Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
da bappa ya daura min.
“Sosai mama tayi farin ciki da yanda doctor yake kula dani, dan yanzu babu abinda muke siya a asibitin, Da Abu ya kare ze kawo.
“ Wata irin shakuwa ce tsakanin sa, da mama..
Har ranta take jinsa, tama dena ce masa doctor, sedai ɗana...
Humaira kuma yaya sama yaya kasa.
A takaice dai ya zama kaman dan gida a wajen mama dan kuwa sukan zauna suna hira sosai yana bata labarurruka da suka shafi aikinsa da kuma labaran duniya, haka zaka dinga jiyo dariyar humairah idan suna hira,
*** **** **** ***
“Zuwan shi kenam ya tawo waje na.
Sedai yanda ya same nine beji dadi ba.
Na hade kai da gwiwa ta ina kuka tamkar raina ze fita.
Buzuwa!!!
Ɗagowa nayi ina goge hawaye na, amman wasu ne suke kara zubowa....
Kujera ya dakko ya zauna...
Meyafaru ? Meyasa meki ? Wani waje yana miki ciwo ne ??
Gaba daya ya gigice se jeromin tambayoyi yake.
Shiru nayi masa dan ban san wace tambaya zan fara amsa masa ba!
Duk yanda yaso yaji abinda ke damuna hakan ya gagara dan na kasa tsayar da hawayen da yake zuba a Idona.
Nasiha ya shiga yi min da kalamai masu kwantar da hankali, ban san sanda bacci ya daukeni ba.
Bayan yaga bacci ya daukeni ya zauna yana kallona na tsawon lokaci kafin ya tashi ya fita daga ɗakin a lokacin mama suna zaune a reception saboda ba’a barin mutane su zauna a dakin majinyata idan rana tayi bari ma mu da muke daki na musamman gudun kar a damemu tunda bama son surutu da hayaniya.
Koda ya fita tunani yake akan meyake damuna.
Nayi karama da shiga damuwa irin haka, insha Allah zan taimaka miki ki fita daga damuwar nan buzuwa!!!!
A hankali kuma ya fara jan ra’ayi na akan na faɗa masa damuwa ta.
Kusan sati biyu yana bibiya ta akan hakan.
Amman na kasa, tayaya zan iya faɗa maka sirri na. Doctor ? na tambayi kaina!
Ina zaune na kafe waje daya da ido naji maganar sa akaina.
Buzuwa! Ɗagowa nayi ina kallon sa.
Becemin komai ba ya juya ya tafi.
Tun daga ranar ban kara ganin doctor ba.
Nurse ce me zuwa ta bani magani da allura.
Gaba ki daya na damu da hakan, ban san na saba da shi ba sai a lokacin, wajen sati daya be kara zuwa ya dubani ba.
Na tambayi nurse yana ina tace min kullum yana zuwa,
Har best nace taje ta kira min shi, Yace mata gashinan!
Amman bai zo ba.
Washe gari da safe, ina zaune na hangosa, ya shigo ɗakin, da sauri na tashi zaune ina murmushi.
Ya jikin ki ? Ya tambaye ni babu walwala a fuskar sa.
Jiki na a sanyaye nace masa da sauki.
Yana zuwa yamin allura, ya bani magani, amman babu sakewa a tare da shi kaman da.
Dan Allah kayi hakuri!!!
Na faɗa ina sunkuyar da kaina ƙasa.
Kinyi min wani abu ne ?
Rasa me zan ce masa nayi, sai hawaye da na fara.
Ki sani na daukeki ne tamkar kanwata, babu shawarar da bazan iyayi dake ba, Duk da cewa kedin yarinya ce.
Amman inajin ki tamkar jini na.
Meyake damunki ?
Kaina nake girgiza masa alamun babu komai.
Shikenan ki sani daga yau bazan kara tambayar ki damuwar kiba.
Nan da kwana biyu zan baki sallamah, Yana faɗa ya juya zai tafi.
“Kayi hakuri Yaya Zan faɗa maka damuwa ta, amman dan Allah kadena fushi dani na faɗa a hankali, cikin kuka.
Bai saka rai da zan faɗa masa haka ba.
A hankali yasaki murmushi, Shikenan zan samu muyi magana.
Bance masa komai ba har ya juya ya tafi.
Yau mama a gida zata kwana saboda angel bata da lafiya, Seda sukayi sallama da doctor, ya rakata titi Sannan ta tafi.
Best ce a tare dani tare zamu kwana.
