JALALUDEEN BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF AYUSHER MUHD.doc

Author :  Ayusher Muhammad Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   33 / 37

96K to 99K   out of 109.4K words

*AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com


No. 7? 0?


Duk wani tsare tsare na plan din Jalal ya kammala, sai da komai yai daidai sannan Ammar ya kalleshi jiki a sanyaye yace " Zainab nakaita har tasha ta hau mota, sai dai Jalal are you sure ba abinda zai faru in mutumin nan yazo?"

Jalal ya dafa Ammar yace " Ammar karka damu koda wani abun zai faru insha Allah sai alkairi."
Ammar ya kalleshi sannan yace " ni ina....."
Jalal ya danyi dariya yace " Ammar are you worried about me?"
Da sauri Ammar ya fizge kafadarsa yasa hannu yadan bigi cikin Jalal yace " ana cikin wannan yanayin shine ko kunya kake tsokana?"
Jalal ya dan hade fuska irinta tsokanar nan yace " Ahhh namanta na daina."
Atare sukai dariya, Ammar ya kalli Jalal yace " magrib tayi mu bari mu nemi hotel mu kwana tinda kai yanzu ka zama prisoner. "

Jalal ya dan harareshi tare da sa hannu a kuncinsa yace " ka tabbatar dai zaka iya bacci ko? Karfa ka kwanta tunanin halin danake ciki yasa ka kasa yin baccin."

Ammar ya girgiza kai yace " Jalal na kula sam baka tunanin komai."

Jalal yai murmushi baice komai ba.
Ammar yace " nidai gobe da sassafe zanje kaduna in kaima Umma sakon sai in juyo amma me suke so?"
Jalal ya kalli Ammar cikin jin dadin kalamansa yace " Ammar!"
Ja baya kadan Ammar yai yace " menenen?"
Jalal ya saki murmushi yace " nagode sosai."
Ammar yace " nifa da a yanda na daukeka na dauka mutum ne kai mai zafi mara kuma san magana amma na kula bayan ka dawo karatun nan kamar ka canza daga yanda nake ganinka."

Jalal yai murmushi yace " ni kaina ina mamakin in ina tare da kai bakina bayasan yin shiru."
Murmushi sukama junansu, Jalal yace " ga Atm dina dan ba kudi a hanuna."
Ammar yace " eh dole ka bani Atm dinka tunda ni banda abinda zan iya basu ai dole kace haka."
Jalal zaiyi magana Zaid ya karaso da sauri yace" nikam yunwa nakeji wai meyasa ku bakwa maganar Abinci? Su haka gidan sarautar suke bazasu bamu abinci ba?"

Jalal ya harareshi yace " ai a matsayin baki mukazo ba dole a bamu abinci ba."
Zaid ya turo baki cikin shagwaba yace " Mami kitaimaki danki yunwa zata kasheshi."
Dariya suka kwashemai dashi.
Ammar yace " Bari mu siyo abinci take away sai muzo nan muci dakai."
Jalal ya girgiza kai yace " a'a kamanta ni prisoner ne dolene in jure yunwa kodan Abdul inya ganni gobe ya fahimci an wahalar dani."
Ammar da mamaki yace " Jalal ban gabe ba?"

Da sauri Jalal ya fara turasu, yace " kuje sai da safe."
Yana kaisu bakin gate ya koma ciki da sauri, Ammar yabi bayansa da kallo zuciyarshi ba dadi.

Sun gama cin abinci wanda Ammar kadan ya iyaci sunyi isha'i sannan suka kwanta, Ammar yayi shiru zuciyarshi ta cika da tunani kala kala, abinda yake tambayar kansa a zuciyarsa shine, Shi yafi cancanta da Seemah ko kuwa?
Wayarsa da ya kashe ya kalla so yake yaji muryar Seemah sai dai inaa bayasan ta tambayeshi me sukeyi anan bayan bazai iya mata karya ba.

