ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 40

48K to 51K   out of 117.2K words

/>
Se lokacin tabari ya dauke ta.

Ganin yanda duk su mamah suke kallon tane yasa tayi kasa da kanta.

A takaice dai kukan rashin sashinta take, a kusa da ita.

Mama itace zata zauna da ita.

Bayan sun dawo gida a daren baban baby yayi mata huɗuba.

Ya haneep! Daman ina son magana da kai dan Allah, akan sunan da za’a sakawa babyn.

Nariga nayiwa yarinya ta huɗuba da sunan daya dace!!!

Yana faɗa ya bar mata ɗakin.

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un! Haneep anya kasowa kanka zaman lafiya kuwa ?

Biyo sa tayi, a hankali tana kiran sunansa.

Cikin shan kamshi yake kallon ta.

Jikin ne?

Wane irin jiki ina maka magana akan sunan yarinyata, kana cewa kasa mata sunan daya dace.

Wane suna ne ya dace da ita bayan.....

Katseta yayi “Kinga dan Allah kiyi hakuri kije ki zauna ki huta Madam!!!.

Mamaki, takaici da bakin ciki duk su suka hanata magana a lokacin.

Se bayan sa data bi da kallo kawai.

Ashe za’ayi yakin da ba’a taba yinsa a gidan nan ba.

Lallai Kashirya yin fito na fito da sadiya Abdullahi Wallahi!!!!!!!

Alhamdulillah a yau na kawo karshen page 20 sai kuma mun hadu a page 21.

Ayi min hakuri a bisa ganin short pages da ake yanzu hakan ya samo asali ne dalilin target din sabon littafina da nake yi mai suna ( Aliyu Zaki ) wanda in sha Allah zuwa new year First Jan zamu fara posting nasa, tare da dan uwa Ubeera, littafin zai kasance Paid Book ne.

Ga kadan daga tallansa.

💫

ALIYU HAIDAR ( THE LION

🦁

)

💫

Paid Book...

By

Rabi’atu Fulani....

&

Ubeera.....

Happy New Year Update......

A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.

Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.

Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.

Seda ya sauke ajiyar zuciya.

Sannan yace only! Bansan taya zan fara tunanin rayuwa babu ke ba, wallahi ina sonki sosai fiye da yanda tunani zai kawo a rai!

Murmushi ta masa, “ka kwantar da hankalinka lovely babu abinda ze faru insha Allah sai alkhairi.

Bai ce komai ba kawai yayi murmushi, yana jin wani masifaffiyar kaunarta tana ratsa bargo da jijiyarta.

Hira suka cigaba da yi mai daɗi wacce kai kana jin yanda suke tattaunawa zaka san yanda masoya biyun suke bala’in son junansu!!!

Hira suke cike da nishadi da farin ciki a tare da su.

Chan dai ya kira sunan ta:

“Only!

“Na’am my champ” ta amsa masa cikin wata kasalalliyar murya wacce Saida ta kara kashe masa jiki, duba da irin yanda ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.

“Kina ganin yara nawa Yakamata ace Mun haifa idan muka yi aure ?

Saida ta dan yi jimmm kafin tace “uhmm yara nawa kake so to kai ranka ya daɗe ? Ta maida masa da tambaya.

Saida ya danyi jimmm kafin yace Ni gaskiya ban wani cika son yara ba, saboda bana son hayaniya kamar yara biyu ko uku sun isa.

“Angama ranka ya daɗe... Zaɓinka shine zaɓin Ma’eesha!

Tsara zaman aurensu suka cigaba da yi da yaran da zasu haifa sunayensu da inda zasu zauna da karatun yaran da komai.

Wayarta ce tayi ringing.... Bloody taga an rubuta da manyan baƙi, batare da ta daga ba ta kalleshi tace special lecturer ya shiga yanzu, naga Maryam ta kirani.

Kamar ƙaramin yaro haka ya taɓe fuska, saboda gaskiya bai ji daɗin katse musu hira da akayi ba.

“Ayyyahh Babe am! Zamuyi waya ai anjima, kuma kaga lecturer dinnan bashida kirki sannan test zaiyi mana bana son nayi missing.”

“Shikenan muje na taka miki zuwa bakin theater ɗin.

Suna tafe suna hira irin ta masoyan da suka shaku da junansu, har suka ƙaraso bakin theater ɗin, yayi mata sallama ya juya wajen motarsa yaja ya tafi tana daga masa hannu.

