ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 40

15K to 18K   out of 117.2K words

wai daman tare kuke ?

Hmm muna zuwa ta fara gudu, keda ki Kasan halin kayarki ta fada tana neman wajen zama.

Bayan gaishe gaishe, ta kara juyowa gareni daugther baki da lafiya naga duk kin faɗa.

A’a na faɗa ina mikewa, na nufi sama.

Tunda akayi hutun Nan bata da aiki se tunani narasa me ke damunta.

Mamah ta faɗa tana kallon hanyar dana bi.

Bari su sakko mukara bincikarta inji ammie” nidai ina jinsu na shige daki.



*** *** *** *** ***

“Babu sallama na faɗa dakinta, tayi daidai tana bacci a kan gadon ta.

Ke har damar baccin rana ma gare ki.

Na faɗa ina nufar toilet din dakin.

Saukar ruwa kawai taji a jikin ta.

Aikam ta tashi a firgice.

Tana ganin nice ta bata rai.

Gaskiya Allah ya isa mutum yana mafarki me dadi kin wani katse masa.

Matsowa kawai nayi kusa da ita na zauna, sai kuma na dora kaina a cinyar ta.

Kuka na fara yi a hankali.

Meyafaru ? ta tambaye ni tana leka fuskata, bance mata komai naci gaba da kuka na.

Ganin har sheshshekar kuka nake hankalinta ya ƙara tashi.

Shikenan Bara na kira ammie.

Hannun ta na rike a hankali nace mata bani da lafiya leemah.

Meyake damun ki ?

Gaba nane yake ta faduwa, kuma bana iya bacci

Ni dai ina ga ranar hutu Aljani nagani.

Na faɗa ina karasa mata kuka.

Aljani kuma ?

Ai Daman ke mahaukaciya ce.

Dallah dagani.

Wlh dagaske nake miki dana kwanta zan dinga ganin idon sa, Ko bacci na fara.

Ganin dagaske nake se kuma ta nutsu.. ke babu wani Aljani fa, kawai dai kinsa hakan a ranki ne,

Yau ba sauran sati daya mu koma ba ? Kaina kawai na gyada mata.

Toh idan mun koma zamu dubasa, Ta faɗa tana tashi.

Wardrobe ta bude ta dakko min sababbin unifoam da jaka da takalmi.

Gashinam dan na ga kayanmu na ss1 sun miki kaɗan, shiyasa nace Abba ya ɗinka mana sabo.

Zan fara mata godiya ta katseni da cewa ke wlh kin dan rame, amman kin kara girma ta faɗa tana dariya.

“Mtssss dallah kyale ni”

Na faɗa ina ɗauke kai na.

Dagaske nasan nima na kara girma tunda duk yawanci kayana sun min kaɗan.

Ina mamata ?

Tana kasa wajen ammie.

Wai daman tare kuke, kika barni anan a gantale ga uwata can a kasa ??

Bata ma jira cewa ta ba, ta fita da gudu.

Mamah! Mamah!!

Bata amsa ba se tagumi data buga tana kallon ta, har ta karaso tana haki...

Mah shine baki kirani ba da kika zo, ta faɗa tana zama a jikin ta.

Ku duka baku da hankali kuta kiran mutum, kaman yana wani waje, ta faɗa tana ture ta..

Toh kiyi hakuri.

Ta faɗa tana kara matsawa.

Sai bayan la’asar su mama suka yi shirin tafiya Ni kuwa nace ba yanzu ba zan dawo daga baya.

Yawwa sashi na, Ta faɗa tana tsalle..

Muka raka su mamah bakin get muka dawo.

Sashi na kinsan me ?

Wai ke wace sashin ki ? Na tambaye ta ina tabe baki.

Ke mana, ta faɗa tana murmushi.

Nima ki canza min suna. Ta fada tana murmushi.

Zanyi tunani na faɗa ina bude fridge.

Ta matsa dole sena canza mata suna, ta hanani sakat, har seda na canza mata da suna “BEST” sannan nasamu ta kyale ni.

A haka nayi kwana uku. Naji dadin zaman zan iya cewa tunda akayi hutu banyi nishadi kaman wannam ba.

Ina komawa gida muka fara shirin koma wa makaranta, bani da matsalar komai, komai idan Abba ze mata tare ze mana.

Ya daukeni kaman yar cikin sa, haka ammie ma.

Sunfi mu kuɗi nesa ba kusa, haka zata tattaro kayanta, ta tawo gidan mu.

