ICCEN DAMUNA COMPELET HAUSA NOVELS BY RABIAT FULANI.docx

Author :  Rabiat Fulani Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   26 / 40

75K to 78K   out of 117.2K words

baiwar Allah....



Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya

🙏





FULANI

TRUE LIFE STORY.....

💫

❣️ ICEN DAMUNA

💫

❣️

PAGE 26

Ya Khalil ne a tsaye a kofar dakin, nan da nan jikina ya fara rawa, kamar an kafeni a wajen naji kafafuna suna rawa kuma na kasa guduwa.

“Wacece wannan”? Maman Uche ta tambaya da hausarta mara daɗi tana nuna min ya Khalil.

Wata tsawa ya Khalil ya daka mata cikin broken yace “ubanki ne! Me ya kawoki gidana ? Barauniya ce ke ?

Maman Uche yar duniya ce, saboda haka tsawarsa ba ta bata tsoro ba, a tsanake ta kalleshi tace “Ni ba barawo bane kaya akayi min talla nazo siya, saboda haka karka sake kirana barawo.

Ya Khalil karasowa yayi cikin dakin, nunawa Maman Uche hanya yayi “bi nan kafin na saka police su kama min ke su kulle.

Maman Uche tana jin maganar police ta dauki hanyar waje bayan ta karbi kudinta da ta bani, yaronta kuma ya ajiye plasma din.

Kusa dani yazo ya saka hannu ya ɗago wuyana, idanuna ne suka firfito saboda naji shaƙar da yayi min, Saida ya ga na galabaita sannan ya saukeni, kallona yake cikin tsana.

“Dan ubanki yaushe kika fara min sata a gidannan ? Cikin hargowa yake maganar.

Kakarin amai nake na kasa magana.

Ban san me ya tuna ba, naga ya tashi ya shiga dakina, ai sai ji nayi cikina ya ɗuri ruwa, ba shiri na yunkura da dukkan karfina na nufi hanyar waje, saidai kafin na kai ga fita daga gidan ya biyoni yasa ƙafa ya taɗoni na fadi rub da ciki.

Dukana yake yi tun ina iya kuka har Saida na daina gane komai, cikina kawai yake duka, fuskata kuwa duk ya farfasata, Saida yaga na daina ganewa sannan ya tsallakeni ya shige cikin gidan.



********* ********** **********

Buɗe Idona nayi na tsinci kaina a asibiti, Maman Uche ce a kusa dani, sai wata nurse a tsaye a kaina.

Sannu suka fara yi min, amma kallonsu kawai nake iya yi.

Sai dare likita yazo a lokacin ban jima da tashi daga wani bacci ba.

Dubani ya sake yi sannan yayi min sannu ya fita.

Sai Wajen karfe tara sannan Maman Uche tazo min da abinci ta dubani.

Labari ta fara bani, ta manta wayarta ne akan kujera da ta zauna muna ciniki shine ta dawo ɗauka saita sameni a halin da nake ciki, shine ta shiga tayiwa mijina magana amma bai kalleta ba, shine ta fita ta nemo taimako ta kawoni asibiti, yanzu kwanana biyu a asibiti, ana jiran farfadowata ne sai ayi min aiki a cire abinda yake cikina, ana jiran kuma mijina yazo ya saka hannu ko babana domin a yi min theater, saidai da kamar wuya ace ɗan cikina yana raye, saidai wani iko na Allah a cewar likitoci.

Hawaye ne suka fara zubo min masu zafi, zuciyata ce take tafarfasa, ban taba jin tsanar wani mutum a duniya ba yanzu kamar Khalil.

Ashe masoyi zai iya rikiɗewa ya koma maƙiyi ? Ashe ya Khalil zai iya wulakantani haka ? Ashe ya Khalil zai iya tozartani ? Ashe ya Khalil zai iya kasheni ? Ashe ya Khalil dama ba ya sona ? Ashe ? Ashe ? Ashe ? Tambayoyi ne a raina maƙil wanda na rasa me bani amsarsu sai wanda nakeda tambayar akansa.

