Chapter 35 Reading ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx Arewa Novels

ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   35 / 40

102K to 105K   out of 117.2K words

ganina dan nadaɗe rabona da gidan.

Daddy ne ya fito.

“Aini nayi fushi daugther”

“Ayya daddy kayi hakuri mana”

“Daddy ba’a fushi da amarya fa kamanta ne”

Mintsinin ta nayi.

Sosai muka gaisa da daddy, bayan ya fita muka sha hira da ammie .

Ya haleepha ne ya shigo, yana ganin mu ya fara muzurai.

Ni dariya ma ya bani, baki na nakai kunnen best.

“A ƙa’ida fa ya dinga ce mana aunty sumayya da haleemah amman ga yanda yake wani muzurai”

Aikuwa kaman haɗin baki muka kwashe da dariya.

Ganin kallon daya ke mana ne muka fara ƙokarin maida dariyar mu.

Kansa kawai ya girgiza.

Seda yamma mukayiwa ammie sallama muka tafi.

Nayi tunanin gida zamu wuce naga tace gidan ta.

“Amman dai ai bamu faɗawa mamah ba ko?”

Bayan gobe ma zamuje gidan.

Ban ƙara magana ba har mukaje.

Kitchen muka shiga mukayi girki, sannan mukayi wanka.



********** ********** *********

Waya naji na ringing, kaman bazan ɗaga ba se kuma na ɗaga.

“Hello”

“Ki fito ina waje”

“Ina gidan best bana gida”

Be cemin komai ba ya kashe.

Ba’ayi 30 minutes ba ya ƙara kira na.

Gani nazo.

Fitowa kawai nayi, na hau saman ta dan nasan haneep be dawo ba.

Rasa me zance mata nayi, kada na tace ni na kira shi.

Ya akai?

“Bani abaya dan Allah zan karbo sako”

Ki buɗe ki dakko mana.

Ban kara musu ba na dakko.

Tsaya Malama, babu kwalliya haka zaki tafi nufin ki ?

Hmmm kawai nace, na matsa gaban mudubin.

Ba wata kwalliya nayi ba kwalli nasaka kawai da lipstick amman sosai nayi kyau.

Rigar na zura na fesa turare.

Sosai nake kallon kai na a mudubin.

“Kinyi kyau sosai.” Ta fada tana kunshe dariyar bakinta.

Harararta nayi nace “Kice ma banyi ba.

Yana cikin mota dan haka ina zuwa buɗewa nayi na shiga.

“Ina wuni, kana lafiya?”

“Alhamdullah kefa ?”

Alhamdulillah.

Masha Allah.

Ya shirye-shirye ?

“Alhamdullah.

Ajiyar zuciya ya sauke.

Beyi tunanin haka zan amsa masa ba, amman alhamdullah ai an samu cigaba.

Duk yanda yake jana da hira na kasa sakewa muyi hirar.

Jaka ya miƙo min a bayan motar, gashinan bansan ina zaki kai ɗinki ba shiyasa ban kai miki ba.

Sannan ya ƙara miko min envolope gashinan ki kai ɗin kin idan be isa ba kimin waya.

Banyi musu ba na karɓa nayi masa godiya.

Shikenam seda safe.

Allah ya tashe mu lafiya.

Bayan munyi sallama na shige cikin gidan.

Waya na mata ta sakko.

Ita ta buɗe jakar.

Shiru kawai tayi ni kaina ido na zubawa ashoben, idan nace beyimin kyau ba nayi ƙarya.

Wayyo sashina!

Murmushi nayi ko kina so?

“Gaskiya har na hango ki a cikin kayan.”

Ashobe ne baby pink, se ratsin fari a jikin sa.

Faɗin yanda yayi kyau ma ɓata baki ne.

Gaskiya zooroad zamu kai ɗinkinnan.

Dariya kawai nayi mata.

Ina jin shigowar motar haneep na korata.

Kwanciya nayi nima ina kallon kayan sun min kyau sosai.



********* ********** **********

Washe gari da wuri muka fita, saboda zamuje kasuwa.

Kayan da zata saka muka siyo Sannan muka kai ɗinkin.

Chasss muka basa kuɗin sa ya bamu time ɗin da zamu zo karɓa.

Koda muka zo gida humaira har tazo.

Dan haka aiki kawai muka fara.

Idan na kalli humaira mamaki nake wai humairah ce da ciki abin Allah.



********** ********** *********

Ranar juma’a aka kawo lefe a ka tsaida sati biyu kacal.

Akwati huɗu da kit ya doctor yayi min tamkar budurwa ba bazawara ba.

