Author : Rabiat Fulani Category : Romantic Hausa Novels
shaleleh!!!! “Wayyo kauna!!!
Nakasa tuno gida, bare hukuncin da za’ayi mini...
Naduba bazan iya Shiga ƙasan gado ba, kuma baxan iya Shiga wardrobe ba, garin dube dube na naga kayan wanki bandamu ba na Shiga cikinsu na boye...!!!
“Ina Jin Mata suka shigo suna dube dube, amman basuga komai ba, har sun juya xasu fita....!!
Saboda tsoratar danayi bansan sanda na fito ba iña kuka...!!!
Salati suke da salallami...!!!! Kalli yarinya kyakkykwa.!
Ke kam meya kaiki aikata haka..???
Kuka nake ina rokon su karsu fada a gidan mu mamata bata da lpy....
Haka Daya a cikin su ta rikeni, Daya ta janyomin hijabi ta rufemin fuskata,
Bansan dalilin rufe fuskan ba, seda muka fito Naga lungun gidan a cike da Yan kallo,,
Kuka nake sosai Dan na ma kasa Addu’a..
Wani gida muka Shiga Ashe matar gidan yar Hisbah ce!!!
Zaunar dani sukayi sannan matar gidan tace “Bamu wayarki.... na bada babbar, Allah yasa basu ga karamar wayata ba,,
Kinji kunya wlh.! Da uniform ma kike yawo; karamar yarinya dake! Dole mu Kira iyayenki, cewar wata ƴar Hisbah”
Duk da kuka nake, bansan sanda nadago na xabga mata harara ba...
Mun Dade a lungun anata maida magana, damu dasu, sannan sukace mutashi a tafi office dinsu.
A lokacin tashin hankalina ya dawo sabo Dan har anyi sallar magriba nida xan koma gida karfe 5:30...
Inaji ina gani muka hau mota dasu, muka nufi ofishin Hisbah, abunda betaba faruwa daniba a rayuwata,
Tsorona Allah da annabi kauna yasamu labari..!!!
Zuwa lokacin da muka karasa ma na nemi kukan narasa,
Sanda muka je magana Ake ta sallar isha’i,
Zuwa lokacin hankalina ya koma Kan mama..
Nasan tana can hankalinta a tashe tana tunanin lafiya? Ko ina na shiga....!!!
Ba’a hadani dashi ba, rabamu akayi da abdool da aka kamani dashi, wajen da aka ajiye shi dabam Nima dabam.
Tambayoyi ne Kala Kala Ake min su, tun ina amsawa har halin nawa ya motsa.....
Dan ban san sanda na ajiye tsoro a gefe ba muka fara fadi in fada dasu....
Dan wanine Naga rainin hankalinsa yayi yawa kawai na yaɓa masa magana, yace “wlh saina kwana....”
Nace masa bakomai hakan ma nasara ce.....
Bamu number babanki!!! Ya tambayeni cikin fushi.
Ba musu nabashi, saboda na Riga na saddaƙar, komai zai faru ya daɗe bai faru ba, duk da a tsorace nake don wlh ina mugun tsoron babana!! Amman yana iya,? Haka na zaɓawa kaina....
“Zuwa karfe 9: sega Abbanmu ya zo!!!
Ina ganinsa na fara hawaye..
Yana zaune aka fada masa abunda nayi;
Suka tasoni nazo gabansa ina sunkuyar da kaina.... Dan nakasa kallonsa,
Tambayarsa ta farko ina yaron Yake, akaje aka taho masa dashi, yaga bawanda Yake tunani bane, Kai tsaye ya rantse! Yace wlh da wancan Dan Iskan yaron ne sena daura muku aure yanzun nan!!! A wajen nan!!
Bansan sanda nace Abba ai kasan ina son shi!!!
Kaina yayo zai dakeni aka rikeshi ana bashi hakuri!
“Nikam a lokacin tunani nake daman da kauna ne a mana aure shikenan na huta”
Duk da acikin tashin hankali nake bansan sanda wani lafiyayyen murmushi ya suɓuce min ba!!!!
