Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
baya samun fuska.
Musamman da ajin mu ya kasance akwai maza, sosai na kara kame kaina.
Dan Allah yana gani na tsani duk wani namiji a rayuwa ta, dan gani nake duk halin su daya babu wani banbanci.
Sosai nake karatu na, dan hadda ma nake, koyaushe da Kur’ani a hannuna ko kuma chasbaha.
Ba wani sakewa nake a gidan muba dan haka bansan meyake faruwa ba.
Shiri naga mama tanayi, kayan snacks da sauran abubuwa, baffan mu be fita kasuwa ba, kuma naga yan uwan sa wasu ma sunzo.
Sedai nakasa tambayar meyake faruwa.
Wajen karfe uku na yamma sega best.
Da ihu ta shigo gidan kaman mahaukaciya Allah yasa little bata hannun ta.
Amarya! Amarya!! Kina ina ?
Da mamaki na fito ina kallon ta, yau kuma haukan nata tanan ya biyo kenan ? Ko wace amarya kuma oho mata.
Mama ta rike tana rawa, har lokacin ina tsaye a gefe ina kallon su, murmushi kawai nakeyi, hannuna ta janyo amman nakasa biye mata muyi kaman yanda muka saba.
Wai mama ina Amaryar ne ? batanan.
Se lokacin nayi magana waike wacece amarya ?
Mtssss ke baki da hankali matsala ta dake kaman ya wacece amarya kuma sashi na.
Wallahi bansaniba dagaske fa.
Bakisan yau aka saka ranar auren humairah da yaya haleepha ???
Gaba daya nama kasa magana, narasa tacewa.
Wanne ya haleepha ? na tambayeta gaba ɗaya idona a waje.
Mtssss!!!
Mamah amman shine baki fadamin ba, nayi Maganar kaman zan samata kuka.
Toh kin maida kanki matar kulle ya kike so na miki, kullum kina ɗaki, magana wannan bazaki ba, ya kike ayi dake toh ?
Amman mama base ki fadamin ba.
Dallah nizo muje mu tattauna.
Hannuna taja muka shige daki muka zauna.
Wai yaushe zaki dawo rayuwar ki kaman da ne sashina ?
Babu rana best! Na fada kamar nayi kuka.
Dafani tayi “Meyasa ?
Saboda ni kaɗai nasan ya nake ji a cikin zuciya ta.
Tunaninsa kike yi ne ?
Meze saka nayi tunanin sa best ?
Kawai dai zuciya ko yaushe tana min zafi akan abubuwan dana aikata.
Ki godewa Allah sashi na, kin tuba batare da lokaci ya ƙure miki ba, sannan iyayen ki sun yafe miki, kuma kince min doctor ya kaiki gidan baba Abbas, toh kinga zuwa yanzu ya kamata ace kin manta da komai da komai.
Yanzu ya kamata ki tsaya ki fuskanci gaba, Nidai gaskiya ina son sumayya ta dawo! Ina son ganin buzuwa a tare dake sashi na, amman gaskiya bana son wannan sumayyar.
Yanzu burina, kema kiyi auren ki, ki......
Aure ????? na katse ta da sauri kamar wacce ta kirawo min mutuwa.
Nida shi ai munyi hannun riga, yayi gabas nayi yamma, na fada ina kau da kai.
Baki da hankali amman ko ? Ta tambaya tana hararata.
Yanzu nidai fadamin yaushe yaya haleepha ya fara soyayya da humaira ? duk matan duniya se wannan yar yarinyar ze aura ? Na fada ina tabe baki.
Dallah to kina bakin ciki ne ?
Ganin yanda take hararata tana kumbura fuska ne yasani dariya.
Natuba kanwar ango yayar amarya.
Yawwa me dame zamuyi da biki, wata uku kacal fa a kasa ka.
Babu abinda zanyi nidai Allah ya sanya Alkhairi kawai na fada da murmushi a fuskata.
