ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 40

21K to 24K   out of 117.2K words

***** ***** *****

A inda ya turamin address anan nasame shi.

Da murnar sa ya kara so waje na.

Yau dai zan gabatar dake a wajen su mommy na, suga matata insha Allah.

Ya faɗa yana jan hanci na.

Ido na nazaro waje, amman dai baka kyauta min ba shaleleh, yanzu taya zani ni kadai babu best ? na tambayeshi kaman zanyi kuka.

Ba gani ba ? muje kawai ya faɗa yana jan hannu na.

Da sallama na shiga ƙasa kasa, niban yarda ba nazo gidan sirikai.

Tsayawa nayi, ni banyi gaba ba kuma banyi baya ba.

Gidan nake karewa kallo, daga waje gini ne me kyau, amman ta ciki ba’a kammala ginin ba, kuma nidai banga alamar mutane a gidan ba.

Juyawa nayi ina masa kallon neman karin bayani.

Muje mana ya faɗa yana basar da kallon da nake masa.

A’a gida zan koma na faɗa ina juyawa.

Only daman kince min kina da nauyi ko ? toh bara muga.

Chak naji ya ɗagani, da sauri na rike sa dan Wallahi tsoro ya bani.

Ni kasauke ni, na faɗa ina kokarin kwatar kaina a hannun sa.

Dariya kawai yake min be ajiye ni ko ina ba se a wani daki.

Katifa ce kawai a dakin se wasu tarkace dan bansan na meye ba.

Hanyar waje na karayi kawai yasawa dakin mukulli.

Dan Allah ka buɗe min na tafi gida kaji khaleel....!!! na faɗa cike da tsoro.

Ki zauna muyi magana toh, muna gamawa zan rakaki ai.

A nesa da shi na zauna..

Zaki ci gaba da karatu ne? Ko kuma aure zaki yi?

Bansaniba nima! Na faɗa har lokacin a tsorace nake.

Toh nidai gaskiya aure zamuyi, idan kin koma gida kuyi Magana da best.

Jin yayi min maganar aure bansan sanda na nemi tsoro na rasa ba, nasaki jiki munata tattauna yanda abubuwa zasu kasance.

Bansan sanda ya dawo kusa dani ba, seda na jini a jikin sa gaba daya.

Dum! Dum!! Dum!!! Haka zuciya ta take bugawa, tunda nake a rayuwa ta babu namijin daya taɓa rungume ni se shi.

Mutsu mutsu na fara.

Kawai ya ɗago kaina ya hade bakin mu.

Gaba ki daya na fito da idano waje, ga rawa da jiki na ya fara, kaina nake girgiza masa amman be saurare niba.

Ban kara firgita da lamarin ba seda naga yana kokarin rabani da kayan jiki na.

Shalele me kake aikatawa haka ? Ka ƙyaleni Ni ba yar iska bace..... Ina fada ina dukan bayansa ina kuka kira nake ya ƙyaleni na tafi wajen best, ya barni Na koma wajen mama, yayiwa Allah ya barni kar ya cutar dani,! Amma inaaa mutuminnan yayi nisa.

Kiyi hakuri sau daya kawai,

Tashi nayi zan gudu da hannu daya ya dawo dani, Natsaya faɗa muku tashin hankalin da nashiga ma ai bata baki ne.

Bazan iya bayyana muku irin azabar dana sha a hannun sa ba, nayi kukan, nayi magiyar, nayi rokon, duk a banza, nayi cizon da duka, duk basuyi amfani ba, ashe kuka ma rahama ne ?

Nayi danasanin zuwa wajen sa a wannan rana, nayi danasanin gudowa na baro best.

Seda ya dawo hayyacin sa shima ya fahimci aika aikar da yayi.

A hankali ya mike ya debo kayana da ya watsar ya sakamin, bani ma da karfin yin faɗa da shi, ko motsi bana iyawa idanuna suna rufe ruwan hawayen da nake fitarwa ne da kuma ajiyar numfashin da nake a hankali ne zai tabbatar maka da cewa ina raye.

Dan Allah ki..... kallon da nayi masa ne da jajayen idanuna yasa yayi shiru da bakin sa bai ƙarasa abinda yayi niyya ba.

Kokarin mikewa nake amman nakasa kawai na fashe da sabon kuka.