Nan dai sukayi rubuce rubucen su akan zamu dawo da safe,
Abbanmu ba boyayye bane shiyasa abun yaxo da sauki,
Bamu muka bar wajen Ba se wajen 11: pm...
Nakasa tsayawa na jera dashi sauri kawai nake zubawa... Koda muka hau napep a tsorace nake da shi, don gani nake kaman ze iya Duka na,
Koda muka sauka ban tsaya jiran Saba, sauri! Sauri! Gudu! Gudu!! Haka na karasa gida...!
Ina zuwa nasamu maman mu a tsakar gida da humaira, yaran sunyi bacci..
Kuka nake sosai nace mama ki yadda dani, wlh ban aikata komai ba, kawai dai naje wajensa ne, sai tsautsayi ya fadamin, amman wlh babu abunda nayi.....
“Ita tama kasamin magana se wani irin kallo da take min”
Tana shirin magana baffan mu ya shigo! Setayi shiru Dan batasan tare muke ba...
Ita wannan yarinyar dole saita zubar min da mutunci hankalin ta Yake kwanciya,
Ina xaune ta wuce da uniform Ashe ba makaranta tafi ba gidan saurayi taje,
Yanxun nadawo daga Hisbah, duk yayana babu mai yi min abunda yarinyar nan takemin, baba ya fada cike da bakin ciki.
Mama ta ma kasa magana sai kukan datake, kukan datake ne yasaka humaira kuka, nima bansan sanda na fara kuka ba,
“ Aure zan Miki ki fito da miji”
Banma Bari ya karasa ba da sauri nace: Abba ni KHALEEL nake so!!!!
Har suna hada Baki shida mama wajen cewa bazai aureni ba,
Nima banyi nauyin Baki ba wajen fada musu zai aure ni,
Ina fada ina kuka...!!
Fada suke ta inda suka Shiga bata nan suke fita ba,
“Ni kam hankali na Baya kansu,
Meyasa kowa yake cewa khaleel bazai aure ni ba ?? Meyasa ??
Nikam ranar ban runtsaba ga fargabar komawar mu wajen hisbah! Ga tsoron Kalmar da kowa yake fadamin akan shalelenah!!!
Baccina dai rabi da rabi ne,
Yayinda ni nabata lokaci wajen tunane tunane ita kuma mama tana can tana kaiwa Allah kukanta!!!!
Karfe 8 muka fita daga gida ko abinci banci ba bare wanka,
Kusan lokaci Daya mukaje da iyayen abdool nikam ko kallansa ba,
Koda mukaje office din ana maida magana tashin farko maganar da Abbanmu yayi tasani mikewa batare da nashirya ba...!!!
A cikin Ku masu aikin Allah, idan har da mai son ƴata sumayya, gata nan nabasa ita kyauta yabada sadaki kawai a daura aure!!
Aure kuma...!!!???
Na shiga maimaitawa cike da tashin hankali, hawaye Kam tamkar an Bude famfo, hankali na bai Kara tashi ba saida Na ga yanda Yan hisbah sukayo chaaaa akaina kowa yana Sona,
Ina zaune suna shawarar, wazai hakura ya barwa wani!
“Nayi danasanin saninka a rayuwata abdool, ban Karu da komai ba a sanadiyarka sai tashin hankali, yanzun gashi nan ina shirin rasa khaleel saboda Kai”
Wadan nan sune tunane tunanen danake ina kuka, Ashe jiya banyi kuka ba yaune nake asalin kuka....
Sumayya! Sumayya!! Ke sumayya!!! Wai tunanin me kike??? Tsawar da Abba yamin ita tadawo dani hayyacina...
Babu komai na fada cike da rawar murya, irin ta me kuka.
Wa’azi suka mana sosai da nasiha.
