ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 40

6K to 9K   out of 117.2K words

/>
Duk da abun da ya faru nasan babu abun da yasauya a zuciyoyin mu...

Idan kin fasa ta fada a hankali! Kaman ba ita tagama min fada ba.

Jin takashe wayar ne Yasa batare da dogon tunani ba nasaka number sa.

Tana fara ringing ya daga

*Kaunaaa!*

*Ammatanaaah!* Ya fada yana jan sunan.

Lumshe Idona nayi kawai dan kasalan daya samin.

Aure za’amin...!! Nafada ina sa masa kuka.

Toh kiyi auren mana!!! Kamar saukar aradu haka naji amsarsa!

Kasan mekake fada kuwa ? Cakk hawayena ya tsaya ina jiran amsarsa.

Yaushe ne auren ? Ya tambaya kawai da ƙoƙarin basar da tambayata gareshi.

Ranar juma’a wai,

Shiru yayi, se kuma yace kin tuna maganar da kike yawan fadamin?

*”BAN TABA SONKA KASA DA YANDA ZAN RAYU BATARE DA KAI BA”*

Toh ki tabbatar min da hakan.

Yana fada ya kashe wayar sa.

Murmushi kawai nasaki.

Tabbas zan tabbatar maka khaleel.

Saukar belt kawai naji a jiki na.

Zuciya ta ta riga ta dake.. meyayi saura? Komai ya kare.

Ka kasheni da duka Abba!!! Na fada masa idona cikin nasa.

Duka na Yake iya karfin sa amman naki guduwa.

Humairah kuka take iya karfin ta.

Amman ni hawaye kawai nake ido na a rufe.

Hakuri take bashi.

Amman ya rantse saina gudu da kaina zai ƙyale ni.

Taurin Kai! Halina ne danasan iyayena basa kaunar sa.

Har ya tsinke a jiki na ban gudu ba, Kuma ban bude idona ba.

Hannu yasa da kafa yana duka na ta ko ina.

Nakasa tashi kaman wadda aka dasa a wajen.

Jin a rungumeni yasa na bude idona a hankali.

Mamah!! Na fada a wahale.

Ki tashi kona hada da ke” ya fada yana haki.

Ta baya naji an Kara rungume ni!

Ko ban Bude idona ba nasan humairah ce.

Ka hada mu duka Ka daka..

Mahmah ta fada tana kuka

Kashemin yarinya zakayi ? Ta tambayesa tana hararsa.

Duk lalacewar ta ina son abata a haka.

Ta fada tana Kara hararsa...

Shiyasa ai kika bata waya ta Kira wancan dan iskan.

Ke kuma baxaki burgeni ba sekin mutu akansa!

Juyawa kawai yayi ya fita ya bar mana gidan.

Rike ni tayi muka Tashi da kyar muka fito waje.

Jikina ko ina ciwo yake

Ruwan zafi ta ɗakko ta gasa min jiki na.

Humairah zo kisiyo Mata magani tasha.

Da sauri na tale bakina xan samata kuka.

Ko kukan jini zakiyi saikin sha. Ta fada tana harara ta...

Kudi ta Mika Mata, ta juya ta fita.

Ita kuma ta dau buta ta Shiga toilet.

A daddafe na mike na shiga dakinta ina bincike, da kyar na samo abunda naje nema.

Dawowa nayi na xauna ina murmushi ni kadai.

Ke lafiyar ki ? Ta tambaya tana tsareni da ido, bakomai mamah! Kawai bansan haka kike Sona ba ai! Na fada cikin sigar tsokana.

Ke ko!! Tafada ita ma tana murmushi.

A zuciya ta nace nasan wannan shine murmushi na, na karshe a tare da ke mamah!!!

Gashi mamah! Humaira ta wacce ta miko maganin bayan tayi sallama ta dawo.

Bata tasha” ta mikomin ba musu na karba nasha!

“Lallai su o’o anji jiki shan magani babu musu ta fada tana rike haba.

Dariya nayi na dago ina kallon ta.

“Oh ni ƴasu!! Humaira da mama ta tashi haihuwa duk ke aka Tara wa muni.

Tsaida dariyar tayi tana harara ta! “mama kin ganta ko ? ta fada kaman xatayi kuka.

Allah mama dagaske nake ana ganin kamar larabawa amman ita koda wa take kama ? Na fada ina zabga tagumi.

Allah mahmah ki Mata magana!! Ta fada kaman zatayi kuka...

Kyaleta humairah ta da wasu idanunta irin na aljanu!!!

“Mamaaah! Nafada cikin shagwaba.