A takaice dai mun riga mun zama daya nida ita.

Amintar mu ya haɗa har iyayen mu.

Yau zamu koma makaranta, gaba ɗaya bana zumudin komawar, dan Allah ya gani a tsorace nake.

Ana gama assembly, direct ss2 muka nufa.

Shikenam munyi ban kwana da ss1.

*** *** *** *** *** ***



“ Mtssss ban taba jin na tsani mutum a kallon farko ba wlh se akan wannan mutumin”

Ɗagowa nayi naga wata tsana.

Ido na be faɗa ko ina ba se cikin nasa.

Da sauri na rike hannun ta ina kasa da kaina.

Bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da gungunin ta.



“Gabatar mana da kansa yayi a matsayin class master din mu, kuma ze dinga mana English.

Nidai ban ɗago ba kaina na ƙasa.

Zan naɗa monita se ku zaba mugani.

Ya faɗa yana kare mana kallo.

Sadiya Abdullahi!! Kusan rabi ajin suka haɗa baki wajen faɗa.

Ta fito gaban allo.

Tanaji amma tayi masa banza kaman bata ajin.

Seda na rike hannun ta da karfi sannan ta mike tana tsaki kasa kasa.

Gani ta faɗa gatsal babu alamar girmamawa.

Dan tsayawa yayi yana kallon ta, se kuma yace muje office.

Bata ce komai har ya fita sannan tabi bayan sa.

Bata dade ba ta dawo da dankwali a hannun ta.

Tana shigowa muka samata ihu. The MONITOR! THE MONITOR!! THE MONITOR!!!

Batayi niyar dariya ba amman seda muka sata dole.

Wlh kudena wani jin dadi, dan babu sani babu sabo yawwa.

Amman dai best ai bazaki dinga saka sunana ba ko ? Na tambaye ta ina marairaice fuska.

Mtssss toh kiyi surutu ki gani.

Gaban allo ta dawo ta tsaya nabaku free satin Nan kowa yayi abun da yaga dama babu me hanashi.

Wani sabon ihun ajin ya dauka gaba daya.

Kaman yanda ta faɗa haka muka cinye satin bata fara dutyn taba ko malami bata kira mana.

Zuwa lokacin jarin mamah yayi kasa abinci ma neman gagar mu yake, baffa kuma abubuwa sun cushe masa.

Ranar Friday da yamma sega best da kullin kayan ta.

Ke kuma lafiya kaman wadda aka koro ? Dan bamuyi da ita zata zoba.

Ke lefi nayi wa ammie.

Dariya nasaka sosai kafin na tambayeta “ gudowa kika yi kenan ?

Zama zanyi ta dake ni ? Ta tambayeni itama tana dariya.

Dakin mu muka je ta ajiye kayan ta.

Ina mamah ? ta fita.

Jakar ta bude ta kwaso mana chocolate, biscuit, dasu alawa.

Ɗaka mata duka nayi a cinya ina cewa “shegiyas da shirin ki kika tawo kenan ?

Tana dariya tace “Zauna wasa.

Se yamma mama ta dawo.

Suka gaisa Sannan muka yi zaman wasa da dariya.

Da daddare mamah ta dafa mana abinci.

Ina ganin ta zubawa kowa ita bata zuba ba.

Banyi magana.

Bansan best ta kula ko bata kula ba.

Da safe muna tashi naga tana ta aiki,

Humaira zoki yo chefane cewar mamah.

Mamah ai nadade da yowa,

Wannan wainar shinkafar zaki mana taji sugar dan Allah, Ta faɗa tana tande baki. Leemah ce ta fada tana lashe baki kamar taga wainar shinkafar a gabanta.

Shiru mama tayi kafin tace waye ya baki kuɗi ? Ta tambaye ta tana tsare ta da ido.

Da sauri ta shiga dakin mu se kuma ta fito da jakarta.

Wlh mama kin gani Abba ne yake bani duk sanda zeyi tafiya sena ke tarawa bana kashewa.

Ni gasu ma ki ajiye min..

Ta debo kuɗin zasu yi 10k ta bawa mama.

Bata karba ba, tace ki kawai ammie.

Matsowa tayi kusa da mamah ta rike ta.

Mama daman ba kallon ƴarki kike min ba bansani ba ? ta faɗa idon ta taf hawaye.

Ba haka bane sadiya.

Indai ba haka bane ki karba muyi amfani dasu toh.

Babu yanda mama ta iya dole ta karba.