Saida taga yayi nisa sannan ta juya ta shiga theater ɗin.

Tana shiga Maryam ta harareta “Juliet ai da karki shigo ki tsaya sai malam yazo” ta karasa maganar tana harararta.

Kafin tayi magana malamin ya shigo dole taja bakinta tayi shiru kafin ya korata waje tayi asarar test din.

******** ******* *******

Kallonsa take cikin tsana me ƙarfi kafin tace:

“Haidar wallahi na tsaneka bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, tun kwanaki nake fada maka haka baka gane ba, wallahi idan zaka zo kofar gidannan namu sau dubu kalmata bazata taba canjawa ba.

Tana gama fadar haka ta juya zata shiga gida, taji ya riko hannunta.

Tana juyowa batayi wata-wata ba ta daukeshi da mari tare da nuna shi.

This is Last Warning, karka sake dora kazamin hannunka koda a jikin hijab Dina bare a jikina idan ba haka ba zakayi nadama wacce batada iyaka!!

Zubewa yayi a kasa a gabanta batare da ya saki hannun nata ba, shadda ce Getzna a jikinsa fara karr da ita, ɗinkin tazarce amma hakan bai dameshi ba, bai ma san da ya zube a gabanta ba.

“Ina rokonki da girman Allah dan girman soyayyar da kike min, badan halina ba, Karki rabu dani....!!” Hawaye ne ya fara zuba a idanunsa wanda ya tilasta masa yin shiru.

Kallonsa tayi da wani murmushi a fuskarta sam babu alamun tausayinsa a idanunta.

“Waye ya taba ce maka ina sonka ? Wace soyayya ce haka a tsakaninmu da har kake haɗani da girmanta ? Haidarr!! Shin zaka iya fada min lokacin da Ni da bakina na furta maka cewa ina sonka ? Kai yanzu kana tunanin akwai mutumin da na tsana a duniya sama da kai ? Ka manta duk abinda kayi min ta hanyar lalata min jiyata ? Kuma saboda yanzu hankalinka ya gushe har kake tunanin cewa zan iya mantawa na fada soyayya da kai ? Kayi kuskure saleem! Idan duk maza sun kare a duniyar nan babu abunda zai saka ni Humairah na fada soyayya da kai! Wannan shine last warning din da zanyi maka, koda wasa karka sake zuwa kofar gidannan idan ba haka ba zan yi maka wulakancin da har ka mutu bazaka manta dani ba!!!

Tana fadar haka ta juya ta shige gida tana tushe bakinta saboda kar kuka ya kubce mata, kukan da take kokarin yi ba wai na rasa saleem bane ko wani abu, face na tuna irin wulakanci da tozarcin da saleem da iyayensa suka yiwa abbanta da kuma ita.

Har yanzu ta tuna sai taji hawaye sun cika zuciyarta......

Shin wane laifi haidar yayiwa Ma’eesha da har tayi masa wannan mummunar tsanar ??

Shin wane wulakanci iyayensa suka yiwa mata iyayen da yasa bazata iya yafe masa ba ??

Shin me ya juya wannan zazzafar soyayyar da suke wa juna zuwa kiyayya ??

Shin Ma’eesha zata janye maganarta ta kin auren haidar ta dawo ta aureshi ?

Shin haidar ya rasa Ma’eesha ne har abada ??

Shin waye haidar ??

Shin wace Ma’eesha ??

Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion

🦁

)

Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.

Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.

Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.

Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.

Goyon bayanku muke bukata.

Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.

Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......

Nagode

🥰

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 21

Duk da yaji furucin nata be juyo ba, sema murmushi da yayi kawai.

Toh ni kuma wace kalar sadiya ce bansaniba a tare dake love.

Uwar baby fa ta hana me gida zaman lafiya da kuka.

Mama kanta ta gaji da wannan kukan da take.

Kuma ta tambayeta me aka mata tace babu komai.

Taya zan faɗa miki mamah, sunan sashina nake so yasa kawa yarta, amman yana cewa yayi mata huɗuba da sunan daya dace.

Kawai seta kara saka kuka.

Nikam haleemah idan mutum ya haihu hankali yake amman kedai naga alamun bazakiyi ba.

Bakinta kawai ta turo gaba taci gaba da kukan ta.

