Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
/>
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 5
Kayi min wannam alfarmar Abban Sumayy......!
Dan Allah kayi hakuri amma nariga na rantse, bazaka fahimci me nake ji ba, yarinyar nan itace babba, amman itace me matsala, bana fatan humairah tayo halinta, shi salim me sauki ne, amman angel gaba dayan ta rainon tace, banasan ta lalatamim yara kaman yanda ta wulakanta kanta da rayuwar ta, domin kafi kowa sanin lalatacciya ce! Abba ya tari numfashin Daddy yana mici-mici da idanu cike da masifa.
Subhanallahi!!! Daddy ne ya katseshi da sauri shima....
“kaida kanka zaka dinga jifan ƴar cikinka da wadannan muggan kalaman ? ya fada da yanayin rashin jin dadin lafazin Abba a tare dashi.
Karya namata ko sharri ? Shima Abba ya katseshi ?
Addu’a zaka bita da ita ba wannan mugun lafazin ba.
Shiru kawai ya masa alamun maganar bata shigeshi ba.
Ina zuwa! Ya faɗa yana nufar cikin gidan.
Bai daɗe ba ya fito da invitation a hannun sa, gashi nan dakai da jama’ar gidanka, Kuma kai nake son ka zamo waliyinta dan Allah....!!!
Yanzu nida kaina zanyi wa ɗiyata auren dole ? Daddy ya faɗa yana zare ido.
Ɗiyar taka ce bataji, shiyasa ako ina nake alfahari da ɗiyata. ( Sadiya yake nufi ) Abba ya faɗa yana murmushi.
Mu ma zamuyi hankali in sha Allah, Daddy ya faɗa yana bata rai.
Anya xukuyi hanlin nan kuwa ? Abba ne mayar masa da tambaya yana taɓe baki.
Zaka ce na faɗa maka. Shima Daddy ya faɗa cikin tabbatar masa.
Zamu wuce dare yayi, Daddy ya faɗa tare da mikewa.
Shikenam nagode Daddyn yara Allah ya bar zumunci.
Bakomai se mun haɗu wajen ɗaurin auren.
Suna tafe a hanya ammie take tambayar sa, ko Abba ya janye maganar auren ?
Murmushi yayi se kuma ya girgiza kansa, “Be janye ba
Kinsan sumayya shi ta gado a taurin kai amman yaki fahimta.”
Girgiza kanta kawai tayi, se kuma tace:
Bansan wanene mijin ba amman na tausaya masa, daughter wanda take so ma sai yayi hakuri da ita bare wanda bata so.
Da hirar nan suka karasa unguwar tudun yola gate 7.
‘’wajajen karfe 7am na farka sedai banyi motsiba,
Tunani nake akan na mutu ko ina raye, sedai motsin da nake ji ya tabbar min da aduniya nake ba a lahira ba.
Se kuma kamshin turaren danake ji a kusa dani. Nasan na dade da dena amfani da shi, meyasa nake jin kamshin sa a kusa dani ?
Kodai.....
Ban karasa tunanin ba na shiga kokarin bude ido na a hankali, don jinsa nake yamin nauyi tamkar ba nawa ba, Hannuna na shiga motsawa sedai shima jinsa nake cikin wani hannun.
Jin motsi a hannun ta yasa ta dago da sauri.
Banyi tunanin ganin ta ba duk da kamshin turaren danaji na zata mafarki ne.
‘’idona tar cikin nata’’
A saman lebe na na furta.
*BEST!!!
Idona yana cikowa da kwallah.
Hannun na kara rikewa.
Kin tashi sashina ? Ta tambaya cike da farinciki.
Sashina! Na maimaita a zuciya, daman zata kara kira na da sunan nan
Idona kawai na lumshe.
“Bara na kira nurse”
Hannun na kara rikewa alamun banasan tayi nisa dani!
Mahmah! Mahmah!!mahmah!!! sashina ta tashi,
Zoki gani mahmah har magana munyi... Mahmah.
Wai baxaki taba hankali ba haleemah? Ko bakisan a asibiti muke ba?
Ta faɗa tana hararar ta.
Kiyi hakuri mama mantawa nayi, ta fada tana tura mata baki.
Girgiza kai kawai mahmah tayi, a zuciyar ta tana ayyana duk kanwar jace.
Nurse tace ta kira tazo ta dubani,
Bayan ta gama Dubani tace a dagani na zauna na huta kafin likita yazo.
Sunzo dagoni nasaki yar siririyar kara saboda azabar da ya ratsani.
Sannu! Mamah dan Allah mu kyaleta leemah ta fada kaman zatayi kuka.
