JALALUDEEN BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF AYUSHER MUHD.doc

Author :  Ayusher Muhammad Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 37

54K to 57K   out of 109.4K words

a waje shi da umma sai dai ba wanda ya iya yima wani magana a cikinsu, sai can Umma ta daure tace " Malam ne dana mahaifin yarinyar da Jalal keso?" Abba ya had'iyi wani abun bai iya ce mata komai ba, tacigaba " mun shiga uku malam yanzu in Jalal yasan..........wani kallo da Abba ya buga mata ne yasa tai shiru, sai dai abinda ke zuciyoyinsu na da yawa.


Jin an kwankwasa kofa ne yasa Umma ta d'aure ta mik'e ta nufi kofar, ta bud'e ganin mutumin dake tsaye ne yasa ta fara ja da baya da baya, tare da cewa Malam? Abba dake zauna ya taso tare da cewa "ke kuma menene inaji da......" ganin Dad ne yasa shi yin shiru, Dad ya makamai wani mugun kallo yace " inasan ganinka." Yana fad'ar haka ya juya.

Abba ya kalli Umma itama cikin tsoro tace " Malam mun shiga uku." Takalmansa ya d'auko ya fita sai dai kana ganinsa kasan ta maza kawai yakeyi anma a tsorace yake.


A d'an gaba da gidansa yaga Dad ya karasa gunsa, yace " Isma'il gani." Juyowa Dad yai ya kalleshi cikin d'aure fuska yace " tambaya ta karshe nazo in maka, daga wannan in har ka sake min karya wlh kaji na rantsema wannan karan ba kamar da bane dazan kyaleka, wlh sai nasa an d'aureka."


Abba ya kalleshi a tsorace, Dad yace " Wayama Fatima fyad'e?"


Gaban Abba ne ya fad'i ya kalli Dad sannan ya had'iyi yawo bakinsa na rawa yace "Malam Isma'il!"

Dad ya d'agamai hannu yace ba abinda nazo ji kenan ba, ka fad'amin abinda na tambayeka ko kuma wlh zakasha mamaki.


Abba yace " Malam Isma'il alokacin wlh ba asan raina......"

Dariya sosai Dad yai sai dai kana gani kasan ta tsabar bakin ciki ne, yace " Amadu kenan, karka sake tunanin zan yanda da kalamanka, kalma d'aya nakesan ji daga gareka, waye ya k'etama Fatima mutuncin ta?"


Abba ya kalleshi idanu a zare, Dad ya karkatar da kai yace " Don't tell me kaine?" Da sauri Abba yace " Me kake fad'a? Ni kuma? Akan me? Kaima kasan ba hali na bane."

Dad yai murmushi yace "a shekaru masu yawa kenan nai tunanin ba halinka bane amma daga baya na gane babu babban munafikin dana tab'a gani irinka, sannan dama na sanar dakai wannan shine tambaya dazan maka ta karshe, yanzu sai ka jira d'anka d'an inaji shi kad'aine zai iya jin amsarka."


Dad nakainan ya juya ya tafi, Abba ya rikice, sai dai kafin ya dawo hayyacinsa Dad har yayi gaba.



Da sauri ya koma gida ya tadda Umma a tsaye tana jeka ka dawo, tana ganinshi ta rike hannayensa tace " ya kukai?" Abba yace " ya tafi yace Jalal zai fad'ama."


Zubewa Umma tai a kasa jin haka tace " Malam meke damunka? Kataba tunanin in Jalal yaji maganar nan abinda zai yi?" Ta mik'e tace "Ko dai nima kana b'oyemin wani abu ne? Indai har abinda ka fad'amin shine gaskiya meyasa bazaka fad'ama Malam Isma'il ba? Karka manta abinda ya faru da shi da iyalinsa saboda kalma d'aya daka furta."


Abba ya kasa magana sai zufa kawai yakeyi, ya kalleta yace " Ban b'oye miki komai ba, kema kinsan haka." Yana kainan yai waje da Sauri....







? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.*

@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com


No. 4? 0?