A haka muka cinye weekend din mu cike da farin ciki.

“Ranar Monday muka yi shirin makaranta.

Nabata unifoam dina ta saka Ni kuma nasaka wadan can.

A bakin get muka sameshi yana duty.

Babu wadda ta gaisheshi a cikin mu.

Muka wuce.

Buzuwa! Naji an kirani daga bayana wata yar SS3 ce a tsaye a bayana tace kije inji wancan malamin, ta fada tana pointing nasa a bakin gate din makaranta.

Tsoro ne karara ya bayyana a fuskata mena masa Ni kuma ?

Kije kiji mana, ta fada tare da juyawa daman itama tana duty ne na taran ƴan late comer.

Best rakani! Na fada Idona yayi ƙwal-ƙwal.

Wa ? Ba dani ba saikin dawo. Ta fada tana yin gaba.

A hankali nake tafiya kaina a kasa.

Gani na faɗa a hankali ina dankwalin ki ? Ya jefo min tambaya kai tsaye.

Da mamaki na ɗago ina kallon sa taya yasan babu ɗan kwali a kaina..... ??

Mu hadu a page 08 gobe in Sha Allah.

Ayi min hakuri da rashin typing kwana biyu wani dalili ne mai ƙarfi ya hanani.

Nagode.....

Nice taku Rabi’atu Fulani.......

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 8

Bansan kina kallo na da wadannan idanun naki.

Ya faɗa kasa kasa yanda ni kaɗaice zanji meyace.

Da sauri nakara kallon sa da mamaki.

Kar nakara ganin ki babu dankwali wuce ki tafi.

Kaina kawai na gyada masa na juya.

Sashina mekika masa?

Wai bansa dankwali ba.

Ji munafiki taya ya gane baki da dankwali ?

Ka faɗa kawai na daga mata, alamun oho waya sani.

Ina son faɗa mata shine wanda nake yawan tunani, ina jin tsoron yanda zata dauki zancen, dan dagaske take ta tsanesa kuma ni harga Allah banga meya mata ba.

Koda ya shigo aji nakasa nutsuwa bare na fahimci meyake koya mana.

Harya gama ya fita daga ajin.

Ajiyar zuciya kawai na sauke na dora kaina akan desk.

Kusan kullum se mun haɗu da shi amman magana bata kara hada mu dashi ba.

Wadan da zasu yi sport a kazo ɗiba ajin mu.. ganin best ta shiga nima sena shiga.

Duk ranar Friday za’a dinga yin wasanni kafin a tashi.

Bamusan waye ya kawo tsarin ba, amman mudai mun ji dadi.

Duk harkar tsalle;tsalle best na sonta dan haka tafini zumudi.

Ranar Alhamis da yamma sai gata tazo gidan mu da kayan ball.

Baki da fari, Sashi na! Taso kiga, Kinga wadan nan kayan zasu yi mana kyau, Tunda dai duk farare ne mu.

Tagumi nayi ina kallon ta. Yanzu kawai saimu hau saka kayan Nan a makaranta. ?

Idan bazaki saba, nizan saka abuna, Tunda nadawo na addabi Abba seda ya siya mana, koda yake ke daman ba’a abun arziki dake.

Shikenan huce haka zan saka.

Yawwa yanzu taso muke kasuwa siyo hijab da hula.

Waike baki da hankali ? Ba wani hijab da zamu siya na makarantar ai ya ishe mu.

Wallahi semun siyo ta faɗa tana karkada kafa.

Ganin rigima takeji kawai nace mata mutafi.

Mamah mun tafi kasuwa ta faɗa ko tanajan hannu na.

To Allah ya tsare.

Wallahi sashina da har ball zan cewa Abba ya siya mana, cewar sadiya wacce har yanzu Hannuna yana cikin nata.

Ai Daman hankali be isheki ba har yanzu.

Ke ai bazaki gane bane Bakisan yanda nake sonta bane.

Muna tafiya muna hira.

A hankali naji zuciya ta, ta sauya bugunta, a jiki na naji kaman yana kusa dani, dan dube; dube na fara a hankali, ban gansa ba.

Ina juyo wa muka yi ido hudu da shi a gaba na.

Kallo na yake tun daga sama har kasa.

Ganin kallon daya kemin nima sena kalli jiki na.

Doguwar riga ce a jiki na, se mayafi da nayi rolling, kaina babu dankwali, fuskata babu komai.

Tsakin danaji ne yasa na juyo ina kallon ta.

