Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
ki tafi gida ma yamma tayi sosai.
Taya kake tunanin zan iya tafiya na barka a wannan halin ?
Janyoni yayi kawai ya rungume ni duk da a tsorace nake banyi kokarin kwace wa ba.
ZAKI IYa ƘARA BANI KANKI SAU ƊAYA ??
Ja baya nayi a tsorace ina tuna azabar da nasha last time girgiza kaina na fara ina hawaye.....
Shikenan ki tafi gida kawai Nasan dama baki sona!!! Abinda ya faɗa kenan ya koma kan gado ya kwanta.
Kamar ya watsa min kasa haka nake idan naji yace bana sonsa, Cikin rawar murya nace:
Da.....za...fi.....fah...!!! Ina fadar haka na rufe idona cikin jin kunya.
Bazanyi miki kamar wancan ba kuma wannan idan kikace na bari zan bari a hankali zanyi, idan baki yarda nayi haka ba zan iya mutuwa...!!!
Da sauri na rufe masa baki nace “TUH”
Yana fara tabani jiki na ya fara rawa.
Dan katawa yayi ki nutsu mana bame zafi zan miki ba.
Kaina na gyaɗa masa kaman kadangariya.
Tun ina fahimtar abinda yake min har ido ya fara raina fata.
Bansan sanda na fara kuka ina ture saba amman ina a banza, wai an tsikari kakkausa.
Duk da na sha wahala amman bata kai ta waccan ranar ba.
Rungume Ni kawai yayi yana karanta min kalaman soyayya masu dadi a kunne na.
Da kanshi ya raka ni toilet nashiga ruwan zafi Sannan nayi wanka.
Gida zan tafi, na faɗa kaina a kasa kamar wata ta Allah....
“Toh ɗago ki kalle ni”
Kafaɗa na make masa,
“kunya nake ji, na faɗa cikin shagwaɓa.
Shikenam ga wannan ya faɗa yana mikamin kuɗi.
Kaina kawai na girgiza masa, Allah sekin karba ko kuma.
Da sauri na karba ina juyawa.
A hankali nake tafiya dan wani iri nake jin kafata.
Ji nayi an rike ni da sauri na juya.
Bara na taimaka miki ki sauka ta faɗa muna sauka daga benen wata budurwa ce mai zubin yan duniya.
Ke buzuwa ce ? Kaina kawai na gyada mata.
Sunana boss lady bani number ki zamuyi magana.
Wayar ta na karba nasa mata number sannan na karasa titi a hankali.
Se a lokacin hankali na ya koma gida dare yayi, kuma ban cewa mamah na fita ba.
Koda na karasa gida, tun kafin na ƙarasa shiga cikin gidan naci wani uban burki saboda abinda na gani a ƙofar gidanmu zuciyata ta fara dukan tara tara.....!!!!!
Kash ku dakacemu anan
Nan ne na kawo muku karshen page 11 sai Allah ya haɗamu a cikin page 12 domin jin me Sumayya ta gani.....
Taku har kullum Rabi’atu Fulani
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 12
Sadiya ce take sakar min Murmushi “haba sashina karaso mana!” Ta faɗa bayan ta ƙaraso inda tare da kama Hannuna.
Ganin yanda nake daga kafata da kyar bata cemin komai ba har muka karasa cikin gida.
Haleemah a ina kika ganta? Mama ta faɗa tana nufo inda muke.
Ashe tana can gida dakin yaya haleepha tana bacci! Ta faɗa Tana ƴar dariya.
Amman dai kinsan dayana garin Nan baki isaba ko ?
Meye a ciki ko yana nan kwanciya ta zanyi.
Na faɗa ina kokarin zama...
Ai tashi zakiyi mutafi bamu ga ta zama.
Da sauri na dago ina kallon ta.
Ni kadai nasan ruwan bala’in da nake gani a cikin idanuwan ta, me yamin zafi nabiki ? na ayyana hakan a raina.
Mamah mun tafi sekin ganmu.
Ta faɗa tana jan hannu na batare da ta jira cewata ba.
Babu yanda na iya haka nabita jikina a sanyaye.
***** ***** ***** *****
Ammie gamu mun dawo!
Ina kika je anata neman ki duk kin ɗaga mana hankali ? Ammie ce take tambayata bayan ta fito daga kitchen riƙe da plate a hannunta.
