ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 40

18K to 21K   out of 117.2K words

A hankali na ɗago jin be tafi ba, kuma se kallo na yake.

Meyasa kike biya waccan mara kunyar ?

Ɗagowa nayi ina kallon sa.

Nace kidena kallo na ko!!! Ya faɗa yana buɗe min idanun sa gaba ɗaya.

Kai bance kadena kallo na sai ni zaka faɗawa haka.

Na faɗa kasa kasa ina turo baki.

Banace kar na kara ganin ki babu dan kwali ba ??

Nidai na shiga uku kodan jarida ne wannan mutumin ?

Kar na kara ganin ki da wannan hijabin.

Yana faɗa ya juya yayi tafiyar sa.

Ko minti biyu da fita beba itama ta shigo.

Tsayawa tayi tana karewa ajin kallo.

Gaba nane ya fara faduwa waye yazo Nan ? Mekika gani ? Na maida mata da tambaya nima.

Babu komai tashi mutafi ga ruwan.

Nifa kunyar fita nake kowa ya gama kallo na! Na fada kaman zan kara saka kuka.

Mtssss dallah ni ki taso”

Ban sake mata musu ba na tashi muka fita.

Kaman yanda muka saba muna tafiya muna rike da juna.

Wai shi mutumin nan baya gajiya da kallo ne ?

Na tambayi kaina ina juyawa inda yake.

Muna haɗa ido nayi saurin janye Idona muka cigaba da tafiya.

***** ***** ******

A haka lokaci yayi ta gudu gashi har mun cinye first term din mu za’ayi hutu.

Zuwa lokacin nida kaina nasan na kamu da muguwar soyayyar uncle dinmu.

Kuma na kasa faɗawa best saboda kiyayyar da take masa.

Bansan ko shima yana sona ba, amman Abu kaɗan zanyi ya hauni da faɗa.

Kije inji uncle Usman buzuwa. Inji head girl ɗin makarantarmu.

“Ni kuma ?”

Eh. Ta bani amsa tare da juyawa.

Ban kawo komai a raina ba natafi.

Banma kula da shi a staff room din ba har na karasa wajen uncle Usman.

Gani uncle, na faɗa ina tsugunnawa.

Buzuwa magana zamuyi dan Allah, Toh uncle Allah yasa lafiya.

Ina fatan zaki fahimce ni ?

Shiru nayi ina jinsa, ban ce komai ba.

Seda ya gama zagaye zagayensa Sannan yace shifa sona yake.

Shiru nayi nama kasa magana.

Jin nayi yasa yace “zan jiraki idan kun dawo hutu ki fadamin amsa dan Allah”.

Toh kawai nace masa dan Allah Allah nake nabar wajen.



Ina fitowa naji an finciko hannuna.

Zan fara bala’i naga shine, kokarin kwace hannu na nake amman nakasa karfin ba daya ba.

Muna zuwa bayan area classess ya saki hannuna.

Ke bakya ganewa ko kuma bakya fahimta ya faɗa yana daga murya baya naja jiki na na rawa.

Babu kowa a wajen se mu biyu gashi yana magana yana matsowa kusa dani.

Kullum se kin bata min rai a cikin makarantar nan ?

Watakam yace yana sonki kin fito kina jin dadi ko ?

Uncle......!!

Kimin shiru ya katseni cikin tsawa.

Kuka kawai na fashe da shi banga me zanyi ba idan ba kukan ba..

**INA SONKI”*

Chak komai ya tsaya min jin wannan kalma daga bakin da banyi zato baa........................!!!!

Mu haɗu a page 09 a gobe in Sha Allah.

Taku har kullum Rabi’atu Fulani.

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 9

Suman tsaye kawai nayi! Har lokacin jiki na be dena rawa ba.

Ina sonkiii ya kara maimaita wa.

Baya kawai nafara yi a hankali, yana matsowa na kwasa a guje nabar wajen.

Best na hango tana nemana, ina zuwa na faɗa jikin ta ina sakin kukan da nake rikewa.

Meyafaru dukan ki yayi.

Na kasa Magana se kara shigewa jikin ta danayi.

Ko ban juya ba nasan yana bayan mu.

Farin ciki ya kamata nayi kodan soyayyar da nake masa amman bansan meyasa nake jin tsoro ya rufe niba.