Mukace in sha Allah baxamu Kara ba,
An kashe case mun fito, wani Dan hisbah ya biyomu babba da Shi, yanawa Abba maganar auren, yace babu matsala ya karbi number sa.
Duk da sun dawomin da waya ta bai basu number na ba.
Haka muka fito muna tafiya baffa nakara min nasiha..
“Nidai ba wannan ne a gabana ba tunda mun rabu lafiya ai shikenan.
Amman nasan nida wayoyi na da fita kuma munyi hannun riga, wata kila harda makaranta ma...
Muka tari napep ya kaimu unguwarmu.
Ina sauri nayi gaba nabarsa a baya naji yace
Sumayya! Ya fada tamkar bai taba dariya...
Na’am Abba.. na amsa idona a kasa... Zo nan!
Gani... hannuna ya rike kaman ƙaramar yarinya ko kuma wadda zata gudu....
Abba ana kallon mu..
Na fada idona taf hawaye...
Kedin ai yanxun ba abar yadda bace ya fada yana kare daure fuska.
Jiki na babu kwari haka na bishi hannu na cikin nasa kaman karamar yarinya....
Be cikamin hannu ba har mukaje gida...
“Shiga..” ya fada yana kallo na.....
Da sallama na shiga, da tunanin koya zamuyi da mama,sedai batacemin komai ba, bayan sannu!
Ita kuwa humaira wata muguwar dariya ta fara harda hawaye! Kawai ma na tsaya kallonta, toh meye abun dariya kuma,
Banma gama tunanin ba,
Tace
Aunty sumy wlh kiyi wanka, kinji warin da kike.
Ba shiri nima duk da halin danake ciki na fashe da dariya.
Nace mata ke wlh nima warin ya isheni...
Sai lokacin mama tayi magana yanzun wankan zakiyi Ko zaman shashanci ?
Mikewa kawai nayi har lokacin da murmushi a fuskata na nufi dakin mu ,na cire kayana na debi ruwa natafi wanka, ina mamakin yanda ba’a kara tada maganar ba.
Ina fitowa nayi alwala don lokacin sallah yayi,
Ina idarwa nashirya, mama da kanta ta kawomin abinci, kadan naci na ture...
Dakin ta na koma so nake tamin fada...amman takiyi...
So nake ko dukana ne tayi... amman yanda ta nuna tamkar batasan da zamana a wajen ba.....
Angel na kira muke wasa... tamkar babu abunda yake damuna nan kam ta ciki na ciki...
Da daddare ina xaune ina danna waya ta... Humairah ta shigo.. kinje inji Abba...
Fadin yanda xuciya ta take bugawa ma.. ɓata Baki ne...
Da kyar na mike kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki cikin sanyi nayi sallama na shiga dakinsa
Gani na fada murya ta ƙasa_ƙasa....
Zauna Malama...
A hankali na zauna... ina jin jiki na kaman ba nawa ba...
Ina wayoyin ki??
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Kawai na fara maimaitawa... shikenan abunda nake tsoro zai faru....
Muryata na rawar kuka nace suna daki...
Ɗiyar albarka je ki ɗauko min... Ya fada yana kallon humaira..
Ɗan jim tayi bata tashi ba..
Jeki mana..
A hankali ta tashi kaman dai bata so aiken ba....
Gashi ta mika masa...
Ke kuma ya fada yana Kara daure fuska...
“Bazan cemiki karki Kara ba.. ki kuma.....”
Shashasha wadda batasan ciwon kanta ba...
Kuma kishirya gobe zakiyi baƙo...
Da bala’in karfi na dago ina kallon sa.. idona duk a waje...
Eh bako nace.
Abba! “Khaleel ɗina fa ? na fada ina fashewa da kuka...
Nagama magana... Tashi daga nan Malama, Abba ya fada fuskarsa a ɗaure Kamar bai taba dariya ba.
Wlh koma wanene Kar ya sake ya zo inda nake...
Ina da Wanda nake so...
Kuma banga Wanda ya isa ya....
Saukar Marin dana jine ya katsemin magana ta...