Zainab kam tunda ta shiga d'aki hankalinta ya kasa kwanciya, ba shakka wannan wulakancin da aka ma Abba ya k'ona mata rai, bata fiya fishi ba haka take sai dai in ranta ya b'aci bata ganin komai, wayarta ta d'auko ta danna number Jalal, ringing uku Jalal ya d'aga tare da sallama ta amsa sannan tace " Yaya dama akwai lokacin da zaizo har ka fifita soyayya akan iyayenka?"

Cikin b'acin rai Jalal yace " ke Zainab meke damunki? Ni kike fad'ama wannan banzan zancen?"

Zainab rai b'ace tace " meye ma bazan fad'ama ba yaya? Akwai abinda yafi b'acin rai irin a wulakanta iyaye? Mahaifinta Har da shake ma Abba wuya? Sannan kai kuma anjima kazo kace kana santa ko me?"



Jalal ya mik'e tsaye idanunsa suka kad'a sukai jaaa, cikin fad'a yace " me kika ce?" Shiru tai bata amsa ba, tsawa ya daka mata yace "ME KIKA CE?"


Nan tai ajiyar zuciya ta shiga fad'amai abinda akai a gabanta, cilli naga yayi da wayarsa kan gadon Sagir, dama Sagir baya nan, wani hucci ya shiga saki ni kaina sai dana tsorata alk'alamin dake hannuna sai daya fad'i, tun yana karami ko a wasa bayasan irin zagin nan na yarinta da ake, d'an shi ko kad'an baya san a zagi iyayensa, bari har me?? Shakemai wuya?.
A zuciye naga ya fito daga d'akin ai da gudu nai gaba nikam kar a huce akaina.....



Ammar kam tunda Jalal ya tafi yake faman lallab'a Seemah sai dai dakyar ya samu tai bacci, sai dai kamar wata yarinya tana bacci tana ajiyar zuciya, Ammar dake tsugunne saitin fuskarta ya saki murmushin ganin yanda take ajiyar zuciya, a hankali naga fuskarsa ta koma ta damuwa, ya matso da fuskarsa saitinta ya kwantar, ya k'ura mata ido, a hankali ya furta " Seemah wani irin so nake miki?
Na jini ne?
Ko kuwa na 'yan uwa ne?"
Ko kuma soyayya ce ta d'a namiji?"

Shiru yai kawai yana kallanta can baisan sanda zuciya ta d'aukeshi ba, a hankali yakai bakinsa kan kuncinta ya sumbata, motsin datai ne yasa ya mik'e tsaye da sauri tare da sa hannu a bakinsa, jiyai d'akin yamai zafi duk da A.C da kuma sanyin da akeyi, bakin window yaje ya tsaya yana firfita da hannunsa.

g&g&g&g&g&g&g&g&g&g&g&g&



Habib kam suna isowa Abuja yai asibiti da Hajiya, suna shiga akai emergency da ita dan gaba d'aya bata hayyacinta, kawo duk ya rikice hakama Habib, dakyar Habib ya lalubo wayarsa ya k'ira Abbansu Zaid sannan ya k'ira Dad, Dad dake hanya jin mahaifiyarsa ba lafiya yasa ya rikice, ya kalli driver yace kara gudu hajiyata ba lafiya, nan ya amsa da to tare da kara gudu.


Habib na kashe wa ya k'ira Ammar, Ammar yana kallan wayar sai data kusa katsewa ya d'aga ba tare dayace komai ba, Habib yace" Ammar kazo Asibiti Hajiya ba lafiya."

Da karfi Ammar yace " me ya sami Hajiyar?"

Seemah dake bacci ta bud'e ido, tana kallan Ammar, Habib ya cigaba " bansani ba nima Ammar gata dai a emergency tana jin jiki."

Ammar yace " *Inalilahi wa ina ilaihi raji'un* bari muzu yanzu." Yana kainan ya katse.


Juyowa yai ya kalli Seemah dake zaune akan gado, ta kalleshi tace "yaya me ya sami Hajiyar?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace "Seemah bansani ba ki tashi dai muje."

Da sauri ta sauko ta gyara d'ankwalinta ta yafa mayafi suka fita.


