Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
na hadiye maganata.
Kuyi hakuri, ku taimaka ku aura min wanda nake so, na faɗa ina kuka wiwi.
Wannan karon in kin tashi, ki tabbatar kin mutu kafin a kaiki asibiti.
Kuyi hakuri Wallahi, natuba, nabi Allah na biku.
Khaleel shine wanda nake so, khaleel shine farin ciki na, Dan Allah kar ku raba ni da farin ciki na, a karo na biyu.
Tashi mama tayi tabar dakin, wanda nasan saboda bata iya juran kuka nane yasa tabar wajen, bata so na karya mata zuciya.
Matsawa nayi na rike kafar baffa, ina rera masa kukan dazan iya cewa tunda ya haife ni, ban taba yi masa shiba.
Hankadeni yayi, shima ya barmin dakin.
Kuka ne tamkar raina ze fita.
Jin an dafani ta baya, najuyo da sauri.
Humaira na faɗa ina rike ta.
Tsuguno wa tayi ita ma, kawai na rungume ta.
Humaira wai ba zasu aura min khaleel ba, humaira aidai kinsan irin son da nake masa ko?
Kiyi shiru aunty sumayya! Kiyi addu’a, duk abinda yake Alkhairi, Allah ya zaba miki shi.
Humaira ni nasan khaleel shine Alkhairina ai.
Shiru kawai tayi min ta kama hannuna, muka fita daga dakin.
“Zan iya cewa rabon danayi kwanan tashin hankali har na manta.
Tsawon kwana uku inata bin kansu, ina lallami nayi kukan, nayi ban hakurin, nayi rarrashin duk a banza.
Dan haka na shirya na tafi gidan best, dan nasan ita ce kawai zata iya tsayamin.
******* ********* *******
Mai napep ne ya saukeni a kofar gidanta, na taɓa kofa Naji a rufe saboda haka na ciro waya na kirata a waya, tana ringing ta dauka.
“Hello best!
Ya akayi ? Abinda kawai tace min kenan, duk da naji ba dadi amma haka na daure tunda Ni nake nema.
“Ina kofar gidan ki” na faɗa ƙasa ƙasa.
Bata cemin komai ba ta kashe wayar.
Tana buɗe kofar na shiga.
Tare muke tafiya a jere, bata kawo komai a ranta ba, saboda nasaka facemask da glass, toh bazata ga yanayin fuskata ba.
Muna zama akan kujera na cire hijab din, da sauran abubuwan.
Ganin yanayi na, kawai tama manta da wani fushi da take dani.
Me yafaru sashina?
Ta tambaya tana rike hannuna.
Zamewa nayi, na tsugunna a gaban ta.
Hannayena na haɗe waje biyu ina kuka.
Dan Allah ba danni ba, ba dan halina ba, dan darajar manzan Allah, ki temakeni kaman yanda Allah ya temakeki.
Me kike so, kin san babu wani abu a duniya da zaki nema a wajena ki rasa shi.
Khaleel nake so best!
Ki temake ni nasamu zabin zuciyata.
Shiru tayi, dan ta rasa me zata ce min.
A hankali na faɗa mata yanda mukayi dasu mamah.
Zama tayi a kasa, ta janyo ni daga tsuguno danayi kaman meneman gafara, kai na ta ɗora a cinyar ta.
“A hankali tace kin san wani abu sashi na ?
“A’a!.
Ban taɓa son wani a rayuwata, kaman yanda nake sonki ba! Kinsan meyake saurin sakani farin ciki?
Nan ma kaina na girgiza mata.
Ganin ki cikin farin ciki da walwala yafimin komai yimin dadi a duniya.
Duk wanda yake saki kuka tsanarsa nake, Wallahi ko wayeshi.
Yau ace kina da abu, ni bani da shi, Wallahi zanyi farin ciki, saboda nasan duk abinda kika samu namu ne mu duka.
Yau ace khaleel mutumin kirkine, zanfi kowa farin ciki da ki aure shi, saboda kina son sa! Ni kuma ina son duk abinda kike so, sedai bazan boye miki ba, Wallahi bana son khaleel ko kaɗan!
Saboda shi ɗin damuwa ne a gare ki da iyayen mu baki daya, Dan Allah sashina ki hakura da auren khaleel!!!
Tunda ta fara maganar naji tana dogon sharhi nasan inda maganarta zata saboda haka tana fara maganar na rufe idona Saida ta kai karshe sannan na budesu.
“Bazan iya ba! Bazaki gane me nake ji a raina a kansa ba”.
