Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
waye haidar ??
Shin wace Ma’eesha ??
Duk amsar wannan tambayoyin suna cikin littafi Mai suna Haidar ( the lion
🦁
)
Zamu fara posting nasa in Sha Allah new year jan.
Labari ne da yasha banban da irin labaran da kuka saba karantawa.
Domin a cikin labarin zaku hadu da cin amana, yaudara, fansa, mamaki, takaici, da sauransu.
Labari ne wanda aka haɗa kwakwalwar marubuta wajen samar dashi, saboda jin dadinku.
Goyon bayanku muke bukata.
Zamu saka lambar wayar wanda za’a tuntuba daga zarar mun fara posting nasa, domin masu bukatarsa su biya su karanta cikin aminci.
Karku manta taku har kullum ce Rabi’atu Fulani......
Nagode
🥰
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 25
Banyi aune ba naji duka ta ko ina ta fuska ta ciki, ya Khalil ne shida karuwarsa suka rufeni da duka kamar Allah ya aikosu, ita tana dukana shima yana yi, naga dai abun ba na hankali bane, ban san sanda na saka dukkan karfina na hankada karuwar tasa ba, aikuwa ta fada ta bayan kujera ta wuntsila kanta ya bugu da tiles din falon.
Ya Khalil yana ganin haka yayi kanta da sauri saboda ihun da ta ƙwalla, kafin ya juyo kaina tuni nayi cikin daki da gudu na rufe da key na bar key din a jiki, zama nayi a kasa ina gursheƙen kuka, kai kace mama aka aiko min ta mutu!.
Ji nake wani abun ya tokare min makoshi, takaici baƙin ciki har da kishi ma, mamaki nake ta ya za’ayi ya Khalil ya kawo min wata banzar mace har cikin gidan aurena ? Kuma wai da wata kazamar karuwa zai hadu yana dukana ? Nidin ? Sai kace ba ammatan ya Khalil ba ?.
Ji nayi ya Khalil yana buga kofar da dukkan karfinsa, nayi kamar ban jishi ba, sai kuma naji shiru, bayan kamar minti uku naji ya dawo yana ƙoƙarin buɗe ɗakin da wani mukullin, nan ma dai yaji yaki shiga saboda na bar key dina a jikin kofar.
“Wallahi ko kizo ki buɗe kofar nan ko kuma idan na kamaki sai na lahira ya fiki jin daɗi” Cikin hargowa yake fadar hakan.
“Idan har ka kamani Dan Allah karka barni da rai ka aikawa da iyayena gawata, mara imanin banza mara imanin wofi, kuma wallahi yanda kaci amanata Allah sai ya bi min hakkina” ina fadar haka na fashe da wani irin kuka wanda kai kana jin haka zaka san me kukan daga kasan ransa yake kukan.
“Sumayya Ni kike zagi ?
Eh na zaga ɗin, kuma Wlh ka fitar min da wannan karuwar daga gidana tun kafin na sake fitowa nayi mata abunda bazata taba mantawa dani ba, cikin kuka nake fadar haka, wanda nasan cewa ko karen hauka ne ya cijeni bazan iya fita yanzu na hadu da yaya Khalil ba, dan yanda yake dukan cikina ya tabbatar min da cewar neman rayuwata yake da ta ɗan cikina, a daya bangaren na raina kuma ina jin tabbas zan iya aikatawa wannan karuwar abinda na kudurta a raina.
“Ke kin isa ki kira wata da karuwa ? Ko kin manta asalinki ne ? Kafin ma aje ga wannan ita ai bata da aure! Amma ke kin manta lokacinda da aurenki kika daukeni kika kai gidan mijinki ? Har kan gadonki kika kaini, ko kin manta ne ?!!!!
Sakkk naji nayi, Ni ya Khalil yake wa wannan gorin ? Ni yake fadawa magana haka ? Idan har aka ce ya Khalil zai taba yi min gori haka ko mama ce ta fada bazan yarda ba, kai impact ma mama ta fada din ban yarda ba, tunda tace ya Khalil ba sona yake ba, amma na nuna inaaa nipah ya Khalil yana sona, wani tunani ne ya keto min ƙwaƙwalwata,
Wata rana ya Khalil ya kunsa min takaicinsa na dawo gida ina kuka, na samu mama tana zaune tana tsintar shinkafa a tsakar gida, ina shigowa na fada jikinta na fashe da kuka.
“Mama meyesa ya Khalil zaiyi min haka.....???
Me Khalil din yayi miki ? Ta fada tana ajiye shinkafar da take tsinta.