Gwalo tamin.. me idon mage kawai, Ta fada tana dariya,

Nima dariya nasaka kawai,



Naji dadin wasannan fiye da yanda zan misalta muku, nayi farinciki sosai,

Koba komai nabar musu abunda zasu na tunawa dani!!!

Munyi rabuwar farinciki bata bakinciki ba.

Na fada ina kallon abun hannuna, fiya fiya ce!

Zan tafi kaman yanda na fada bazan iya rayuwa babu Kai ba khaleel!!!

Nafada ina Kai kwalban bakina...............!!!!!

Mu haɗu a page 04 idan Allah ya kaimu

Taku har kullum FULANI

🤍



💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 4

Mahmah! Mahmah!!mahmah!!! Halima ce take ƙwalawa mama kira tun daga ƙofar gida.

Keda ita bansan sanda xakuyi hankali ba, wannan kiran ai seki fadarwa da mutum gaba.

Mama Ta fada cikin faɗa.

Batabi ta Kan fadan ba tace,

Mamah tana ina ? mamah ina SASHENA ? ( Sunan da Take kirana dashi kenan saboda soyayya da amintar da take tsakaninmu ) tajefa mata tambayoyin lokaci Daya!.

Ke lafiyar ki ? Ki nutsu mana.

Mama sashina ? ta Kara tambayar ta cikin tashin hankali.

Aunty haleemah bata Dade da Shiga daki ba, cewar humairah da take zaune a gefen mama tun shigowar halima.

Wayyo Allah na! Ta fada tana nufar dakina hankali a tashe.

Ganin duk yanda take a firgice ne yasa suka bi bayanta gaban mamah na faduwa.

Tana tunanin mena fada Mata haka da hankalin ta ya tashi.

Idan bata manta ba yau shekara Daya da rabi, rabon haleemah da gidan nan, meyasa waya ɗaya xata firgitata haka ? Tayiwa kanta tambayar dabata da amsarta.

Koda suka shiga dakin a durƙushe suka sameta a gaba na ta rike hannu na tana kuka tamkar ranta zai fita.

Karki min haka sashina! Dan Allah kiyi hakuri ki tashi.

Ta fada tana Kara fashewa da kuka!!!

Ita kanta mamah ganin kwanciyar da nayi saida gabanta yayi tsananin faduwa, Ta dai San lafiya kalau babu yanda xa’ayi mutum yayi kwanciyar nan.

Bata karasa tsorata ba seda ta matso kusa dani taga kumfa na fita ta Baki na, ga kwalba a kusa dani.

Humairah ce taga mama ta dafe kanta sakamakon hajijiyar da ta kamata tana shirin faɗuwa, ba shiri humairah ta tallafota.

Kamar wadda aka tsikara ta mike tana surutu cikin tashin hankali “tabbas wani abu ya samu sashina bazan taba kyaleshi ba, kodame Yake takama wlh, ta fada cike da yanayin alwashi!

Waje ta fita dasauri, tana ƙwalawa saurayinta kira da ya kawo ta a mota ya Mukhtar! Yaa Mukhtar!!! Sashina,!!

Ta fada tana nuna masa cikin gidan hankalinta a matukar tashe.

Ki nutsu mana ta musamman me ya samu sashen naki ?? Me ya faru da ita ???.

Muje kawai ta iya ce masa,

Baiyi musu ba ya bita,

Da sallamah ya Shiga gidan, halima tana gaba yana bayanta ta nufi dakin da nake ciki,

Ganin halin da nake ciki baiyi wata wata ba ya sunkuceni yayi waje dani, hankali a tashe ya sakani a cikin mota mamah da humairah suka shiga suka tallafeni, halima kuma ta shiga gidan gaba amma kuma gaba dayanta tana baya, saboda yanda ta waigo tana ta min sannu ta zuro jikinta gaba daya inda nake.

Tukin yake da sauri ya saka double signa! Saboda tsabagen sauri tare da fatan Allah yasa ta rayu dan yanda suka ga na sha wuya kuma jikina ya saki gaba dayansu sun cire rai dani.

Wani private hospital muka nuna kai tsaye batare da ya tambayi mama ba saboda yasan a yanda nake dinnan idan aka je asibitin gwamnati zan iya wafati kafin likitoci su zo kaina, muna zuwa aka shiga emergency dani manyan likitoci ne suka zagayeni sunata fama a kaina sama da awa huɗu sai shige da fice suke.

Duk fitowarsu sai su mama da halima sun taresu saboda tashin hankalin da suke ciki saidai likitocin suce musu “muna iya ƙoƙarinmu ku cigaba da addu’a”

Halima kuwa sai tsuma take tana ƙwafa tana son na warware taje wajen dan iskan can ta Tata masa rashin mutunci, halin da nake ciki ne kawai ya taka mata burki.