Fita yayi be dade ba ya dawo, bai bi ta kan kukan da nake ba ya dauke ni a hannun sa, har kofar gida a cikin napep ya sani, ya bashi kudin da zai kaini gida drop.

Kije zamuyi waya! Ko kallan sa banba.

#### #### #### ####

Direct gidan su best na nufa, ina ni ina zuwa gida, idan baso nake zuciyar mah ta buga ba.

Da rarrafe na shiga gidan dan bazan iya taka kafata ba, falon babu kowa inda Allah ya temakeni kenan

Na kusa karasa hawa benen ta fito daga daki.

Tsayawa tayi tana kallon ikon Allah ke meyasa baki da hankali ? idan kika faɗa fa ?

Jin ban bata amsa ba yasa ta tsaya tana kallon fuskata, se kuma ta matso a hankali.

Me...ya....sa...meki ? Ta faɗa a rarrabe.

Banza na mata naci gaba da tafiya ta ina hawaye.

Da kyar nakai kai na dakin ta.

Tana bayana tana kallon ikon Allah, tace ina kika tafi kika barni kuma bayan nace ki jirani ??

Still dai ban bata amsa ba na nemi wajen Zama zan zauna, ban san na fasa wata ƙara ba saboda masifaffiyar azaba da ta ratsani, ji nayi kamar ana zubar min dakakkken barkono a ƙasana.

Ina kika je ? Ta jefomin tambayar ne a cikin tsoro mamaki da ɓacin rai duk a tare, magana nake miki daga ina kike ta faɗa tana nufoni fuska a haɗe......

Wallahi seda gaba na ya faɗi na manta wacece ita. Amman yau sak sadiya Abdullahi ta komamin.

Magana nake miki.

Kuka kawai nake amma na kasa Magana.

Kofar taje tasawa key, ta dawo.

Ke fadamin daga gidan ubanwa kike.

Ta faɗa tana jijjiga ni..

Na kasa mata magana dan wallahi tsoro take bani.

Saukar marin danaji ne ya yanke min tunanin da nake. Fadamin ta kara kawo min wani marin.

Kuka kawai na fashe da shi na juya da rarrafe ina neman hanyar guduwa.

Gidan ubanwa zaki Wallahi sekin fadamin inda kika je ta faɗa tana saka kuka, dan ko ba’a fada mata ba ganin yanda nake fama da rarrafe tasan dole wani abun ne ya faru.

Wajen khaleel!!! Na faɗa cikin gunjin kuka.

Chak kukan nata ya tsaya, Ni kuma nawa ya karu.

Wa....wa....ye kha..leel kuma!?

Ta tambaye ni kaman me koyan magana.

Shiru namata na ci gaba da kuka na.

Seme ya faru kuma, ta kara tambaya ta a sanyaye.

Kasa ce mata komai nayi se kasa da nayi da kai na.

Bata karamin magana ta shiga toilet, bata jima ba ta fito.

Kiiiii haka ta jani kaman kayan wanki, ina ihu ina ce mata zafi amman bata bi ta kaina ba.

Towel ta miko min bance mata komai ba na juya ina cire kaya ina kuka.

Kiiiii ta kara jana, wai kashe ni zakiyi ne, na faɗa ina kara samata kuka.

Menene Amfanin rayuwar ki ta mayar min a zafafe.

Shiga! Hannu na nasaka a ruwan da sauri na janye, A kara ruwan sanyi, na faɗa ina tsiyayar da hawaye.

Bansan ya akayi ba nidai kawai tsinta ta nayi a cikin ruwan a zaune an jefani kamar kayan wanki.

Duk yanda nayi kokarin fitowa Na kasa Dan da mugunta ta danneni a ciki.

Nariga na saddakar daman se abun da nagani kawai.

Seda ruwan ya huce ta fita ta bankomin kofar tashi nayi da kyar nayi wanka.

A zaune na sameta ta zabga uban tagumi tana kuka kaman ance mata ammie ta mutu ko daddy.

Ina zama kusa da ita tashi ta koma kasa ta zauna.

Na kara matsowa kusa da ita, kawai tabar min dakin ma gaba daya.

Na dade a zaune cikin tashin hankali, kuka, damuwa, bakin ciki, tsoro, ɓacin rai, Kai da komai ma, sannan kuma ga fushin da best ta ɗauka dani.