Tana zaune a reception kafin likita yazo ya bamu magani sannan ayi shara ace su shigo.
Ina zaune ina tunani kaman yanda nasaba, naji maganar sa a saman kaina.
Wai yaushe zamu dena tunanin nab ne ?
A zuciya ta na ayya na ranar da zuciya ta, ta mallaki abinda take so.
Kujera ya ja ya zauna.
Beyi magana ba nima haka tsawon lokaci.
Meyasa kake son sanin damuwa ta ? Na tambaye shi, ina tsare sa da idanuna
Saboda bazan juri ganin ƙanwata a cikin damuwa ba, kin san ina miki kallon ƙanwata ta jini ? Yanda bazan ga ƙanwata cikin damuwa nayi shiru ba kema hakane, na damu dake ne shi yasa na damu da jin damuwarki, amma idan baki daukeni dan uwa bane har kike jin bazaki iya fada min damuwarki ba to karki damu. Ya fada da wani murmushi wanda kana gani kasan iyakacinsa saman lebe.
Zan faɗa maka !!!!! Na fada a sanyaye sannan na rufe idanuna wasu hawaye Masu ƙuna suka fara zubo min.
“ *ASALIN LABARINA*”
Sunana sumayya Abubakar mai nasara! Nidin haifaffiyar kano ce.
Mahaifina cikakken bafulatani ne.
Mahaifiyata buzuwar nijar ce, bata da kowa a garin kano.
Mu 4 dine a wajen iyayenmu
Ni Sumayya, humaira, salim, auta Fatima zhara, bappanmu ɗan kasuwa ne na kayan gwanjo a kasuwar wambai.
Farin ciki nake tayi yau zan shiga secondary school, jss 1.
Tun daga bakin get ta ganni, ni ban ma ganta ba, da gudu ta karasa ajin su.
Kuzo kuji ta faɗa tana haki, tsabar gudun da tayi, an kawo wata makarantar nan yau,
Kunga idon ta ?
Ta tambaye su tana kifkifta idanu.
A’a suka haɗa baki wajen faɗa.
Kuna ganin idon ta kunsan bata da kunya, kuma ba irin na mutane bane, Nasan kuma ajin mu za’a kawo ta.
Waya faɗa miki ? Wata a gefe ta tambayeta.
Zaku gani dai!! Ta faɗa da kwarin gwiwar abinda fada.
“Bayan interview da akayi min aka miƙani JSS 1A
Da sallama na shiga, kaman nasan jira na suke fuskata ko alamar fara’a babu.
Can karshen ajin na tafi na zauna.
Tunda na zauna suke kallo na, ban shiga harkar kowa ba.
Bayan wani lokaci nayi kasa da kaina ina rubuta sunana ajikin littafi, naji magana a saman kaina.
Ke ya sunan ki ?
Banza namata.
Harta kara maimaita wa.
Sannan na ɗago.
Doguwa ce siririya wankan tarwaɗa
Ina gama kallon ta na maida kaina na cigaba da abunda nake, Littafina ta dauka
“Sumayya Abubakar mai nasara!”
Kara ɗagowa nayi kawai ina hararan ta.
Fita tayi daga ajin, bata dade ba ta dawo, ita da malami.
Sunaye naji ana kira, duk wanda aka kira ya fita gaban allo.
Sumayya Abubakar mai nasara! Da mamaki nadago.
A hankali na fito.
Kune masu surutu idan malami baya aji kenan ?
Malamin ya tambaya yana juya bulalar hannunsa.
Juyawa nayi ina kallon ta, se a lokacin na kula da dankwalin kanta baki ne, ba fari ba.
Bulala biyar biyar yake yi.
A rayuwa ta banasan duka, saboda koya aka dake ni sai yayi min tabo a jikina.
Malam nifa karya take min banyi surutu da kowa ba, na faɗa ina matsawa baya.
Monitan kike cewa tana miki karya ?
Ya tambaye ni yana matsowa inda nake.
Kara matsawa nayi,
Kika ƙara taku daya bulalarki ta koma Goma” ya faɗa yana haɗe rai dan yaga abun nawa yana niyyar zama wasa.
Haka yazo ya min bulala biyar a kafa.
Sannan yace ta kara rubuta wa ya juya ya fita.
Yana fita na janyo hijabin ta, na shaƙeta hadi da cewa “Dan uwar ki yaushe nayi surutu ?”
Na tambaye ta ina zare mata ido.
Badai uwata ba sedai taki ita ma ta faɗa tareda kama wuyana itama.