Sosai mutane suke mamakin wazan aura haka.

Me gyara aka kirawo wacce zatayi min gyara, Koda tazo, gidan ammie muka koma dakin best, can ake gyaran ko rana bana fita, ya rabb kar kuzo kuga yanda nayi kyau.

Ga magungunan *momma’s zhara* ga gyaran jikin da ake min.

Na yarda da magana best yanzu zanyi aure.

Ni kaina jiki na sha’awa yake bani bare kuma wani.

Ya doctor be ƙara zuwa waje na ba se ana sauran kwana biyu *doctor’s day* shi kansa yanda yake kallo na har kunya naji wallahi.

“Za’ayi taro kuma akwai maza sosai a wajen...., se kuma yayi shiru.”

Jiki nane yayi sanyi sosai.

“Ki kula koda abokaina ban amince ki sake ba, kinji me nace miki”

Ya faɗa cike da umarni yana tsare ni da idanunsa.

Kaina kawai na gyada masa.

Zaki iya tafiya.

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!! Kawai nake maimaita wa a raina.

Dan narasa inda zan ajiye maganar tashi.

Ni daman nasan shima kallon dayake min kenan.

Shiyasa tun farko nace ma ni bazani wani taro ba.



********** ********* **********

Washe gari da wuri muka tafi kunshi da gyaran kai.

Sosai mukayi kyau muka fito shar damu.

Ranar event karfe hudu muka tafi kwalliya.

A gida best tabar little.

Tun ana min kwalliyan ake ta santi nidai bance komai ba, dan Allah kaɗai yasan fargabar dake raina.

Sosai mukayi kyau nida best.

Kayan baby pink ne da ratsin fari.

Na best kuma fari ne da ratsin baby pink.

Se wajen bayan isha’i yazo dauka ta a gidan kwalliya.

Itama best haneep yazo ɗaukarta.

Kaina a ƙasa ta shigar dani motar.

Lumshe idona kawai nayi, kamshin turaren sa na ratsa hancina.

Ina wuni, na faɗa ƙasa ƙasa.

Alhamdullah.

Daga haka bamu ƙara magana ba.

Ta gefen ido nake kallon sa, yayi kyau sosai cikin fararen coat ɗin daya saka, komai na jikin sa farine, masha Allah kawai nace a raina.

Koda mukaje wajen mun daɗe bamu fito ba seda suka gama shiryawa wajen.

Fita yayi daga motar, ina shirin buɗe wa ya buɗemin da kansa.

Hannun sa ya miƙo min, alamun na riƙe.

Amman nakasa sema ɓoye hannun dana ke.

A hankali ya tsugunno ya riko hannun, duk yanda naso kwace wa na kasa.

A haka muka nufi hall din hannunmu cikin na juna.

Sosai wajen yayi min kyau sosai.

A tsanake ake gudanar da event ɗin babu wata hayaniya.

Sosai abun ya ƙayatar dani, dan gaba ɗaya likitoci ne da nurses.

Abun yayi kyau sosai.

Bayan an tashi muka fito Nida ya Ahmad muna rike da hannun juna, Saida muka zo bakin gate aka kirashi, ya tsaya yana magana da mutanen da sukayi masa magana wa’yanda da alama abokan aikinsa ne.

Ji nayi an kirani “Buzuwa!

Juyowa nayi ina kallon sa.

Abdul! Na faɗa a hankali, me kake anan wajen ?

Se kuma nagansa da kayan security.

Abdul shine wanda aka taɓa kamamu a hisbah.

Ze bani amsa na juya jin taku a baya na.

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un kawai nafara a fili, ganin yanda ya nufo fuskarsa cike da ɓacin ran daban taɓa gani ba tare a dashi.



Yana nufo ni nafara ja da baya.

Jin yanda ya finciki hannuna ne yasa kawai na tsaya.

A haka har mukaje mota.

Har lokacin hannuna na cikin nasa kuma riƙon da yayi min bana wasa bane.

“Ya Ahmad hannu na da zafi, dan Allah kasake ni.”

Waye kike magana da shi?

Shiru namasa kawai.

Jin yanda ya ƙara rikon ne yasa nace zakaji min ciwo fa.

Waye shi nace miki, jin yana neman jimin ciwo ne bansan sanda nace masa.

Abdul ne!

Wanene Abdul meye haɗin ki dashi?

Rasa ta inda zan masa bayani nayi gaba ɗaya.

Tsawar daya min ce tasaka kawai nace masa.

Shine wanda aka taɓa kamamu a hisbah!!!!!!!!

