JALALUDEEN BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF AYUSHER MUHD.doc

Author :  Ayusher Muhammad Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 37

57K to 60K   out of 109.4K words

bata fahimci inda maganar ta dosa ba saboda ta baro gun Jalal tazo zata shiga ta tuna d'azu ance ta fita, hakan yasa ta jingina da kofar sai dai adaidai lokacin taji Hajiya tace " Kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il kuma ka rike yarinyar nan Amana."

A iya saninta mahaifinta ne Isma'il to wace yarinya ya rik'e amana?


Dawowar Habib da likita ne yasa itama ta mik'e ta wuceta sukai da sauri, tabishu da kallo tare da tsayawa a bakin kofar, Duk 'yan d'akin sun rikice ganin yanda jikin Hajiya ya tashi sosai, sai dai har yanzu hannunta kankame yake dana Dad, likita na zuwa suka shiga kok'arin daidaita numfashinta, sun wahala sosai ganin jikin ba dad'e yasa sukace kowa ya fita ya barsu, nan Dad suka fito kowa jikinshi a sanyaye, idanun kowa ka kalla kasan suna cikin tsananin tashin hankali, Dad na fitowa yaga Seemah a tsaya tana hawaye ganin yanda jikin hajiya yake, hannun ta ya kama sukai waje.

Nan aka rufe kofar, kowa yayi jugum yana addu'oi, sai da likitocin sukai minti 30 kafin su fito, suna share zufa, Abba da Dad da kawo suna ganinsu suka matsa kusa dasu, Abba yace " ya jikin nata?"

Likitan yace " kushiga sai dai kuyi a hankali karku kuskura kuyi abinda zai tada mata hankali ko taga abinda bataso, yin hakan babbar matsala ce, sannan kar ad'inga hayaniya a kusa da ita.

Suna kai nan sukai gaba, Habib ya matso kusa yace " Abba ya kamata ku koma gida, munyi yawa a asibitin gudun hayaniya ya kamata ka d'auki Mami da kawo ku koma gida, shima Ammar ya d'au Seemah su tafi inyaso ni zan zauna anan."



Abba yace " haka ne amma sai dai zuciyata bazata iya kwanciya ba in na tafi."

Kawo yace " nima kunsan bazan iya zuwa wani gun ba inbar matata anan ba."

Sunyi shiru kafin Dad yace " mu zauna anan ai mu ba maganar da zamuyi, kai Habib ku koma gida."

Habib ya kalli Dad yanasan yai musu anma yana tsoro, Dad ya kalli Kawo yace "kawo kaima kaje gidan yaya kai wanka kaci abinci inyaso da daddare sai ka dawo."

Haka suka yanke shawara Dad da Abba suka shiga ciki, Habib ya kalli Ammar yace " Ammar ka d'au mami da kawo gida."


Mami ta kalli Seemah itakam kasan ranta tana tausayin yarinyar tace " Mu wuce da Seemah ma kwana acan, sai ta kwana gun Zara."

Seemah ta kalleta jiki a sanyayi, Mami ta d'aga mata kai tare da mata murmushi, Ammar ya kalli Seemah sannan yace "muje kawo."

Sun fita Habib yabi bayansu da kallo, bayaji zai bar asibitin nan, juyawa yai ya shiga ciki, Dad da Abba na zaune jugum-jugum.

Ya koma gefe ya zauna.


Jalal kam yana fita daga asibitin ya shiga k'iran wayar Abba, sai dai bai d'aga ba, hankalinsa ya tashi ya rasa me ma zaiyi ga shi gobe monday yanada aiki bare ya tafi birnin/gwari yanzu, ga yamma tayi.

Haka ya cigaba da gwada number Abba sai can harya cire rai sannan yaji an d'aga, da sauri yace " Abba?" Jiyai ance " waye?" Da mamaki Jalal yace " ba number Abba bane?" Mutumin yace " wlh bamusan wayar waye ba d'azu muka ganta a shagon nan k'ila wani ne ya mantata."