Tarar numfashina tayi ta hanyar cewa “Yana cutar dake sumayya”!
Cikin sauri nace wlh Yanzu ya dena best!
Hmm kiyi hakuri toh, gaskiya bazan iya kai ki halaka da kai na ba, bazan iya kaiki inda kullum zaki kasance cikin azaba da....!!!
Ya isheki haka! Na katse ta.
Na rokeku gaba ki dayan ku, kun ƙi, kisani koda saka hannunku ko babu Wallahi babu abinda ze hanani auren khaleel.
Ina gama faɗa na mike ina maida hijabi na.
Hanyar waje na nufa kai tsaye.
Hannu na ta rike.
Kisani auren khaleel da zakiyi, shine babban kuskuren da zaki aikata wa rayuwar ki sumayya.
Kuma Ki sani daga ranar da kika aureshi kinyi bankwana da farin ciki a rayuwar ki! Daga ranar ne zaki fara kuka da danasanin kuskurenki na baya.
Na haɗa ki da girman Allah karki aikata haka.
Babu abinda ze hanani auren khaleel, koda yankan naman jikina, ze dinga yi.
Ina faɗa mata haka na zame hannuna na tafi.
******* ********* ********
Daga nan gidan ammie naje.
Bayan mun gaisa ban biye sharenin datake ba.
Nace ammie daddy yana nan ?
Bata tankamin ba, ta tashi ta shiga dakin sa.
Ajiyar zuciya na sauke, dan hakan nufin yana nan.
Duk kowa fushi yake dani akan shalele.
Baki na turo gaba ina hararar gefe nace dan duk Basu san meye soyayya ba shiyasa suke min haka.
Bayan wasu mintina na tashi na shiga dakinsa.
A zaune na sameshi yana kallon tv, ina shiga na zube kasa na gaisheshi.
Be karbi gaisuwata ba, yace ya akayi ?
Daddy daman....., nan na kwashe duk yanda muka yi da bappa da mama da kuma best na fada masa.
Bazaki aureshi ba! Shima ya faɗa kai tsaye.
Hannu kawai na ɗora aka na fasa ihu.
Wayyo Allahna na shiga uku, Ni yanzu babu mesona Wallahi sena shiga duniya kowa ma ya huta.
Zan kara fasa wani ihun, idona ya faɗa kan yaya khalipah yana ƙoƙarin shigowa.
Da sauri na shanye ihuna, na fara rarraba ido.
Ganin ya shigo yana kallona yasa nayi sauri na nutsu.
Kallona yayi fuskar sa babu alamun rahama.
Yace ke ya akayi ? Ihun me naji kina yi ?
Da sauri cikin rawar murya nace “Ba....bu ko....mai
Babu komai nake jiyo maganarki a sama ?
Ina bawa Daddy labari ne!!!
Ze kara wata tambayar.
Daddy yace haba haleepha abar min yarinyata haka.
Kinji me nace bazaki aureshi ba.
Hawaye kawai nake, dan Babu damar magana.
Se yamma na koma gida.
A tsakar gida na samesu, dukansu a zaune akan tabarma.
Wucewa nayi na zauna a can nesa dasu nace:
“Mamah! Shareni tayi ko kallon inda nake batayi ba.
“Bappa! Ban jira ya sharenin ba kamar yanda nayi tunani na dora da fadin “Wallahi tunda nabiku ta lallama kun ƙi, toh ko zaku kasheni, babu abinda ze hanani auren wanda nake so.....!!!
Gaba ɗaya Idona ya rufe sai zuba rashin kunya nake yi da tsiwa, wasu abubuwan ma da nake fada Ni kaina idan zaka shakeni bazan iya kawosu ba har ya zuwa yanzu da nake baku wannan labarin.
Saida Bappah yaga ba gama na zauna ina kuka sannan yace “toh Shikenan se ki zaba ko mu ko saurayi.......!!!”
Ku gafarceni a bisa tsaya anan da nayi, da kuma rashin samun update na tsawon kwana uku hakan ya samu ne a bisa wani babban dalili, zaku ga wannan page din bashi da tsayi har yanzu banyi free bane bana son na bar masoyan ICEN DAMUNA pending Shiyasa nayi wannan a karba da manage.
Mu hadu a page 18
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
Nagode.......
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 18
A hankali na maida kallo na kan mama, dan so nake naji ta bakinta, ita ma.
Kike kallona, aurennan har dai kikayi shi daidai yake da na sallamawa duniya ke sumayya!!! Ta faɗa da kakkausar murya.
