ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 40

36K to 39K   out of 117.2K words

ga kazar amarcinki.

Kasan da yunwarta aka kawoni gidan nan.

Be karamin magana ba.

Ya zauna a bakin gadon.

Uban****ka ne ya siyi gadon da zaka hau ? Sauka maza!!!! Na faɗa da wata irin tsawa.

Saroro yayi kawai ya tsaya yana kallona.

Bazaka tashi ba? Na faɗa ina zare masa ido kaman wata Uw***ar***sa.

Mikewa yayi ya zauna a gefe kawai yana kallona.

Juyawa nayi na kwanta ina jan tsaki, tsohon banza kawai.

Bansan adadin lokacin daya dauka a zaune a kasa ba.

Ina bacci naji ana shafani, murmushi nasaki, baba tsoho kenan!

Sedai na daidaici inda hannun nasa yake, dama kayan aikin na kusa dani,

Besan tayaya ba, seji yayi na yankeshi da reza.

Da sauri ya dauke hannun sa, Yarfe hannun yake cikin raɗaɗi, ke wai baki da hankali ne ?

Ƙatuwar mahaukaciya ka auro ai baba tsohon banza.

Ya kara matsowa.

Na tashi zaune, na fito da wukakena Sababbi dal dasu sai sheki suke.

Tsayawa yayi ya kasa karasowa inda nake.

Kai a dakikin tunanin ka, ni zanyi zaman aure da kai ? Kayi kuskure toh! Namiji daya tak shi yake da ikon tabani yayi yanda yaga dama da jikina..... Ban bari yayi magana ba na dora da fadin...

Bara kaji na faɗa maka wannan auren baze hanani rayuwa da shi ba, Ko yanzu naji ina bukatar sa, zan kirashi zai zo kuma har cikin gidanka, muyi yanda mukaga dama, Kaga shikenan ma mun huta biyan kudin hotel.

Na ƙarasa maganar ina kashe masa ido daya.

Fitar min daga daki dan ganinka, na samin tashi zuciya.

Tashin hankali ne rubuce kan fuskar sa.

Kai dallah ka fita ni bacci zanyi.

Ganin bashi da niyar fita na dauki wuka na jefa masa.

Da sauri ya kauce.

Bazaka fita ba, na dakko wata wukar ina nufosa da gudu.

Shima da gudu ya fita da katon tumbin sa a gaba.

Ganin yanda yake gudun.

Bansan sanda na zube a kasa ina dariya ba.

Dariya nake tsakani na da Allah harda hawaye.



******* ******* ********

Satin amarcin da kowa ce amarya take alfahari da shi, nikam shi yazamar min satin tijara da yaki a gida na.

Kullum da akwai kalan rashin mutuncin da zan masa, Idan kuwa yan uwan sa, suka zo da sunan, sunzo ganin amarya, hauka nake musu fiye da yanda kuke tunani.

Su kansu yan uwana idan sunzo ba kula su nake ba.

Humaira kadai nake sakarwa fuska.

Ni kam na kwantar da hankali na, abinci nake ci me rai da lafiya.

Bani da matsalan komai a gidan.

Sedai bakin cikin tozali da wanda bana kauna.

Wajen wata daya duk tijarar da nake masa baya biye min.

Sedai wata kalan rama da yayi, gashi tsufan sa, ya kara fitowa sosai,saboda bashi da kwanciyar hankali kota sisin kwabo a cikin gidan.

Haka zan kira kauna, musha soyayyar mu a waya a gaban sa.

Sedai Bai taɓa tanka min ba, maganganu ba kalan da bama yi.



******* ******* ********

Zaune yake yayi tagumi abun duniya duk sun dameshi kai kana gani kasan baya cikin kwanciyar hankali da farin cikin aurensa da yarinyar nan.

Kansa nazo na tsaya ba ko sallama kai kana ganin yanda na rike kugu kasan tijara ce fall raina.

Yawwa nace ba! Inaso zan fita unguwa da saurayina ko yazo Nan gidan ko ka barni ni naje wajensa saika zaba.

Dagowa yayi ya kalleni kafin yace me zaki je yi masa ?

Zan je inason mu hadu ne domin inada bukatarsa. Abinda na fada kenan cike da gadara da rashin *”M”*

Bai ce komai ba Naji ya tashi yayi sama dani, sai cikin daki, kokawa na fara yi dashi saidai mutumin har yanzu da kwarinsa, jefani yayi kan gado yayi min rumfa yayi min rada cikin kunnena “ ba iya saurayinki bane namiji, Nima namiji ne kuma inada mazantaka fiye da tasa.

