ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   39 / 40

114K to 117K   out of 117.2K words

Koda muka samu nutsuwa kasa sakina yayi.

Fuskar shi nake leƙawa amman yaƙi bari mu haɗa ido, ni kuma na dage dole seya kalleni, shi kuma yaƙi.

Dariya ce ta kwace min ganin dagaske kunya ta yake ji, tunda gashi yaƙi haɗa ido dani.

“ Allah seka kalleni nidai.”

Tashi yayi ya shiga toilet da sauri, binshi nayi mukayi wankan tare.

Duk yanda naso ya kalleni ya ƙiya, magana ma yaƙi yi, ya zamar min kaman wani kurma.

Abinci muka je muka ci, muka dawo parlor muka zauna muna kallo.

Yana zaune ni kuma kaina yana kan cinyar shi ina kwance.

“ Ban taɓa tunanin jin wannan kalmar daga bakin ki ba.”

“Nayi tunanin kawai kina zaune da nine Dan baki da wani zaɓi.”

“ Ashe nima.....

Hannuna na ɗora akan bakin shi, dan jikina duk yayi sanyi, yanda yake min magana cikin sanyin murya yana samun jin tausayin shi sosai.

“ Kamanta da komai Haskenah mu fuskanci gaba dan Allah.”

“Kar ka kuma jin a ranka bana sonka, a’a ina sonka sosai.

“Ngd sosai buzuwa ta.”

Murmushi kawai nayi masa.

Sosai muke zuba soyayya a cikin gidan nan.

Ji nake tamkar ban taba soyayya ba, se a wannan lokacin.

********** ********* *********

BAYAN WATA SHIDA

Shiri nake tayi da sauri, yau muke sunan humaira, ta haifi yar ta mace sunyi wa mama takwara.

Best se waya take min, duk na matsu nima na fito daga gidan.

“Dan Allah ki nutsu ki shirya a hankali.”

“Ayya HASKENAH duk ba kaine ka jamin ba, kabarni na kwana ka hanani, kuma yanzu kana cewa na nutsu.

Tun jiya nake mita, babu rarrashin daban yiwa bawan Allahn nan ba amman yace bazan barshi ya kwana shi kaɗai ba a gida.

Ganin faɗa nake ji, se be biye min ba.

Muna tafiya a hanya ina ta cin magani abuna.

“Allah da kinsan yanda fuskar ki take idan kina fushi da bakiyi ba.”

Ban bashi amsa ba naci gaba da hararar hanya.

Kanshi kawai ya girgiza me hali ai baya fasa halin shi.

Koda muka je gidan sunan, buga masa motar shi nayi naci gaba da tafiya.

Shi dariya ma na bashi.

Tayi abu kuma da shi take fushi, duk faɗan rashin gaskiya ta iya shi.

Tuno dalilin fushin ne yasa yayi dariya.

Daga wanka ta fito, ta ganshi yana shirya, ita takawo kanta gare shi da kanta, kuma bayan tasamu abinda take so ta hau fushi da shi.

Yanda ta sauya gaba daya yana jikinta ya sauya cikowar kirji haske da kiba sannan ga yawan bukatarsa da take yasa ya fuskanci wani abu, shi likita ne fa! Saboda haka ba abinda za’a layance masa.



********* ********* *********

Ina shiga gidan na ware nama manta da wani fushi nake.

“Sashina, daman jiran ki nake yau zan yaye little.”

“Dan Allah ki barta ta dan kara jan lokaci best.

“Baze yiwu ba idan ba haka ba zatayita rashin lafiya ko kuma kina son tasha ciki ne.”

Baki na saki ina kallon ta.

“Kike kallo na naga kema cikin gare ki.”

“ Yanzu ke har kinyi wani cikin, gaskiya ne chabbb.”

Sosai nake tsokanar ta ganin bata son su ammie su gane, danaga tawowar su zan fara.

“ Kema fa cikin nan gare ki sashi na.”

“ A’a kin manta baya ne dani.” Gaba ɗaya ni ban ɗauki maganar ta seriose ba.

“Kaman yanda nayi alkawari nice zan yaye little, dan haka nace tabani ita na tafi da ita.”

“Kunyi magana da doctor?”

Banza na mata.

Da Daddare yazo mutafi, dan haka da little na fito a hannu na.

Yayi tunanin da maman ta zamu tafi seda nace masa yayeta zanyi sannan yaja muka tafi.

A hanya yake tsokana ta.

“ Haskenah ina son wannan kamshin naka, zokaji dan Allah.”

Kawai yarinya tajani har kan gado da kanta, kuma tsabar rashin gaskiya nake faɗa miki buzuwa, wai ta hau fushi dani, kome na mata ohoooo.”