Da sauri na ɗago!
Mama ce a tsaye a kaina tana huci, kuka na fashe dashi nace,
Mama! Marina kikayi ?
Ko zaki rama ne ? Tadawo min da tambayar...
Shiru nayi ina tunani baran iya tuna ranar da mamah ta dake ni ba..
Bata Duka, fada ma ba sosai take ba...
Da gudu na tashi na fita a dakin.
Kuka nake kaman raina zai fita.
A ina xan samu waya na Kira khaleel..
Nashiga uku na lalace...
Bansan sanda bacci yadauke niba...
Washe gari mama bata Shiga harkata ba gaba Daya....
Kukan ma nagaji da shi har nayi shiru... idona ya kumbura yayi jajur... haka fuskata...
Da yamma Abbanmu ya shigo gidan..
Ke Tashi ki shirya” fuskar nan a hade.
Banga fuskar magana ba.
Dan haka hijab kawai na dauka nasaka.
Wlh! Wlh!! Wlh!!!
Sau nawa na rantse?
Da hannu na na nuna masa uku.
Baki da Baki ne ?
Uku.. na fada murya ta a dashe...
Sumayya idan kikaje kikayi abun da bashi kenan bs sena miki abun da baki taba tunani ba.
Wuce kije yana jiran ki a waje.
A hankali nake tafiya dan jiki na gaba daya babu kwari...
Barka da fitowa gimbiya!
Naji an fada.. a hankali na juya ina kare masa kallo....
Bakinciki da takaici sune suka hanani magana.. sai kumburarrun idanuwana dana sakar masa.
Masha Allah wlh kin fi kyau a kusa...
“Uwar kyau nafi ba kyau ba”
Na fada ina harararsa, Kai bakaji kunya ba ? Me zakayi da yar cikin Ka?
Idan har mafarkin aurena ma kake kadena, Dan ina da Wanda nake so. Na rufe ido ina zazzaga masa rashin mutunci.
Tsaya ki saurare ni... ya fada cikin lallashi..
Uban me zan saurara ?
Na katseshi cikin tsawa...
Ban tsaya Kara jin maganar sa ba na juya gida ina kuka...
Ina Shiga na zauna a tsakar gida, iya karfina na fasa ihu... Wayyo Allah na. Meyasa ni ba’a sona a gidan nan. Birgima nake kamar ƙaramar yarinya.
Ganin mama tayo kaina yasa na gudu daki na xauna na cigaba da kukana.
Ba kuka ba, ko mutuwa zakiyi. Babu abunda zai hanani ɗaura Miki aure ranar juma’a..
Nan da kwana huɗu kenan...
Chak kukan ya tsaya na fara dambe da numfashi na.............!!!!
Mu hadu a page 03 idan Allah ya kaimu Gobe
Taku har kullum Fulani
🤍
✨
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
BY
RABI’ATU (FULANI)
Young talented writers association (YOTA)
A har kullum ina Jinjina gareki garkuwata mahaifiyata Abar alfaharina
❤
️
Sadaukarwa ga aminiyata Daya tilo
Amina muhammad haruna
Maman xhara
🤍
Wannan shine rubutuna na farko... Wanda ya kasance True Life story ne da ya faru a labarin wata baiwar Allah....
Yanda na fara lafiya Allah yabani ikon kamallashi lafiya
🙏
☺
️
FULANI
TRUE LIFE STORY.....
💫
❣️ ICEN DAMUNA
💫
❣️
PAGE 03
Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!! Humairah ta fada da karfi tana kuka.
“Abba dan Allah kayi hakuri Ka kyaleta.
Ta fada tana jijjigani.
Ko mutuwa xatayi baxan canza ra’ayi na ba.
Aure ranar juma’a babu fashi... Ya fada yana juyawa.
Mamah dai tana tsaye tayi shiru bazaka taba gane a wane hali take ciki ba.
A take a wajen zazzaɓi ya rufe ni da ciwon Kai.