Bazaku taba canzawa ba mamah ta fada tana matsawa gefe ta kyalemu.
‘’daga inda muke take kallon mu, Duk da ba wata magana muke ba.
A zuciyarta godiya kawai take wa Allah na tashina da yayi.
Tabbas tanawa sumayya soyayyar dazata iya cewa kaf cikin yaranta ba wadda takewa irin ta.
Yarinya ce me biyayya, ga jin ƙan mahaifa, tana da tausayi da jin ƙan ƴan uwanta.
Alla ya shiga lamarin ki, ya kawo miki mafita, Allah ya shiryamin ke ta faɗa a zuciya tana goge hawayen ta.
‘’9am bata karasa ba ammie suka zo ita da humaira, ganin ina bacci sai basu tashe niba, amma sunji daɗin cewa na farka har nayi magana.
Seda doctor yazo sannan aka tashe ni.
Dubani yayi, ya ware maganin da za’a bani bayan na sha tea.
Allura ya fara haɗawa,
Ina ganin haka dama na fara kuka.
Yana matsowa kusa dani na daga hannu na zan dake shi duk da babu ƙwari a jiki na..
Shi dariya ma na basa..
Haba buzuwa! Babba dake kina kukan allura ?
Harara na galla masa dan ko nace zanyi magana murya ta ba fita zata yi ba.
“Best ce a kusa dani, dan haka na rike hannun ta ina mata kallon karta bari yayi min.
Hade rai tayi ta dawo gaba na ta tsaya, tana hararan sa.
Allah ba zaka mata ba tunda bata so, ta faɗa tana tsareshi da ido.
“Ikon Allah taron dangi kuma zaku min ? Kuna ina nurses kuzo ku shigar min nima.
Ya fada yana matsawa.
Duk wajen babu wanda beyi dariya ba, saboda yanda yayi kaman da gaske yaji tsoron.
Haleemah matsa daganan! Mama ta faɗa babu alamar wasa a fuskar ta.
Gefe ta matsa amma bata bar kusa dani ba.
Haka akayi alluran, ni akewa amman ita ce meyin kara,
To ni ina ma naga muryan karan ? Sedai hawaye kawai.
“Yawwa wannan tabon na jikin ta zan rubuta mata magani da sabulu a siyo tana amfani da shi, insha Allah ze fita da wuri.
Se a lokacin na kalli hannu na, gaba daya shatin duka ne, na sauran jiki na ma haka yake, ya kwanta abunsa akan farar fata ta.
Ido na kawai na lumshe, ina karajin zafin Abba a raina.
Toh mun gode doctor cewar ammie.
Best ce ta karbi ta kardar taje pharmacy ta siyo..
Kafin ta dawo har na koma bacci. Sai Wajen 12 na tashi
Yawwa sashina daman jira nake ki tashi.
Zani gida nayi wanka, sannan zanje wani waje yin wani aiki, zan iya daɗewa amman zanyi kokarin dawowa da wuri.
Tunda ta fara magana nake kallon idon ta, nasanta ciki da bai, jiki na ya riga ya bani me zata aikata.
Dan Allah karki aikata komai kinji best ? Na faɗa ina raurau da idanu.
Tsugunnowa tayi daidai kunne na, kema kin san duk wanda yaci bashin haleematu seya biya.
Hannun ta na kara rikewa ina girgiza mata, hannun ta na kara rikewa, idona harya tara hawaye, karkimin haka best dan Allah.
Hannun ta ta karɓe ta sakar min murmushin da seda gaba ya faɗi.
Ta juya ta tafi
“Tabbas wajen zata je, ya subhanallahi.
Khaleel!!! Na kira sunan ina fashewa da kuka.
Kedai kuka baya miki wahala yanzu zata dawo fa, cewar ammie.
Bazaki gane ba na ayyana haka a raina.
“A gurguje taje gida tayi wanka, riga da wando tasaka, seta dora kimona a jikinta, sannam tayi rolling ta fita..
Allah kadai yasan wutar dake cin zuciyar ta daga jiya zuwa yau, ta tabbatar kuma idan bata amayar da ita ba bazata samu kwanciyar hankali ba..
Direct kasuwan su ta nufa, don tana da tabbacin yana can adaidai wannam lokacin, kaman yanda tayi tunani tun daga nesa ta hangosa, a hankali ta furta, koren maciji a cikin koriyar ciyawa.
Tana karasawa wajen Batare da tunanin komai ba ta daukeshi da mari, ji kake tassss!!! Irin marinnan me ɗaukar hankalin wanda ya ji shi.