Kullum cikin yiwa haneep kuka take da takura masa akan sunan baby, saidai yaƙi yarda ma ya bata haɗin kai kullum sai zolayarta yake ya maidata kamar wata kwarkwar.

Tace ita ko ba komai ya faɗa mata sunan daya sawa yarinyar amman yaki.

Kememe tace baza tayi tayi taron suna ba.

Anyi rarrashin amman ta tubure bazata yiba.

Ana gobe suna mama ta zauna da ita ta dinga nuna mata abinda take son bata kyauta ba, tunda mahaifin yarinya yanada halin daukar dawainiyar suna kuma yaji ya gani bai kamata ace ita ta watsa masa da kuma dangi ƙasa a ido ba. Da kyar mama ta shawo kanta ta amince zatayi taron sunan.

******** ******** ********

Hankalina gaba daya yana gida, tunani nake ta ya zan samu waya nayi waya da gida ? Kawai na yankewa kaina idan yayi bacci na ari wayarsa tunda ya hanani tawa, idan yaso saina kira gida.

Wajen 1 na tashi na dare na na jawo wayarsa da ya jefar a gefe yana bacci, chatting yake da alama bacci ya daukeshi, har na dauko wayar na cire security din da naga yayi amfani dashi dazu ina kallonsa ta gefen ido, ina budewa sako ya shigo ta Whatsapp, kamar zan wuce sai naga wani sako da ya dauki hankalina ya shigo.

Hotuna ne suke shigowa daga wata lamba anyi saving da HONEY!!!.

Shiga Whatsapp din nayi na shiga chat dinsu da ita na bude hotunan da ta turo, sakin wayar nayi ta fadi a kasa da ƙarfi.

Ƙarar faɗuwar wayar a tiles ne yasa ya farka a baccin da yake, ganina yayi kamar wata Statue na ƙame dafe da ƙirji,

Bina yayi da kallo sannan yabi ƙasan da kallo yaga wayarsa, tashi yayi ya dauko wayar yaga fuskarta tayi ratsa ratsa ta fade, gaba daya wayar taci screen da censor.

“Bakida hankali ne ? Me ya kai hannunki kan wayata da har kika fasa min ita ? Cikin ɗaga Muryar yake maganar kana ganin yanda yake magana zaka san ransa yayi masifar ɓaci.

Ban tanka masa ba na tashi na shiga toilet na zauna har yanzu hannuna yana kan ƙirjina, mamaki, kishi, tashin hankali, fargaba, takaici, baƙin ciki, da komai ma sun haɗar min saboda gamon da nayi......

Tun yaushe khalil ya kasance yana cin amanata da wata wai HONEY ? To anya ma kuwa da iya ita kadai yake cin amanata ? Wane tabbacin nake dashi na cewar iya ita kadai yake kulawa ? Wani kuka ne ya kubce min mai mugun ƙarfi wanda ban san na sakeshi ba, jiyowa nayi yana buga kofar sakamakon na kulleta.

Ammatana me ya faru ? Kukan me kike ? Wani ne ya rasu ? Ko mafarki kikayi ne ? Duk a lokaci daya ya jero min wannan tambayoyin.

Takaici ne ya ƙara ƙumeni, wato shi bai ma san me yayi ba kenan ?

Duk maganar da yake ban bude kofar bandakin ba kuma ban daina kuka ba, sai Wajen asuba sannan nayi alwala na fito yin Sallah,

Samunsa nayi ya koma bacci abinsa, kallo daya nayi masa banyi na biyu ba, na tayar da sallahta.

Bayan na idar haka na kuma zama ina kukan shi kuwa bai ma tashi sallar ba, wacce a dan zaman da nayi da Khalil na fahimci baya son sallah akan lokaci, Nima kuma ba damuna tayi ba, yau din ma dan na rasa ya zanyi ne na tada sallah akan lokacin.

Kukana ne dai ya kuma tashinsa a bacci, sakkowa yayi ya zauna a kasa ya jawoni jikinsa, ammatana ki fada min me......

Ban bari ya karasa ba na janye jikina daga nasa da karfi cikin tsawa nace “karka sake taɓani! Kaje wajen Honey din taka da take Turo maka hotunan tsiraicinta ka rungume amma karka sake taɓani!!!!

Ina fadar haka kuma saina sake fashewa da kuka saboda wani kishi da naji ya sake taso min.