Waike lafiyar ki, Malama kina daga min hankali ki fadamin idan wani ɗan iska ne ya tabamin ke, inje inci uw***ar mutum.

A hankali na sake ta na nufi ajin mu cikin sassarfa dan bazan juri ci gaba da zamanmu a waje daya ba.

Har muka je gida bance mata kala ba.

Da daddare na yankewa kai na hukunci.

Tabbas ina matukar son ka uncle amman soyayyarmu bazata taɓa yiwuwa ba saboda best bata sonka.

Zuciya ta bakiyi min adalci ba, meyasa kike son abinda bata so ?

Har cikin raina naji na sadaukar da soyayya ta saboda farin cikin ta.

Gaba ki daya na koma silent, magana ma wahala take min.

A haka muka cinye hutun mu muka koma makaranta.

A bakin get muka sameshi a tsaye hannayen sa cikin aljihu.

Zo nan ya faɗa yana kallan mu, Ko kallan sa banba na wuce.

Koda naje class ina zuwa na duba time table naga muna da shi, Ban zauna ba na fita, na tafi wani ajin na ɓoye.

Gabaki daya na toshe duk wata hanya daze ganni, ko magana ta hada mu.

Nasan bayasan ina sport.

Dan haka yanzu nakeyi koda best tace baza tayi ba sena takura mata munje.

Ada idan nasaka hijab ina janyo sa ya rufe gashi na, amman yanzu da kaina nake baya da shi ya fito sosai.

Gaba ki daya na sauya dabi’u na a makarantar.

Best tayi tambayar dalili har ta gaji ta zubamin ido.

*** *** *** *** *** ***

“ Sauri nake tayi gaba ki daya hankali na, ba’a kan hanya yake ba.

Jin yanda aka finciki hannu na, koban duba ba nasan shine.

Meyasa kike son azabtar da zuciyoyin mu ? Ya tambaye ni.

Fuskarsa cike da ɓacin rai.

Zuciyoyin mu kuma ? Na maida masa tambayar sa.

Akan me zaki dena zaman aji ?

Ina zama faa!!

Kan sa ya dafe kawai.

Sau nawa zance miki kina saka dankwali ?

Uncle bani kadaice me zuwa ba dankwali ba fa...!?

Ya isheki haka ya faɗa da karfi.

Baya naja ina gunaguni.

Saboda ina sonki bashi ze baki damar wulakanta niba.

Nasan kina so na meyasa kike haka ?

Ni ban taba sonk..... Kasa karasawa nayi ganin kallon da yake min.

Seda na runtse idona Sannan nace ba... ba... na so...sonka....!!!!!

Na faɗa ina in ina.

Karya kike!!! Tun ranar da kika fara ganina kika fara sonaa!

Kaman yanda tun ranar da idona ya shiga cikin naki na fara sonki.

Kuka kawai nasaka masa,

Bana sonka ka kyale ni.

Na faɗa cikin ɗaga murya Nima da son gaskanta karyar zuciyata. Wacce Nasan cewa karya nake idan nace bana sonsa.

Ganin yana matsowa kusa dani na juya zan gudu.

Hannu na ya rike gam.

Zan rabu dake! Da sauri na ɗago ina kallon sa.

Eh zan rabu dake ki kalli ido na ki fadamin ba kya sona!!!

Seda na tattaro jarumta ta gaba daya Sannan na kallesa.

Baze yiwu muyi soyayya da kai ba, Na faɗa a hankali.

Meyasa ? Ya tambayeni hankali tashe...

Kaje kanemi soyayya ta a wajen best, Idan har ta amince ni kuma namaka alƙawarin zan soka.

Ina gama faɗar haka na kwace hannu na na tafi.

Shiru yayi yana kallon bayana. Yana tunanin Ta yaya ze nemi yarinyar Nan, yarinyar dayake ganin kiyayyar sa a idon ta batare da yasan meya Mata ba, taya ya zeje mata da Wannan maganar yayi tunanin zata saurare sa.

Amman ya iya bashi da wani zabin dan dagaske yana son yarinyar.

***** ***** ***** *****

Bayan kwana biyu da maganar ya shigo ajin mu ban fita ba kaman yanda na saba kwana biyu, Shima beyi tunanin zezo ya same niba daga ganin yanda ya kafeni da ido.

