ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 40

60K to 63K   out of 117.2K words

Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!

Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.

Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......

Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??

Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??

Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??

Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?

Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??

Shin waye haidar ??

Shin wace Ma’eesha ??

Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion

🦁

)

Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.

Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.

Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.

Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.

Goyon bayanku muke bukata.

Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.

Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......

Nagode

🥰

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 24

Tunda na shiga daki ban fito ba sai washe gari duk da wata yunwa da take dukana haka na daure na zauna a daki, dan sauran chin chin din da nayi ne kawai nake ci shima kuma ya kare!.

Zuwa karfe Goma na safe naga na daina ganewa, yunwa tana neman yi min illa, ba shiri na fito daga ɗakin na nufi kitchen, saidai dole naja nayi turus saboda abinda na gani!

Kitchen din ne aka sakawa mukulli aka kulle! Ji nayi kamar na dora hannu aka na fashe da kuka saboda takaici ga kuma wata azababbiyar yunwa da ta ke cina.

Tunawa nayi da cewar ina ganin wasu spare keys a dakinsa a cikin drawer saboda haka na nufi dakin nasa idona rufe, saidai shima nan naja nayi turus saboda dakin a rufe yake.

Dakina na koma na debo mukullin dakina na dinga gwadawa har Saida ya bude.

Shiga nayi na dinga bincike dakin domin basa drowar tasa, Saida na sha wahalar duba na gansu a aljihun wandonsa, wani wando da kullum yana sakale a jikin kusa!

Da sauri na fito nazo na bude kitchen din na girka taliya guda biyu na juye a katon food flask na gyara kitchen din na maida komai mazauninsa sannan na kulle kitchen din na maida mukullin dakinsa na kulle na dawo dakina shima na kulle kaina a ciki, hannu baka hannu kwarya na zauna ina cin abincinnan Saida na kusa cin rabi sannan na ajiye a wajen na zube na dinga bacci sai bayan ƙarfe biyu warin wiwi ya sake tayar dani.

Ina tashi wata yunwar ban kakkauta ba haka ba kuma jawo abincina na ƙara duka!!! Sallah na tashi nayi sannan na sake dawowa na kwanta sai wani baccin.

Haka awanni da kwanaki suka dinga shuɗewa, rayuwa ta dinga turawa, rayuwa tana canjawa ta kowanne fanni amma Banda ni, kullum ina kunshe a daki indai Khalil yana gida, ko baya gidan ma bana sakewa saboda anytime zai iya dawowa, na koma girki da dare, saboda kullum wajen sha biyu zuwa daya na dare yake fita, baya dawowa Sai bayan asuba wani lokacin ma sai shida na safe.

Ni kuma wannan lokacin da yake fita shine lokacin girkina, zan girka abinci mai yawa wanda zai isheni a wunin ranar, sannan zan dibi ruwa mai yawa na shiga dashi dakina, wanka kuwa dama a dakina nake yi saboda inada toilet saboda haka banada matsalar buƙatar banɗaki! Ta inda Allah ya taimakeni wannan cikin nawa ba me laulayi bane wanda zai dinga sakani ciye ciye da shaye shayen abubuwa, kawai dai nasan inada cin abinci harda na hauka sai bacci kuma da nake samu shima idan na kwanta yunwa ce kawai take tashina.

Hutun da na samu ne yasa na kara haske da kiba sannan wannan cikin ya saka na ƙara cika, ba abinda ke damuna sai kewar gida.

Nayi binciken wayata a dakin ya Khalil har na gaji da nema, na kasa samunta, ba yanda na iya haka na hakura, kullum haka zan zauna gurum kamar wata kurma, saidai idan kewar mama ta cikani da best sai nayita kuka, baccine yake lallashina, dan dole idan bacci ya daukeni nayi shiru.



********* ********* *********

Yau cikina yake cika wata na uku, hankalina ya fara tashi yanzu.

