min da hankali, Saida ya tabbatar da hankalina ya kwanta sannan ya ajiye wayar, bayan yayi min alkawarin zai zo gobe sai mu ga yanda zamu bullowa abun, wannan ne ya ɗan kwantar min da hankali har na samu relief.
********* ********** **********
Washe gari ya Ahmad ya ƙaraso da yamma, bai shigo gidan ba yana daga waje kawai ya kirani a waya.
A hankali na ƙaraso bakin motarsa, ya doctor ina wuni.
“Alhamdullah buzuwa! Kefa ?
Idanuna ne sukayi narai-narai zanyi kuka.
Murmushi yayi yace yadai ?
Ganin yana murmushi ne yasa na fashe masa da kuka.
Meyene abin kukan ? Ya tambaya yana bata rai.
Ina hawaye nace “kana jin fa bappa abinda yace, bayan kasan Ni ba tsarin aure a tare dani, kuma ma ban bawa Kowa fuskar ya kulani ba bare na kawowa bappa shi! Kaga kenan babu wanda zan kaiwa ba!.
Kina da shi mana ya faɗa yana kallo na.
Shiru nayi alamar tunani, se kuma nace “a’a ni banida, ni yanzu ko aure zanyi ai ba auren soyayya bane ya Ahmad!
Auren menene ya tambaya fara’ar fuskar sa na raguwa.
Kaddara ya doctor! Duk wanda na aura yanzu ba auren soyayya bane, na rigada na ajiye soyayya.
Ko kaɗan ban kula da sauyawarsa ba.
Shikenan ni zan kawo mijin kina so?
Da sauri na ɗago ina kallon sa, sedai yaƙi bari mu haɗa ido.
Abokina yace yana son na masa mata toh zan bashi ke, ai banyi lefi ba ko?
Murmushi nayi danni wasa na ɗauka, kawai na daga masa kai.
Jeki gida toh.
Har na fara tafiya na juyo baka da lafiya?
Lafiya ta lau me kika gani?
Naga idon ka yayi ja sosai.
Babu komai tafi gida. Abinda yace kenan ya fara kokarin tada mota.
Koda naje gida, marairaicewa mama nayi ni wajen best zani.
Hararata tayi kafin tace Amman duka yaushe kuka rabu sumayya ?
Mama magana zamuyi fa! Na fada ina shirin yi mata kuka.
Shikenan, karki daɗe dan Allah.
Yawwa mamana! Daki na koma na dauko hijab, nayiwa mama sallama na fita.
********* ********** **********
Zaune muke parlon.
Ni kin sani a gaba kinki magana ina da abinyi fa sashi na.
Seda na harare ta sannan na ɗauke kaina, na faɗa mata yanda mukayi da baffa da ya doctor.
Gaskiya ban taba sanin baki da tausayi da hankali ba se Yanzu.
Da mamaki nake kallon ta, me ya faru to ? Banada tausayi kamar ya ?
Eh wallahi sashina, kina nufin baki gane doctor sonki yake ba ko yaya? Zai zauna ne yayi ta bibiyar ki haka kawai batare da wani abu a ransa ba?
Ni.....ba....ya sona, na faɗa a rarrabe.
Toh fadamin ƙinki yake ? Tace tana hararata.
Yayana ne kawai amman babu kalmar soyayya a tsakanina da shi.
Hmmm ai shikenam, shi kuma tunda tsoron ki yake seya ƙi faɗa miki, sema cewa da yayi se haɗa ki da abokinsa ko?
Se ya zauna a wannan karon ma ya rasaki! Kallonta kawai nake ganin yanda ta dage sai zuba masifa take, kamar wata uwarmu Nida ya Ahmad din, Sai ma ta bani dariya.
Dole kiyi dariya mana Zan kirashi shima muyi magana.
Dan Allah karki karasa zubar da mutuncina da yayi saura a wajen sa, Bai taba cewa yana sona ba!
Hmmm kawai tace.
Ganin duk munyi shiru ne na miki nace mata tafiya gida zanyi.
Ke kin isa ma ? Ba inda zaki wlh tunda baki son gsky.
Ba yanda na iya haka ta hanani tafiya sai da nayi sallar la’asar.
Har bakin hanya ta rakani na samu mota sannan ta koma.
Tana komawa gida ta dauki waya ta danna masa kira.
Gaisawa sukayi ya tambayi lafiyarta da na little da kowa da kowa, ta amsa masa da cewar kowa yana lafiya.
Sannan ta ɗora da faɗin yanzu sumayya tazo min da wani zance shine nace bara na kira naji.
Shiru yayi yana tunani.
Wane zance kuma haleemah ?
Wai zaka haɗa ta aure da abokin ka ?? Shiru yayi bai bata amsa ba.
Meyasa zakayi haka doctor ?
Menayi wai haleemah? Bakyason abokin nawa ne ?
Share tambayar sa tayi kawai ta ƙara jefa masa tambaya.
Tsawon wane lokaci zaka ci gaba da dakon soyayyarta ?
Tsitt yayi kaman ruwa ya cinye shi.
Nasan kana sonta meyasa bazaka bayyana mata ba ?
Yaushe nace miki ina sonta wai ?
Shima ya tambaye ta.
Duk wanda yaga yanda kake kallon ta yasan kana sonta amman bansan meyasa kake wahalar da kanka akan abinda baze maka wahalar samu ba.
Kana da tabbacin idan har ka rasata a wannan karon, zaka ƙara samun ta??????
Kallon ɗan uwa take min haleemah, bazan so narasa ta gaba ɗaya ba, a yanzu ta shafe babin soyayya a cikin zuciyarta.
Ni kuma ita nake so ba gangar jikin ta ba, zan ƙara bawa zuciya ta haƙuri a karo na uku.
Amman bazan iya zama da macen da bata sona ba!!!
Ina mata soyayyar da ban taɓa yiwa ko wace ƴa mace ba! Amman taya kike tunanin zan zauna da ita bata sona??????
Tirƙashi......
Mu hadu a ICEN DAMUNA page 29 ICEN DAMUNA ya dauko cittah
🥰
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
Talla!
💫
Talla!!
💫
Talla!!!
💫
💫
ALIYU HAIDAR ( THE LION
🦁
)
💫
Paid Book...
By
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.
Seda ya sauke ajiyar zuciya.
Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!
Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.
Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.
Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!
Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.
Chan dai ya kira sunan ta:
“Only!
“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?
Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.
Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.
“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!
Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.
Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.
Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.
“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”
“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.
Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.
Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.
Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.
Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.
******** ******* *******
Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:
“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.
Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.
Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.
This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!
Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.
“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.
Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.
“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!
Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.
Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......
Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??
Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??
Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??
Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?
Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??
Shin waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)