Bayan ya gama mana karatu, Yace

Sadiya Abdullahi, biyo ni office yanzu.

Bata ce komai ba tabi bayan sa.



Shiru yayi dan ya rasa ta ina ze fara.

Chan dai ya dake yace magana zamuyi dan Allah,

Toh ina jinka.

Inason ki fahimceni kuma karki kalleni da wata manufa kin san komai kaga ya faru ga bawa muƙaddari ne bawa bai isa ya zaɓawa kansa ƙaddara ba, ina neman alfarmarki ta neman yardarki na shiga rayuwar ƴar uwarki, domin ina sonta.... INASON ƘAWARKI BUZUWA.....!!!

Da mamaki take kallan sa tunda ya fara magana, baki buɗe.

Dagaske ina sonta dan Allah ki tayani neman soyayyar ta. Ya faɗa yana hada hannayen sa.

Shiru tayi dan ta rasa abinda zata ce, mutumin data najin yanda yan ss3 suke son sa shine zece yana son sashin ta.

Koda yake ba abin mamaki bane, ba kowane namiji ne ze iya dauke kansa akan taba, ta ko ina ta cancanci a sota.

Murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba.

Kanemi soyayyar ta idan har ta amince ni bani da matsala.

Ke nake so ki tema kamin ai ya katse ta da sauri.

Shikenan zanyi Magana da ita insha Allah, Yanda muka yi zaka jini.

Yawwa ngd sosai.

Bayan ta fito daga wajen uncle ta tsaya a waje, wasu abubuwan suka dinga faɗo mata waƴanda nake yi idan naga uncle da kuma yanda nake nuna ɓacin rai idan ta zageshi, Murmushi kawai tayi domin ta fuskanci duk yanda akayi na fuskanci yana sona ko kuwa ma ya taɓa fada min Nima kuma na fada soyayyarsa ga dukkan alamun da ta gani..... Amma kuma meyesa ta kwana biyu kuma taga na canja na daina tsoronsa ?? Bata da amsar wannan tambayar saboda haka kawai ta nufi aji tana cewa a ranta koma mene zata gano.

Seda neman duniya bata ganni ba.

Har aka tashi ban bari mun haɗu da ita ba saboda nasan duk yanda akayi yayi mata maganar soyayyata da yake nema.

Koda tazo gida naso guduwa amman narasa hanya, dole na zauna bani da yanda zanyi.

Meyasa kika aikata min haka sashi na ? Meyasa ? Ta faɗa kaman zatayi kuka.

Mena miki ?

Kunyi magana da uncle ko bakuyi ba ?

Nace “bamuyi ba” ina kauda kaina gefe.

Ƙarya kike yayi miki maganar soyayya. Shiyasa kwana biyu kika fara canjawa gaba daya kin rasa nutsuwarki domin kema kina sonsa! Sai yanzu ma Ni hankalina ya dawo jikina na fahimta, yaushe kika fara ɓoye min damuwarki sashina ? Ban kai ki fada min damuwarki bane ??

Bana sonsa! Dan bazan taba iya son abinda bakya so ba best.

Ni ce miki nayi bana sonsa ? Nifa ba sonsa ne banayi ba, kawai haushi yake bani, ba dan komai ba sai dan bana son namiji mai yawan gwalli, kuma idan ma bana sonsa kema sai ki ƙi shi ki cuci kanki ?

Best bazan iya son abinda baki so ba ne gaskiya.

Toh nidai na karɓeshi kema kuma dole ki karɓeshi.

Kallan ta nake sosai, da son gano yanayinta ko gaskiyar abinda take fada,Sedai ban fahimci komai a fuskar taba.

Zanyi tunani akai, ya ammie na ?

Na faɗa Ina canza mana wata hirar.

** *** **** ***** ******

Washe gari muna tafiya tace tsakaya kigani sashi na, A bakin get zamu haɗu da uncle Ibrahim.

Nidai ban tan kamata ba. Kaman yanda tace kuwa tunda ga nesa muka hango sa.

Koda muka je ban tsaya ba Da ya tsayar damu itace ta tsaya.

“ Ya kukayi da ita ? Ya tambaye ta cikin zakuwa.