Kayan abincin da suke kitchen sun dauko hanyar karewa, gaba ɗaya hankalina ya fara tashi saboda tunanina yanzu ya juya kan abinci, sannan yanzu ya Khalil tun ranar da muka dawo daga asibiti bamu sake haduwa ba, saidai rannan na hangeshi a wajen da suke shaye shaye shida abokinsa!

Ban san ta ya zan tunkareshi da maganar abinci ba tunda bai ma san ina dibar na kitchen ba.

Yanzu bayan damuwar gida da kewarsa sai damuwar tunanin karewar abinci kuma, ya Khalil bazan ce ban damu dashi ba saidai inason nuna masa na tsaya akan maganata kuma Sannan inason na haifi cikina ko ma ta halin ya ya ne, shiyasa na daukeshi na jefashi a baya saboda kar naje damuwarsa ta kara min wata damuwar.

Yau gaba daya babu ruwa a famfon banɗaki, gashi inason yin wanka, ga bukata ta banɗaki amma ba ruwa, kuma gashi bana son fita waje domin gujewa haduwa da ya Khalil.

Haka na daure da bukatar banɗakin ta kamani sosai na daure na fita samun ruwa a rijiyar gidan.

Da kyar na iya jawo ruwa a rijiyar gidan saboda dan banzan zurfi, na kai minti talatin kafin na cika bokitin, tunani na fara yi ta yanda zan daukeshi na kai dakina.

Idea din jan sa zuwa dakina ce tazo min dan gaskiya bazan iya daga bokitin ba ko a da bare yanzu da nayi nauyi, saboda haka na dage ba takarkare na fara jan ruwan zuwa dakina, Saida naje zan shiga part dinmu daga tsakar gidan sannan na lura da mutum a tsaye a bakin kofa yana kallona!!!!!

Ji nayi gabana yayi wani mummunan faɗuwa, kauda kaina nayi na cigaba da jan ruwan da tunanin idan naje shiga dole ya matsa min.

Saidai ko gezau, kamar ma ba tunkararsa nake ba.

“Zan wuce” abinda kawai nace kenan.

Bai amsani ba dai ya tsaya yana kallona, da wani irin expression a fuskarsa, ƙyale ruwan nayi na raɓa ta kusa dashi zan wuce.

Jawoni yayi jikinsa, “ke baki jin magana ko ?

“Ni me nayi ? Na fada ina tsuke fuska.

“Bazaki zubar da cikinnan ba kike so kice ko me ne ?

“Bazan zubar ba!

Murmushi yayi sannan ya sakeni yace “Ni dake mu zuba mu gani, wallahi bazaki taba jin daɗina ba idan baki zubar da cikinnan ba.

Yana fadar haka ya juya ya koma cikin falo, ban ce masa komai ba na cigaba da jan ruwana zuwa cikin falon, daga nan kuma na jashi zuwa part dina.

Saida naje tsakiyar falon sannan na lura da mutum biyu ne a dakin ashe....!!!!!!

********* ********** **********

Mama ce ta farka a firgice saboda mummunan mafarkin da tayi da humairah, tana farkawa ta fashe da kuka, kukanta ne ta tashi bappa da yake baccinsa.

“Maman yara me ya faru ?

Bappa sumayyata na gani a wani yanayi da take buƙatar taimakonmu, dan Allah bappa ka yafe mata sannan muje Lagos mu dubata.

Kallonta bappa yayi “kin ɗauki Lagos cikin gidanki ne da zaki ce aje neman mutum can batare da address ba ? Lagos ko Kanada address din mutum ma zuwanta aiki ne ga namiji bare kuma g mace, saboda haka ki daina zancen zuwa Lagos, ƴarki yanda ta tafi haka zata dawo, tana sane da cewar muna raye kuma munada hakki akanta amma tayi mana wannan diban albarkar ta bamu ladan haihuwarta da mukayi, bazan yi mata baki ko na tsine mata ba, amma dai ganin da kyau da wuya sumayya tayi shi, indai ba wai Allah ne yayi shirin yi mata talala ba.

