Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
tsane ki, babu ni babu ke, ina ruwan ki da rayuwa ta ne ma.
Duk haukan da nake mata bata cika niba, har muka je gida.
Ihuna da mama ta jine yasa ta fito da sauri.
Dan Wallahi tayi tunanin wani mugun abun ne ya sa meni.
Hankadeni tayi kawai.
Ganin yanda muka tsaya kaman masu shirin dambe
Mama ta matso da sauri meyafaru ?
Babu komai ta faɗa tana dauke kanta.
“Mamah khaleel dina ta mara kuma Wallahi idan ya rabu dani akan hakan duk abinda na mata ita tajawa kanta.
Hawaye ne ya fara zubowa best “akan namiji, namijin ma daba sonki yake ba, shine kike fadamin haka ?
Na faɗa miki wacece ke ? uwa ta ce ke ?
Ki sani akan khaleel zan iya rabuwa da kowa, idan nace kowa ina nufin kowa!
“Haɗa kayan ki ki koma wajen sa, cewar baffa da bansan yana gidan ba.
Da hanzari na shiga daki na fara dibar kaya na.
Wai kin haukace ne sumayya! Magana nake miki fa, indai akan abin nan ne zanje nabawa khaleel hakuri.
Ban kulata ba naci gaba da abinda nake.
Jaka ta na dakko na fito.
Mama tana zaune dafe da kanta.
Humaira kam kuka kawai take.
Ita kanta best kuka take kaman hauka.
Shikenam kiyi hakuri, zanje na bashi hakuri! Dan Allah ki dakata! Ta faɗa tana rungume ni.
Hannayen ta kawai na banbare a jiki na.
Hanyar waje kawai na nufa.
Bansan ya akayi na faɗi a kasa ba sejin saukar duka danayi ta ko ina, duka na yake tamkar Allah ya aikoshi baki da amfani, da haihuwar ki gwara barin ki sumayya!!
Kokarin tashi nake amman nakasa.
Ganin dukan yayi yawa, duk tsoron dukan ta se jinai ta rungume ni tana bashi hakuri, dan Allah baffa kayi hakuri
Bazata kara ba, sashi na, ai bazaki kuma ba.
Zan kuma! Na faɗa a dake. Malama nace ki kyale ni, ana dole ne na faɗa ina kokarin raba jikina da nata.
Tashi daga nan haleemah”
Bazan iya ba baffa kayi hakuri Dan Allah ka kyaleta.
Daki kawai ya shige ya bar mu a tsakar gidan.
Yana barin wajen na hankade ta na mike.
Zo mutafi sashina
Kije ki nemi sashin ki a wani waje, amman badai niba.
Kiyi hakuri dan Allah.
Tsaki kawai naja na shige daki ban tsaya na kara saurararta ba.
Zubewa kawai tayi a kasa tana kuka, mama sashi na tace ta tsane ni, wai babu ita babu ni, Mamah akan namiji sashina zata rusa amintarmu.
Dan Allah mamah ki bata hakuri Wallahi zanje har kasa zan durƙusa nabawa khaleel hakuri Amman kice karta rabu dani.
Janyota kawai mamah tayi ta rungume Ta rasa me zata ce mata ma.
***** ***** ***** *****
Tun daga wannan ranar nazama nida jaka babu maraba, na riga na saba da duka, abinda bana duka ba yimin shi baffa yake.
“Nasha wahala kafin nasamu khaleel ya fara saurara ta, zan iya yin sati ina kiran sa baze daga ba, duk message din dazan masa baze min reply.
Idan har ya neme ni bukatar sace ta taso.
Kullum kuka nake ina rokonsa akan ya kulani ya bari komai ya wuce.
Rayuwar da muke da khaleel kamar ma ƙaramin soyayyarsa ake a raina fiye da Da.
Ana haka kwatsam ya haleepha ya dawo hutu.
Yaji labarin duk abinda yake faruwa kuma bansan a ina ya jiba.
Har gida yazo suka gaisa da mama sannan yasani a gaba muka koma gidan ammie.
Babu duka babu zagi, amman punishment din da yake bani gwanda yasani a gaba yayi ta duka.
Nayi baki na rame har lokacin kuma banji zan rabu da shi ba.
**** ***** ****** *****
Yau kam ji nake idan banga khaleel ba zan iya mutuwa.