A ranar kwana nayi ina kuka saboda zafin abinda ya Khalil yayi min, yanzu shikenan ɗan da na ƙwallafa rai a kansa ya khalil ya kashe min shi ?

Ba’ayi min aikin ba sai wata washe garin, an ciro ɗa namiji amma ba rai kamar yanda likitoci suka fada, an bani shi na rungume yaron a ƙirjina ina jin wani sonsa yana ratsani, na sha kuka sosai yaro mai kyau kamar babansa.

Ba abinda zan ce da Maman Uche dan ta daukeni kamar ƴar cikinta, ta kula dani a asibitin nan sosai, ta kashe kuɗi akaina har na rasa bakin yi mata godiya ita da mijinta, anan ne nasan ashe ta taba zaman arewa tana yabonmu mutanen kirki ne mun yi mata halacci shiyasa itama ta kyautata min jin dadin abinda akayi mata.

Satina biyu a asibitin amma kullum saita kawo min abinci.

A ranar da na cika sati biyu ne ya Khalil yazo asibitin, ina kallonsa na ɗauke kai kamar yanda shima yayi, wata tsanarsa nake ji a raina mai kyau, ji nake a duniya yanzu banada maƙiyi kamarsa.

Takarda kawai ya ajiye min a jikina ya juya ya fita daga ɗakin.

Ban bi ta kanta ba na cigaba da tunanin da nake, amma lokaci zuwa lokaci hankalina yana kan takardar ina son budewa.

Waya naga an ajiye min again a saman takardar, daga kaina nayi na sake kallan wayar, wayata ce ya Khalil ya dawo ya ajiye min, ya kuma sake juyawa ya fita bai ce komai ba.

Yana fita na jawo takardar na fara karantawa “𝑁𝑖 𝑖𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙 𝑛𝑎 𝑠𝑎𝑘𝑖 𝑚𝑎𝑡𝑎𝑡𝑎 𝑆𝑢𝑚𝑎𝑦𝑦𝑎 𝐴𝑏𝑢𝑏𝑎𝑘𝑎𝑟 𝑠𝑎𝑘𝑖 𝑢𝑘𝑢!!!!!

Na rasa me zanyi a wannan lokacin! Murna zanyi ko bakin ciki ?

Hawaye naji suna zubo min masu ɗumi a fuskata, nidai gashi nan ina jina sakayau ba bakin ciki ba farin ciki kuka nayi ta yi sai Wajen karfe sha biyu na dare sannan nayo alwala nazo na tada sallah, sai Wajen asuba sannan na hakura na zauna ban jima ba aka tada sallar asuba na tashi nayi sallar asuba, a wannan lokacin dai ko Sarkin sata bacci yayi kadan ya saceni, wayata na jawo na kunna.

Fuskar wayar na kalla, hotona ne da na best akan lock screen wallpaper, akan home screen kuma hoton ya Khalil ne, ba shiri na shiga na canjashi da wani.

Phone call history Dina nake ta kalla a raina Ni kaina kunyar kiran gida nake, na rasa wa zan kira! Mama ko best ko ya Ahmad ? Ko kuwa humairah ? Shahada nayi na danna kiran best dan ita kadai ce zata fahimceni kuma bazata taba guduna ba.

********* ********** **********

Kamar a mafarki take jin ringing na wayarta, bata jima da komawa bacci ba bayan tayi sallah dan lokacin baifi karfe shida ba, ya haneep kuwa yana masallaci ma bai dawo ba.

Tsaki tayi ta jawo wayar ta ɗora a kunne batare da ta duba waye me kiran ba, cikin magagin bacci tace “Hello!

Shiru taji anyi, sai kuma take jin kamar kuka daga ɗaya bangaren, bude ido tayi tana fatan Allah yasa ba wani ne ya mutu ba, tunanin duba wayar taga me kiranta ma batayi ba!.

“Hello waye yake magana!

“Best!!!!!!