Jalal yace " ina ne nan d'in?"
Mutumin yace " gurin buga kati ne."

Gaban Jalal ya fad'i wato da gaske Abba yake? Ya d'aure yace " ku ajiye wayar zan k'ira azo a amsa."

Nan sukai sallama, Jalal ya k'ira number Umma, sai data kusa katsewa ta d'aga tare da Sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Umma d'am Allah Abba fa?"

Tace " ya fita yanzun nan yamanta wayarshi a shagone shine yakesan yaje ya duba."

Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Umma d'an Allah kinsan wani Alhaji Isma'il?" Yai tambayar cikin sanyin murya.

Umma kam gabanta ne yashiga dukan uku-uku, tace " Jalal anya kuwa?"

Yad'an jinjina kai sannan yace " maybe ke baki sanshi ba amma ba shakka Abba yasanshi, bakomai bari in kara neman Abba."

Dasauri Umma tace " Jalal ba ruwanka, karka kuskura ka tambayi mahaifinka Malam Isma'il."

Da mamakin kalamanta Jalal yace " Malam isma'il? Da alama kema kinsanshi kenan, d'an nidai a sanina Alhaji nace ba malam ba, kuma daga yanda kika fad'i sunan Umma ya nuna kinsanshi."

Umma ta had'iyi yawo tace " Jalal ka rufamana asiri d'an Allah kabar yarinyar nan, in a da ina tunanin zai iya yiwuwa ka aureta sai dai yanzu......"

Tana zuwa nan tai shiru idanunta suka zubo da kwalla, ganin tana alamar kuka yasa ta katse wayar tare da zana a gun, tace a filin Jalal yazamuyi? Ya Allah gani gareka!!


Abba ne ya shigo tare da kallanta yace " menene kuma?" Umma ta taso tazo kusa dashi tace " Malam ya zamuyi? Jalal fa yasan kasa Malam Isma'il."

Abba sai da jikinsa ya amsa, ya kalli Umma kawai ya shige d'akinsa, yawo ya farayi a tsakar d'akin "Yasan Halin Jalal sosai, idan yaji abinda na aikata ta dalilinsa bana tunanin zai tab'a yafe ma kansa."

Idanu ya runtse ya tuno laifin daya aikata saboda tsoron kar a tab'amai d'ansa, bai taba tunanin abinda ya aikata zaizo ya damesu a wannan lokacin ba, shi daga baya ma yafara tunanin ko rashin lafiya da zaheera ke fama dashi alhakin abinda ya faru ne, yasani sosai ya aikata lefi mai karfi anma ya zaiyi?





Jalal kam wayarsa yabi da kallo mamaki kalaman Umma ne suka dameshi, lalai akwai wani abun a kasa kuma dole ne yasan menene wannan abun, tunani yafara gun Dad yakamata ya koma ko gun Abba?

Ajiyar zuciya yai yace " Abba zaiyi wuya ya sanar dani, zan kara komawa gun Dad inji ko shi zai fad'amin." Da wannan shawarar ya shiga cikin d'akinsu.




? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com



No. 4? 3?


Seemah kam tunda suka shiga mota ba wanda yai magana kowa da abinda ke damunsa, har suka isa gidan itadai Seemah kanta na kasa bayan sun isa mami da kawo suka fita Seemah ta kalli Ammar tace " yaya ni kad'ai zan kwana anan?"

Murmushi ya mata yace " ke kad'ai ce anan d'in? Ga Zahra ga mami nan?"

Tace " kasan bamu saba ba please ka shigo kaima saika kwana gun Ya Zaid inkananan sai hankalima yafi kwanciya."

Yai shiru shidai sam bayasan kwana a gun Zaid saboda Zaid hana shi bacci yakeyi ya d'inga mai surutu kenan sannan in 12 tayi kuma sai ya shiga waya da 'yan mata sam ya hanashi bacci, amma ya zaiyi? Bazai bari Seemah ta takura ba.

Seemah ta kalleshi jin shirun yayi yawa tace " Yaya na!!!!"

