JALALUDEEN BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF AYUSHER MUHD.doc

Author :  Ayusher Muhammad Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   28 / 37

81K to 84K   out of 109.4K words

yace " Au bama zancen aikinka ka k'ira kamin ba?"
Jalal ya saki Murmushi yace " Sagir d'an Allah kabani amsa."
Sagir baice komai ba ya katse layin.
Jalal ya girgiza kai fuskarsa d'auke da murmushi, jiyai am dafashi ta baya, ya juya Kafilu(d'an gidan goggo) ne da abokansa, Jalal ya kara sakin fuska yace " Kafilu?"
Kafilu yasa hannu a hab'a dayake shi mutum ne mai barkwanci, yace " Haba tun dana karyo kan lungun nan nake ganin haske d'an nima hasken na d'inga bi, abin mamaki hasken ya d'ireni anan."

Jalal ya kalleshi yace " Au nine nake haskem kenan?"
Dariya Kafilu yasa yace "Sosai ma, abinka da sabun shiga, saurayi zaiyi sabon aure."
Ya fad'a yana kallan abokansa, Dariya dukansu suka kwashe mai dashi, har Jalal d'in.
Ya cigaba " ni gashi ina shirin kara ta uku amma kai sai yanzu zakai d'aya gaskiya dai anji kunya."

Kallan mamaki Jalal yamai yace " Kafilu? Ka rufa mana asiri ina zaka kai mata uku?"
Dariya suka sakeyi Kafilu yace " ah to kaidai ba d'an boko ba sai kayi ta zama ni ai sai na ciki hud'un nan rass."
Jalal ya girgiza kai yace " Lalai abin naka babba ne, kaje kana kwance a kwarama ruwan zafi."
Suka kara sa dariya, Kafilu yace " tab, ai sai dai suyi ta fad'a akaina ni kuma inzauna akan kujera ind'inga kad'a kafa."

Jalal ya kalleshi cikin mamaki yace " Allah ya shirya, wato kai fad'an ma dad'i yake maka."
"Sosai ma."
Sun dad'e suna hira suka d'anje yawo.



Seemah kam duk motsin datai sai ta tuna, Shikenan Jalal ya zama ba nata ba, yana can yau za'a kaimai matarsa, wani sabon kishi da takaici ne ke nukurkusarta, kwankwasa kofar dataji ne yasa ta mik'e tare da bud'e kofar, Ammar ne ya kalleta fuskarsa d'auke da murmushi ya bud'e mata hannayensa yace " Suprise! !!! "
Ta kalleshi tare da matsamai, Ammar ya shiga yana cewa " Kodai in koma? Kamar wannan kanwar batai farin cikin ganina ba."

Seemah ta shiga ciki batare data amsa ba, a kan kujera ya zauna tare da nuna mata kusa dashi, ta karaso ta zauna, ya kalleta ya d'an langwab'ar dakai yace " ko in tafi?"

Kai ta girgiza mai, alamar a'a yace " in bakyasan na tafi to lalai ki saki fuskarki."
Ya fad'a tareda had'e fuska, Seemah ta kalleshi cikin shagwab'a tace " Fuskata fa a sake take."

Ya juyo yai murmushi sannan ya mik'e ya dawo gabanta ya tsugunna, ta kalleshi tare da yin murmushi ganin yanda yake kallanta, tace " Yaya kallan fa?"

Ya kara kafeta da ido yana mata wani kallo yace " Seemah bansan ganinki cikin damuwa kema kinsan haka."
Ta d'auke idanunta da sauri tare da juyar dakau tace " Yaya?"
Ya mik'e tare da juyawa ya fara tafiya, jikin gado yaje ya tsaya, ba tare da ya juyo ba yace " na sani Seemah, soyayyar da kikemin ta 'yan uwantaka ce bawai ta saurayi da budurwa ba, a da na d'auka nima wannan soyayyar nake miki, amma bayan sanin ba jinin mu d'aya ba na gane cewa soyayyar danake miki kala biyu ce."
Ya juyo ya kalleta idanunsa sunyi jaa, yace " in har bazaki iya aurena ba wani abu, ni zan iya hakura koda kuwa sanki zai kasheni zan jure, abinda bazan iya jurewa ba shine inganki cikin bakin ciki."