A asibiti kuwa Likitoci sundai yi nasu k'okarin sai dai su kansu sunsan inaaaa, ganin dai ta dawo hayyacinta yasa aka bata d'aki, kawo ya zauna kusa da ita, ya rik'e mata hannu, yace " Sannu Hajiya!! Bakiji yanda naji ba nad'auka kema mutuwa zakiyi ki barni kamar yanda sauran matan nawa sukai."

Hajiya tai murmushin karfin hali tace " Isma'il fa?" Kawo yace " yana hanya."

Habib ne ya shigo shi dasu Abba da mami, da sauri Abba ya karasa kusa da ita, yace " Hajiya?"

Ta kakaro murmushi tai tace " D'an nan kaima tasoka akai?"

Sannu hajiya abinda ya fad'a kenan, ta d'aga kai sannan ta kalli Mami dake mata sannu, tace yauwa Allah ya muku albarka, sukace Amin.

Abba ta kalla zatai magana sallamar su Ammar ta katseta, suka shigo shi da Seemah, Ammar ya kalleta duk ta rame yace " matata ya banje gaidake ba sai in ganki akan gadon asibiti?" Tace " yaushe ka shigo?"

Murmushi yai sannan ya gaida kawo dasu Abba, Seemah ma ahankali ta gaidasu, sai dai mami ce kawai ta amsa, Ammar ya kalli Abba da kawo yace" wooo yanzu kanwar tawa mai tsada tana gaidaku shine kukai shiru?"

Kawo ya kalleshi yace " Ammar kana nan dai yanda kake." Hajiya kam tunda Seemah tai gaisuwa ta kafe ta da ido, Abba ganin haka yana tsoron kar ciwonta ya tashi yasa yace " Seemah d'an fita waje, Habib dake tsaye ya kallesu, ba shakka matsalar daga Seemah ne ba Ammar ba.


Seemah ta d'ago ta kalli Abba, tsawa ya daka mata yace "bakiji me nace ba,"

Duk ta rikice tama rasa hanyar fita, Ammar ne ya jawota jikinsa yace " me kakeyi hakan Abba? Yaza'ai yarinya tazo gaida kakarta ka nemi korarta?"

Abba yace " Ammar ina wasa dakai ne?"

Ammar yai ajiyar zuciya yace " yahkuri in na b'atama rai Abba sai dai ba inda Kanwata zataje inkuma anaso ta fita to sai dai ku fita tare."

Yana kainan ya jata sukai waje.

Seemah duk ta rikice kawai hawaye takeyi.

Jalal kam a sukwane yaje gidansu Habib sai dai mai gadi ya sanar dashi yanzun nan motar Farida ta fita suna asibiti, hakan yasa da sauri yasa mai machine d'in yabi bayan motar.

Sun isa asibitin, Farida ta fito da sauri tai ciki, shima ya bita, a harabar gun ya kallo, wata kamar Seemah, hakan yasa ya tsaya yana kallanta, Seemah kam hannun Ammar ta rike kam dan jikinta duk rawa yake, ganin haka yasa Ammar ya jawota jikinta ya rungume, Jalal dake tsaye yaji ransa yayi mugun b'aci, karasa wa yai inda suke Ammar ya d'ago ganin kafar mutum ya kalleshi, da mamaki yace " Jalal? Me kake anan?" Seemah najin sunan tai saurin d'agowa ta kalleshi.


Idanunsa sun kad'a sunyi jaa dama ga bakin cikin abinda aka mai ga kuma wani sabon salo, babban yaya namiji ya kama rungume kanwarsa, Seemah ta kalleshi da idanunta dake hawaye tace " My Deen?"

Kallanta yai yace " Meemah me kike anan?"

Ta kalli Ammar sannan ta kalli Jalal, Ammar yace " kai ya kamata kabada wannan amsar, mu tinda ka ganmu anan ai akwai dalili, Jalal yace " Dad nake nema."