Fara shafani yayi yana matsa min breast ya dora bakinsa a wuyana ya fara kissing yana lasa ta ko ina kamar tsohon maye.

Shiru nayi masa yana ta abunsa ganin nayi masa shiru yasa yayi tunanin ko na saduda ne, kayansa ya fara cirewa ya jefar da riga gefe ya cire wando daga shi sai singlet da boxer.

Rigata ya cire min da dogon wandon da ke jikina ya cire min pant, zirr haka yayi min bakomai a jikina shima kuma sai ya fara kokarin cire boxer na jikinsa.

Cire boxer din yayi sannan ya fara lalube yana kokarin saka min gabansa a nawa gaban, cikin zafin nama na danƙi gabansa a hannuna na murɗe da dukkan karfina kamar zan tsinketa.

Wani ihu ya saka wanda idan ba dan gidanmu yanada zurfi ba to da tabbas makota sun jimu.

Saida na ga ya galabaita kafin na sakeshi ya fadi a kasa yana matagungun.

Tsallakeshi nayi na wuce falo bayan na kwashi kayana a hannu.

******* ******* ****

BAYAN WATA BIYU



Lokaci yanata turawa amma mutuminnan ya gagara cika min burina na sawwake min, ban san wane kalar rashin mutunci zanyi masa ya sawwake min ba. Narasa ya zanyi ya sake ni, naci masa mutunci, na ciwa yan uwan sa, amman duk a banza.

Ni har nama rasa wane kalan wulakanci zan masa.

Tunanin kiran Khalil ne yazo min raina dan tunda nayi aurennan bamu hadu ba, Ni ban fita ba shi bai zo ba. Ko wulakancin da nakewa baba abbas na cewa zamu haɗu da saurayina duk set up ne amma ban taba kawo hakan a raina ba.

Numbersa, na saka na kira, har ta gama ringing be daga ba, banyi zuciya ba nakara kiran sa, nan ma bai daga ba.

Again na sake try a karo na uku, wannan karon nayi Sa’a tana shiga ya daga,

“Hello yammatana”

Uhm Kauna!

Ya dai yammatana me ya faru ?

Please kazo!

Ina zanzo ?

Gidana mana.....!!!

Saida yayi shiru kafin yace anyaa kuwa yammatana ?

Bana son nazo gidanki kuma mijinki ya ganni yazo yayi min shirme.

Kazo ba abinda zai faru wallahi in Sha Allah.

Kin tabbata ?

Cike da kwarin gwiwa nace Eh shalelenah.

Saida yayi jim kafin yace Toh shikenan zan zo Anjima.

Yawwa shalelenah Mmmuuaahh na fada cike da farin ciki tare da yi masa kiss, muka ajiye waya.

******* ******** *******



Da yamma yazo, aikam nayi masa girki me rai da lafiya.

Meyafaru kike nema na ?

Nagaji da auren nan, so nake mu kawo karshensa a yau! Na faɗa cike da ƙwarin gwiwa.

Ta yaya?

Karka damu Zan shirya komai.

Owk kawai yace ya nemi waje ya zauna shima kamar gidansa, muka dasa babin hira.

Wallahi ji nake babu wanda ya kai ni farin ciki a duniya,

Meya kai zama da masoyi dadi ?

Babu na ayyana hakan a raina.

Seda na dai-daici lokacin dawowar sa yayi na shiga dakina, duk na hargitsa gadon, baka isa kace babu ba’a aikata wani abu a kansa ba.

Shigo khaleel, babu musu ya shigo.

Neman waje yayi ya zauna a gefen gadon Nima na zauna dab da shi.

Motshin shigowar mai gidan naji ya saka na kara shigewa Khalil muna magana ƙasa-ƙasa da kuma wata dariya wacce take nuni da cewa kamar ina cikin farin ciki, shima kuwa Khalil ya biye min.

Jiyo dariya da yake yi ne a cikin dakina yasa da hanzari ya shigo.

Ina ganinsa na cewa Khalil shalelenah ga baba ku gaisa.

Tsugunnawa yayi a kasa cike da iskanci yace baba ina wuni......

Baya kawai malam Abbas yaja dafe da kirji dan ya dauka bazan taba iya kawo wani kato gidan mijina ba dakina na sunna! Ya dauka duk iskancina a iya baki ne.