Duk da na tsorata ban nuna ko a fuskata ba.
Juyawa kawai nayi, na koma daki.
Da daddare khaleel ya kira ni, jikina babu ƙwari na daga.
“Hello!
“Meyafaru ammatana na jiki somehow ?
“babu komai kauna!.
Anya kuwa ? Ba haka na saba jinki ba fa.
Da gaske kauna bakomai, na fada da son nuna masa bakomai.
Okay shikenan to! Yanzu Kina jina!? Angama komai na gidan da zamu zauna, babu abinda zaki tafi dashi, nasaka miki komai!!!
Ji nayi wani irin farin ciki ya lullubeni, a lokacin na nemi duk wata damuwata na rasa.
Zagewa mukayi muka ci gaba da shirye-shiryenmu, a waya.
Seda yaji ina hamma yace na kwanta.
Koda na kwanta na nemi bacci narasa, dan neman mafita kawai nake ido rufe.
Har na fara bacci na buɗe idona kaman wadda aka tsikara.
A hankali nasaki kayataccen murmushi.
Baba musa! Yes na faɗa da karfi.
Baba musa yayan baffa ne, a dan batta yake, wajensa zani da maganar nan.
Amman kuma wani hanzari ba gudu ba sumayya! Keda bakya shiga cikin yan uwa, tayaya lokaci daya zakije masa da maganar aure ? Wata zuciyar ta katse min hanzari.
Wata zuciyar kuma tace kije ki gwada sa’arki mana, da wannan tunanin na kwanta a raina.
“Da safe ina ta shi na kira khaleel, nace masa ina bukatar kuɗi, be tambaye ni, me zanyi dasu ba ya turamin.
Da wuri na shirya, ban bi ta kan mama ba, nayi ficewa ta daga gidan.
Sai yamma muka sauka a danbatta saboda motarmu da ta lalace a hanya, daga tasha na hau mashin ya kaini har kofar gidan.
Da sallama na shiga, gaba ɗaya akayi min cha da idanuwana, murmushi na kakalo na fara gaishe da matansa.
Amarya yau kece a garin namu ?
Yaƙe kawai nayi.
Yaran na rarrabawa tsaraba, suma matan na basu kayan dana kawo musu wanda na siya a tasha.
Ruwa aka kawomin da abinci, sedai ban ciba dan bakomai nake ciba.
Baba musa bayanan ?
“Bara akira miki shi” Cewar uwar gidansa.
“Yawwa” na fada da jin dadin sa’ar da na tako ta samunsa dan shima ba mazauni bane.
Uwar gidan ce ta kara katse min tunani ta hanyar fadin “Amman kwana zaki mana ko ?
Murmushi nayi “a’a anty huwaila yau zan koma bazan dade ba.
Amma baki kyauta mana ba idan baki kwana ba, rabonki da gidannan tun kafin a saka ranar bikinki fa ?
Murmushi kawai nayi, hira muka ɗan dinga tabawa sama sama sama har ya shigo gidan.
Tsugunnawa nayi na gaisheshi ya amsa fuskar sa cike da walwala.
Bayan mun gama gaisawa yace Ina ɗan uwana ?
Yana gaisheka baba, ina mamakin kaunar da take tsakanin baba da kawu Musa.
“Aikam ina amsawa!!!.
“yawwa baba Musa Daman wajenka nazo!
Toh toh taso muje ciki!!!.
Babu musu na bisa a baya.
Bayan mun sake gaisawa.
Kawai na fara masa kuka, baba aurena ya mutu, har na gama Idda da sati ɗaya.
Baba wanda aka aura min da farko bana sonsa, ai kun gansa a wajen daurin aure babba ne, kullum seya dakeni, ga cin mutunci, ban taba kai karar saba kawai ina kwance ya rufe ni da duka yace naje ya sake ni saki uku.
Bayan na dawo, jiki na duk tabon duka, amman haka baffa ya rufe ido yace lefina ne.
Yanzu kuma wani ya fito, ze aure ni, yace baze aura min shiba Kuma Wallahi baba ina sonsa. Nan na kwashe karya da karya zalla na fadawa kawu Musa.
Ashsha Abu beyi dadi ba, har yanzu Habu bai dena taurin kai ba kenan ?
Bance komai se kuka dana cigaba da rera masa.
Ni zan daura miki aure insha Allah ki kwantar da hankalinki.
Wata wawuyar ajiyar zuciya ce ta kubce min ban shirya ba.
Yanzu yaushe iyayen yaron zasu zo.