Da kyar ta kamani muka shiga daki ba kuka nake ba amman wani kalan numfashi nake ja.
Kiyi kuka sumayya!
Nakasa magana se binta da nake da kallo...
Wani wahalallen bacci ne ya dauke ni ba tare dana shirya ba.
Hannu na..na cikin nata..
Ganin yanda nake a cikin baccin yasa ta gane ba dadin sa nake ji ba.
Tashi tayi ta tafi wajen mamah.
Tana xuwa ta sameta ta zabga tagumi tana kuka...
A hanzar ce ta matsa kusa da ita mamah! Meyafaru ? Ta tambayeta tana kokarin maida hawayen ta.
“Humairah yaron nan ya cuce ni, ya canzan halin yarinya gaba daya, Wannan ba tarbiyyata bace, Danasan sumayya xata hadu da Shi a makaranta, dana hana ta karatun, gwara ta zauna bata da ilimi da halin daya jefamin yarinyata, Ta fada tana Kara fashewa da kuka.
Kiyi hakuri mamah! Dan adam baya tsallakewa kaddarar sa.
Sumayya khaleel ne tata kaddarar kici gaba da Mata Addu’a, Komai zai wuce tamkar be faruba, cewar humairah
Mama ce ta tari numfashinta Yaushe humairah ? Yau shekara 4 ana abu daya!!
Rungume mama kawai humairah tayi suna kukan baƙin ciki
Kamar mafarki haka abubuwan da suka faru suke dawowa tunani na, A firgice na tashi.
Kaman wadda aka tsikara, da gudu na tafi dakin mamah duk da jirin da nake gani...
Mamah dan Allah Kira min ita a waya...!! na fada a galabaice.!
Gaba dayan su tsayawa kallo na sukayi, da mamaki a fuskar su!!
Dasauri mah ta boye mamakiñ ta..
Wa zan Kira Miki ? Ta tambaye ni...
Seda na lumshe Ido na na fadi sunan a hankali...
*”Haleemah”*
Ba kun rabu ba?
Ta kara jefomin tambaya..
Har lokacin ban bude idona ba, “nace mama mutuwa ce kawai zata raba mu... amman muddin dayan mu tana raye... bazata taba rabuwa da ɗaya ba.
Na fada ina cize baki na.
Gaba dayan su farinciki ne ya bayyana a fuskokin su...
Bata Kara magana ba ta miko min wayarta...
Dakin mu na koma..
Nayi searching number ta na kira “FIRST DAUGHTER”
Tana fara ringing gaba na ya fara faduwa, nasan ta nasan halin ta,
Tana da taurin Kai,
Muryar tace ta dakatar da tunani na.
Amincin Allah ya tabbata a gare ki uwa ta gari, ta fada tana dariya..
Bansan nayi kewan ta har haka ba seda naji muryan ta.
A hankali nace!
“BEST”
Kaman ba zatayi magana ba Se kuma tace:
Lafiya ? Ta tambaye ni a dakile!
Aure za’a min!! Na fada ina fashewa da kuka.
Batare da dogon tunani ba tace”
Shine abunda ya dace da ke.
Tsoho ne fa...!!! na fada ina kara samata kuka
Koda baya iya tafiya tsabar tsufa haka zaki aureshi.
Har yanzun ina sonsa na fada a hankali kaman me tsoron fada.
A sahun dakikai bansan a wanne ya kamata nasaki ba!
Kaman yanda na fada miki sedai ki zaba ko ni!
Ko wancan taƙadirin dan iskan...!!!
Na fada miki ba dan iska bane.! Natari numfashin ta dasauri.
Baxaki taba canxawa ba karki kara kirana a waya” ta fada ranta a bace.
Cikin kuka nace “Idan har aka matsa da auren nan wlh sena KASHE KAINAH!!!
Tasanni tasan halina, tasan sarai zan aikata.
Shiru tayi nima haka amman kuka nake a hankali.
Nasan tashin hankalin ta taji ni cikin damuwa!