Kara rushewa da kuka mama tayi ta sauko daga kan gado tana rokan bappa akan ya yafe min.

“Maman yara! Inada tabbacin bazaki fini son yaranmu ba, amma da bukatar duniya ta koyawa sumayya darasi ta yanda bazata taba mantawa ba, mu bazamu iya koya mata ba, tunda munyi ƙoƙarin hakan amma bai yiwu ba, saboda haka mu bari duniya ta koya mata, Yana fadar haka ya juya ya cigaba da baccinsa.

Kuka mama ta zauna ta cigaba da yi, sai Wajen uku na dare sannan ta tashi ta shiga sallah, sai asuba sannan ta hakura tayi sallar asuba ta zauna lazumi, karfe shida ta ta tashi humairah sallah tayi sannan ta aiketa wajen malam Hamza mai almajirai, abun sadaka ta sake bata ta kai masa sannan ta rokeshi akan a sake dagewa da addu’a dan Allah, sannan idan ta dawo ta biya ta sanar da best idan ta samu lokaci tana nemanta!



Wajen uku na rana Sannan humairah ta dawo tare da best, har mama zata yi fada akan dadewar humairah sai best ta bata hakuri, Cewar itace ta riketa tace saidai su taho tare.

Daki suka shiga mama ta zauna ta labartawa best yanda sukayi da bappa sannan take tambayarta ko a danginta ba wanda ta sani wanda yake Lagos ?

“Wallahi mama babu, saidai zamuyi maganar da ya haneep nasan bazai rasa sanin wa’yanda suka san Lagos ba!

“To dan Allah kiyi masa maganar, hankalina bazai taba kwanciya ba idan sumayya bata dawo ba! Sai kuma ta fara sharar hawaye.

“In Sha Allah mama”

Sun tattauna sosai akaina sannan best tayiwa mama sallama akan in sha Allah duk yanda ake ciki zata yi mata magana, kuma itama ta bangarenta zata saka a dage da addu’a.

Sai a lokacin mama ta ɗan kwantar da hankalinta.

********** ********* **********

Mace ce a kwance ta ɗora kanta a jikin ya Khalil shi kuma yana shafa kanta sannan suna kallo a TV.

Kishi, bakin ciki, takaici, ɓacin rai, duk ban san ta inda suka bijiro min ba, ban kara tabbatarwa da cewar ina son ya Khalil ba sai yanzu da naga wannan abun, banyi wata wata ba, kuma ban san a ina na samu karfinnan ba sai gani nayi kawai na daga botikin ruwan da na debo na juye musu aka gaba dayansu.

Weather ce ta sanyi saboda haka ruwan yazo musu unexpected, cikin razani da firgici Dukansu suka mike tsaye.

Kashhhh a gafarceni da yin page dinnan short shima, hakan ya samo asali ne da abubuwan da suka sha min kai, mu hadu a page 25 domin jin me zai faru a gaba.

Taku har kullum Rabi’atu Fulani

Talla!

💫

Talla!!

💫

Talla!!!

💫

💫

ALIYU HAIDAR ( THE LION

🦁

)

💫

Paid Book...

By

Rabi’atu Fulani....

&

Ubeera.....

Happy New Year Update......

A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.

Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.

Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.

Seda ya sauke ajiyar zuciya.

Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!

Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.

Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.

Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!

Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.

Chan dai ya kira sunan ta:

“Only!

“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.

“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?

Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.

Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.

“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!

Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.

Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.

Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.

“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”

“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.

Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.

Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.

Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.

Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.

******** ******* *******

Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:

“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.

Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.

Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.

This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!

Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.

“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.

Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.

“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!

Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.

Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......

Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??

Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??

Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??

Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?

Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??

Shin

21 / 40