A wannan dare mutane 4 idanunsu baiga baccin kirki ba.
Jalal wanda yake tunanin ya gobe zata kasance musu, Abdul wanda bakincikin abinda Jalal yamai yasa mutane duk sun fara juyamai baya ciki kuwa harda shugaban kasa, dan da sukai meeting duk yanda Abdul yaso yabama shugaban kasa nashi ra'ayin a lokacin suna meeting ya hanashi, inzaiyi magana sai ai saurin katseshi, shi yasa ya kosa gobe tai danya dau babban hukunci akan wannan Jalal din.
Sarki wanda tunani ya hanashi barci, yana tsoron abinda zai faru gobe cigaba zai kawoma kasarshi ko kuwa matsala?
Sai Ammar wanda tunanin abubuwa suka hadu sukamai yawa.


Washegari da sassafe Abdul ya kamo hanya, Ammar ma ya wuce cikin garin Kaduna, baisha wahala ba wajen samun asibitin saboda kwarewa da suna da asibitin yai.

Number dakin da Jalal ya turomai ya nufa, tsaye yai a waje yana kwankwasawa, wani likitane yazo wucewa ya kalli Ammar yace " ba shiga zakai ba?"
Ammar yace " shiga zanyu amma naji shiru."
" Ka shiga patient din maganarta bata fitowa ita kuma mahaifiyar tata tana gu likita."
Ammar yamai godiya sannan ya tura kofar ya shiga.
Zahida na kwance sai motsa jikinta takeyi tana kiran Umma cikin muryarta da bata fitowa sosai, da sauri Ammar ya karasa gunta ya tsaya ta baya, Zahi najin motsi tace " Umma sosa min bayana kaikayi nakeji, jinake kamar wani abun na yawo."

Ammar yai tsaye yana kallan yanda takeyi rasa yanda zaiyi yai, Zahida takara cewa " Umma dan Allah ki sosamin zan mutu."
Ammar yasa hannu daya ya rufe fuskarsa sannan ya sa hannu a aljihu ya dauko biro yafara sosa mata a baya fuskarsa na gefe.
Zahi jin kaikayin yayi yawa ga umma ba gun take sosa mata ba tace " Umma dan Allah ki sosa min sosai ba nan bane."
Idanu Ammar ya zaro tunaninsa daya ina umman take to? In taganshi yace mata shine wa?
Gashi kuma bazai iya sa mata hannu a baya ya sosa mata ba, Zahida ta rasa ya zatai, zatai magana Umma ta shigo dakin, Ammar ta kalla da mamaki tace " Bawan Allah me kake a ciki?"
Da sauri Zahida tace " Umma? Waye?"
Umma ta matso ta gabanta tace " wani namiji ne."
Idanu zahida ta zaro bakinta na rawa tace " Umma ina yake?"
Ammar ne jiki a sanyaye ya dawo ta gabanta, ai tana ganin namiji ta saki ihu da karfinta na gaske, tare da runtse idanunta.

Umma tai mamakin yanda muryar ta tafito, ta kalli Zahida tace " menene? Wani abin ya miki?"

Ta fada tare da kallan Ammar da sauri Ammar ya girgiza kai alamar bai mata komai ba.
Zahida ta bude ido a hankali tare da sa kuka cikin kuka tace " Umma hannu fa yasamin a bayana."

Da sauri Umma ta kalli Ammar cikin mamaki tace " Hannu?"

Ammar ya kalli Zahida yace " yaushe na sa miki hannu? Kingani ne sanda nasa hannun ko kuwa?"
Zahi ha harareshi tace " to me kamin?"
Umma a zuciye take kallan Ammar tace " bawan Allah kai ko kunya bakaji ba? Baiwar Allah bata da lafiya shine zakazo ka sa mata hannu a baya?"