Basu tsaya sun dubata da kyau bane ammie amman tana dakin mamah tana bacci fa. Cewar Barrister sadiya ( lol
😄
tunda ta koma lauyata ta karfi da yaji sai kareni take, wanda Nasan jira take ta samu space ta gasani a kotunta )
Bata jira cewarta ba muka wuce sama.
Muna zuwa ta rufe kofar tasaki hannu na.
Wani irin kallo take min, Ni kuma nayi kasa da kaina.
Kaman dai ace mama ce ta rutsani.
Kara bashi kanki kika yi ? Rayuwar da kika zabawa kanki kenan ?
Zagaye kawai ta fara a dakin.
Zan hau gadon ta na zauna, da sauri ta matso, Wallahi jeki ki wanke najasar ki.
Banbi ta kanta ba na
Zauna dan jiki na duk ciwo yake min.
Zama itama tayi kawai tasani a gaba tana kallo kaman tasamu tv.
A haka nayi bacci, bansan sanda ta kwanta ba itama.
Da safe neman duniya na nemi waya ta na rasa, nasan ita ta dauka, amman bance ta bani ba.
Wajen kwana uku waya ta na hannunta.
A kwana na hudun ne nace mata base kin dauke waya zansan babanki ne ya siya min ba.
Kallo na take da mamakin furucina.
Fuuuu taje ta dakko wayar ta miko min.
Banyi musu ba na karba.
Kiransa nayi tana fara ringing ya daga.
Ina kikasa wayan ki ?
Babu charge nabashi amsa.
“Kinsan yanda hankali na ya tashi kuwa” ?
Kayi hakuri nima kana raina shalelenah! Ya jikin naka ?
“Ba sauki. Ya fada cikin wata kasalalliyar murya.
Har yanzu ?
Eh amman karki damu.
Shikenan zan kiraka dan Anjima.
Ido kawai ta zubamin
Bakuwar number naga tana kira na,
“Hello Boss lady ce”
Oh ykk, ? ( Tana fadar haka na ganeta itace wacce muka hadu da ita ranar da naje wajen Khalil a hotel )
Nrml, yane yaushe zaki fita ?
Fita kuma ? na tambaye ta.
Ehmana Ni yanzun gani zani raihan hotel, ki fito muje mana.
Da sauri na kashe wayar ina kallon ta ina rarraba ido cikin rashin gaskiya.
Bata cemin kala ba, ta fita daga dakin.
Message naga ya shigo waya ta ina dubawa naga khaleel ne.
Yana son mu hadu Anjima wajen karfe 4.
Owk kawai nace masa.
Koda na shirya zan fita bata ce min ci kanki ba.
Haka naje yauma na basa kaina batare da gardama ba.
Tun daga ranar khaleel ya maidani tamkar matar sa, bana taba ce masa a’a, indai ze bukace ni zanje wajen sa batare da ja inja ba.
A kalla mun kai wata uku a haka muna wannan rayuwar, tun ban sababa har nasaba.
Sedai ko kaɗan bana jin dadin rayuwar da nake yi da shi, kawai dai babu yanda zanyi da shi ne, bansan ɓacin ransa, amman nida kaina nasan be dace ba.
Best bata karamin magana akan saba koda wasa, ta zuba min ido kawai. Mun ma rage mu’amala baka man daba, Duk da har lokacin ina gidan su a zaune.
Ita tama maida karfin rayuwar ta yanzu a wajen mamah, tabarni a wajen ammie.
Ta gefe guda kuma ga sabuwar kawata itama tana kwaidata min na dinga Binta wajen samarin ta zan samu kudi.
Sedai na faɗa ba kuɗi ne yasani a rayuwar da nake aikata wa ba soyayya ce.
Sauri nake tayi zan tafi yana jira na, sedai yau haka kawai naji gaba na yana faduwa batare danasan dalili ba.
Lafiya lau naje wajen sa, har na fito daga hotel din babu wata matsala...
Ina shirin fita daga bakin get kawai naji ance.
“Pretty” kasa motsi nayi daga inda nake, Duk duniya namiji daya ne yake fadamin sunan nan, yaya haleepha ne Yaushe ya dawo gari ? Na tambayi kaina batare da na juya ba.
Yaya haleepha shine yayan best, dan akalla ya bata shekara 13.