Ta window na tsaya kawai ina kallon waje har ya fita daga gidan,
Ajiyar zuciya kawai na sauke, nima na fice daga gidan.
Bayan mun gama abinda zamuyi, yace min yau zezo zance waje na, amman gidan su best zezo.
Ban kawo komai a raina ba nace masa toh.
Yauma a hanya muka hadu da boss lady.
“Baki da kirki” cewar Boss lady.
A’a wlh babu waya a hannu na ne shiyasa ban neme kiba.
Toh muje a siya mana, tsayawa kawai nayi ina kallon ta, muje ta faɗa tana jan hannu na.
Amman meyasa naga duk tabon duka a jikin ki ?
“Babu komai” na fada ina kauda kai.
Bata kara min tambaya ba har muka je ta siya min keypard da layi.
Godiya na mata sannan muka rabu.
Bayan sallahn isha’i Khalil yazo..
Waya yamin nace ganin nan,
Ganin ina kwalliya, yasa best tace ina zani ?
Zance zanyi na bata amsa ina ɗauke kaina.
Dan har lokacin ba sakewa nake da ita ba.
Duk kuwa yanda take son mu dawo daidai.
Kawai ta fara rawa da ihu kaman sabuwar kamu.
A hankali nayi murmushi bazata taɓa canzawa ba...
Ganin nayi mata murmushi ne, yasa ta matso ta rike ni.
Yaushe kikayi sabon saurayi ?
Muje ki ganshi, na faɗa Ina danne dariya ta.
A raina kuwa cewa Ke yanzu best ko a mafarki akace miki naso wani seki yarda ? Hmmm daman nasan ba kaunar khaleel kike ba, Muje nayi maganin ki.
Dole naje na ganshi ai, tashi mutafi na shirya.
Wallahi dariya tabani, se rawar jiki take.
Muje na faɗa ina yin gaba.
A waje muka sameshi ya juya baya.
A hankali murmushin fuskarta ya juye ya koma zallan ɓacin rai.
Zata juya yace best babu magana, tsayawa tayi kawai.
Ammatana kawo min ruwa mana pls!
Toh kauna! Na faɗa cikin murmushi tare da juyawa.
Bayan na tafi ne Khalil ya kalli best cikin wani malalacin murmushi yace:
Kaga ƙawar Amana! To ykk ?
Ganin best bata kulashi bane tana shirin juyawa ta koma cikin gida yasa yace baki ji ba yammata..... Cakk ta tsaya.
Ke a daƙiƙin tunaninki kin mari banza kenan ? Inaaa baki isa ba yarinya!!!!.
Meka isa kamin ? Na mari banza mana!!! Best ta faɗa cikin dakewa da ƙwarin gwiwa.
Waya faɗa miki ? Na miki alkawarin a yau zaki biya farashin marin da kikayi min.
Ka fita daga rayuwar sumayya malam! Best ta faɗa tana nunashi da manuniya cikin masifa.
Bai bari ta karasa maganar ba ya tari numfashinta “Ai na dade da fita daga rayuwarta, itace mayya, ta riga tasan dadi na, toh bazata iya rabuwa dani ba, Koda yake ita a haukan ta auren ta zanyi ko ?
Koda matan duniya sun kare mezanyi da karuwar gida?
Waya san iya adadin mazan da take bi ?
Kasa juran cin zarafin sa tayi, har batasan sanda ta daukeshi da mari ba.
Lafiyayyen murmushi ya sakar mata, kaman dama abinda yake jira kenan.
Haleemah!!! Na kira sunanta da karfi.
Karuwa ta ita zata min wannan faɗan ya faɗa kasa kasa.
Ina kara sowa wajen yace karkiyi magana kinji ammatana.
Ki kyaleta kawai ya faɗa yana janyoni jikin sa.
Meyasa kika mareshi ? Cikin bala’in da yake ci na nake mata magana.
Tama kasa magana tsabar ɓacin rai.
Kawai dannace ina son tayi magana da baffa akan maganar auren mu, shikenam fa, ta fara zagi na.
Ina bata hakuri kuma ta mare ni.
Amman karki damu, zan iya jure komai akan soyayyar ki.
Juyawa kawai nayi na rungumeshi, ina bashi hakuri ina hawaye.
Fakar Idona yayi ya ɗagawa best Gira daya tare da sakar mata murmushin mugunta.
Da gudu ta juya gida tana kuka.