Hmmm!!!! Kawai tace min.
Ya makarantar ? Ta fada tare da kau da maganar.
Alhamdullah karatun na mini daɗi sosai.
Hira muka ci gaba da yi, duk da rabin hiran akan bikin ne.
“Zan iya cewa Alhamdullah dan duk tabon jiki na ya fita, sedai tabon da yake a zuciya yana nan babu inda yaje, shima jiki na ya fara dawowa, dan haka babu abinda zan cewa Allah sedai godiya.
Ta ɓangare daya karatuna ya fara nisa, dan daman can da karatuna sedai shiririta kawai.
Ga shirye-shirye bikin humaira nata matsowa, shiri ake babu kama hannun yaro.
Gyaran jiki sosai ake mata a gida.
Har yau bandena mamakin wai ya haleepha ne ze aure taba.
Sosai yanzu muke shiri da baffa tamkar wani abu bata faruwa na rashin jituwa a tsakanin mu ba.
Yau haka kawai naji ina son zuwa gidan best.
Dan bana zuwa ko ina iyakacina makaranta.
Mama na tambaya, tace sedai na tambayi baffan.
Koda na faɗa masa kuɗin mota kawai ya bani.
Angel na shirya dan tamin rakiya.
Koda na fito mama ƙaremin kallo take, se kuma tace naje na saka kwalli da powder.
Ayya mama nikam kwalliyan me zanyi, hakan ma isa, na faɗa ina ɓata rai.
Toh kiyi zaman ki kawai ba yanda na iya haka nasaka kwallin amman ban saka powder ba.
Yawwa koke fa mace babu kwalli ai ba mace bace.
********* ********** *********
A bakin titi ya saukeni me napep din a kafa nake karasawa gidan ta.
Buzuwa! Buzuwa!! Juyowa nayi banga me kira na ba, se wata mata mara kyan gani dana gani a baya na.
Dauke kaina nayi kawai naci gaba da tafiya.
Buzuwa ta kara kira na.
Tsayawa kawai nayi ina kallon ta, a raina ina jin kaman nasanta.
Baki ganeni ba ko ? Bosslady ce fa.
Mamaki, tsoro, firgici ne duk yasameni a lokaci ɗaya, kallon ta nake sosai ina son tabbatar da zancen ta.
Kidena mamaki buzuwa.
Kalli yanda na koma, babu komai a cikin rayuwar bariki da bijirewa iyaye se nadama da danasani mara amfani.
Tabbas nasan ko hakkin ya’yan dana lalata baze barni ba.
Bansan yara nawa naja harkar bariki ba.
Yau ki kalle ni kiga yanda na zama.
Kawata ce, tace min akwai wani Alhaji me kuɗi nazo muje, na bita saboda na yarda da ita.
Tabbas buzuwa na samu kuɗi, amman na samo cuta.
Hiv ce ta maidani haka, duk kudin dana samu ya tafi a magani.
Ban karu da komai a bariki ba buzuwa.
Kuka take sosai tana bani labari.
Ni kaina da take bawa labarin kuka nake.
Sosai na kara tsorata da lamarin duniya.
Yanzu me kike anan ?
Gidan karɓar sadaka nazo.
Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!!
Kawai nake maimaita wa.
Bansan dame zan temaka miki ba, amman zo muje.
Har gidan best mukaje da ita nace ta jira ni a kofar gidan ina zuwa.
Da sallama na shiga tana zaune ita da little suna kallo, ganin a yanda na shigo mata a birkice ne yasa ta ajiye little tana tambayar ko lafiya.
Idan kina da cash ki bani Please.
Cewa tayi batada kudi bai wuce dubu biyu ba, nace bazaiyi ba, saboda haka ta bani atm nata na tafi zuwa wajen me POS.
Dubu ashirin na ciro na mika mata nayi mata kwatancen gidan mu “ki samu kizo gidanmu zamuyi magana.