Ko daga baccin mutuwa taji wannan sunan da kuma Muryar bazata manta me ita ba, da sauri ta duba fuskar wayar taga waye me kiranta! SASHENA ta gani sunan radau a fuskar wayar, marin kanta tayi dan ta tabbatar da ba mafarkin da ta saba bane.

“Tabbas ba mafarki bane! Ta fada a bayyane.

Ba mafarki bane best sashenki ce take kiranki, Sumayya ta fada tana me rushewa da kuka.

Wani irin kuka best ta fashe dashi “ina kika shiga ? Ina kika saka wayarki ? Meyesa ba’a samunki ? Meyesa zakiyi mana haka ? Ko zakiyi fushi da kowa ai bazakiyi damu ba! Kina ina yanzu ? Haka ta dinga jero tambayoyi batare da ta jira an bata amsa ba.

Ina Lagos yanzu, ki tura min kuɗin dawowa yanzu da kuma wasu rarar kuɗin.

“Nooo ki fada min inda kike zamu zo nida ya haneep mu taho dake.

Saida na tambayi address a wajen wata nurse sannan na fada mata.

To dan Allah ki bar wayarki a kunne zan hadaki da mama yanzu zani gidanta.

Ina ajiye waya ta kira haneep tace yayi sauri yazo gida.

Ba shiri ya baro masallaci, yana zuwa ta bashi labari da jallabiya a jikinsa ya dauketa suka tafi gidan mama lokacin.

Ko kofa ba’a bude ba suka kwankwasa, mama Saida gabanta ya fadi tace to wannan lafiya ? Lokacin tana ƙoƙarin haɗa wuta “waye ? Ta tambaya tana kokarin tasowa, a lokacin ma bappa ya fito daga daki jin kwankwasa kofa.

Mama nice! Best ta fada.

Da sauri mama ta bude kofa tana tambayar lafiya kuwa ?

Haki best take yi kamar wata wacce tayi gudu.

Kamata tayi suka karasa cikin gidan, haneep ya biyosu, sai a lokacin mama ta ganshi, tambaya mama take lafiya, amma best ta kasa magana.

“Sumayya ce ta kirata a waya da safennan yanzu tana so zata dawo gida a tura mata kudin mota, da alama addu’arki ta karbu mama, shine ita kuma halima take ta wannan hakin saboda farin ciki, yanzu ma haka ta kwatanta inda za’a sameta, to in Sha Allah nida best zamu bi Flight din yamma zamu je mu taho da ita!! Ya haneep ne yake wannan dogon bayanin.

Zubewa mama tayi a kasa tana hawayen farin ciki, sai kuma tayi sujjada ga Allah, yanzu Sumayyata ce ta kiraku ? Kai alhamdulillah!!

Kiran Sumayya best ta sake yi, ringing biyu ta daga, tana ɗagawa ta mikawa mama, Muryar Sumayya ce tayi mata tsinke a kunne ta hanyar yi mata sallama.

Kuka mama take tace sumayya!!!

Nan kuma sai kuka, sumayya na kuka itama na kuka.

Ki gafarceni mamah! Bazan sake bijirewa umarninki ba in Sha Allah. Kiyi hakuri ki bawa bappa hakuri shima.

Shhhh!!! Bakiyi komai ba, mun gafarta miki har bappan naki ko bappan yara ? Mama ta fada tana kallon bappa da tun dazu yake tsaye bai ce komai ba.

Ƙwalla ce a Idonsa kai kawai ya gyadawa mama.

Nan fa hira ta barke gida ya ɗauki hira har bappa aka bawa waya yayi magana da sumayya, humairah da angel duk sun tashi dan a lokacin da best tazo suna bacci.

Likita ne yazo zagaye dole SUMAYYA tayi sallama ta ajiye wayar, su best kuma suka tafi gida shiri.

Suna fita mama ta mikawa humairah waya akan ta kirawo mata ya Ahmad, ba shiri ta labarta masa komai, yayi farin ciki matuka.