Ammar ya nuna mata biro yace" kinga abinda nasa mata nan, Umma tunda na shigo take kiranki akan ataimaka mata kaikayi ya isheta shine fa nasa biro nadan sosa mata, batasan banbancin hannu da biro bane?"
Umma ta kalli Zahida datai kasa dakai, Ammar yadan harareta yace " memakon ki godemin shine zakimin ihu?"
Zahida ta dago ta kalleshi, kaikayin ne ya cigaba da damunta tace " Umma bayana."
Umma ta kalli Ammar tace " dan Allah kadan kira mana likita."
Ammar ya fita, yana fita yai dariya a fili yace " lalai wannan kanwar Jalal din."





Jalal kam an kulleshi a can bayan gidan sarki a wani dakin da ko window babu sai daga can sama akadanyi hudi kadan kadan haske yana shigowa, yunwa yakeji sosai dan tana neman galabaitashi, duk yanda sarki yai dashi akan yaci abinci jiya amma yaki yarda.
Jin ana bude kwad'an dakin da aka rufeshi yasa yai saurin komawa lungu ya rakub'e, ana gama budewa Abdul ya shigo wasu maza kosassu suna biye dashi, Jalal ya kalli Camerar da suka saka yanda ba wanda zai gane, kasa yai da kansa.
Abdul ya shigo cikin isa, ya kalli Jalal tare da kwashewa da wata muguwar dariya, Jalal ya dago a hankali ya kalleshi, Abdul ya kalli dakin tare da jinjina kai yace "good dama haka nakeso ni wannan ma ya maka dadi dayawa."
Jalal ya kafeshi da ido, Abdul ya kalli mutanen yace ku fara.
Ai kafin Jalal ya fahimci mai zasu fara yaga sun matso sun kama dukanshi, sai da sukamai duka sosai, sannan Abdul yace " ya isa haka."

Sannan ya basu umarni su fita, kusa da Jalal yaje wanda duk jikinsa an jimasa ciwuka ya dago yana layi, Abdul ya sakeshi yamike tare da cewa " Jalal kai yaro ne, bakasan komai na rayuwa ba, taya zaka hada kanka dani? Nine fa Senate Abdul, akan can wata yarinya da kake kira da sunan 'yata daban santa ba har zaka nemi halakamin rayuwa? Kai din banza, me kake dashi? Me kuma zaka iya?"

Jalal cikin layi yace " Anya kuwa kanada imani a rayuwarka? 'Yarka ce fa? Baka tausayin abinda kama mahaifiyarta?"
Abdul ya kalleshi tare da nunashi da hannu yace " karka sake cewa 'yata wato so kake rayuwata ta hallaka ko? Meyasa tunda sanda ina karamin dan siyasa bakuzomin da zancenta ba sai yanzu da kukaga na girma ina neman wuce matsayina?"
Yai ajiyar zuciya yace " Fatima ta rasu, sannan banaji kunada wata shaidar da zata tabbatar da ninai fyaden nan, in kuma kanada ita ka tabbatar ka bani tun kafin nasa a kama iyayenka."

Jalal ya mike tare da yin wata dariya yace " me? Bamu kawo maka zancen ta ba tunda? Ita kanta yarinyar banaji zataso ganinka a rayuwarta, saboda tafi karfin ace mutum mai irin wannan zuciyar shine zata kira a matsayin uba, kuma tazauna dashi."


Abdul ya matso tare da wankama Jalal mari yace " Nima baso nake ta kirani da hakan ba, sannan daga kai har Amadun sai na nuna muku banbancin da dakuma yanzu."

Jalal yai murmushin karfin hali yace " Ko tambayar Malam Isma'il ma bakayi? Mutumin da kama sharri ka wulakantamai rayuwa."

Abdul yai murmushin mugunta yace " Isma'il? Ha ha ha au hardashi kuka hadu zaku wulakantani?"
Jalal yai shiru, Abdul ya matso tare da cewa " Ka koma ka sanar dasu abinda na maka sannan ka fadamusu nine na mata fyaden me zasu iya min? Yarinyace nace ta fadi kudin datake so nizan bata amma bawai a matsayin 'yata ba."