“Mama Khalil ya daina Sona, da wata na ganshi dazu kuma yanzu nayi masa magana bai ma damu ba, sai ma cewa yayi wai shi ai mijin mace hudu ne, ina fadar haka na kara fashewa da wani irin kuka.
“Sumayya! Ni na haifeki saboda haka dole na fada miki gaskiya, Khalil bazai taba aurenki ba! Idan ma ya aureki wata ran zai goranta miki, Khalil baya sonki, zan iya rantse miki akan hakan, a yanda na fahimta da yanda yake miki gadara ji yake kamar alfarma ma yake miki soyayyar da yake dake.
“Sumayya!! Ki sani duk abinda ake fada akanki yana dawowa kunnena, yanda ake aibata soyayyarku da yanda ake muku kallon kuna fasikanci tare yana dawo min, ban taba daukar hakan ba saboda nasan ƴata bazata taba cin amanar yardar da nayi mata ba, amma dai ki sani zuciya, yau da gobe tun bana ɗauka zan iya ɗauka.
Idan da zan baki shawara ki ɗauka da sai nace ki rabu da Khalil!!!!
Ɗaga kaina nayi na kalli mama nace “mama bazan iya rayuwa ba shi ba! Shine zaɓin raina, ina masa son da bazan iya rayuwa babu shi ba! Ina fadar haka na maida kaina na kwantar a jikinta.
Murmushi mama tayi ta cigaba da shafa kaina “ke a tunaninki yanzu Khalil yana sonki ? Mutumin da baya tsoron ɓacin ranka ai baya sonka.
“Mama fa yana Sona, kawai dai dan sabanin da ake samu ne irin na soyayya.
“Sumayya ba baki nake miki ba amma dai mafi girman kuskuren da zakiyi a rayuwarki shine auren Khalil dan Khalil ba sonki yake ba!!!
Ina jin ta fadi haka na tashi daga jikinta tsam ina tura baki na shige daki.
“Mama na fara nadama!!!! Na fadi haka ina kuka bayan abinda ya wakana tsakanina da mama ya dawo min.
Kuka nake sosai, da gaske nadama ta fara kamani, nadama nake me ƙarfin gaske, ina jiyo ya Khalil yanata surfa min gori iri iri da kuma bakaken maganganu amma ban bi ta kansa ba. Yanzu ta kaina nake dan wani irin nauyi naji ƙirjina ya fara yi ga ciwon kai, kuka nake tun ina iya yi har muryata ta dushe, dag ƙarshe dai daina jiyo maganar ya Khalil nayi wanda da alama ya fita.
A wajen bacci ya daukeni nima ba shiri.
********** ********** *********
Best ta tambayi ya haneep akan maganar ko yanada sani a Lagos ?
Saidai yace bai san kowa ba, amma a abokansa akwai wa’yanda suka sani, amma ta bari gobe sai suje su samu mama akwai maganar da Zasu tattauna.
Washe gari da safe zai fita wajen karfe tara ya ɗauki best suka tafi gidan mama, a lokacin bappa bai jima da fita ba.
Bayan an gaisa little tana jikin mama, sai ya haneep ya fara magana “mama! A yandai ban san wani wanda muke tare dashi a Lagos ba, saidai a abokaina baza’a rasa wa’yanda suke da wa’yanda suka sani a Lagos ba, ko wa’yanda suke da ido, idan ana so zan iya tuntubarsu su tayamu duba, saidai wani hanzari ba gudu ba.
Sumayya aure take yi acan Lagos ba wani abun ba, idan har muka saka wani ya bibiyar mana ita hakan zai taba mata mutuncinta, duk yanda zamuyi masa bayanin cewa aure take bazai yarda ba, zai ɗauka ta tafi yawon shashancine saboda haka nan gaba Wannan abun zai iya taba mata mutuncinta da na yaranta zuwa gaba aure ma sai yayi mata wuya, kin san rayuwar nan yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, a shawarce a matsayina na danki mama kuma yaya a wajen Sumayya kamar yanda kika dage da addu’a kuma kika saka ana hakan to mu cigaba da yi, Allah maji rokon bawansa ne tabbas zai amsa rokonmu zai juyo da hankalinta gida.
Gyada kai mama tayi dan tabbas sai yanzu ta hango abunda haneep ya hango mata, barin ma dai yanda aka sakawa rayuwar ƴarta Idanu a unguwar nan cewa zasuyi an nemota a lagos a wajen shashanci.
Cigaba da kwantar mata da hankali yayi har Saida ta gamsu da cewar ba sai an nemo Sumayya ba, sai bayan ƙarfe goma ya tafi uzurinsa ya bar best a gidan mama akan ta cigaba da kwantar mata da hankali idan ya tashi daga kasuwa zai biyo su tafi.