********** ********** *********

Bayan na ajiye waya kuka nayi ta yi, lallashin duniya naki shiru, nadama ce nake yi me tarin yawa, tare da jin kunyar family Dina da kowa ma, saboda yanda suka dage akan kar naje Lagos gashi gashi, amma nayi kunnen uwar shegu.

Yanzu gashi duniya da kuma soyayyar da na zaba sun koya min darasi mai wuyar koya.

Bacci ne ya daukeni ban sani ba, ashe a allurar da likita yayi min akwai ta bacci.

A daren ranar su best suka ƙaraso, lokacin ina bacci still, best zama tayi tana ta kallona kamar tayi kuka saboda yanda na rame na ɗashe, gaba daya kamar ba Sumayya ba.

Sai Wajen sha biyu na dare na farka, lokacin ya haneep ya tafi masauki, ita kuma best tana zaune tare dani, kafin ya wuce saida ya fara nemo mn abunda zanci idan na farka.

Ina farkawa naga best a kusa dani, rufe idon na sake yi na sake budewa, saidai still itace a zaune a gabana tana kallona ta toshe bakinta tana son hana sautin kukanta fitowa.

Tashi nayi zaune na rungumeta sai sabon kuka, kuka kawai muke muna rike da juna, saidai muka sha kuka muka koshi sannan na lura da baby a kwance a gefena tana bacci! Kallon best nayi mai nuna alamun tambaya, gyaɗa min kai kawai take ba magana.

Ɗaukar babyn nayi na rungume, sai hawaye, a lokacin kewar Marigayin babyna ya fado min, kuka biyu nake, na kewar rashinsa da kuma na farin cikin ganin dan best.

Wata sabuwar hirar ce ta balle, nan ne best ta bani labarin cewa babyn ai sunana aka saka mata, farin ciki kamar nayiwa best sujjada, Nima haka na kwashe labarin duk abinda ya faru tun zuwana Lagos har zuwa yanzu, ba abinda na boye mata, ya Khalil yasha zagi, tsinuwa, jafa’i, bala’i, da komai ma ya shasu, ban tanka mata ba duk abinda take cewa, dan Ni kadai nasan me nake ji akan khalil.

********** ********* **********

Da safe ya haneep ya kara siyo mana kayan kari muka karya, Maman Uche ce tazo dubani kamar yanda ta saba, saidai ganina da baki yas tayi turus.

Gabatar mata dasu nayi suma n gabatar mata da su, mun jima anata hira mukayi sallama da maman Uche saboda da yamma zamu wuce gaba daya, kudi na karba a hannun best mai yawa na bata tare da yi mata godiya, sannan na karbi lambarta wacce zan iya samunta.

******** ******** ********** Karfe biyar jirginmu ya tashi sai Kano, zo kaga farin ciki, zo kaga kuka a wajen mama dani da sauran yan gidan, ya Ahmad ma yazo saidai ba magana sai kallon juna, sai hawaye, yau har bappa Saida yayi hawaye, fadar irin farin cikin da ake yi yau a gidanmu kai kasan fada bata baki ne.

Tun ina ɗari-ɗari har Saida na dan saki jikina, ganin ba wanda ya tayar min da magana, a daren yau na bawa gidan labarin zaman aurena komai da komai ban ɓoye ba, nan ma dai kukan akayi, sannan Khalil ya sake shan tsinuwa, a gidanmu yau best ta kwana, kwanan hira muka yi yau, hira ba kama kafar yaro.

“Daddare ina kwance mama ta kawo min abinci, sedai duk yanda naso naci abincin na kasa ci.

Damuwa dan kare a cikin raina, nakasa yarda da abun da khaleel yamin, har yanzu ina mamaki.

Kalaman sa, suna min ciwo a duk lokacin dana tunasu, gashi duk daren duniya se sunzo kaina.

A yanzu idan akwai wata kalma da natsana a duniya ita ce kalmar soyayya.