Seemah hawaye suka gangaro mata, ta kalleshi cikin tausayi, sai dai ta kasa magana juyawa yai yafara takawa, da niyyar barin d'akin, mik'ewa Seemah tai da sauri ta zo ta rungumeshi ta baya (abinka da rainon da ba na kasar nan ba, bare sun taso tare basu d'auki hakan komai ba.)
Cak Ammar ya tsaya, tare da had'iyar wani abu, idanunsa na neman kawo ruwa, Seemah cikin kuka tace " Ba haka bane Yaya, ba haka bane."
Hannunta ya zare tare da juyowa saitinta, hannu yasa ya share mata ta tsugunna a kasanshi tasa kuka tace " Yaya ya ya zanyi? Ni kaina haushin kaina nakeji, banasan abinda nakeyi, tayama za'ayi zuciyata ta kasa tsanar wanda mahaifinsa shine sanadiyyar wulakantar mahaifiyata, kila ma shine sanadin rasa rayuwarta?"
Ta kalli Ammar idanunta na zubar da kwalla abin tausayi tace " Yaya inaji bana cikin hankali na, a da nad'auka ko ganinsa bazan nemi sakeyi ba, amma da kaina na fita gunsa, kuma na kasa ko tambayarsa bare inyi masa masifa, yaya anya mahaifiyata zata yafemin?"

Ammar ya share kwallarsa shima, ya tsugunna kusa da ita tare da rike hannayenta, ta cigaba da kuka sannan tace " Yaya ka taimakeni kasa na manta da Deen d'an Allah, in daina mafarkinsa da tunaninsa, banasan na........"

Hannu yasa ya rufe mata baki, ta kalleshi hawaye na cigaba da zubowa, har kan hannunsa, baice mata komai ba, sun dad'e a haka, Kafin a hankali Ammar ya zare hannunsa daga kan bakinta ya kalleta yace " Ya isa kukan haka, banasan ki zubarda hawaye koda kuwa akainane bama akan wani ba, hakan nasa zuciyata shiga wani hali."
Kallansa tai ta kasa magana, yace " bari naje masallaci."
Ta d'aga kai a hankali, ya mik'e ya fita, ta bishi da kallo, jikinta ya kara sanyi, taya zata ki jinin Dad, a yanda takejinta koda Dad wani can talakan gaske ya d'auko yace Seemah wannam nakeso ki aura, bataji zata bijire masa bare Ya Ammar? Mutumin datasan bazai tab'a barinta ta wulakanta ba bare yasata kuka, jinin Dad, sannan a 'ya'yan Dad d'in ma wanda tafi shakuwa dashi tafi kuma sansa? To amma meyasa take neman b'ata masa rai saboda Deen? Meyasa?
Wani sabon kuka ne ya kara zuwa mata........





An kai Amarya, mutane sun cika a gidan Jalal su kafilu a gaba suka sashi aka siyo kaza da lemon kwalli da hollandiya mai sanyi, Kafilu sai tsokanarsa yakeyi, sunje shiga gida Kafilu ya kalleshi yace " Jalal sai naga kamar farincikinka baikai zuciya ba."
Kallansa Jalal yai baice komai ba, Kafilu yai dariya yace " ko duk ka kosa ne kayi......."
Harara Jalal ya dokamai yace " kai wannan ya dama mai iyalai."
Kafilu ya kalleshi yace " Kai!!!!! Ai abin ne....."
Jalal ya kara makamai wata hararar yace " bamasan jin sirrinka uban 'yan surutu, Allah ya shiryeka."






Nima nace Ameen, d'an kuwa fad'ar sirrin aure babbar illa ce......Allah yasa mu kiyaye Ameen.







? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*


?& @&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

_I Sincerely dedicated this page for you *ASY KHALEEL*._=?
?


No. 7? 0?