Sosai na shanye dariya ta, dan nima se Yanzu abin yake bani dariya, tabar kunya ce kawai na naɗe ta duk dan kada yasani a gaba da tsokana, kuma gashi dai ban tsira ba.

“ Allah sena rama.”

Dariya yayi sosai.

A hanya ya tsaya yayi wa little siyayya sosai, harda katifa ya siya mata karama me net sannan muka wuce gida.

Wanka na mata na shirya ta tsaff na kwantar da ita, aikam bata daɗe ba bacci yayi gaba da ita.

Nima wanka nayi nashirya, na nufi ɗakin shi, yayi wankan shi tsaff yana ta tashin kamshi.

Jikin shi na shige ina shinshina shi.

“ Oh ni Ahmad shi kuma wannan babyn abinda yake saki kenan.”

Ban bawa maganar shi muhimmanci ba naja shi muka tafi ɗakina.

Gyarawa little kwanciya nayi a katifar ta, sannan muma muka kwanta.

“Yayana!.”

“Uhm ƙanwar yayanta”

“Yayana”

“Me kike so?”

“Kai kai nake so yayana”.

Ban bashi damar magana ba na haɗe bakin mu, na rasa meyake damuna yanzu na zama rigimammiyar karfi da yaji.

Shi kam naga hakan dadi yake masa sosai.

Little batamin rigima ko kaɗan daman ta saba dani, dan ji nake da kyar idan zan mayar da ita.

Ko waya na kira maman ta vedio call tana jikina, babu ruwan ta da ita.

Zuwa yanzu dai nima na yarda cikin gare ni, babu rashin lafiya babu komai, ko ciwon kai banayi, abinci kam duk abinda nasamu ci nake.

Kamshi ne kawai matsala ta, kamshin ya doctor kawai nake so, kuma ba’a kaya ba a’a a jikin shi.

Cikin best ma ya fito dan banjin ta zarar mu zata wuce wata ɗaya.

Little daga yaye ta guji maman ta, dole ta hakura ta zuba mana ido.

Cikina tsayina yabi da jiki na, beyi girma ba.

Muna ta siyayyar haihuwa, nace ayi scaining ya ƙiya yace shi duk abinda yasamu yana son shi Allah ya sauke ni lafiya.



Best ta riga ni haihuwa, ta haifi ɗanta namiji, me kama da babansa sak.

Ansha shagali ranar, yaro yaci sunan daddy, zamuna ce masa ayaan.

Bayan sati shida da haihuwar ta nima Allah ya sauke ni lafiya na samu yar mace.

Duk wanda yazo barka sedai yace min Allah ya raya haleemah.

Ni dariya ma suke bani, watakam kowa dai yasan sunan yarinyar nan tun kafin babanta yayi mata huɗuba.

Haka zan sakata a gaba nayi ta kallo, yanzu zanga dani take kama Anjima naga tayi kama da babanta.

Sosai nake son kyakykyawa babyna.

Wani lokacin idan ina kallon ta haka idona ze ciko da hawaye yanzu wannan kyautar ni Allah yayi wa ?

“Allah Alhamdulillah”

Sosai mukayi shali ranar suna yarinya taci sunan ta halimatus’ sadiya zamuna kiranta AYAANAH yarinya ta taci sunan best.

Dan bana haɗa kaina da ita, nida kaina nasan yar gidan best ce.

Sosai nake shan rigima da little dan haka take cewa zata ɗauke ta.

A halin yanzu banida bakin magana face na kasance kullum cikin godiyar Ubangiji.

Allah ya gama min komai ya azurtani da miji nagari.

Ga Iyaye na gari, ga aminiyar arziki Sannan ga yaran mu guda 3.

Toh babu abinda zan cewa Allah sedai nace Alhamdullah!!!!.

********** ********* **********

AFTER 6yrs

Bayan shekara shida rayuwa ta canja min sosai, yarana uku Ayaana, sai mai bi mata namiji an saka masa sunan mahaifin yaya Ahmad muna kiransa da Daddy sannan auta mai sunan mahaifiyarsa ana kiranta da imaan.

Bangaren best yanzu yaranta hudu bayan little tayi maza biyu mace daya hudu kenan, humairah kuma yaranta biyu yanzu tanada cikin na uku.

Rayuwa tayi kyau sosai sai godiya ga Allah banada sauran damuwa a yanzu, ya Ahmad bai barni na zubar da hawaye ba koda wasa, saidai idan hawayen farin ciki, bangaren mama yanzu tana sana’a a gida ta kayan miya busassu da jarin da na bata.

Lamarin ya Khalil kuwa naje unguwa nake samun labarin cewa yan sanda sun kamashi a can Lagos sunyiwa wani babban mai kuɗi yahoo sun kashe masa manyan kuɗaɗe sama da ₦100M shida abokansa har sun kashe ₦30M a ciki dama kuma akwai zargin fashi akansu, saboda haka a yanda naji ance an yanke masa hukuncin shekara ashirin a gidan yari.