Ammar ya jinj??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ina kai sannan yace " tunda Dad kake nema bayanan." sannan ya kama hannun Seemah zai koma cikin asibitin da ita, da sauri Jalak ya kamo d'ayan hannunta, ta juyo ta kalli Jalal ta lumshe idanunta, Jalal ya sakar mata murmushi sannan ya kalli Ammar yace " sry yayan Seemah inasan magana da ita."
Wani kishi ne ya kama Ammar ya bugamai wani kallo, Jalal mamaki ya kamashi, ba shakka wannan kallan ba kallan yaya bayasan shi bane kallan kishi ne, amma......Ammar ne ya katseshi da cewa " ka manta me ka mata?"

Jalal da sauri ya kalli Seemah, meya mata? Nan Seemah ta tuno kalaman Zainab, a hankali tai fara baya, tana kokarin zare hannunta, jisukai ance " *Me kukeyin hakan?*
Da sauri suka juya dukansu, Dad ne a tsaye rai a b'ace.










? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*



@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com



No. 4? 1?


Dad yana karasowa gun ya kalli Ammar wanda ya kauda kai, yace " me kakayi anan bayan a ciki ya kamata in ganku?"

Seemah ta matso kusa da Dad tace " Dad ni na fito dashi, kayi hakuri."

Ammar ya kalleta yace " Dad taya za'ayi ace Abba ya kore Seemah daga ciki? Ban fahimci me hakan yake nufi ba."

Da sauri Seemah tace " Dad ba wani abun bane, Ya Ammar kaya ya d'au abin da zafi ne."

Jikin Dad yai sanyi ya kalli Seemah cikin tausayinu sannan ya maida idansa kan Jalal harzai mai magana ya fasa ya juya tare da cewa Seemah muje ciki, itakam idanunta nakan Jalal shikansa kallanta yakeyi, kallan juna suke cikin wani yanayi, Ammar ya kalli yanda Seemah ke kallan Jalal jiyai ransa ya sosu, Dad ya juyo ganin Seemah batada alamar tahowa, Dad a harzuk'e yace " Seemah wuce nace ko?"

Dasauri tace " to dad." Tana juyawa Jalal yace " Dad inada magana."

Dad ya juyo ya bugamai wani kallo, ba shakka Jalal yananan kamar yanda yasanshi, sai dai yasan dabadan abinda ya faru ba yasan da amintarsu da Ammar bazata rabu ba.

Had'e rai yace " Jalaludeen sunan ka ko?"
Jalal ya d'aga kai yace " Eh, amma ban fahimci menene dalilin dayasa kaje har gidanmu kacima mahaifina mutunci ba."
Dad yace " me kace?"

Ammar ya matso yace " kai gyara bakinka wani shirman kake fad'a?"

Seemah ta kalli Jalal sannan ta kalli Dad tace "Dad kaje gidansu ne?"

Dad dake kallan Jalal yace " ka koma ka tambayi mahaifinka abinda ke faruwa bawai kazo nan kanamin shirme ba."

Jalal ya kalli Dad yace " Na d'auka maganar ni da Seemah a tsakanin mu zai tsaya amma yaza'ayi kamar kai kaje har ka shake mahaifina? Me yayi?"

Dad yai d'an wani murmushi a ransa yace " Jalal kenan bai mantashi ba halayensa nanan, tun yana karami baya shakkar tambaya."

A fili yace " bakaji amsata bane? Nace ka koma ka tambayi mahaifinka wanda a fili za'a d'auka mutumin arzik'i ne amma a zuciya" ya jijiga kai......

Ran Jalal yakai matuka gun tunzura, Seemah ta kalli Jalal ganin yanda idanunsa sukai yasa jikinta yai sanyi, Kallansa tai idanunta sun cika da kwalla, Jalal ya kalli Dad yace " ban fahimci kalamanka ba? Kasan mahaifi nane? Ko kuwa a ganinsa dakai yau shine yasa kake fad'ar haka?"


Dad ya kalleshi yace " indeed you are smart tunda har kai tunanin haka, sai ka koma ka tambayi Amadu ko ya sanni."


Amadu? Jalal ya maimaita, ba shakka wanda yasan Abba ne yake fad'a masa haka, to amma ta ya? Dad ya kalli Ammar dake jin kalamansu cike da mamaki yace " Ammar muje ko? Ina bukatar ganin Hajiyata."