Kashhhh mu hadu daku a page 32

Nice taku Rabi’atu Fulani

A page din da ya gabata zaku ga an saka page 29 bayan kamata yayi ace ya zama page 30 saboda haka akasi aka samu, page 30 ne.

Nagode

https://chat.whatsapp.com/KwLWS5ecBTt446RcWPdOF3?mode=ems_copy_t

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 32

Be ƙara magana ba ya cika min hannun.

Kewayawa yayi ya shiga Mota Ni kuma ina tsaye, Saida na gaji da tsayuwar sannan na shiga aka ja muka tafi.

Sosai nayi kokari na shanye kukan daya ke son kwace min, Ga gabana da yake faɗuwa.

Takurewa nayi har muka je gida.

Nakasa fita daga motar shima becemin komai ba.

Nan ma Saida nagaji da zama sannan na fita.

A hankali ya lumshe idon sa.

Bawai yana zargin ta da wani abu bane a’a kawai yana kishin ta sosai.

Sannan yanda take ɗari_ɗari da shi yana ƙara tunzura zuciyar sa, gaba ɗaya ta sauya masa taƙi ta sake da shi, daman yasan soyayya zesha wahala kafin yasamu amman koba komai ace tana sake wa da shi ko magana ne suyi, shi hakan ya wadatar da shi.



********* ********* *********

Ina ganin jiri haka na shiga gida.

Bawai ina son ya doctor bane, a’a kawai ina tunanin yanda su mamah zasuji idan yace ya fasa aure na, ya zasuji ace a karo na biyu an fasa bikin yar su ? Ina zuwa nan a tunani na fashe da kukan danake ta riƙewa tun a motar.

“Meyafaru sashi na ?”

Kaina kawai na girgiza mata, na tashi nabar mata ɗakin, ɗakin baffa na tafi dan nasan can ne babu mutane kuma kaɗaici nake bukata.

Bansan adadin lokacin dana ɗauka a zaune ba ina saka da warwara.

Seda na gaji dan kaina sannan natashi nayi wanka da alwala.

Sallah nayi bayan na idar na ɗaga hannaye na sama zanyi addu’a.

Jinayi zuciya ta karye, wani irin rauni ya rufe ni, idona kawai na rufe nabawa hawaye na damar zubar da kansu.

“ Ya Allah nasan niɗin me tarin laifuka ce a gare ka, ya rabb natuba, ya Allah ka gafarta min zunubansu, ya Allah na rokeka ka sassauta min badan niba sedan nasan kaiɗin me yawan yafiya ne ga bayinka.

Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Kuka ne yaci karfina nakasa ci gaba da addu’ar.

Zame wa nayi na kwanta akan daddumar, bansan sanda bacci ya ɗauke ni ba, nayi Sa’a ranar bappa baya nan yaje ƙauye.

Da asuba na koma ɗakin mu bayan nayi sallah.

Da safe haka natashi ganinan kawai, amman ina jin a raina a shirye nake da karbar duk kaddarar da tazo min, sedai fatan fatan Allah yabamu dangana, nida iyayena.

********* ********** *********

Sosai nake kallon mamah tayi kyau cikin leshin da ta saka.

Humaira da best kayan su iri ɗaya suka saka, sunyi fesss abinsu.

“Waike kina zaune sauran befi 30 minutes a daura auren ba, dallah ki tashi ki shirya”

“Ba zanyi ba kanwar uwata” na fada ina dauke kaina.

“Haba sashi na dan Allah ki tashi badan halina ba”

Banza na mata kawai nama juya mata baya na kwanta.

“Ah lallai abin naki azimun ne.”

Ban tankan mata ba nayi kaman ma bacci ya ɗauke ni.

Haleemah ina sumayya take ? Ammiey ce take tambayar best yayin da ta shigo dakin da muke.

Nuna mata inda nake a kwance tayi.

“Subhanallahi daugther meyafaru ?”

“Wallahi ammie lafiyar ta lau iskanci ne kawai yake damunta”

Ba tabi ta kanta ba tazo ta ɗago ni.

Ganin kuka nake yasa best ta matso kusa dani.

“Meyafaru sashina ?”

“Dallah ina ruwan ki ba masifa kike min ba” na faɗa ina hararar ta.

“Rabu da ita daugther na tashi ki kishirya kinga an kusan ɗaurin aure.

Bance mata komai ba na tashi na shiga wanka.

Shiryawa nayi a cikin baƙin leshina, sosai ya haskani.

Komawa nayi na zauna.