Lokacin da naji labarin haka na wuni sukuku, gaskiyar masu magana suka ce soyayyar farko bata taɓa mutuwa, haushin kaina na dinga ji a bisa damuwa da na dinga yi a kan halin da nake ciki, ya Ahmad yayi tambayar duniya nace masa bakomai kawai yanayina ne bana jin dadinsa, ba dan ya yarda ba ya kyaleni, amma haka ya dinga min abubuwa ko zan manta na koma cikin yanayina na baya da ya sani, ganin yanda ya damu ne da kuma yanda yake bani kulawa ya saka na tattara komai na watsar, na fuskanci mijina na cigaba da bashi kulawa da nuna masa soyayya sannan na dage da tarbiyyar yarana.

Alhamdullah! Alhamdullah!! Alhamdullah!!

Allah na gode maka Allah kaine abin godiya, ya rabb Nagode maka daka bani damar fara wannan littafin lafiya kuma nagama shi lafiya.

Wannan labarin gaske ne ya faru da wata baiwar Allah da ta bukaci a sakaye sunanta, so zaku ga na canja sunaye duka da kuma wasu location ɗin, hakan saboda tsaro ne, ban kara komai akan labarinnan ba, idan ba bude abubuwa ba na fito dasu a bayyane, sai kuma wasu da bai kamata a fada ba da na cire, saboda haka wannan labari gaske ne an rubuta shi dan ya zama izina ga na baya, wa’yanda suke fifita soyayya a saman komai, domin su gane masoyansu na gaskiya irinsu ya Ahmad da kuma masu soyayyar karya irinsu Khalil.

Nida na bada wannan labarin yanzu haka ina tare da mijina da yarana shida muna rayuwar farin ciki alhamdulillah tare kuma da aminiyata kuma yar uwata best, ina fatan Allah ya bar mana zumuncinmu har aljanna, Ameen thumma Ameen, dan Allah idan kun karanta labarinnan kuyi min addu’a da bakunanku masu albarka, Nagode, wa’yanda kuma a labarinnan na basu haushi suyi hakuri ba kirkira bane bawa baya taba wuce kaddararsa.

Nagode Nagode Nagode.

Tammat bi hamdullahi, anan zan dakata a littafinnan mai albarka ICEN DAMUNA.

*JINJINA TA A GARE KA*

*YA UBBERA* *ƊAN UWANA ƊAYA TAMKAR DA DUBU BABU WATA KALMA TA GODIYA DA ZATA NUNA MAKA JIN DADI NA KUMA BABU WANI ABU DAZAN BIYA KA DASHI SEDAI ZAN KASANCE MEYI MAKA ADDU’A ADUK HALIN DANA KASANCE.* *ALLAH YA BIYA KA DA GIDAN ALJANNAH TARE DA MATA TA GARI*

*KAMAN DAI YANDA KUKA SANI ICEN DAMUNA SADAUKARWA NE GA AMINIYA TA AMINA MUHAMMAD HARUNA MAMAN ZHARA* *KIYI YANDA KIKE SO DA SHI MIEMIE ICEN DAMUNA MALLAKIN KINE*

*Icen damuna fan’s group, icen damuna discussion board, icen damuna group fulani na alfahari daki*



*INA GODIYA A GARE KU*

*SHAREEFAH MUHAMMAD*

*MIEMIE YOUGURT AND MORE*

*NI’IMATULLAHI*

*KARYMAT*

*NAJA’ATU (MRS MUHAMMAD KHABIR)*

*DAMA DAI WADAN DA BAN AMBACI SUNAN SU BA*

*NAGODE DA ƘWARIN GWIWAR DA KUKA BANI*



*NABARKU LAFIYA TAKU HAR KULLUM*

*RABIA’TU KABEER ACHADU* (*FULANI*)

SAI MUN HADE A SABON LITTAFIN MU ME SUNA *ALIYU HAIDAR THE LION*

*NAGODE!!!!*

Talla!

💫

Talla!!

💫

Talla!!!

💫

💫

ALIYU HAIDAR ( THE LION

🦁

)

💫

Paid Book...

By

Rabi’atu Fulani....

&

Ubeera.....

Happy New Year Update......

A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.

Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.

Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.

Seda ya sauke ajiyar zuciya.

Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!

Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.

Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.

Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!

Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.

Chan dai ya kira sunan ta:

“Only!

“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.

“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?

Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.

Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.

“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!

Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.

Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.

Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.

“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”

“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.

Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.

Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.

Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.

Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.

******** ******* *******

Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:

“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.

Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.

Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.

This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!

Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.

“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.

Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.

“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!

Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta

39 / 40