Daman ranar juma’a yace, saboda ba taro za’ayi ba daurin aure ne kawai, ba taro zamuyi ba.
Toh suzo nam zan aura miki shi.
Yanzu bara na shirya muje can Kanon tare.
Duk da na tsorota da zuwan sa, bance masa komai.
Idan ya gano karya nake fa ?
Ai nasan ba zasu taɓa tonamin asiri ba.
Dan kaf dangin mu babu wanda yasan meyake faruwa a cikin rayuwa ta.
******* ********* *********
Bayan mun dawo Kano.
Gaba na yana ta faduwa dan bansan meze faruba.
“Mama tayi mamakin ganinmu tare, kallo na kawai take ni kuma naki bari mu haɗa ido da ita.
Waya tayiwa baffa yazo yana da bako.
Be dade ba ya karaso gida.
Da murmushi ya tarbi dan uwan nasa, bayan sun gama gaisawa, da hiran yaushe gamo.
Baba musa yawo masa zancen daya kawoshi.
Ba shawarar ka zan nema ba, umarni ne dole a aura mata wanda take so Domin ko a addini bamu ga inda akace ayiwa mace auren dole ba, kuma kai ba budurwa ma kake son yiwa auren dole ba bazawara!!
Kaga kuwa abun naka yayi yawa, saboda haka ban lamunce ba.
“Shikenan yaya amman babu saka hannu na acikin wannan auren.”
Duk yanda baba musa yaso baffa ya sakko akan furucinsa ya ƙi sauka ya kafe akan lallai fa shi ba hannunsa a aurena, dole haka kawu Musa ya kyaleshi.
Ki faɗa wa saurayin naki, su zo nan neman auren ki, Ni kuma zan basu insha Allah!
Toh baba na gode, Allah yasaka da Alkhairi.
“Ameen ameen yarinyar kirki tashi ki shiga ciki.
Tashi nayi na shiga daki na barsu suna kara tattaunawa baba Musa yana kara tausar bappa.
Bayan na shiga Daki na kira khaleel na labarta masa duk abinda yake faruwa sannan na fada masa abinda nayi yau.
Farin ciki yayi sosai tare da nuna min abinda nayi shine daidai kuma shine mafita.
********* ********* *********
Ranar juma’a aka daura mana aure da khaleel.
Auren da babu mahaifina a cikin sa, haka kuma babu daddy.
Best ma bata zoba, haka ammie.
Humairah ce take tayani haɗa kayana, tana kuka tana fada min zatayi kewata Ni kuwa ba wannan ne a gabana ba murnar zan kasance da abun sona kawai nake.
Bappa ne ya bankaɗo labule ya leko, “ SUMAYYA tabbas kin nuna min iyakata kuma kin nuna min ban isa dake ba, kin tozartani a idon duniya da idon mijin da kika aura kin nuna musu ban isa dake ba! Bazanyi miki baki ba, duniya ce ta ishi kowa riga da wando, kuma ta ishi bagaruwa jima, sannan ita duniya wanda bai zo cikinta ba ma jiransa take, gari zaki bari yanzu, tabbas ba fata nake miki ba amma zakiga abun da muke guje miki nida mahaifiyarki da duk wani mai sonki. Hakkinmu ma nida mahaifiyarki bazai barki ba. Aure ne tsakanin keda masoyinki yau an daura, kin zama tasa, yanzu saiku kashe kanku dan soyayya. Yana gama fadar hakan ya saki labule ya juya yayi tafiyarsa.
Jikina duk ya mutu, ji nayi kamar na fasa tafiya, duk iskancina nasan idan bappa bai saka min albarka a aurena ba da wuya naga daidai, ina ganin wa’yanda ma sukayi aure da yardar iyayensu yanda auren yake karewa na wannan zamanin bare kuma ni.
Wata zuciyar ce kuma tace to ke meye na damuwar tunda kin auri wanda kike so yake sonki ? Kawai ki dage da kyautata masa da yi masa abinda yake so, in sha Allah bazakiyi danasani ba.
Da wannan tunanin na cigaba da hada kayana.
Washe gari zan tafi zuwa tashar mota inda kanwar Khalil da kuma kanwar mamansa zasu sakani a mota da kuma kaninsa daya abokinsa daya, su zasu rakani wanda a cikin dangina ba wanda ya amsa zai rakani.
Washe gari na fito da jakunkunana, abokin Khalil da kaninsa har ciki suka shigo suka dauka suka fitar min dashi waje.
Mama ce