Tana son tsayawa a asibitin.

Sai can likitocin suka fito suna share gumi suka ce iyayen Sumayya su biyoni office.

Gaba dayan su suka nufi office din.

Mukhtar yana waje yana jira,

Itama halima bata ce ya Shiga ba amma tabi bayansu umma.

Garin yaya Tasha fiya-fiya ?

Tambayar da likitan ya fara jefa musu kenan, Shiru sukayi ba amsa.

Kallansu Yake yana nazari,

Alamu sun nuna tabbas sunsan dalilin.

A jiyar zuciya kawai yasauke

Se kuma ya maida kallonsa kan mama wacce ko ba’a fada masa ba yasan mahaifiyata ce saboda ga kama nan.

“Cikin ikon Allah mun samu nasarar ceto yarinyarki ta fita daga hatsari, amma dole muyi mata aiki da gaggawa gaskiya.

Idon mama cike da hawaye tace, ka taimekeni kamar yanda Allah ya taimake ka likita ka ceto min yarinyata kar na rasata!!

“Kiyi hakuri hajiya kuyi Mata Addu’a in Sha Allah komai zaiyi daidai” ya faɗa da sigar lallashi.

Yanxun kuyi kokarin biyan kudin aikinnan a yau a samu a Mata aikinnan

Tunda ya fara magana ta rufe fuskan ta se yanxun ta bude..

“Nawane kudin aikin ? Ta tambaya a hankali

500k ya bata amsa yana kallonta.

Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, cike da sanyin jiki mama ta amsa da toh ta fara tunanin inda zata samu 500K.

Ita dai tasan bata ajiye ba kuma bata bawa wani ajiya, dan ko kayan dakinta za’a siyar tasan baza’a haɗa 500k ba. Fitowa sukayi dukansu jiki a sanyaye.

Ita kanta humairah ta saddaƙar cikin muryar kuka tace, Shikenan xan rasa yar uwata wayyo Allahnah!!!

Wata muguwar tsawa halima ta daka mata tare da fadin baki da hankali ?? Sashen nawa ce zata mutu ? Gaba daya ta fita cikin hankalinta jin ana kirawa sashenta mutuwa!!!

Gaban mama ta tsugunna wacce tayi zaman yan bori a wajen saboda tashin hankali,

Cikin ƙwarara kanta tace,

“Mahmah ki kwantar da hankalinki, na Miki alkawarin babu abunda xe samu sashina, in har ina numfashi in Sha Allah.

Shiru kawai mahmah tayi tana kallon gaskiyar abunda take fada acikin idonta.

Na yarda dake halima Allah yayi muku albarka ya tashi kafadun yar uwarki!! Ta fada cike da bata tabbaci.

Gyada kai halima tayi kafin tace,

Mamah bara na sallami Mukhtar.

Toh muje namasa godiya, nima.

A’a mamah ki kyaleshi, ta fada tana katse mama.

*Love*! Ta kirasa a hankali bayan ta karasa wajensa,

“Ngd sosai kaje gida Ka huta,

Taya kike tunanin zan iya tafiya nabarki a cikin damuwa soulmate ? Mukhtar ne yake tambayar halima bayan jin abinda tace

Bakomai fa zata samu sauki in sha Allah kaje kawai.

Nasan wace ita a wajen ki

Dan haka nima zan tsaya,

Saboda ita kika hana auren mu,! Kince lallai se kun dawo daidai zaki aureni, Tabbacin ita din me muhimmanci ce garemu.

Taya kuma kike tunanin xan tafi na barki ? Baze yiwu ba soulmate.

Kuka ne ya kwace mata tace love bana son wani abun ya samu sashina,

Ki kwantar da hankalinki,

Bara na Kira Daddy ina zuwa.

Tana kiran Daddy ringing daya ta daga, tare da sallama.

Dad sashina! Ta fada tana Kara fashewa da kuka,

Subhanallahi me yasa meta ?

Cikin kuka tace tana asibiti za’ayi mata aiki tana asibiti,

Kuma kudin 500k ne!!!

Kasan basu da kudin nan! Yanzun ina ji ina gani zan rasata ?.

Ki nutsu mamana ya fada cikin sigar kwantar da hankalin, kinsan sumayya ita ma ƴatace ko ? To Nima bazan bari wani abun ya sameta ba bari na tura miki kuɗin sai a shiga da ita theater din yanzu yanzu.

Cike da murna halima ta fara yiwa Daddy godiya da da addu’a.