Banbi ta kanta ba seda muka gama zancen mu, ya gama min famfon daya zauna a kaina tsaf.
“Ina zuwa na sameta a kwance cikin bargo, yayewa nayi na fizgo ta kasa banyi wata wata ba nima na dauke ta da mari.
Ina son daga yau ki fita daga rayuwa ta da khaleel, kome zanyi rayuwa ta ce dan haka babu ruwan ki.
Bama iya rayuwar ki da khaleel ba, har rayuwar ki zan fita a cikin ta, daga yau bani ba ke.
Saida gabana yayi wata mummunar faduwa jin cewar zata rabu dani! Dan duk rigimar da nake da best ina jinta araina kuma bana jin zan iya rabuwa da ita.
Cikin rawar murya nace “Ra...bu....wa.... Kuma” ???
Eh! Ta faɗa cike da tabbaci, Kisani banyi lalacewar da zaki dinga wulakantani akan wani takadirin ɗan iska ba.
Ki zaba koni ko khaleel!!!
Shiru nayi cikin tashin hankali na kasa cewa komai.
“Ki zaɓa nace!!!” ta faɗa da karfi.
Dukan ku ina sonku! Na fada ina rike hannunta.
Wancakalar da Hannuna tayi kafin tace “Ƙarya kike SUNAYYA!!!!”
Namiki alkawari daga yau bazan kara miki magana, ko kuma na nuna inada alaƙa da ke, har se kin dauki daya cikin mu biyu!!!
Hankalina idan yayi dubu ya tashi, domin bazan iya rabuwa da khalil ba kuma bazan iya rabuwa da best ba. Gashi best ta gindaya min wannan sharadin mai wuyar bi.
A hankali na fara ja da baya.
Idona cikin nata, tana kuka ina kuka Har nabar dakin.
Ina fita ta durkushe a kasa ta kuka.
Da gudu na shiga gida kaman wadda aka koro, Dare ne ko mama batasan a gidan na kwana ba seda safe.
Ta fini taurin kai, bata taɓa fadar abinda bazata aikatashi ba.
Amman nima a shirye nake, na rabu da kowa akan khaleel.
“Tun daga ranar data fita daga rayuwa ta...
Rayuwa ta ta kara lalacewa, mun hade da boss lady, lokaci zuwa lokaci ina binta yawo.
Nabata labarin soyayya ta Da matsalan da nake fuskan ta a gida.
Ita tabani shawarar shiga islamiyya, saboda nasamu damar yawo na akai akai.
Kuma nayi nasara, mama tana ta murna na shiryu, sedai ina ba haka bane.
Wulakanci kala kala khaleel yi min shi yake.
Ban isa na kula ko wane namiji ba, shi kadai yake so nayi rayuwa da shi.
Ranar da ya gano ina bin boss lady naga tashin hankalin, da tunda nake da shi ban taba gani ba.
Bansan yana kishi naba se a lokacin, itakam ta daku a hannun sa.
Ni daman fuskata bata rabo da shan mari a hannun sa sedai idan be ganni da wani namijin ba.
Duk kudin da nasamu tarawa nake ban taba kashewa ba, duk lokacin da naga muna cikin matsi zan dakko muyi amfani da shi, dan lamarin baffanmu ya kara taɓarɓarewa.
Zuwa lokacin iyayen mu sun fahimci, mun samu matsala da haleemah.
Haka aka taso mu a gaba, juyin duniya mu fadi abinda ya hadamu, amman munki.
Anyi fadan, anyi rarrashin, anyi nasihar, anyi barazanar amman duk a banza.
Ya haleepha ya dake mu, amman Abu yaci tura.
“A haka naci gaba da gudanar da rayuwa ta, wadda kullum danasanin ta nake yi, ban taɓa kwanciya da namiji ba tare dana zubar da hawaye ba.
Soyayyar khaleel itace jarabawata Wadda har yanzu akanta nake.
Daga nan na dora da bashi labarin rayuwata har zuwa kwanciyata yanzu a asibiti da auren da baba yayi min, har zuwa yanzu da nake bashi labarinnan ban ɓoye masa komai ba.
***** ***** ***** *****
Shiru wajen yayi, bayan na gama bashi LABARINA bakajin komai se karan fanka, Se kuma sheshshekar kukana.
Kansa yana kasa bazaka ce ga halin da yake ciki ba.
Da hannun sa ya nunamin yana zuwa.