********* ********* ***********
Wata gigitacciyar yunwa ce ta tasheni ba shiri na farka, agogon dakin na kalla naga karfe sha daya na dare, da sauri na jawo ragowar abincina na fara ci, saidai ba shi da yawa saboda haka ina gama ci na fara tunanin yanda zan sake dafa wani.
Ina nan zaune sai Wajen sha biyu da rabi naji fitar ya Khalil tare da yarinyar nan, inajin yana mata magana akan kar ta dawo gobe zai kirata da kansa.
Yana fita na fito na kulle gidan na shiga kitchen dan kar ma ya dawo ina girki.
Idan ba Idona ne ke min gizo ba sai nace gaba daya babu shinkafa gas ya taho karewa sannan ga taliya ma bata wuce carton daya ba gaba daya dai abincin bazai wuce sati Daya ba, a yanda nakeda cin abincinnan sosai.
Dafawa nayi na dawo na bude gidan sannan na shige daki na kulle.
Saida na gama ci na koshi saina fara tunanin yanzu idan abincinnan ya kare ya zan yi ?
Sadakina ne ya fado min a rai! Ranar da aka daura min aure aka bani sadakina a hannu a hanya muna hanya na bawa ya Khalil sadakin akan ya ajiye min ( Ni ga ƴar daɗi soyayya ) yanzu kuwa nasan da wuya ya bani sadakina, amma dai zan gwada tambayarsa.
Sai Wajen shida ya shigo ya kwanta yana bacci a falo, daga kofar dakina na zauna ina jiran ya tashi, ban fi minti talatin ba kuwa ya tashi yin fitsari, yana tashi yaga Nima na mike tsaye, bai kalleni ba yayi hanyar banɗaki.
“yawwa nace ba!
Idan ya waigo ya kalleni to bangon dakin ya kalleni, shigewa daki yayi na tsaya a wajen ina kunkuni.
Bai jima ba naga ya dawo, zai koma kan kujera ya kwanta nace “yawwa nace maganar sadakina da na baka ajiya lokacin muna hanyar zuwa nan, inada bukatarsu.
Saida yaja iska kafin yayi min reply dan har na fidda ran ce wani abun sai kuma naji yace “kin daukeni wanda bai san abinda yake ba ko ? Uban waye zai ciyar dake bayan ba jin maganarsa kike ba ? Ko kin ɗauka ban san kina bude kitchen ki dafa abinci ba ? To kin dafa sadakinki, sisi bazan baki ba, sannan joy da kika jiwa ciwo na kaita asibiti anyi mata dressing shima a cikin sadakinki, Naira biyar bazaki samu ba, kuma ki fice min daga nan kafin na tashi.
Kuka na zube a wajen ina yi kamar wata yarinya, ganin ya tashi ya nufo inda nake ba shiri na gudu daki na rufo ƙofa, ina cikin dakin ina zuba masa Allah isa.
Tunani na fara yi kenan ya zanyi yanzu ? Da me zan ceci kaina da dan ciki daga wannan yunwar ? Anan ina zaune ina tunani bacci dai ya sake daukata.
********* ********** *********
Haka rayuwa ta fara turawa a haka har Saida na cinye abincin gidan gaba daya sannan hankalina ya kara tashi, ba wanda na sani a garinnan bare na nemi taimako gashi bana da waya.
Maman Uche ce ta fado min a raina yau yana bacci a Ɗakinsa n fito na jawo kofata na mayar na rufe kamar akwai mutum a ciki, lallabawa nayi na fice daga gidan har Saida naje gidan Maman Uche.
Ina shiga ta tareni da murna “yalinya mai cau yau kece a house dina ( da yake hausarta bata gama cika ba kuma sannan da yarinya mai kyau take kirana ).
Murmushi nayi nace yau na kawo miki ziyara ne Maman Uche.
Kama hannuna tayi muka shiga daki, nan muka zauna muna dan hira sama sama saboda ba fahimtar hausarta nake sosai ba Ni kuma ba turanci na iya ba bare broken, Dan turancin nawa baiyi kwari ba, ina dai ji amma bana iya mayarwa shima broken din dan kadan nake ji bana iya mayarwa.
Can na nisa nace “maman Uche anan garin waye kika sani mai Siyan kayan daki ?
“Kece zaki siyar ? Ta tambayeni da hausarta ba daɗi.
Nace eh!
Okay ina siya Ni nan da kika gani komai da ruwana, me zaki siyar muje gidan ki nuna min ?