Gaba daya wajen juyowa akayi ana kallonsu.
Ba zafin marin ne yasaka yayi suman tsaye ba, sedan mamakin wadda ya gani a gaban sa, iya sanin sa ya rusa amintar, toh meya kawo ta wajen sa ?
Hakan na nufin wani abu ya samu sumayya!
Dum gaban sa ya faɗi, amman babu alamar hakan akan fuskar sa..
Mugu, macuci, azzalumi, mayaudari.
Murmushi ya sakar mata tamkar be damu da abunda ta masa ba.
A dake yace ta mutu kenan ? Ya tambayeta yana sakin wani ɗan iskan murmushi.
Kai ka isa ta mutu a dalilin ka, kaiɗin banza, kasani tananan cikin koshin lafiya, cikin aminci, burinka baze taba cika ba.
Sumayya ai ta dade da mutuwa! Ya katse ta har lokacin da murmushin mugunta a fuskar sa.
Muga ? Ya fada yana duba hannun sa, yatsunsa uku ya kar kada a fuskar ta, shekarar ta uku da mutuwa, wannan ai ba sumayya bace, gangar jikin tace.
Ya fada yana kara sakar mata wani malalacin murmushi.
Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Sekinyi danasanin abunda kika aikata, ke bazan miki komai ba, dan nasan ba damuwa zakiyi ba.
Amman ki fara tunanin meze faru da ita sashin naki, zan taba wadda nasan ganin ta cikin damuwa shine tashin hankalin ki.
Muzuba mu gani ta faɗa masa cike da ƙwarin gwiwa tana barin wajen.
“Beyi yunkurin dakatar da ita ba dan yasan zamanta a wajen hadari ne a wajen sa.
Zuciyarsa azalzalar sa take ya tattaka ta, sedai yasan ko giyar wake ya sha Bama ze fara yunkurin taɓata ba, dan yasan wane ubanta”
Koda ta koma asibiti ɓacin rai ne sosai a tattare da ita, duk yanda tayi kokarin ɓoye ɓacin ran bai ɓoyu ba.
Tambayar duniya kuma taƙi magana, Duk yanda naso mu haɗa ido taki yadda.
Hakan shiya ƙaramin tabbacin bata aikata abin arziƙiba.
Yau juma’a, kwana na biyu a asibiti kenan.
Abba baizo ba ban damu ba kuma, dan ba bukatar ganin sa nake ba nima.
Gaba daya na sakankance da maganar auren, tunda ina asibiti wane aure za’amin da wannan tunanin hankali na ya kwanta.
“Ina zaune ina shan tea ya shigo ɗakin, ɗauke kaina nayi tamkar ban gansa ba.
Murmushi yayi yace ta yaro mai take bata ƙarko.
Duk da haka ban juyo ba.
Jin ya ajiye min abu akan cinyata ne yasa na juyo,
“Kudi ne!!
Kallan sa nake da alamun ina bukatar ƙarin bayani akan fuska ta.
Hankalin sa kwance yace sadakin kine, na daura miki aure yau da Alhaji Abbas.... kamar yanda nayi alƙawari.
Ban san sanda nasaki kofin hannu naba,
Na fara dambe da numfashi na........!!!!!!!!!!!
Cizon Hannuna nayi da fatan ace na farka daga mummunan mafarkin da nake.... Wanda yake neman zautani a cikin baccina!!
Saidai ga mamakina Abba na sake gani a gabana da kuɗin dai akan cinyata wanda yake ƙara tabbatar min da cewa ba mafarki nake ba aurena aka daura kuma wannan sadakina ne akan cinyata.......
Mu hadu a page 06
Taku har kullum ( Rabi’atu Fulani)
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 6
Tashin hankali wanda ba’a sama sa rana, gumi ne yake tsatstsafomin ta ko ina,
Tamkar babu fanka a dakin, numfashi na wani iri ya kemin dan ji nake duk wata kofar iska ta toshe min a a wajen.
Ganin ina neman faɗowa daga kan gadon mahmah tayi saurin riƙoni
Idon ta taf hawaye tace ka kashe ta ka huta, ni daman tunda naganka nasan ba alkhairi ne ya kawo ka ba, ta faɗa tana hararar sa.
Murmushi yayi yace ko mutuwa tayi bani da damuwa tunda na sauke alƙawarin dana ɗauka.
Yana gama faɗar haka ya juya.
Sumayya! Sumayya!! Sumayya!! Ta shiga faɗa da karfi, tana jijjiga ni.
Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un! Ta faɗa tana fashewa da kuka.