Faɗa ne ya kaure a tsakanin mu da kyar a ka raba mu.
Har aka tashi da mun haɗa ido zan harare ta ko kuma na mata daƙuwa.
Koda na koma gida mita nake tayi.
Harda mama ta gaji tace kona yi shiru kota make ni.
Muna zaune baffa ya shigo gida ya zabga tagumi.
Lafiya Bappansu ? mama ta tambaye sa, tana ajiye masa ruwa.
Lafiya alhamdulillah kawai kwana biyu kasuwar sai godiya abubuwa duk sun tsaya cakk!!! Ya faɗa yana sauke tagumin.
Allah ya shiga cikin lamarin cewar mamah tana zama kusa dashi.
Ameen. Ya amsa tare da kalloni.
Ke ya makarantar ?
Ba lafiya na faɗa ina matsowa kusa da shi.
Wlh baffa wata mara mutunci ce monitanmu......
Be bari na kara saba ya katse ni.
Kadai bazaki hankali ba, har kin fara faɗa da mutane ko ? Ya tambaye ni yana tsare ni da ido.
A’a na faɗa ina Turo baki, ni haushina ma bai bari na karasa labarin ba.
Washe gari dana je makaranta da shiri na, na tafi, dan Wallahi mugun jin haushin figaggiyar yarinyar can nake ji..
Aikam tana shigowa nataso nazo wajen ta.
Banza me kama da yan China.
Ke kuma me idon mage, ta faɗa tana rike kugu, da alama itama a shiryenta tazo.
A rayuwa ta na tsani a faɗa min haka haushi nake ji.
Zanyi magana malami ya shigo dole na hakura na kyale ta.
Tun daga wannan ranar kullum se naja ta da faɗa hankali na yake kwanciya.
**** **** **** ****
Yau tunda nazo nake jiran ta tazo muyi faɗa Amma shiru bata zoba, duk nabi na damu..
Ranar gaba ɗaya jiki na babu ƙwari, washe gari ma bata zo da wuri ba.
Idanunnan sunyi luhu luhu alamun kuka.
Har aka fita break bata da niyar fita.
A haka naje nayo siyayya na ajiye a kusa da ita.
Malama muci na faɗa ina ɗauke kai na.
Bazan ciba, itama ta faɗa tana kauda kanta.
A hankali na rike hannun ta, meyasaki kuka ? Na tambaye ta jiki na a sanyaya.
Shiru tayi tana tunani, can kuma tace ammie nace bata da lafiya, ta faɗa tana kuka.
Kiyi hakuri zataji sauki kinji.
Na faɗa da tausayin ta fal raina.
Kai kawai ta gyada min, ya sunan ki ? Na tambaye ta.
Baki san sunana ba ? Ta tambaye ni da mamaki.
Dole sena sani na faɗa ina harar ta.
Yar dariya tayi tace “Sadiya Abdullahi.
Tun daga Wannan ranar muka dena faɗa, a hankali sabo ya fara shiga tsakanin mu da ita.
Tana da kirki sosai, amman akwai jan faɗa, tana kaunar faɗa, koba da ita ake ba yanzu zata ce ta siyi faɗan. Bata da tsoro ko kaɗan.
Ni kuma bani da faɗa sedai tsokana, Ga ɗan banza tsoro.
Ta ɓangaren baffan mu zan iya cewa komai ya tsaya masa cak, kasuwa ta dena Gara masa, saboda ana weather na zafi kuma kayan sanyi yake siyarwa, ahaka jarin ake dan tabawa ayi cefane to shima yanzu ya janye.
Allah yasa dama mama na yar sana’arta a gida toh shine rufin asirin mu a yanzu..
“Wani irin sabo da shakuwa ne ya shiga tsakanin mu da sadiya, duk inda kaje a makarantar kace yan biyu to mune nida leemah wacce na daina kiranta da sunan da mutane suke kiranta dashi ( sadiya ) Nice kawai nake ce mata leemah.
Ita kuma tana kira da
*”Buzuwa”*
Gaba daya sunana ya bata a makaranta idan bakace buzuwa ba, baza’a taɓa ganeni ba.
Kwanci tashi a sarar me rai yau gamu muna zana jinior candy.
Mun gama exam lafiya se jiran sakamako.
**** **** **** ****
Zaman gida baya min dadi ko kaɗan, rayuwar gidan mu gaba daya ta canza kaman ba ita ba.