Soyayya gaba daya karya ce, tunda har masoyi ze iya cutar masoyin sa, tabbas soyayya karya ce.

Bana bukatar namiji a tare dani a yanzu.

Rayuwa ta kawai zan gyara da gobe na.

Amman yanzu babu lissafin namiji a tare dani.

********* ********* **********

Wata kalan rayuwa nake tamkar dai bani ba, na koyi miskilanci ta karfi da yaji.

Ko da yaushe ina zaune shiru dani, bani da aiki se tunani.

A duk lokacin da zan tuno irin rayuwar da nayi kuwa sedai kawai naita zubar da hawaye.

Tabbas khaleel ya cutar dani cutar mafi muni a duniya.

Duk yanda nake tunanin dame na karu a rayuwa da khaleel ban samu komai, se tarin baƙin ciki.

Ya cimin mutunci yaciwa iyaye na, kuma na kasa komai a kai.

“Duk yanda mama take jana ajiki na kasa sakewa da ita.

Saboda gani nake gaba daya ban cancanci wannan kulawar datake bani ba.

Tsakani na da baffa kuwa, kadaran kadaham.

Yau a kalla nayi wata biyu a gida, a madadin na fara maida jiki na, sema wata sabuwar ramar da nakeyi.

Mama tayi rarrashin har ta gaji.

Da zan iya nima da na cire komai a raina kodan kwanciyar hankalin mama.

Amman ina nakasa, kullum ji nake tamkar a lokacin komai yake faruwa dani.



********** ********** *********

Tun da na tashi ina kwance, abin duniya duk ya dameni.

Ko shayin da mama ta kawo min na kasa sha.

Har wajen 12 ina kwance.

Sallamar sace tasa na tashi zaune amman ban fito ba, ina jin sa suna gaisawa da mama.

Sosai mama tayi masa godiya kuma tasaka masa albarka.

Bakomai fa mama ita ɗin ai kanwata ce.

Idona kawai na lumshe ina jin yanda ya kara samun matsayi a cikin zuciya ta.

Sumayya!

MaMah!

Bakiji yayan ki bane?

Gani nan ai.

Ina zuwa wajen mama ta tashi.

Zama kawai nayi nakasa ce masa komai kaina a kasa.

Buzuwa!!!

Uhm ya doctor.

Meyake damun ki? Wani waje na miki ciwo ne.

Kirjina na nuna masa, zafi yake min ya doctor! Ciwo yake min sosai! Bana iya bacci ya Ahmad! Inajin tamkar na mutu nabar wannan duniyar, nagaji da rayuwar gaba daya.

Rayuwa ta bata da amfani.

Kuka nake tamkar raina ze fita ina dafe da kirjina..

Innallilahi wa’inna ilaihir’raji’un!!! Kawai yake maimaita wa.

Shikenan ya isa haka dan Allah kiyi shiru.

Kaman yace na kara sautin kuka na, kawai na kara fashewa da kuka.

Ɗagowa yayi zemin magana yaga mama a tsaye tana hawaye.

Mama zamu je asibiti na dubata.

Se kun dawo!

Tashi muje.

Tashi kawai nayi nabi bayan sa, muka nufi motar sa.

Har mukaje asibitin kuka nake.

Ya isa haka mana, kiyi shiru dan Allah.

Nakasa tsaida kukan.

Gaba ɗaya na birkita mishi tinani har besan sanda ya daka min tsawa ba.

Malama nace kiyi min shiru, ya kike so nayi ne a’a! Wani ya aike ki ne? Sanda ake hana ki maganar wa kikaji?

Wallahi kar na kara jin kukan ki a wajen nan!!

Tsitt na shanye kukan se ajiyar zuciya da nake ta saukewa, gaba daya ya bani tsoro, bansan ya iya faɗa har haka ba.

Kan kujera kawai ya zauna ya lumshe idon sa.

Munfi minti 30 a haka.

Sumayya!! Ya kira sunana a hankali.

Kumburarrun idanuwana kawai na ɗago na zuba masa.

26 / 40