A tare da hakan kuma banji na tsani khaleel ba, saima jin cewar bazan iya rayuwa ba idan babu shi. Saidai inajin haushinsa na rokon da na dinga masa amma yaƙi saurara min. ( Saboda sakarci irin nawa )

Magani da ruwa ta ajiye min.

Ta koma ta ci gaba da kukan ta.

Bansan me tacewa ammie ba se gata tana min sannu, kaman dai bani da lafiya.

Shiyasa nake hanaku guje guje, ai gashinam yanzu kin gurde Kafa.

Sannu Allah ya kiyaye gaba.

Ameen nace ina kallon ta.



“Seda nayi lafiyayyar jinya ta sati 1, waya ta tun ranar ban kara kunna ta, saboda kiran da yake min da test din ban hakuri.

Ga baki daya ta fita daga harkata, bata min magana, bata zama inda nake Har tsoron yi mata magana nake, saboda tamkar me jiran kirissss yanzu zata hauni da masifa.



##### ##### #####

“Wayata na kunna, kaman me jira, ina kunnawa kiran sa na shigowa.

Ji nayi kawai ance Bani wayar.......!!!!!!!!!!!

Kash ku dakaceni anan domin jin waye ya karbi wayar sai ku bini a page 11.

Kuyi hakuri a bisa gajerun pages da nake muku yanzu hakan ya samo asali ne saboda busy din da nayi kwana biyu bana samun damar typing sosai amma in sha Allah na kusa yin free zaku dinga jin dogon typing.... Nagode taku har kullum Rabi’atu Fulani.....

💫

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 11



“Bani wayar!!!” sadiya ta kara maimaita wa a dake.

Me.... za...ki....yi da ita ? Na tambaya cikin rawar murya.

Zanci kan uw**ar wanda yake kiran kine! Ta faɗa kaman me shirin yin dambe.

Ayya best be kamata ki zageshi bafa.

Sakin baki kawai tayi tana kallo na.

Da kyau! Rama masa, nace ki rama masa! Ta faɗa tana yowa kai na.

Baya naja ina hararar ta,

Waike sau nawa zance miki banasan dambe ne ?

Na faɗa ina son kautar da maganar.

Kinsan wani abu ? Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Duk wanda naji na tsane sa, bana kaunar sa, kina tare da shi to tabbas cutar dake yake yi. Shiyasa tun a kallon farko naji na tsane shi, Kuma ko yanzu dolen ki ki rabu da shi ɗan iska mai zubi da aljanu kawai....!!! Ta faɗa a harzuƙe

Bazan iya rabuwa da shi ba, na katse ta cikin kuka.

Har yanzu babu abinda ya sauya a soyayyar da nake masa ina masa soyayyar dani kai na bansan adadin ta ba, Ina sonsa da gaba dayan zuciya tane.

Kwanakin nan da nayi ba tare dajin Muryar saba Ni kadai nasan halin da nake ciki Bana cikin farin ciki best saboda farin ciki na yana a tare da nasa, dan Allah ki barni dashi zanyi farin ciki best!!! Kuma Nasan zaki so farin cikina kema. Na faɗa cikin gunjin kuka.

Tsantsan mamaki ne ya hanata magana.

Kinsan illar daya miki a cikin rayuwar ki sumayya ???

Ya bani hakuri fa, kuma yace beta ba se akai na, nima dan yana sona ne, Sannan aure na zeyi.

Kanta kawai take girgiza wa tana hawaye ka cuce mu khaleel yau shekarar ku biyu, ko kofar gidan ku Beta ba zuwa ba, kuma kike tunanin ze aure ki ?? idan har kina mafarkin ze aure kine, ki farka, dan baze taba auren ki ba, koda kuwa matan duniya sun kare!!!

Ya isheki haka na faɗa cikin tsawa! Daman nasan ba sonsa kike ba dan haka babu abinda ze hanani auren sa, Kisani ina sonsa, kuma ban taba sonsa kasa da yanda zanyi rayuwa ba tare da shi ba.

Banjira cewar taba na juya ko kaya na ban diba ba na tafi gida.

Ban taba ganin nisan gidan mu daga gidan su ba se ranar, tafiya nake ina kuka, har gudu nake, tamkar mahaukaciya.

“Ko sallama babu ina zuwa na faɗa kan mama ina sakin sabon kuka.

Meyafaru ? Ta faɗa tana riko fuskata.