Ya kalleta yace " to kanwata muje ko?"

Wani dad'i ne ya kamata sannan ta bud'e motar ta fito.
Tare suka shiga Falon, Zara na tsaye a bakin window dama tunda mami tace da Ammar sukazo take lek'ensa, ganin ya fito yasa ta kara gyara fuskarta ta tsaya a bakin kofa.

Suna kwankwasa wa ta bud'e tare da wayancewa tace " Seemah na d'auka sai nazo na d'aukoki da kaina." Seemah tad'anyi yake tace " Zara ya kike?" Lafiya ta fad'a sannan ta kalli Ammar tace " laaaa Ya Ammar ai ban kula da kaiba."

Hararar wasa ya mata yace " anya kuwa kanwata? Bayan naga haske d'azu ta mota kamar da mutum a tsaye ta labule yana lek'e?"


Idanu ta rufe tace " kai yata bansan waye yake lek'e va."

Dariya Ammar yai yace gaskiya kam da alama ku 2 ne a falon.

Ta turo baki tace " yaya ai ko ka sani sai ka basar haka fa akeyi."

Seemah tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsunta, Ammar baiba Zahra amsa ba yace " kanwata kuje ciki kiyi sallah nima bari nai sai in dawo muyi hira ko?"

Kai Seemah ta d'aga alamar eh, Ammar ya kalli Zahra yace " Zara a kuma kularmin da kanwata."

Bai jira amsartaba yai waje, Zahra tabi bayanshi da kallo tana Murmushi sai daya fita sannan ta kalli Seemah tace " muje ciki." bata amsa ba kawai itama ta fara binta sun shiga d'aki Zahra ta nuna mata toilet, Seemah ta wuce ta shiga.



Tsaye tai a toilet tana kallan kanta a madubi, itakad'ai tasan me takeji a zuciyarta, Deen zai yi aure? Ta maimaita kalaman Zainab data mata a waya, hawayene ya ziraro mata ga mamakinta jitai kuka ya b'arke mata sosai, tsugunnawa tai kawai tana kuka.

Zahra dake d'aki ta na jiyuta matsowa tai jikin toilet d'in tace " Seemah menene?"
Kuka sosai takeyi Zahra mamaki ya kamata ta dad'e tana bugawa amma bata bud'e ba, Seemah kam ta dad'e tana kuka kafin ta daina, ita dana saninta d'aya dama batazo kasar ba kwata kwata da bata had'u da Jalal ba bare har sanshi ya kamata haka.



Alwala tai ta fito, Zahra ta kalleta tace "Seemah menene?" Jijiga mata kai kawai tai alamar a'a ta wuce ta d'au sallaya.





&&&&&&&&&&&&



A asibiti kuwa Hajiya ta samu bacci mai karfi saboda allurar da aka mata, da daddare Habib da saninshi ya kwanta yai lamo kamar bai bacci, Abba ganin kamar Habib yayi bacci ya kalli Dad yace " Isma'il inada magana da kai."


Dad ya kallleshi yace " inaji."

Abba yaja numfashi sannan yace " Isma'il tambayar dai dana maka shekara ashirin da suka wuce ita nakesan in sake maka, Isma'il tsakaninka da Allah bakasan mahaifin Seemah ba?"

Dad ya kalli Habib ganin da alama bacci yake yace " yaya wlh wlh bansan komai akai ba, sau nawa kakesan in rantsema." Ajiyar zuciya yai sannan yace "yaya kasan wa nagani yau?"

Abba ya girgiza kai, Dad yace " Amadu nagani."

Mik'ewa Abba yai yace " dafatan kasa an rufe mana shi?"

Dad yai tsaki yace " ai ni abinda nagani yasa ma nakasa mai abinda ya kamata, kasan mahaifin waye?" Abba ya girgiza kai, Dad yace " wai mahaifin Jalal d'in da Seemah keso ne."

Da mamaki Abba ya koma ya zauna yace " mene? JALAL? Taya hakan zata faru?"