“Maye ya cikan sa da kansa.... ta faɗa tana hararar gefe.

Ni wlh dariya tabani ma.

Waye kuma maye ? na tambaye ta ina murmushi.

Wannan bakin malamin ne yake kallon ki da idanun sa kaman na Mayu.

Da sauri na hadiye murmushi na ganin sa kusa damu, kuma na tabbatar yaji abunda tace.

Beyi magana ba yayi wucewar sa kaman be sanmu.

Gaskiya bakida mutunci, yaji abunda kika cefa na faɗa kaman zanyi kuka, Dan Wallahi dagaske banji dadin abinda tayi ba.

Mtssss toni ina ruwa na.

Haka muka je muka siyo hijab din da hula, Duk raina a bace.

Da muka dawo gida ma ko kallan ta banyi ba, har ta yiwa mama sallama se kuma ta dawo.

Amman dai nasan ba kanin uban mu na zaga ba ko ? Kike wani ci min magani.

Bance mata komai ba har ta gaji da masifar ta tafi.

Ni Wallahi yanzu kunyar sa ma nake ji, ita bata da hankali, bansan sanda zata canza hali ba, idan bata sonka ako ina seta nuna, idan tana sonka ma haka.

**** **** **** ****

Washe gari Friday karfe 9 aka fara shirin wasa,

Kaya muka canza..

Buzuwa dan Allah wannan gashin kine ? Inji wata a baya na.

A’a gashin doki ne ta bata amsa tana harar ta.

Waike aka tambaya ne, na faɗa ina harar ta.

Bana kitso ko kaɗan ko yaushe kai na a tsefe yake, kuma bana kaunar dankwali.

Dan haka ko yanzu dan babu hijab kawai nasaka a kaina.

Best kinyi kyau wlh, na faɗa ina murmushi kayan sun haskata sosai.

An faɗa miki nidin ta wasa ce ? itama tana ta faɗa tana dariya, Se kuma ta dena dariyar tana kallona tace Wallahi kinyi bala’in kyau sashi na. Komai ya fito, Ni dai gashin gaban kanki zaki sammin da sajen ki.

Mtssss ke baki da hankali wani lokacin, na faɗa ina jan hannunta.

A hankali muka fito daga aji muna tafiya, hannun mu cikin na juna.

Filin wasa muka nufa kai tsaye.

Seda muka je nayi danasanin zuwa Malaman mu maza duk suna wajen, a hankali na kalli kai na.

Oh oh best kalli da duk Malamai maza a wajen nidai na koma class na faɗa ina juyawa.

Wallahi babu inda zaki se munyi.

Ba yanda na iya haka na tsaya duk nakasa sakewa.

Jinai a jiki na ana kallo na, ban juya ba duk da ina jin idanun sa a kaina, kasa jurewa nayi bansan sanda na juya ta barin da nake jin yana wajen ba.

Wani irin kallo yake min da seda gaba na faɗi.

Idan har ido na daidai yake nunamin kaman gargadi yake min da idon sa.

Toh amman mena masa ?

Nima bansaniba.

A haka aka rarraba mu, nida best hand ball muka zaba.

Tun muna wasa ina jina a takure, han na ware, muke wasan mu cikin nishadi.

Muna gudu bansan ya akai ba wata ta jamin hijabi, kawai seji nayi hibijin da ribon din sun fita a jiki na.

Da sauri na dur kushe a kasa.

Jiki na rawa kawai ya fara jin idanun jama’a a kaina.

Best! Na faɗa murya ta na rawa.

Tana can hankalin ta baya kaina.

Ganin ana kallon waje daya ana kus kus yasa itama ta juyo taga me ake yi.

Yanda ta hangoni ne yasa kawai ta fara gudu ta kara so waje na.

Sashi na ta faɗa tana rufeni da jikinta rungume ta kawai nayi ina hawaye.

“Hijabi na” na faɗa a hankali.

Da sauri ta dakko ta saka min, se kuma muka mike muka nufi ajin kusa damu. Zauna bara na kawo miki ruwa kisha.

Ta juya da sauri ta fita.

Kifa kaina kawai nayi ina kuka Nida kaina bansan ne kewa kuka ba.

Amman naji haushin yanda malaman mu suka zubamin ido kaman Mayu.



“ Kukan me kike ?

Da sauri na ɗago jin Muryar sa daf dani, Yana tsaye hannun sa cikin aljihun wandon sa.

Babu komai na faɗa ina kasa da kaina.

6 / 40