Dariyar da yaji mun cigaba da yi ne ya dawo dashi daga dogon tunanin da ya tafi... Kawai juyawa yayi ya tafi dakinsa bai ce komai ba.

Dawowa yayi hannunsa ɗauke da takarda fara a naɗe ya miƙo min.

Khalil ne ya karba ya karanta a fili

“Ni Abbas na saki matata sumayya saki uku!!! Idan ta samu miji tayi aure”

Kafin Khalil ya gama karantawa tuni malam Abbas ya fita daga gidan ma gaba ɗaya.

Cike da farin ciki na rungume Khalil ina sumbatarsa, Saida muka gama shashancinmu sannan muka baro gidan.

Wayata kawai na ɗauka da hijab muka fito daga gidan,

Muna fitowa muka ga malam Abbas a kofar gidan yana zaune dafe da kansa,

Ina zuwa! Cewar Khalil

Matsawa yayi kusa dashi yayi masa magana ƙasa ƙasa wacce ban san me yace masa ba! Sannan ya dawo yaja Hannuna muka tafi.



******* ******** ********



Saida Khalil ya kaini har bakin layinmu sannan ya tafi Nima na tafi gida.

Da sallama na shiga gidan ina ƙwalawa mama kira mama! Mamah!!

Tana bakin murhu taji ina kwala mata kira ji tayi kamar kunnenta yana mata gizo, idonta a kofar gida har sai da Na shigo “kwana biyu da baki nan kunnena har ya huta! Har yanzu ba zakiyi hankali da wannan kiran ba.

Cike da shagwaba nace “to Mama nadawo ai!

Ban gane kin dawo ba ? Ta tambayeni a tsorace.

Ya sakeni saki uku!

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!! Salati kawai mama take maimaitawa kafin ta dora da fadin

Kin kashe auren yanzu sumayya ? Duka duka kwananki nawa da auren ? So kike ki ja min zagi a dangi da unguwa ? Sai hawaye..... Shar shar wani na korar wani haka mama take zubar da hawaye.

Cike da tashin hankali na ƙarasa wajenta da niyyar lallaminta saidai ganin da nayi ta nunoni da tabaryar da take daka ne yasa na ja tunga na tsaya dan na san tabbas zata iya bazar dani tunda naga ranta ya ɓaci.

Mama bata iya ɓacin rai ba amma duk ranta ya ɓaci to bata iya fushi ba.

Ki jira ubanki ya shigo tukunna saiki san me zaki ce masa.

Gefe naja ina tura baki deep down Kuma ina jin tsoron haduwata da bappa, dan nasan karonmu ba sauki.

Da daddare baffa ya dawo ya same ni a tsakar gida na bararraje.



Nunani yayi yana kallon mama yace wannan kuma me take yi min a gida har yanzu bata tafi gidan mijinta ba ? Yaushe aka daura auren da har zata fara yawon unguwa ?

Jin mama tayi shiru yasa ya kalleni ya daka min tsawa uban me kike yi min a gida a wannan lokacin nace ???

Muryata na rawa nace Ba....ppa ya.... Sa..ke..ni...

Saki kuma ?

Nace eh bappa ya sakeni ne ?

Cikin wani karaji bappa yace uban me kika yi masa da har ya sakeki ?

Nace wlh bappa bakomai kawai yazo ya bani takarda kuma gata.

Karɓar takardar yayi yana karantawa a fili, Yana gama karantawa ya kalleni yace

“Ki sani bazaki yi min zawarci a cikin gida ba! Saidai kinemi Wasu iyayen badai muba Wallahi!!!!

Cikin wata irin faduwar gaba na dago ina kallon bappa dan san tabbatar da abinda yake cewa.... Saidai a fuskarsa ko idonsa babu alamun wasa na waiga na kalli mama naga ta ɗauke kanta daga kanmu, ga humairah kuma tana kuka............!!!!!!!

Ku dakaceni anan domin jin yanda zata kaya saimu a haɗu a page 16

Nagode taku har kullum Rabi’atu Fulani

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

BY

RABI’ATU (FULANI)

Young talented writers association (YOTA)

A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina





Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo

Amina muhammad haruna

Maman xhara

🤍

Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 16

Tashi ki barmin gida!

Ina zani baffa ? Na fada ina zaro Idanu.

“Gidan ubanki zaki! Ya faɗa ina daka min tsawa.

To ai anan nake yanzu.

Kin san Allah SUNAYYA baki fita kin bar gidannan ba zanyi ajalinki kafin kiyi nawa ? Baffa ya faɗa ina nunani da idanunsa da sukayi jajir,

Mikewa nayi na nufi hanyar ƙofa, tare da hijab din da nazo dashi da kuma wayata.