Dad ya runtse ido yace " kabari kawai Yaya abin ya d'auremin kai, ko ya akai Jalal har yazo company d'in mu yana aiki har suka had'u da Seemah? Har hakan ta faru?"

Abba yace " Ikon Allah kenan, amma ai yanzu komai yazo gidan sauki, shi kansa Amadun ai ko kace ga Seemah ka bashi bazai aminta ba."


Dad ya kalli Hajiya bai kara magana ba.



Habib kam ya gama daskarewa agun da yake, meke faruwa? Ba Dad bane mahaifin Seemah kenan, sannan me? Bai masan mahaifin Seemah d'in ba? Meke faruwa kenan? Sannan mahaifin Jalal mene?"


Inaaaaa ai ko mai zai faru dole ne gobe a bashi amsoshin tambayoyinsa d'an kuwa shine babban d'a kuma dolene yasan sirrin gidan su, bazai kara bari a sashi a cikin tunani haka ba.









Jalal kam kwata kwata idanunsa basuga bacci ba zuciyarshi cike take da tunanuka kala kala, me ake nufi da Abba yasan Dad? Fitowa yai daga d'akinsu bai damu da daren dayai ba a waje ya zauna yai shiru yanaso zuciyarsa ta bashi amsar tambayoyinsa sai dai sam ya kasa lissafo komai abu d'aya dai daya tabbatar ma ransa shine, tabbas Dad yasan Abba kuma alak'ar dake tsakaninsu ba wai alak'ace ta mutunci ba, yazaiyi da auransa da ake shirin yi ranar asabar?





B'angaren Seemeh kuwa tana zaune a falo kusa da Ammar, Zahra nata jansa da hira, itakam Seemah a zaune kawai take ba ta sa musu baki ba, can Ammar shirun Seemah yafara damunsa ya kalleta yace " Kanwata menene?"

Kallansa tai batace komai ba, Zahra cikin zolaya tace " ba dai kuka zaki sake mana ba ko?"

Seemah ta kalleta kawai tai kasa da kanta, Ammar jin haka yasa ya kalli Seemah yace " kanwata kuka ki kai?" Shiru tai hakan yasa Ammar yagane matsalar, Zahra ya kalla yace " Zahra d'an bamu guri muyi magana please. "

Zahra ta kallesu sannan ta mik'e jiki a sanyaye ta fita, Ammar ya kara matsowa kusa da Seemah yace " Kanwata menene?"

Idanunta ne sukai rau rau tace "yaya kaima kasani ai."

Goshinsa ya rik'e yace "oh God Seemah akan Jalal ne?"

Kallansa tai cikin kalar tausayawa tace " yaya dama banzo kasar nan ba."

Murmushi yai yace " Seemah kenan."

Ta kalleshi tace " Yaya inasan intambayeka wani abu, d'azu naje shiga d'aki naji ana zancen Dad duk abinda suka mai wai kuma ya rik'e yarinyar amana."

Tai ajiyar zuciya tace " Yaya ban gane kalaman me suke nufi ba."

Ammar yai shiru can yace " Seemah ni kaina ban fahimci inda kalaman nan suka dosa ba, a farko na d'auka da ni suke to amma daga baya na gane ba ni bane, to amma me kalaman suke nufi?"

Ta jinjina kai tace " mu tambayi Dad gobe sai muji ko?"
Kai ya d'aga alamar eh
...











? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*



@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com



No. 4? 4?



A daren ranar Jalal da Habib idanunsu basuga bacci ba.

Washegari ya kama litinin, Habib zaune a d'akin da Hajiya take kallan Abba da Dad kawai yake yana tsananin mamakin yanda suka iya b'oye wannan sirrin batare da sun sanar ba, bayan ya gaidasu ya koma gun Hajiya ya zauna ya kalli Dad yace " Dad bari naje gida in dawo sai kuma kuje."

Abba yace to in kaje daga nan ka biya tagurin Mamie ka amso min sak'ona, Habib yace "to" sannan ya mik'e ya fita.