Muna mugun tsoron sa dan baya mana wasa.
Jiki nane kawai ya fara rawa dan nasan yau dai me kwatata a hannun sa se Allah.
Ki gudu shine kawai abinda zuciya ta, ta rayamin.
Aikam na tattare rigata, na daga kafata daniyar guduwa kawai naji ya rike ni gamm.
Tun kafin yace min komai, kallon daya kemin bansan sanda nafara rusa kuka ba.
Fuskarsa tayi jajir saboda ɓacin rai da fushi.
Fincikata kawai yake, yana buɗe bude motar sa ya hankaɗani ciki.
Gudu yake tamkar ze tashi sama be tsaya ko ina ba se a gidan ammie.
Tun kafin ya gama parking na fara kokarin budewa na gudu, amman nakasa saboda yayi locking na ƙofar.
Yana buɗe motar nima na bude ina neman hanyar da zanbi na cece ki kaina.
Amma ina yayi min riƙon tsam, dan idan nayi kwakwkwaran motsi zan iya karyewa.
“Gashi kaman haɗin baki, mama da baffa suna gidan, sun zo yiwa daddy sannu da dawo daga umara.
Wayyo Allah na nashiga uku na lalace, hannu na a saman kai.
Ita kanta best ganin yanda muka shigo batasan sanda ta mike tana neman hanyar guduwa ba.
“Wallahi kika matsa daganan senaci ubanki.....!!!!” ya faɗa yana nuna ta
Ke!! Tsawar daya min nidai bansan sanda nasaki fitsari ba.
Uban me ya kaiki hotel ?
Tsit dakin yayi kaman ba kowa.
Ba magana nake miki ba faɗa yana zabga min mari.
“Bakomai wlh bakomai.”
Belt kawai ya zare ya fara zubamin, Fadamin me kika je yi a hotel Dukana yake kamar Allah ya aikoshi, Gashi ya take min ƙafa yanda bazan gudu ba.
Zan faɗa Wallahi zan faɗa dan Allah kadena duka na.
Nashiga uku wayyo Allah na.
Ammie ki temakeni ze kashe ni. Babu wanda yayi kokarin ƙwatata a hannunsa dan ammie da mamah kuka suke.
Wajen saurayi na naje! Na fada bayan jin saukar wani belt a wuyana wanda ya gigita min lissafi.
“Daman kina zuwa ?
Eh kayi hakuri dan Allah Wallahi bazan kara ba.
Tun yaushe kike zuwa wajen dan iskan ?
Tun ranar candy mu!!
Karya kike! Ya faɗa yana ci gaba da duka na.
Wallahi ka tambayi best kaji.
Tana ganin yayo kanta ta fara neman hanyar guduwa tana kuka, tana yarfe hannu.
Wallahi babu ruwana na hanata bata jiba.
Kiiiii itama ta janyo ta, haka ya hada mu ya daka san ransa.
Ku tashi maza kuyi kneeldown.
Da kyar nake motsa jiki na saboda Wallahi babu karya na daku.
Maza kimin bayani ya faɗa yana kallo na.
Yasan matsoraciya ce ni, shiyasa ma ya fara tambayata.
Ganin yana neman kara tashi tiryan_tiryan haka nabasu labari.
Sauran ke ya faɗa yana nuna ta babu yanda ta iya haka ta faɗa masa komai da ta sani itama.
Bani wayar ki, tana motar ka, na faɗa ina kuka.
Zuwa lokacin kukan da mamah take ma bata baki ne.
Tana me nazama haka.
Ita kanta ammie tunanin datake kenan.
Daddy ne yayi gyaran murya, duk muka juya muna kallon sa, “ku tashi ku tafi dakin ku!”
Har rige rigen tashi muke.
Muna zuwa ta damko wuyana, Wallahi sena rama dukana a kanki.
Daman nasan yanzu ai bakya sona na faɗa ina kara fashewa da kuka.
Bansan yanda aka karke a kasa wajen daddy ba.
Sedai duk wata hanyar fita an toshe min ita.
Waya ma haka Harta best an hada an kwace.
Wahala kala kala, ya haleepha bamu ita yake a cikin gidan nan.
Nidai dana gaji na hado kaya na nace masa gida zan tafi.