Ta amince!!

Farin ciki ne ya bayyana sosai a fuskar sa.

Sedai ina neman alfarma ɗaya a wajen ka.

Faɗi ko menene insha Allah zan miki.



“Bata taɓa soyayya ba..bata kula maza tana da matukar rauni dan Allah karka cutar da ita...”

Nayi miki alkawari in Sha Allah!!

“Ngd” ta faɗa tana juyawa.

Tun daga wannan ranar muka fara soyayya da shi. Idan nace soyayya ina nufin soyayya.

Faɗin yanda nake sonsa ma bata baki ne, Ina kishin sa, Kishin da zan iya cewa ko kaina bana yiwa shi.

Zan iya sadaukar masa da komai nawa Idan nace komai ina nufin komai.

Ciki harda farin ciki na, Idan har shi zeyi farin ciki shine buri na.

***** ***** ***** *****



“Yau gashi muna shirin gama secondry school.

Zuwa lokacin nazama cikakkiyar budurwa.

Ina da tsayi sosai, bani da wata kiba. Sedai masha Allah ina da hips daidai jiki na bani da manyan breast, Zan iya cewa komai daidai yake da tsayin da Allah ya bani.

Kyau na ya kara fitowa, Ina da tsayin fuska, Idanu wana manya ne bawai sosai ba.

Ƙwayar ido na brown ce, Shiyasa wani lokacin suke cemin me idon mage!

Babu abinda zance wa Allah se godiya a bisa halittar da yayi min.



“Zuwa lokacin faɗar soyayyar da muke da khaleel ma bata baki ne.

Yana sona sosai sedai har lokacin be taba zuwa gidan mu ba yace se munyi candy.

Amman duk gidan mu babu wanda besan labarin saba.

Mun zana jarabawa lafiya se jiran sakamako.

Ranar candy mu.. zan iya kiran ta da bakar rana domin daga ranar ne babin kaddarata ya fara, Daga ranar ne natashi daga sumayya Abubakar mai nasara,

Nadawo wata sabuwar sumayyar.

Daga ranar ne na tashi daga rainon mama, Na koma rainon khaleel.

BAƘAR RANAR DA BAZAN TAƁA MANTAWA BA.......!!!!

RANAR CANDYNAAA........

Kash mu a page 10 domin jin yanda zata kaya.

Yanzu ma za’a fara....

Taku har kullum Rabi’atu Fulani.

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 1O

Sauri muke tayi muje gidan mu dan daga nan gidan ammie zamu wuce.

A can zamuyi celebration na gama makaranta.

Muna zuwa muka tarar da sabon abun farin ciki, daddy ya siya mana waya nida best.

Tata blue Black.

Tawa baby pink.

Kowa favorite colour dinsa ya bashi

Fadin farin ciki da muka yi ma bata baki ne.

Muna zama na fara saka number sa, Dan buri na nayi masa albishir.

Hello kauna.

Ammatana!

Albishirin ka na faɗa cike da zumudi.

Goro fari tasssss.

Daddy ya siya mana waya nida best.

Congratulations! Amman banji dadi ba ya riga ni, ni naso nabaki kyauta.

Amman bakomai ina nan ina shirya miki gift.

Anjima zan miki waya kizo ki karba.

Wowww pls fadamin mana shalelenah, Na fada da shagwaba.

A’a only idan kin zo zaki gani!

Shikenan zamu zo da best!

A’a ke kadai zaki zo.

Shiru nayi ina tunani.

Abu ne fa na masoya haba ammatana.

Amman shikenam tunda baki yarda dani ba.

Ba haka bane Shikenan seka kirani.

Yawwa sweetheart!

I love You.

Bayan mun gama wayan shiru nayi ina tunani anya ya kamata naje wajensa ba tare da best ta sani ba ?

Bansan ɓacin ransa babu yanda na iya dole naje.

Karfe 5 na shirya nace mata zani nadawo yanzu.

Ina zaki ? Yanzu zan dawo fa, na faɗa cikin rashin gaskiya, Toh bara na shirya mutafi. Nasan dama sai ta fadi haka. Ban nuna komai ba nace:

“Toh kiyi sauri.

Wanka ta shiga na fita da sauri ina cewa kiyi hakuri best.



****

7 / 40