Mamah ina son khaleel sosai! Mamah taba zuciya ta kiji yanda take bugawa. Wallahi mama idan ban aure shi ba zan iya mutuwa, Na faɗa ina kara rungume ta.

Bata hanani kukan ba kuma bata rarrashe niba, A haka nayi bacci a jikin ta.

Gyara min kwanciyar kawai tayi tana shafa kaina.

Bacci nake amman se ajiyar zuciya nake sauke wa.

Humaira! Ta kwalla mata kira.

“Na’am mama gani!

Kinsan khaleel din da sumayya take so.

A’a amman dai inajin suna waya wani lokacin Wani abu ya faru ne ?

Babu komai, je kici gaba da abinda kike.

Tunda na dawo gida bana iya cin abinci, bani da aiki se kuka.

Ina ganin kiran wayar best amman bana dauka kaman yanda shima bana daukar nasa kiran duk da yanda zuciya ta take azalzala ta dana ɗauka.



**** ***** ***** *****

Ina kwance kiran sa ya shigo waya ta, seda ta kusa yankewa na daga.

Shiru nayi, dana daga

Sallama naji anyi daga can barin kuma ba muryan sa bane.

A hankali na amsa.

Dan Allah ina Magana da sumayya ne ?

“Eh itace”

Kina Magana da abokin khaleel ne, daman wajen sati biyu yana asibiti, kuma sunanki kawai yake kira, dazu aka sallame sa, shine nace bara na kira ki.

Bansan sanda na tashi zaune ba ina tambayar sa meyasa meshi ?

“Ina khaleel din bashi wayar!”

Gaskiya baze iya amsa waya ba a halin yanzu.

Yana ina na ? faɗa jikina na rawa dan Allah yana gani hankali na ya tashi.

Zan tura miki address din da yake sai kizo ki duba shi!!!

Ba tare da dogon tunani ba, na tashi na shirya ko mama banwa sallama ba na fice daga gidan.

“Koda naje ban damu da tsayawa duba ina neba nidai kawai burina na ganshi.

Number dakin daya turamin na tambaya, aka nunamin bene na hau.

Ina zuwa nayi knocking,

Banjima a tsaye ba aka buɗe.

Da sauri na karasa kusa da shi na yaye bargon daya rufa, khaleel na faɗa ina rike hannun sa.

“Khaleel!” Na kara faɗa ina dora hannuna akansa.

Dayan hannun nasa yasa ya ɗago ni, meyasa kuka baya miki wahala ne ammatana ?

Ko bakisan hawayen ki daraja ne dasu ba ?

“Duk sanda naga kina zubda hawaye anan nake jin zafin”.

Ya faɗa yana nuna saitin zuciyar sa.

Wani kukan na karasa masa me ya sameka ?

Kin dena kulani! Bakya daukar waya ta!! Ya kike so nayi !? ya faɗa kaman shima ze saka kukan,

Nabaki hakuri bazan kara ba kuma naga ma kedin mallakina ce ko kuma wajen wata kike so naje ?

Da sauri na girgiza masa kaina dan wani irin kishi ne ya tasomin.

Toh kin gani! Amman kiyi hakuri insha Allah bazan kuma ba!

Shikenam ya wuce meyake damun ka ?

Marata ce take ciwo ya faɗa yana kai hannu na kan marar tasa.

Da sauri na kwace hannu na ina zare ido.

Matsoraciya ya faɗa yana wani malalacin Murmushi.

Murmushin nima kawai nayi.

“Ina best ? Ya tambayeni still hannunsa cikin nawa.

“tana gida”.

Ina fatan batasan meyafaru a tsakanin mu ba ? dan sirrin mune wannan Ni dake kawai ba best.

Ya tambaye ni yana tsare ni da idonsa.

Kaina kawai na gyada masa.

Kokarin mikewa yake, ya koma da sauri yana sakin kara.

Bansan sanda na hau gadon ba ina tambayar sa lafiya ?

Mutuwa zanyi only, marata zata fashe ya faɗa yana runtse ido alamun yana jin jiki.

Toh kasha magani mana na faɗa idona na cikowa da hawaye.

Kece maganin ai, ya faɗa yana kallo na.

Ni kuma na tambayeshi da mamaki.

Eh! Toh mezan maka?

Bakomai bazaki iya ba, ya faɗa yana juyamin baya

“Ka fadamin mana”.

A’a ki barsa..

8 / 40