Da sauri nurse tazo wajen ta karbeni a hannun ta.
Ki kwantar da hankalin ki mahmah suma tayi.
Amman zamu mata alluran bacci saboda zuciyar ta na bugawa ba bisa ƙa’ida ba, ana bukatar tasamu hutu!!!
Mama ba bakin magana sai hawaye.
Nurse ɗin na tafiya ta riko hannu na, Allah ya baki ikon cinye jarabawar ki.
Koda na farka banyi ko wane yunƙuri ba.
Tana zaune kusa dani kanta a kasa, a hankali na fara kokarin tashi zaune, sedai na kasa.
Motsin dataji ne yasa ta ɗago da sauri.
Gaba ɗaya fuskarta tamkar ba tata ba.
Idunuwan ta sun kubura suntum, fuskar nan a kumbure ita ma, Kamani tayi na tashi zaune.
Sannu SASHENA!!! Kallon ta kawai nayi.
Kina buƙatar wani abu ne ??
Ɗauke kaina kawai nayi daga kallon ta.
Ganin ta a haka na karyamin zuciya.
Nasan taurin zuciyar best, duk abinda ya risinar da ita ba ɗan karami bane.
Bara na kira mahmah. Bance mata komai ba har ta tafi.
Tare suka dawo, itama maman daga ganin fuskar ta taci kuka ta gode Allah.
Magana suke min Ni dai iya kaci na, na bisu da ido toh mezan ce musu ?
*** *** *** ***
Da daddare sega ango yasha manya kaya, yazo da ledoji a hannun sa.
Har kasa ya tsugunna ya gaida mahmah.
Ta amsa kadaran kadahan
Wani mugun tsaki da best taja ne yasa gaba daya muka ɗago muna kallon ta..
Fuuuu ta fice daga dakin kaman me Aljanu.
Mama tashi tayi tabi bayan ta.
Ranki ya daɗe sannu da jiki!
Ya jikin ?
Idan har gadon da nake kai yayi motsi toh nima tabbas na motsa.
Tunda yake surutun sa ko ɗagowa na kallesa banyi ba Bare yasaka ran jin magana daga gare Ni.
Haka ya gaji da babatun sa ya tafi.
Koda su mahmah suka dawo suma duk maganar da suka min ban ta kasu ba.
Da safe da doctor yazo dubani ba rigima na tsaya ya min allura.
Shida kansa seda yayi mamaki.
Best ya kalla yake mata alamun lafiya da ido.
Girgiza masa kanta kawai tayi, itama jikin ta duk a sanyaya.
Buzuwa ko kallon sa banba, Ko da yake karma ki kulani, danni idanunnan naki tsoro yake bani.
Ɗagowa nayi na galla masa harara kawai.
Ni natafi toh, Anjima zan zo muyi magana.
Ya fita yana kiran best da idanu.
Meyake damun ta ne?
Ya tambaye ta yana kallan ta.
Idonta tafff da hawaye tace” bakomai.
Ki fadamin pls!!!!
Da gaske babu komai fa.
Shikenan!!! Ya faɗa yana tafiya..
Tunda ga ranar ban karawa kowa magana ba, bana uhm, bana uhm uhm.
Anyi nasihar, anyi rarrashin amman duk a banza.
Bana iya cin komai sedai ruwa, ko tea, shima se an matsamin..
Kullum doctor zezo ya karaci tsokana ta ko kallan sa banayi.
“A hankali ya maida zuwa waje na, sau uku a rana...
Da kansa yake zuwa ya bani magani, ya dena turo nurse, hatta allura shi yake min.
Har lokacin daba na aikin saba ma zuwa waje na yake.
Bansan ta yaya na fara sakewa da shi ba.
Ina iya yi masa magana daya biyu haka.
Idan har kaga magana to best ce, Ko kuma doctor.
A hankali shakuwa ta fara shiga tsakani na da shi.
Saboda mutum ne me barkwanci, ga iya magana rabin maganata dashi nasiha ce da yarda da ƙaddara sai kuma ya ɗan dinga jana da hira yana zolayata, baya barina na zauna ina tunani, a haka sabo ya dinga shiga tsakaninmu har ya zamana idan ba da best ba to bazaka ji maganata da kowa ba sai shi, ta kai ta kawo su biyu kadai nake iya yiwa murmushi, shima sai yayi abun dariya nake iya murmushi amma dariya kuwa har na manta rabon da nayi ta, ahaka mama godewa Allah take tunda na fara sakewa, ina iya magana, tana fatan Allah yasa dai nayi hakuri da ƙaddarata na zauna a gidan mijin