Karki damu mamanah Nima gani nan zuwa a wane asibiti kuke ?

Fada masa tayi sannan sukayi sallama ta koma cikin asibitin.

Mukhtar ne ya taimaka mata da cike ciken da za’ayi saboda bata cikin nutsuwarta.

Tunda aka shiga tiyatar sun Kasa zama.

Zagaye kawai suke a harabar a reception.

A kallan sun dauki 2 hours kafin su fito...

Amman ji suke tamkar kwana biyu sukayi suna Jira.

Yuuuu! Haka suka bi bayan likitan wannan karon harda Mukhtar cikin bin likitan domin jin halin da ake ciki.

Alhamdulillah munyi aiki cikin nasara yanzu munyi mata allurar bacci in Sha Allah zuwa gobe da safe zata farfaɗo.

Godiya sukayi ga Allah kana suka godewa likita, sannan ya kara musu da shawarwari akan su guji ɓacin raina, sannan suka baro office ɗin.

Haleemah kije gida naga dare ya fara yi, cewar mama.

Mamah konaje bazan iya bacci ba senaga tashin ta,ta fada tana hawayen farin cikin jin cewar sashenta zata farfaɗo da safe.

Shikenan toh ya isa mun gode sosai halima haka mama ta fara jera mata addu’o’i, humairah tana amsa wa tare da halima.

Kinyi waya da ammie ?

Eh suna nan tafe tare da Daddy.

Suna cikin maganar suka karaso, harda kayan abincinsu.

Gaisawa aka shiga yi tare da yiwa juna jaje sannan mama tayiwa Daddy godiya bayan halima ta sanar da ita cewar shi ta kira ya biya kudin aikin.

A cikin hirar ne mama ta fada musu duk abunda ya faru bata boye musu komai ba, jigum jigum suka yi suna jimamami kamar wanda akayi mutuwa.

Ke kuma ya akai yau kika karya alkawarin ki kikaje wajen ta?

Abba ya jefawa haleemah tambayar, seda ta tura bakin ta gaba sannam tace babu komai.

Murmushi kawai sukayi, sun san bazata taba fada ba ai daman.

Amintar yaran tana burgesu, kome Daya zeyi, baze taba fada ba, Basa fadar lefin junansu.

Har yau Basu san dalilin dena maganar muba, kawai rana daya suka ga mun dena magana, Anyi nasihar, anyi barazanar amman babu wadda tayi aiki.

Har dukan mu yaya haleepha yayi amman babu abunda ya canza.

Katse musu tunani tayi ta hanyar fadin,

“Amman wallahi abba bazan kyale wancan banzan ba!

Mama ce tace, Nima ina tunanin wannan karan dole hukumah ta Shiga tsakani.

Babu wata hukumah dan hatsabibi ne, ni nasani mama.

To Allah ya masa abun da ya mana.

“Amin suka fada suna hada Baki

Mamah ina abbansu ?

“Baze zoba ai!

Ta fada cikin wani irin alamu dake nuna taji zafin abun sosai, dan humairah tace ta sanar dashi a waya, lokacin suna hanyar zuwa asibitin.

Shikenan.

Abba ya kalli mahmah zan biya muyi magana da shi, dan hannunka bazai taba ruɓewa ka yanke ka yar ba.

Toh kawai tace ta dauke kanta cike da ƙunar rai.

Murmushi kawai ammie tayi Mata sukayi sallama.

Koda suka je a kofar gida suka samu Abba a tsaye

Yana ganinsu ya tarosu yana murmushi

Bayan Daddy ya bashi hannu sun gaisa suka samu waje suka zauna a shimfidar baba dake kofar gida.

Wai meyake faruwa abbansu ? ( Da yake haka yake ce masa shima haka Abba yake kiran Daddy )

A hankali yamasa bayani, Da kuma hukuncin Daya yanke.

Ajiyar numfashi Daddy ya sauke kafin ya nisa yace, Shikenan bazan hanaka yi mata hukunci ba, Amman ka bari tasamu lafiya.

Ko gawar sumayya ce se ankai gidan Alhaji Abbas, dan Allah abbansu karka ce wani abun ina ganin girmanka wlh amma na rigada na rantse.

Daddy ne yace ba hanaka aurar da ita zanyi ba amma a yanzu dai ka dan saurara tukunna tunda ga halin da take ciki.

Wallahil azeem babu abunda ze hanani aurar da sumayya ranar juma’a saidai idan mutuwa tayi......!!!!!!!

Mu hadu a page 05

Taku har kullum Rabi’atu Fulani

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....

3 / 40