Har ƙasa ta tsugunna tana min godiya.
Sallama na mata na koma cikin gidan.
********* ********* *********
Kuka sosai nake wa best.
Ina bata labarin boss lady.
Ke yanzu tausayin ta kike ji ? Ta tambaya tana Taɓe baki
Sosai best! Na fada ina hawaye.
Mezaki mata yanzu, zan temaketa watakila nima Allah ya temake ni.
Tayaya?
Naji yaya Ahmad yace kyauta suke bada maganin, toh kinga zan iya sawa ya temake ta.
Ke ture ta maganar taimako yanzu, shin kin lura da ya Ahmad yana sonki kuwa ??? Dafe kirji nayi ina kallon best baki bude, sai kuma nayi dariya nace bakida hankali ke wlh, wane irin so kuma ?
Dukan cinyata tayi tace “ke wlh da gaske nake miki fa!!!!!
Bugun ƙirjina ne ya karu, tunanuka ne suka fara gilma min a rai.
Ayi min afuwa yau page din ba tsawo sosai a karba da hakuri
Mu hadu a page 28
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
Talla!
💫
Talla!!
💫
Talla!!!
💫
💫
ALIYU HAIDAR ( THE LION
🦁
)
💫
Paid Book...
By
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.
Seda ya sauke ajiyar zuciya.
Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!
Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.
Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.
Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!
Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.
Chan dai ya kira sunan ta:
“Only!
“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.
“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?
Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.
Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.
“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!
Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.
Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.
Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.
“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”
“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.
Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.
Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.
Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.
Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.
******** ******* *******
Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:
“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.
Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.
Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.
This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!
Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.
“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.
Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.
“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!
Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.
Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......
Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??
Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??
Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??
Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?
Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??
Shin waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 28
Sosai maganar best ta dakeni saboda abu ne da ban taba kawoshi a raina ba, ko kusa ko alama, ta ya za’a ce ya Ahmad yana Sona ? Bayan duk yanda yasan tarihin jiyana ? Wanda bai sani ba ma idan yazo ya sani tabbas bazai aureni ba, a tunanina ya Ahmad kawai yana tausayina ne da daukata a matsayin kanwarsa, kuma ko ya Ahmad zai ce yana Sona ma bazan yarda ba domin ban dace dashi ba, cutarwa ce a gareshi ace yanda yake a nutsen nan ya aureni, gaskiya bazaiyiwu ba, bama zan amince ba.
“Ke ai bakida hankali! Baki san ma abinda kike fada bane, ta ya ma za’a ce haka ? Na fada ina hararar best.
Dariya tayi tace “shikenan! Time will tell! Zamu jira lokaci.
Harararta kawai nayi bance komai ba.
Nifa gwanda da kika zo, bara na dakko mana dinkunan bikin mu.
Abu nata matsowa kuma naga idan na tsaya jiran ki, ba zamuyi abin arziki ba.
Bance mata komai ba har ta hau saman.
Yawwa duba kiga sunyi kyau?
Sosai nake kallon kayan sunyi bala’in burgeni, sedai basu bani sha’awar insaka su a jiki na ba.
Sunyi kyau sosai, gaba ɗaya dogayen riguna a kayi mana.
Duk a yaushe kika bada ɗinkinnan ? Na tambayeta ina kallonta.
Kedai zauna, yanzu mayafai, da jaka da takalmi se sarka zamu karasa siya.
Keda wa ? Nikam nadena saka mayafi, wadannan kayan ma Ni bezama lallai nasaka su ba! Na fada ina ajiye kayan da suke hannuna.
Cikin zolaya best tace Kwarai kuwa nima nasani ustaziya.
Dariya nayi kawai nace “kepah banza ce!!!
Abinci ta kawo mana muka ci duk da taga na kasa sakewa gaba daya yau din, abu biyu ne suka hanani sakewa, na farko bosslady na biyu maganar ya