Sun shiga cikin d'akin, nan Kafilu ya samu abinda yake so wato hira, shikam Jalal ko kallan Zainab dake lullub'e cikin mayafi baiyi ba, Sai can d'aya daga cikin abokin Kafilun ya tab'ashi yace " ya kamata mu yafi fa."
Nan suka ba kawayen Amarya dubu biyar kud'in siyan baki sannan akai addu'a suka fita.
Toh fa!!!! D'aki ya rage daga Zainab sai Jalal, zaman dukum sukai wato zaman kurma har na wajen minti talatin, kafin can Jalal ganin zamanshi anan bashi da amfani ya mik'e ya kalleta, yace " Zainab?"
"Naam"ta fad'a cikin sanyin murya.

Yace " bud'e fuskarki mana muyi magana."
A hankali ta zare mayafin idanunta a kasa, tasha kwalliya d'an kuwa tayi kyau, sai dai wanda akai dominsa baimasan tayi ba, kallanta yai yace " ungo wannan." Ya fad'a tare da mika mata leda, hannu tasa ta karb'a tana kallansa.

Yace " Abincine ki samu kici, inadai kinyi Sallah?"
A hankali ta furta " eh, amma kai yaya kaci abincin ne?"

Ya d'an juya kai yace " ni na koshi, kedai kici abinci sannan ki shiga d'aki ki kwanta d'an nasan kingaji."

D'agowa tai ta kalleshi, duk da dai itama tasan ba santa yake ba amma bata tab'a tunanin abinda zai ce mata kenan ba.
Kai kawai ta d'aga, yai cikin d'akinn, dama d'aki d'aya ne da toilet a cikin d'akin sai falo, toilet d'in ya shiga yai alwala yai sallah a d'akin.


Itakam dakyar ta iya cin cinya guda d'aya sai yoghurt d'in data d'an kurb'a tai shiru tana tunanin wannan abu, kawayenta jiya sun bata labarin yanda maza ke kula da mace ranar da aka kaita, yau gashi ita taga wani abu.

Jalal bayan yayi addu'oinsa ne ya fito falon tare da kallanta yace " kinci abincin?" Ta d'aga kai, yace " Good, kishiga ki kwanta."
Ta kalleshi tare da mik'ewa tai d'aki, har takai bakin kofa tad'an juyo, ganinshi tai ya kwanta akan doguwar kujera, tace " yaya kaifa?"
Ya kalleta kad'an tare da cewa ni inanan.

Kallan mamaki tamai sannan tace " yaya."

Jalal ya had'e rai yace " to so kike inshiga mu kwanta tare?"
Shiru tai tana kallansa, yace " ki wuce kije ki kwanta karki damu dani."


Shiga tai cikin d'akin ta zauna a bakin gado tai shiru, ta rasa ma me zatai, shikam Jalal waya ya d'auko yai tai binciken abinda yasa gaba wato sanin harkar karatun law dana mass com.
Yana cikin binciken ne yaga wata kungiya masu bada scholarship na PTDF sun bud'e a fara siyan form.
Nan fa ya sai katin yana fatan Allah yakaimu gobe ya tafi cafe yaje ya cike.






Haka rayuwa ta cigaba, 'yan taron biki sun watse, sai dai tsakanin Jalal da Zainab, intai abinci ta bashi ya ci sai kuma gaisuwa, kamar yanda ta saba kullum tana cikin gida kamar da, wannan ne ya rage mata kewa da kuma sanya abin aranta.





Hmm rana bata karya, yau tun safe ake ta shirye_shirye a gidan Abba kowa ya shiga hidima, kowa murna yake yi banda Seemah wacce kwai yake take yima kowa, tana tsaye a kitchen d'an Mami tasata kullum ta d'inga shiga kitchen tana ganin yanda Zahra da mai aikinsu ke girki, yau dai ita kad'ai ce a kitchen d'in tana dafama Dad indomie babban burinta Dad yaci abincin ta, Ta dage tana ta aiki sai kace mai dafa sakwara duk ta b'ata kitchen d'in, ji tai an rufe mata ido ta baya, tai murmurishi tace " Ya Ammar ka tashi?"