Jeki ya faɗa yana dauke kai, bansan gatse yamin ba, seda nazo wucewa ya janyoni ya zabga min mari.
Ammie ce ta fito tana masa fadan dukan yayi yawa, yayi hakuri yabamar mu haka ai munci bazamu kuma.
“Ni kam abinda basu sani ba neman haukacewa nake dan Wallahi khaleel nake bukata.
Wajen sati biyu bana ganinsa gashi bama shiri da best.
A hankali naje na zauna kusa da ita, dan Allah kiyi hakuri kinji Aminiyas insha Allah bazan kuma ba namiki alkawari Na faɗa ina rike hannun ta.
Dan Allah dagaske kike ?
“Ehmana.
Rungume ni kawai tayi tana hamdala.
Tun daga ranar muka dawo kaman da.
***** ******* ******
A hankali natafi wajen ammie inata kame kame.
Meyafaru ? Ta tambaye ni tana kallo na.
Ammie nayi kewan mamah ne! Na faɗa ina sunkuyar da kaina.
Toh nidai kinga yayan ku yace kar nabarki ki fita.
Allah ammie bazan dade ba! Na faɗa ina marairaice mata.
Karki dade.! Ta fada tana kallona da kallon gargadi.
Toh na faɗa cike da zumudi.
Ko sama ban hau ba ban tsaya ko ina ba se unguwar su khaleel.
Tun daga nesa na hangoshi.
Kauna!!! Na faɗa da karfi.
Da sauri yazo waje na.
Me kike anan ?
Wajen ka nazo mana!
Gidan rannan kawai yaja hannuna muka shiga.
Karki kara zuwa nemana.. kinsan kwana nawa a police station kuwa ?
Da mamaki nake kallan sa.
Eh yayanki ne ya kaini.
Rungume sa kawai nayi ina kuka.
Beyi wata wata ba kuwa ya karbeni hannu bibbiyu.
Duk wata kewar sa danayi seda ya fanshe min.
Daganan gida na wuce wajen mamah.
Tamkar komai be faru ba haka ta karbeni.
Baffa kuwa ko kallo na beba.
Tun daga wannan ranar nasamu hanyar haduwa da khaleel.
Zuciya ta, tariga ta dake.
Yan mata jimana, tun daga nesa yake bina yana min magana.
Tsayawa nayi ina bashi hakuri ya rabu dani, inada wanda nake so.
Ina ɗagowa na hangoshi yana nufo inda muke a fusace.
Yanayin da naga fuskan sane ya bani tsoro.
“Shalelenah.......” na fada cike da tsoro.
Kafin na rufe bakins kawai naji saukar mari a fuskata...............
Tirƙashi......
Anan na kawo muku karshen page 12 sai mun hadu daku a page 13
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 13
Dafe kunci kawai nayi ina kallonsa cikin mamaki.
“Cikin tsawa yace uban waye wannan ??
Baya naja a hankali ina zubar da hawaye.
Nace miki waye shi ?
“Khaleel dan Allah ka tsaya ka saurare ni.”
Wani marin ya kara kawo min”.
Ke kin isa ki kula wani namijin a duniya Bayan ni ? Kin isa waye shi nace miki ?
Kaina kawai nake girgiza masa nakasa magana.
Bandamu da mutanen da suke kallonmu ba, nidai buri na kawai kar yayi fushi dani.
“Tun daga nesa ta hango marin da yamin, da sauri ta runtse idonta,
Danji tayi tamkar ita ya mara.
Ganin yanda ya tara min jama’a ne, kawai yasa ta fara gudu.
Bansan tayaya ba, bansan kuma ta ina ta biyo ba, nidai kawai naji karar mari.
Ni kika mara ? Ya faɗa yana yowa kanta.
Na mare ka, waye kai, ta faɗa idonta yayi jajir.
Haleemah!!! Bakida hankali, khaleel ɗin kika mara ?
Zoki rama masa, na mareshi.
Kanta nayo kaman mahaukaciya,
Bata ma bari na karaso ba, ita ta karaso inda nake.
Hannu na kawai ta rike ta fara ja.
Ihu nake, ina Kiran sunan sa, khaleel! Khaleel!! Khaleel!!!
Ko juyowa beyi ba tamkar dai bai sanni ba.
Khaleel karka min haka dan Allah.
Ki sake ni, na