Wata kofa ya shiga wadda ina kyautata zaton toilet ne.
Jingina yayi da bayan kofar ya lumshe idonsa,
Tunda ya dora idon sa akan ta yaji ya kamu da soyayyar ta.
Ko yanzu data bashi labarinta, babu abinda ya sauya a soyayyar da yake mata sema ƙaruwa da tayi, tausayin ta yake ji.
Tabbas gayen nan ya cutar da ita, cuta mafi muni a rayuwa, amman bazata taɓa fahimta ba a yanzu.
A yanzu ita da makauniya babu maraba , idon ta a rufe yake.
Soyayyar da take masa bata bari ta banbance daidai da ba daidai ba.
Shi ɗin kawai take gani, a gaban ta.
Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un! Shi kuwa Khalil Ina zai kai wannan hakkin ?
Dr yanzu tunaninsa shine ta yanda zai fara fahimtar da ita illar Khalil a rayuwarta, saidai kuma yasan tabbas idan yace haka zaiyi yasan ya ɗauko hanyar da yarinyar nan zata tsaneshi, kenan ta ina zai fara taimakonta ?
Da sauri ya bude idon sa tuna cewar yanzu matar aure ce.
Ya zanyi da soyayyar da nake miki sumayya ???
A hankali ya fito ya zauna yana kallona.
Yanzu wane hukunci kika yanke akan auren nan ? Ya faɗa yana karantata.
Murmushi na sakar masa koda naje zan dawo, dan bazan taba zaman aure da namijin da ba khaleel ba.
Shi nake so, shi nake kauna, khaleel shine Burin zuciya ta.
Meyasa bazaki yiwa mahaifin ki biyayya ba ?
Bani da mahaifi ai, ya dade da mutuwa!!!!!!!!
Tirƙashi.....
Ku gafarceni a bisa tsayawa a daidai nan.
Mu hadu a page 14
Taku har kullum Rabi’atu Fulani.
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 14
Me kike nufi ? Ya tambayeni yana zare idanu.
Nasan ya tsane ni, ya dade da dena yimin kallon yar sa, taya kake tunanin ni zanci gaba da daukar sa a matsayin mahaifi ? Baze taɓa yuyuwa ba!!!!
Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!
Kawai yake maimaita wa a cikin ransa.
Wai ana samun irin soyayyarnan a zahiri dama ?
Me mutumin nam yayiwa yarinyar nan ?
Dogon nazari ya faɗa duka ki zagi ba zasu taba saka ta saduda ba Sedai a jata a jiki a hankali a nusashsheta a nuna mata illar wanda take so yake da ita.
Zanyi amfani da wannan wajen dawo dake hanya sumayya, Kedin baki dace da rayuwan Nan ba, gaba daya. Ya faɗa a ransa, yayi nisa a dogon tunaninsa yaji ana.
Yaya doctor!! Yaya doctor tunanin me kake ? Na faɗa ina ƙyasta hannayena.
Babu komai.
Dare yayi ki samu ki kwanta ki huta, kuma Banda kuka da tunani.
“Toh.”
Yana fita na tashi zaune. Kuka nake, zuciyata zafi take min, dafe kirji na kawai nayi dan radadi yake min.
Jinake tamkar a lokacin komai yake faruwa dani.
Gaba ki daya ranar ban rintsa ba.
Da sassafe yazo dubani, sedai kaman yanda yayi tunani hakan ne ya kasance, domin idanuna duk sun kumbura alamun nayi kuka ban samu bacci ba.
Shima beyi bacci ba dan ga idanunsa nan duk sunyi ja alamun akwai bacci a cikinsu.
Flask na Tea din da yake kusa dani ya jawo ya haɗa min tea ya bani, babu musu na karba na sha.
Allura ya haɗa ita ma banyi masa garda ma na tsaya yamin.
Be dade da gama min ba, bacci ya dauke ni.
Ganin na samu bacci ne yasa ya sauke ajiyar zuciya.
Best ce ta shigo daga pharmacy din da taje siyo min wani magani taga doc a gefen gado yana kallona murmushi tayi kafin tace: Doctor yau kaine da wuri haka.
Nazo duba kawar ki ne. Ya faɗa yana basarwa tare da fatan bataga yana kallon yarinyar nan ba.
Bata ce komai ba ta ajiye maganin a gefen gado ta zauna a gefen gadon da nake suna dan hira jifa jifa.
****** ****** *******