Agoggon Hannunsa ya duba karfe 7 na safe kenan, gida ya wuce yai wanka ya sa kaya sannan ya fito, gidan su Zaid ya wuce.


Bayan ya isa a bakin gate yaga Ammar, nan suka gaisa sannan Ammar ya tambayeshi jikin Hajiya, Habib yace " Da sauki, sai dai inasan magana da kai."

Ammar ya kalleshi da mamaki yace " akan me fa?"

Habib ya dafa kafad'ar sa yace " inaso ne kazo kuje gurin Mamie ina tunanin a wannan lokacin ita kad'ai ce zata warware mana abinda ke faruwa."

Ammar ya jinjina kai yace " ni kaina ban fahimci kalaman da Dad da Hajiya sukai jiya ba kuma da alama mu 2 ne kawai bamu san me suke nufi ba a d'akin."

Habib yai shiru can yace " Nagano maganar akan Seemah ne duk da bansan gaskiyar abinda ke faruwa ba."

Gaban Ammar ne ya fad'i ya kalli Habib yace " amma yaya........"

Habib ya katseshi yace karka damu mud'ai je ciki tukunna.

Nan suka shiga cikin gida, Zahra suka gani tana goge goge tana ganin Ammar ta mik'e tare da gaidasu, Habib yace " Zahra ina Mamie?"

Ta amsa da "tana d'aki."

Basu kara mata magana ba sukai hanyar d'akin mamie, sun isa suka kwankwasa, daga ciki Mamie tace su shigo, nan Habib ya murd'a kofar tare dayin sallama, Mamie ta amsa tare da mik'ewa ta rufe littafin Husnul Muslim d'in dake hannunta.

Ta kallesu tace " Habib kai ne?"

Habib ya shiga tare da zama a kasa kusa da inda take, Ammar ma ya zauna nan suka gaidata ta amsa fuska a sake tare da tambayar jikin Hajiya.

Sunyi shiru kafin can Habib yace " Mamie jiya da daddare sam idanuna sun kasa runtsawa tunani kala-kala sai daga karshe zuciyata tabani amsar tambayoyina."

Yai shiru bayan yazo daidai nan a kalamansa, Mamie ta kalleshi tace " ina jinka Habibu, mecece amsar?"

Habib yai ajiyar zuciya ya d'ago ya kalli Mami.


Daga d'aki kuwa Seemah ce ta fito daga toilet, tai saurin sa kaya ta fito a falo taga Zahra tace" Zahra ina ya Ammar? "

Zahra tace " yanzu sukai d'akin Mamie shida Ya Habib."

Murmushin farin ciki tayi tai hanyar d'akin da sauri fuskarta d'auke da murmushi tazo daidai zata kwankwasa kofar taji muryar Habib yace " Mamie da farko dai na gano abubuwa guda 2, na farko Seemah ba 'yar Dad bace, sannan abu na biyu babu alak'ar jini tsakanin Mu da Seemah wannan dalilin ne yasa Dad yake san had'ata aure da Ammar."


Tunda Habib yafara magana Ammar yake kallansa idanunsa cike da tsananin mamaki, kallan Habib yai yace " Ya Habib meye hakan kake fad'a? Kasan me bakinka ke furtawa kuwa?"

Habib ya d'ago ya kalli Ammar sannan ya maida dubansa ga Mamie data runtse ido ta sani tun jiya a asibiti dole ne zargin kalaman da Dad da Hajiya sukai ya bayyana.

Habib ya kalli Ammar yace " Mamie dan Allah ki sanar damu abinda ke faruwa, wannan ne kad'ai hanyar dazai sa mu taimaki kanwarmu sannan shirin auren da Dad yake sai munsan dalili tukunna abin zaiyiwu d'an ni tun sanda Dad yace Ammar ba d'ansa bane sam zuciyata bata aminta ba."




Seemah kam ta kame a tsaye silalewa tai ta zube akasa kamar abinda ba ya motsi haka

20 / 37