Tsam ya tashi ya koma gefen gadon yana murmushi, mamaki ne ya kamani to meye abun murmushi kuma ? Is it a joke ? Na tambayi kaina.

Maganarsa ce ta katse min tunani, “dama dan saboda wannan kike ta kuka ?

Baki bude na kalleshi nace bai kamata ace nayi kishi akan hakan bane ? Duk yanda na tsare maka kaina amma kai ka kasa tsare min kanka ? Da aurenmu fa shalele ? Amma kake bibiyar wata ? Da me na gaza maka ? Ina fadar haka na sake fashewa da kuka.

Murmushi ya sake yi mai sauti yace “kika tsare min kanki a ina ? Ko kin ɗauka ban san mazajen da kikayi mu’amala dasu a wajen bayan ni bane ? Duk wasu maza da kika kula na sani! Kuma inada record na mu’amalarki dasu, da iskancin da kikayi da kowa.

Saboda haka karki bata min rai ki jawo zamanmu ya daina daɗi, yanda kika ga wannan abun to ki barshi a haka, idan ba haka ba bakin ciki ne zai kasheki SUMAYYA!!!!!

Kallonsa nake ina mamaki ji nake kamar a mafarki! Yau shalele ne ya kira sunana haka ? Yau shi yake min gorin iskanci ? Idan ma hakane waye ya fara batani ? Yau Ni yake jinginawa kalmar iskanci ?

Rufe Idona nayi na sake budewa domin tabbatar da ba mafarki nake ba! Still dai Khalil na gani a gabana, wannan ya tabbatar min da cewa ba mafarki nake ba.

Cikin kuka nace “amma shalele ka cuceni ka yaudareni ka yaudari zuciyata! Da auren namu kake bin wata macen ? Bazan taba yafe maka wannan zaluncin da kayi min b.......

Taurari naji sun gifta min ta idanuna, can kuma sai wani raɗaɗi da naji ya ziyarci kuncina, da mamakin me ya faru na dago ina kallon Khalil, ganinsa nayi a tsaye a kaina yana nunani.

“You have to be very careful, Yakamata ki san da wa kike magana! Ni mijinki ne kuma na gaba dake. Karki sake gigin fada min maganar banza, har Ni zaki cewa azzalumi ?

An fada din azzalumi, ai zaluntata kayi, ka dakeni kuma ka hanani kuk.......

Maruka biyu ne suka sake ziyatar kuncina, karfin marin Saida ya saka na zube a ƙasa, Khalil ya saba marina tun muna soyayya amma bai taba yi min marin da ya kai wannan ba.

Wasan da nake miki da kuma sake mikin da nake ne yasa kika rainani har kike iya fada min maganar banza, to Wlh saina gyara miki zama a gidannan.

Yana gama fadar haka ya shige banɗaki ya barni a wajen dafe da fuska hawaye ma sun daina zubo min.



******** ******** ********

Yaya haneep ne ya shigo ɗakin best a daren ana gobe suna.

Zama yayi kusa da ita, ta juya masa baya tana tura baki, dan har ga Allah burinta a sakawa baby sunan sashenta amma yaya haneep yaƙi amincewa, meyesa zaiyi mata haka ? Ranta duk a bace yake.

Rungumota ta baya yayi ya rada mata a kunne, “Allah raya mana LITTLE SUMAYYA.....!!!

Waigowa tayi da sauri cikin mamaki tace “ban fahimta ba love!.

Murmushi yayi yace “ina magana ne akan babynmu da taci sunan sashenmu.

Da wani irin mugun sauri ta rungumeshi tana dariya da hawayen farin ciki a lokaci ɗaya.

“Nagode! Nagode sosai love! Ka biyani, ka sakani farin ciki, kamar yanda ka sakani farin ciki kaima Allah ya sakaka!! Addu’a ta cigaba da kwarara masa yana amsawa da Ameen.

Gaba daya best ta kasa ɓoye farin cikinta ta kasa shiru! Bakinta yaki rufuwa, kawai kallon yarinya take tana murmushi tana kallon yaya haneep, saidai kuma jifa jifa saita share hawaye na rashi da kuma kewar sashenta.

Yaya haneep kallonta yake cike da farin cikin ganin tana cikin farin ciki, dan rabon da ya ganta a haka tun ranar da SUMAYYA ta bar gari.

“Love burina me zanyi miki na daina ganinki cikin damuwa bayan wannan ? Dariya tana miki

17 / 40