Sakinta yai tare da juyowa saitinta yace " Seemah ya akainkiga ganeni?"
Ta d'an harareshi kad'an tace " lalai ma Yaya, tambayar dazakamin kenen? Inada hanyoyin sanin kaine dayawa."

Ya kalleta cikin jin d'adin kalamanta, ta kalleshi tare da cemai "yaya yau Dad nakema girki."

Ammar ya hau saman kanta daga gefe ya zauna tare da cewa " lalai duk wannan d'in na dad ne kenan? Bama a tuno da ni?"
Ya d'an matso ta da fuskarta kusa dashi yace " ur husband to be."
Kasa tai dakai da sauri sannan ta d'ago ta d'an kankance ido tace " oh ni yaya yaushe ka zama haka wai?"
Murmushi yai sannan ya nunata da hannu yace " yazanyi tunda kanwata ta maida ni haka?"

Ta d'an juya kai tace " gobe dai zan tafi ai."
Yad'an bata rai yace "gaskiya ji nake kamar zan biki, bansan ya zanyu ba inkika tafi MEEMAH."

Da sauri ta d'ago ta kalleshi gabanta ya fad'i, idanunta yaga sun ciciko, cikin tsoro yace " SEEMAH? Menene?"

Ta share hawayenta tare da saurin maida kanta kan girkinta tace " please yaya karka kara cemin Meemah."

Ammar da mamaki yace " meyasa? Naga kinasan sunan?"
Ta kara goge kwallar vata amsa ba kawai ta cigaba da yanka albasa, aranta tace" sunan da Deen ke kirana dashi ne, na rabu dashi ina fatan zuciyata ta manta dashi sai dai banasan wannan sunan ya fito daga bakin kowa sai shi, tunda mun rabu dashi wannan sunan inasan ya zama tarihin daya rage tsakaninmu."


Ammar kallanta kawai yakeyi, har ta gama nan ya tayata gyara kitchen d'in.

A ranar da yamma aka sanya ma Ammar da Sewmah sannan Junaid da Zainab ranar aurensu nan da shekara 2 daidainan Seemah ta gama karatunta a hankali ta dawo sun karasa shiri, itama Zahra ta gama nata.

Washegari Seemah da Dad da matarsa suka calla England.



Jalal kam yayi sa'a ya samu wannan scholarship d'in murna kamar yai me, nan ya fad'ama Abba shima ya tayashi murna duk dadai a kasan ransa yasan manufar Jalal, nan fa yafara shirin tafiya dan kasar Germany ya cike karatun d'an Jarida, d'an yaga a can shekara 2 ne an gama.


Yagama komai shima sannan ya calla kasar Germany d'an yin nasa karatun.





? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

?& @&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com


No. 6? 1?


*Bayan Shekara Biyu*



Seemah nata sauri dan ganin lokacin fita makarantarta yana neman kurewa yau ne suke taron kammala karatun degree da sukai, ta fito cikin riga da wando, rigar pink ce an rubuta sunanta a baya sai wando jeans baki, shigar da kowa zaiyi kenan, mayafi ta d'auka black tai rolling d'in kanta dashi tayi kyau sosai ta zura abaya baka ta d'au jaka ta fita.
A falo ta tadda Dad na karatun jarida ta gaidashi ya amsa yana cewa baby kin fito? Ta d'an turo baki tace " A'a Dad nifa nace banasan Baby nan shekarata fa 22 yanzu."

Yai dariya tare da cewa kiyi sauri ki fita sai mun iso, ta juya tana mai bye bye da hannunta, motarta ta fad'a ta kunna wakar data saba ji ta Kabhi Kush nan ta fara tuki cikin kwarewa, agoggon ta data ajiye a saman kan motar ta kalla tai murmushi tace " Good morning Deen." Ta fad'a tare da murmushi, tana isa makaranta tai parking sannan ta fito, ta shiga cikin kawayenta turawa da indiawa suka hau murna dan kuwa ba karya ranar murna ce.