Wata kalan rayuwa muke da bansan akwai ta ba duk da bakomai nake fahimta ba a lokacin.
Assalamu alaikum jama’ar gidan nan, Na shigo kona koma ?
Ta faɗa daga soro tana dariya.
Kar kishigo inji mama ita ma tana dariya.
Da sauri ta shigo
Allah mamah kin dena sona ta faɗa tana bata rai.
Toh kece haleematu bakyaji wani lokacin.
Ni dai shikenan ta faɗa tana kwalamin kira.
Buzuwa! Yar buzuwa ta!!!
Mamah batanan ne ?
Ta faɗa tana nufo dakin da na buya.
Dallah fito kiji, ta faɗa tana janyo ni.
Jarabawar mu ta fito yanzu zamu shiga ss1, shikenan mun zama yan mata ta faɗa tana tsalle.
Biye mata nayi sannan muka zauna tsara yanda zamu dinga yi tunda mun zama yan mata yanzun.
Haka muka gama shirmen mu sannan muka rabu.
Ranar Monday muka shiga SS1.
Makarantar mu muka koma bamu canza wata ba, sedai ba yan ajin mu na jinior ne a ajin muba,
Amman dai nida kawata muna tare.
Alhamdullah zance dan lafiya lau muka gama ss1.
Zuwa lokacin zan iya cewa dagaske mun zama yan mata.
“Ranar hutu na fara ganinsa a assembly..
Yana tsaye ya juya baya yana waya.
Dogo ne sosai, irin Giant dinnan....
Bansan meyake jan hankali na akansa ba.
Amman time_to_time sai Najuya ina kallon bayan sa.
Ina cikin kallonsa ya juyo yana wayar,
Karaf idanunmu suka sarƙafe a cikin na juna.
Wata irin muguwar faduwar gaba ce ta same ni a lokacin.
Nakasa dauke idona akansa.
Zuciyata sai tambayata take Wanene wannan ?????
Waye shi ?
Meye wannan nake ji a game dashi ?
Meyesa naji faɗuwar gaba da na kalli cikin idonsa ???
Mu hadu a page 07 domin samun amsar tambayoyin da Ni kaina ban san amsarsu ba a lokacin!!!!!!!
Taku har kullum Rabi’atu Fulani
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 7
Wanene kai ? na kara tambayar zuciyata meyasa zuciya take bugawa da karfi ??
Ke!!! Ta faɗa da karfi tana jijjiga ni, me kike kalla haka ?
Babu komai mutafi tun dazu angama, na fada da son basar da zancen
Mun fara tafiya na kara tsayawa cak na juya, Shima ni yake kallo.
Muna tafiya tana tamin zuba banma san me take cewa.
Wai uban me kike tunani ta faɗa tana mintsini na.
“Babu komai.
Har muka rabu bata karajin baki na.
Da sallama na shiga dakin mama.
Aunty sumy yanzu da kun koma hutu Shikenan kun zama yan SS2 ? Ta tambaye ni cike da ɗoki.
Tsaki kawai na mata ban bi ta kanta ba naje na zauna.
Meyafaru ? Mamah ta tambaye ni, tana ƙaremin kallo.
Babu komai na faɗa ina kwanciya.
Bacci ne ya fara ɗauka ta, kamar a mafarki na fara ganin idon sa cikin bacci na.
Da sauri natashi zaune, baccin da banyi ba kenan.
Da daddare ma haka na nemi bacci narasa, duk juyin da zanyi tunanin sa ne kawai zai zo kaina.
Ga baki daya narasa walwalata, bani da nutsuwa, nakasa sakewa a hutun nan.
Mama tayi tambayar har ta gaji.
Ina zaune nayi tagumi abin duniya ya ishe ni.
Natashi da sauri..
Mama! Mamah!! Mamah!!!
Wai bana hanaki yimin kiran nan ba ? Ta tambaye ni cikin faɗa.
Baya nayi ina tura mata baki, Ni gidan ammie zani.
Ki bari nayi wanka sai muje.
Toh, kawai nace.
Bata dade ba ta shirya muka tafi har humaira.
Ammie! Ammie!! Ammie!!!
Ya rabb zaki firgita ni, daga ke har waccan yayar taki kuta kiran mutane kaman makafi haba....!!!
Toh ni ba kewan ki nake ba, na faɗa ina tale baki kaman me shirin saka kuka.
Naji zonan, ta faɗa tana janyoni.
Da sallama mamah da humaira suka shigo gidan.
Ta amsa fuskar ta cike da fara’a,