“Yawwa tawo ayi kwalliya”

“Banso” tana takuramun na sakar mata kuka dole ta kyaleni badan taso ba.

********** ********** *********

Wata iriyar faɗuwar gaba ce ta ziyar ce ni, wadda zan iya cewa ban taɓa jin irin ta ba, hannu na na ɗora a kan kirjina jin yanda yake amsamin kaman ze fashe.

A daidai lokacin kuma naji karar shigowar massage waya ta.

INA TAYAMU MURNAR AURE INA ROKON ALLAH DAYA HAƊA MU DA DUKKANIN ALKHAIRAN DAKE CIKIN WANNAN AUREN ALLAH YA BAMU ZAMAN LAFIYA ME ƊORE WA UBANGIJI YA KAƊE DUKKANIN WATA FITINA

HAPPY MARRIAGE LIFE

MRS AHAMD MUHAMMAD AHMAD!!!!



Gama karanta saƙonsa yayi daidai zubowar hawayena akan fuskata.

Jin yanda ake ta sakin guɗa a cikin gidan mu kawai na fara kuka sosai.

A yanda muka rabu jiya banyi tunanin ze aure ni ba, nayi tunanin shima a yau ranar daurin aure ze janye yace ya fasa, meyasa ya Ahmad ? Meyasa ya doctor ? Why zaka aure ni bayan ban dace da kai ba ???

Ina a wannan halin ta shigo da gudu ta rungume ni, kuka take kuma tana dariya da magana a lokaci ɗaya.

“Sashina an ɗaura auren ki, sashi na kinyi auren da dukkanin mai sonki zaiyi farin ciki da shi, Alhamdullah! Alhamdullah ya rabb! Alhamdullah Allah mun gode maka Allah kaine abin godiya”

Gaba ɗaya ta rasa ina zata saka kanta tsabar farin ciki.

Jin yanda wayar ta take ta ringing ne ta fara bala’i “haba Ko waye yau besan banda lokacin sa bane” ganin me kiran kuma seta saki murmushi tana goge hawayen ta.

“Hello love! An ɗaura auren sashina yau”

Ta bangaren sa murmushi yayi Sannan yace mata” yau buri ya cika ko best ɗin sashinta ?”

“Sosai love”

“Toh ki faɗa musu gamunan zamu zo da ango.”

“Toh se kun kara so”

Tissue ta ɗakko ta goge min fuska ta tass, Sannan ta ɗaura min ɗan kwali, haka ina ji ina gani taita fesamun turare, har kaina nake ji yana hawa.

“Masha Allah sashina yau ji nake babu wanda ya kaini farin ciki”



********** ********** *********

Muna a haka suka shigo cikin gidan, hannun best na rike ganin tana niyar tafiya ta barni, dawowa tayi ta zauna bata ce komai ba.

Kawayen mu ne suka shigo amarya ta fito.

Kaman wadda aka ɗaurewa kafa haka naka sa motsi.

Mikewa tayi sannan nima ta ɗago ni, mayafina ta ɗora min a ka.

Dagaske jiri nake gani, dan jinayi kafata na harɗe ni.

Masha Allah matar doctor!

Muna fito wa aka fara buɗa, be jira karasowarmu ba ya matso ya karɓi hannuna ana best.

“Me guri yazo dole ne tabar ya naɗe” ta faɗa tana dariya.

Ansha hotuna da vedios kaman me.

Seda aka gama sannan yaje gaida mamah.

Hannuna mah ta rike ta haɗa da nasa waje ɗaya, sannan tace!

“Ahmad nabaka amanar sumayya ka kulamin da ita ko bayan raina”

“Insha Allah mahmah nayi miki alkawari”

Addu’a akayi mana sannan sukayi sallama suka tafi.



********* ********** **********

Karfe huɗu malamar da zatayi walima tazo.

A gidan ammie akayi, anyi wa’azi sosai akan hakkin mata akan miji, da kuma hakkin miji akan mata, sosai wa’azin ya shigeni ba kaman na aure na da baba Abbas ba.

Anyi addu’a sosai a wajen.

Karfe shida aka tashi daga taron.

Ammie ce ta rike ni har ɗakin ta, ruwan wanka ta haɗa min da yaji turarruka kala_ kala, koda na fito da kanta ta shirya ni.

Best ce ta naɗa min lifaya da kanta, Sannan tayi min feshin turare.

Seda ta gama tsaff sannan ta ƙaremin kallo” gaskiya bazan gaji da faɗa ba doctor yana cikin Alkhairi wiiiiii”

Har muka shiga motar ya haleepha tana tsokana

35 / 40