An gama shirya komai nan mutane suka fara isowa, taro ya fara gudana, Seemah kam sai zirga zirga takeyi fuska a had'e waya ta d'aga ta kira Ammar abin haushi bai d'aga ba tai kwafa sannan ta kara kiransa, nan ma bai d'aga ba, haushi ya turnuko ta ta kira Ya Habib, ringing biyu ya d'auka ta shagwab'e murya tace " Yaya sun taho?"
Habib ya kalli Ammar yace " Wayyo kanwata kiyi hakuri bazasu samu damar zuwa ba."

Idanunta sukai rau rau tace " Harda Ya Ammar?"
Habib ya guntse dariyarsa yace " Ahh Ai Ammar ma bayanan ya tafi meeting. "
Cikin masifa tace " Meeting?"
" eh akwai wani babban Project da muke san yi ne to shine......"
Katse wayar tai a zuciye ta koma ciki.

Zama tai tare da hard'e hannayenta lalai ma Ya Ammar d'innan, ko a mafarki bata tab'a tunanin zai fifita aikinsa a kanta ba kwalla ta zubo mata, ta share tare da d'aukan wayarta kamar yanda ta saba, numberta datai saving ta bud'e ta tura ma kanta sako kamar haka " Deen yau an b'atamin rai, Ya Ammar da Ya Junaid bazasu hallaci taron kammala karatu na ba."
Tana gamawa ta turama kanta, tun bayan tahowarta duk abinda ya sameta sai ta tura ma kanta sako da zummar Jalal ta turama hakan na saukaka mata zuciyarta duk da kuwa tasan ba zai gani ba.

Tana nan a zaune wata kawarta yar Korea Yoo jung ta shigo, dafata tai tace mata " Someone is looking for you."
Seema ta kalleta tare da tab'e baki tace " Yoo Jung I am not in the mood to joke with you. "
Tai mata murmushi tace " 3 handsome men and one young girl."
Seemah ta kalleta da sauri sannan ta mik'e tsaye tace " are you sure? "
Ta d'aga mata kai tana murmushi da sauri Seemah ta waje.

A tsaye ta hangosu daga nesa, Ya Junaid, Ya Habib, da Ya Zaid, ta saki murmushi ganin Zahra a kusa dasu, juyawa ta d'anyi da kanta da alama wani take nema, ganin ba kowa yasa ta karaso kusa dasu, tare da kallan Ya Habib tace " Yaya shine d'azu baka fad'amin bako?"


Zahra ta matso kusa da ita tace " Seemah oh ni ashe zan ganki?"

Seemah ta d'an harareta tace " ni bansan wani dad'in baki yausge rabon da ki kirani?"
Junaid ya d'an matso kusa da Zahra yace " yanzu kuma metayi? Daga zuwa ganinki?"
Seemah ta juya kai tace " dama nasani ai yaya yanzu ka daina sona."
Zaid ya matso saitin kunnenta yace " kyalesu ni kaina bana shiga harkarsu sun zama super glue. "
Dariya tasa ta kalli Zaid tace " Ya Zaid at least kai nasan kana bayana."


Sun je shiga kawai taji jikinta ya bata kamar ana kallanta juyawa tai a hankali, da sauri ya lab'e a jikin bango, ta d'an kurawa gun ido kad'an Zaid ya kalleta yace " muje mana."
Ta d'an juya kai maybe mistake take, wanda ya lab'e ya fito tare da bin bayanta da kallo yai murmushi yace " Congratulation Meemah."

Ya juya yana murmushi, direct Airport ya nufa.



Seemah kam suna zazzaune a sama akan kujera ana kiransu d'aya bayan d'aya ana basu kwallin karatun diploma d'insu, kallan kofa take tayi d'an bataga Dad ba har a lokacin, kanta ta sukuyar fuskarta ba yabo ba fallasa, an kira sunanta kenan, ta mik'e a hankali tare da kara kallan kofa, wa zata gani? Ammar ta gani a tsaye ya hard'e hannayensa yana mata murmushi, itama murmushin tamai wani farin ciki ya kara kamata, a hankali ta karasa ta amsa sannan aka tafa mata ta koma ta zauna fuskarta d'auke da fara'a.

A hankali Ammar ya

28 / 37