Bai jira abinda Jalal zai fad'a ba yai gaba, Ammar ya bishi a baya, Seemah ta kalleshi tace " Deen meke faruwa?" Kallanta yai idanunsa a kad'e yace " Meemah I don't know, ni dai kawai ancemin Dad d'inki yaje gida har shakema Abbana wuya yayi, shiyasa nazo inji, to amma yanzu I am confused, ya akai Dad yasan Abba?"

Seemah ta kalleshi jiki a sanyaye, tace " Deen nasan Dad d'ina kwarai, duk da nasan bayasan alakarmu hakan bazai sa ya shakema Abba wuya ba, akwai dai wani abun."

Jalal ya d'ago ya kalleta jiki a sanyaye ya jinjina kai yace " karki damu kije gun mara lafiyar."

Yana kai nan ya juya, har yad'anyi nisa tace " Deen?" Tsayawa yai tare da juyowa ya kalleta ta matso kusa dashi kad'an tace " Can you promise me something? " kai yad'an langwab'ar tacigaba " can you promise me you will always love me?"

Wani sansanyar murmushi ya sakar mata ya lumshe ido sannan yace " u are my first love how can I stop loving you? "

Itama murmushi tai tace " yazanyi ind'ingajin muryarka bani da waya?"
Wayarshi ya mik'a mata tare da zare layinsa dayake amfani dashi yabar Etisalat d'in da ba wanda yasanshi dashi dama saboda browsing yake amfani dashi.

Ta kalleshi sannan ta kalli wayar tace ta meye? Yace kiyi using wannan ni nasai wata.


Murmushi tai harsai da fararan hak'oranta suka fito tace " karka damu nasan yanda zanyi inada idea."

Yad'an harareta kad'an yace a hakan? Tace zaka gani.

Tana kainan ta juya ta fara tafiya, tsayawa yai kawai yana kallanta zuciyarshi tayi wani sanyi.......



Dad kam yana shiga Abba yace " Isma'il tund'azu ina ka tsaya Hajiya na nemanka?"

Da sauri Dad ya matsa gunta, ya rik'e hannayenta, tana ganinshi ta rike hannunsa itama tace " Isma'il nasani ka ga rayuwa, kaga tashin hankali duk da dai muma mun gani a shekara 20 data wuce, sai dai abinda ka gani bai kai namu ba."

Dad ya kalleta sam yamanta da Habib da Ammar agun d'an hankalinshi nakan mahaifiyarsa, Hajiya ta cigaba" nasani haryanzu bakamanta azal d'in daya fad'a maka ba, 'yan gari sun tsaneka saboda abinda bakai kayi ba, matarka mahaifiyar 'ya'yanka wannan abin shine ajalinta, wannan dalilin yarabaka da kasarka muma dole ne yasa mukabar garin."

Tai ajiyar zuciya tare da share hawayen dake zubo mata, ba itaba hatta mamie da Dad hawaye suke, Ammar kam da Habib kallansu kawai suke mamakin kalaman nan suke.

Hajiya tasa hannu ta share mai hawayensa tace " kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il ka rik'e yarinyar nan amana....."
Kawo ya kalleta yace " ya isa Karki kara tada ma kanki hankali ki kuma k'ara tadama d'anki."

Kallan Isma'il tai zatai magana numfashinta ya fara yankewa Dad ya rik'ece yace " a yi sauri ka k'ira Likita." Duk ya rikice Habib yai saurin fita, Yana bud'e kofa yana fita, yaga Seemah tsugunne a waje, bai kulata ba yai sauri yai gaba.


Ammar kam gaba d'aya kwakwalwarsa ta rufe, meke faruwa? Me kalaman Hajiya ke nufi? Wa aka rike? A iya saninsa 'yar Dad mace d'ayace Seemah to mekenan?






? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*


@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

_This page is for you my Yar uwas, my cwty my chocolates, much luv to you=?
? Maijiddah_

ayushermohd.blogspot.com


No. 4? 2?


Seemah kam gaba d'aya kanta taji yana wainawa,

19 / 37