Mama ce ta rikeni tare da cewa, bakida hankali ne ?

Baki iya bada hakuri ba ?

Mama yasan fa bana son wanda ya bani! Ta ya yake tunanin zan zauna da mutumin da bana s...... ?

Saukar marin da Naji ne a kuncina yasa maganata ta ɗauke ba shiri, kafin na ankara sai saukar duka Naji ta ko ina.

Baba ne yake dukana idonsa ya rufe idan ya jawo wannan ya buga min sai ya jawo wannan ya buga min.

Ban motsa daga inda nake tsaye ba, kuma ko ehem ban ce ba, Saida ya gaji da kansa sannan ya ƙyaleni ya koma gefe yana dafe kansa, yarinyar nan ta dage sai ta kasheshi da baƙin cikinta!

Cikin takaici yace wallahi yarinyar nan ko shakka bana yi wani abun tayiwa malam Abbas da ya kasa jurewa har ya saketa, kuma zuwa da safe zan bincika idan har na samu wani abun kikayi masa wlh bazaki ji daɗina ba SUMAYYA!!!.

Yana gama fadar haka ya juya ya fita a gidan.

Mama ce ta zauna tana min nasiha fada da gargadi duk akan ƙin zaman gidan malam Abbas da nayi.

Nidai ina jinta tana shiga ta hagu tana fita ta dama.

******* ******** *******

Ina bacci da safe Naji bappa yana magana da mama kamar a mafarki, yana bata labarin abinda malam Abbas ya labarta masa na duk abubuwan da nayi masa, tun daga ranar kaini gidansa har jiya da ya sakeni da kuma dalilin sakin.

Mama ina jinta tayi shiru nasan da alama abun ne ya jijjigata ta rasa bakin magana.

Ina jiyo bappa yana magana kamar mai shirin kuka, “Yarinyar nan kamar ita kadai na haifa ? Ita kadai ta dage saita zubar min da mutunci a idon duniya ? Me take nema a duniyar nan fisabilillahi !!! Bana son nayi mata baki ta kara lalacewa amma yarinyar nan tabbas so take saita kasheni.

Ji nayi mama ta rufeni da duka Idona yana rufe Shiyasa ban jiyo shigowar ta ba, dukana take da dukkan karfinta tana kuka bappa shima yana falo ina jiyo kukansa humairah kuka angel kuka.

Ni kuwa Idona a kekashe amma dai tabbas hankalina a tashe take a bisa kukan mama da angel, ko kadan bana son zubar hawayen mama sannan bana son naga angel tana kuka.

Nasan kukan mama a gareni babban bala’i ne.

Da kanta ta gaji da dukana ta fita ta barni a dakin duk jikina Yana yi min ciwo.

******* ******** ********

Shiryawa nayi da niyyar zuwa gidan BEST, bayan na shirya nayiwa mama sallama akan zani gidan best, ko kallon inda nake bata yi ba Saboda haka na juya na fita.

Kwatancen da humairah tayi min shi na bi har kofar gidan, saboda ban taba zuwa ba, duk zamana a gidan malam Abbas ban taba sha’awar fita ba.

Da sanda na shiga gidan kamar wata barauniya, motsi Naji a kitchen nasan tana can. Ina shiga gidan na canja murya nace “Assalamu Alaikum ga kayan miya busashshe!!!

Daga cikin kitchen din tace Allah ya bada sa..... Sai kuma tayi shiru, da gudu ta fito daga kitchen din, tana ganina ta ƙaraso da gudu muka rungume juna muna dariya kamar sababbin kamu.

Ciki muka shiga muka ne jafar da mayafina muka kara tsayawa muka kalli juna muka sake kwashewa da dariya,

Zama mukayi aka fara hirar yaushe gamo, can nace ke dalla wai baki iya tarbar bako bane ko ruwa babu ?

Waige waige ta fara alamun neman wani abun.

Nace Wai me kike nema ne ?

Baƙuwar tawa nake nema.

Dariya na sheke da ita nace Ni zakiyiwa iskanci ? To wace baƙuwar bayan ni ?

Wani kallo tayi min kafin tace wlh saidai ki tashi muje mu karasa hada abinda zamu ci amma dai ke ba baƙuwata bace.

Tashi nayi muka nufi kitchen muka karasa aikin gaba ɗaya. Muka bararraje a kasa muka fara cin abinci, muna

13 / 40