“Ah ah! Na fada ina zare Idona, ai idan mijina yasan zan siyar miki sai ya kusa yankani, gobe weekend nasan zai fita da safe zuwa inda yake zuwa ban san dai ina yake zuwa ba, idan ya fita zan zo nayi miki magana sai muyi sauri kije ki siya.
Da wannan yarjejeniyar na bar gidanta dan bana son jimawa kar ya Khalil ya tashi mu hadu.
Har na dawo bai tashi ba, na shige cikin daki, dan abinda na ciyo a gidan Maman Uche ne ya rikeni a wannan daren, amma zuwa safiya kamar anyi min sata a cikina, dan wata azababbiyar yunwa nake ji inata lekensa ta taga har Saida ya fita wajen bakwai na safe, yana fita Nima na dauki mayafina sai gidan Maman Uche da sauri muka zo na nuna mata deep freezer din dakina, matar nan saboda kanwar barauniya ce saita siya dubu arba’in, wacce idan lafiya lafiya ne saita kusa ɗari, ban damu ba haka na siyar mata, na kwashi kudi naje na siyi carton din taliya uku da kuma kayan mai da yaji sannan nayo refilling na gas, ( a duniya ba abinda take burgeni sama da taliya da manja ko farin mai ) gaba daya kuɗin da ya rage min a hannu bai kai dubu biyar ba.
Bayan kwana uku na kuma kiranta ta kuma Siyan kayan kallona na cikin daki, dalilin da yasa nake bata kayan dakina saboda nasan ba shigowa yake ba, bazai san na siyar ko ban siyar ba.
******** ********* *********
Haka rayuwa ta dinga turawa Saida ya zamana na siyar da komai na dakina saboda yunwa, kawai katifa ce yanzu a dakin sai kayan ruwa, gadon ma na siyar katifa nake yar wa na kwanta wardrobe Dina ma na siyar kayana suna Ghana must go. Tsakanina da ya Khalil ba magana, saina yi sati ban ganshi ba, bai damu da cina ko sha na ba, sau biyu a tsakankani yanzu yana dukana kuma muguntarsa na fuskanci idan zai dakeni cikina da kaina yake hari, shiyasa na samawa kaina lafiya na daina bari muna haduwa, Maman Uche yanzu ita na ɗauka yar uwa a garinnan, har kuɗi yanzu tana iya bani idan yaso saimu warware a cinikayyar da muke.
Cikina yanzu yana kan wata na bakwai, ya girma ya fito sosai, yanzu na rage bacci abinci ne dai har yanzu ban daina ci ba, saidai karuwa ma da cin yayi, dan yanzu lokaci daya ina iya cinye taliya daya ko sama da haka ma, yanzu ina dafa taliya leda uku ne, a wunin rana daya nake cinyeta.
Waya kuwa na gaji da nema, wani abun Allah kuma har yanzu banyi tunanin Siyan waya da kuɗin da nake samu ba, ( a wannan lokacin na yarda da cewa yunwa tana iya canja mutum gaba daya ta canja masa mindset, )
Kwana biyu yanzu abincina ya dauki hanyar karewa na koma lallabawa, a da ina cin leda uku yanzu na koma cin leda daya da rabi zuwa biyu, ba’ayi nisa ba, shima abincin ya kare gaba daya, wunin yau ruwa nake ta sha saboda ban san me zan siyar ba yanzu na siyi abinci, ji nayi ina niyyar mutuwa da raba hanya na dauki hanyar gidan Maman Uche muka je ta duba plasma din falo ko zatayi mata ( bahaushe yace da rigimar ciki gwamma ta waje, da wannan tunanin nayi wannan kasadar ).
Mun gama ciniki ta siya dubu ashirin da biyar ta bani kudina casss tasa yaronta ya dauki plasma aka ya dora muna juyawa muka ga mutum a tsaye a bakin kofa da jaka a rataye a kafadarsa yana kallonmu...........!!!!!!!
Tirƙashi jama’a ammatan shalelenta fa ta zama barau....barau.....
🤭
Ba ruwana kar team Sumayya suce na kirata barauniya,
Mu hadu a page 26 in Allah ya yarda nice taku har kullum Rabi’atu Fulani.
Talla!
💫
Talla!!
💫
Talla!!!
💫
💫
ALIYU HAIDAR ( THE LION
🦁
)
💫
Paid Book...
By
Rabi’atu Fulani....
&
Ubeera.....
Happy New Year Update......
A zaune suke suna wa junansu wani sanyayyen kallo, wanda duk wanda yaga yanda suke kallon, yasan sun nutse sosai a cikin kaunar junan su.
Gajiya tayi da irin kallon da yake mata dole yasa tayi ƙasa da idon ta.
Lovely!!!!! Taja sunan sosai tana marairaice masa.