Alhamdulila Jalal ya fada burinshi ya cika Abdul ya aminta da bakinsa shiya ma Fatima fyade.
Wani abu ya danna, kan kace me sai ga 'yan sanda sun taho sun zagaye dakin gaba daya....




*Gaisuwa My Samra Thanks alot Sis......*d'd'd'



? *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com


No.7? 1?



Abdul jin loudspeaker yai ana kiran sunansa, jikinsa ne ya shiga rawa ya matso kusa da Jalal tare da shakemai wuya da karfinsa, Jalal ya fara kakari, ko meya tuna kuma sai yai saurin sakinsa yana yin baya baya yana cewa " nafi karfin wannan, nine Senate Abdul wanda mutane ke so."

Jalal yarasa dalili kawai ganin yanda yake rawa da jikinsa yasa tausayinshi ya fara ziyartar zuciyarsa, kallansa yai idanunsa sun ciciko da kwalla matsowa yai kusa dashi ya rike hannunsa yace " wacce irin rayuwa kai? Bayan rashin adalcin dakama Fatima baka jin tausayinta da dana sanin abinda ka aikata a kasan zuciyarka?"



Hawaye suka zubo ma Abdul ya kalli Jalal yace " Fatima ta rasu dolene ni danake darai inyi rayuwar danakeso."
Jalal cikin wata sanyin murya ta ban tausayi yace " zaka iya rantsuwa tun bayan abinda yafaru baka taba dana sani ba? Sannan baka taba tunanin 'yar ka ba?"

Bakin Abdul ya fara rawa, kai ya shiga girgizawa hawaye na zubomai, Jalal ya kara matsowa kusa dashi yace " Zaka iya rantsuwa?"

Abdul ya dago jajjayen idanunsa yace " in ma nayi dana sanin ko tunaninsu menene amfaninsu yanzu? Fatima ta rasu ba tare da na nemi yafiyarta ba, sannan yarinyar data haifa ban taba ganinta ba bare inma san sunanta kana tunanin akwai amfanin da tunanin zaimin ko dana sanin?"

Jalal yai ajiyar zuciya yace " You are not a cruel person, da ace kai mugune da randa nazo gidanka dazancen nan bazaka barni na fita ba sannan da bazaka ce sarki ya kamani ba sawa zakai a kasheni ba tare da kowa ya sani ba, sai dai na kasa gane kai wani irin mutum ne da kake kokarin canza abinda ke zuciyarka."

Abdul ya kalli Jalal tare da share hawayensa yace " da farko I am not greedy but zama da abokai da cusa min ra'ayuyuka da kuma matsayi na power danake samu ba, hmmm bansan sanda nima na riked'e gaba daya na zama haka ba, bana tausayin kowa burina daya ne insamu abinda nakeso......"

Kasa karasa maganar yai, jiki a sanyaye ya dago tare da yima Jalal murmushi yace " hmm inaji Allah ne ke nemana da rahama shiyasa ya baka damar tsayar dani daga cigaba da abubuwan danakeyi."

Hanyar kofa ya nufa, da sauri Jalal ya riko hannunsa yace " 'Yar ka fa?"

Abdul ya runtse ido yace " a'a karka sanarda ita komai, in har bata gan ni cikin mutuncina ba bazan bari ta ganni cikin wannan yanayin ba."
Yana kainan ya bude kofar 'yan sanda suka matso tare da samai ankwai.


Shiru Jalal yai zuciyarshi kuma ta shiga radad'i abinda yake fata ne ya tabbata but meyasa yakejin shi haka?.



Ammar ne suka dawo shida likita, suna shiga dakin Zaid ya kirashi a waya, yace na siyo kayayyakin kana ina? Ammar ya fadamai number dakin nan Zaid ya taho, likita bayan ya duba Zahida yace bari yasa a kawo mata magunguna, yana fita Zaid ya shigo, Umma ta kallesu tace " ban gane ku bafa?"
Ammar yai kasa dakai tare da gaisheta yace " Ammar ne dan gidan Malam Isma'il."

Cikin tsananin mamaki Umma ta kalleshi tace " Ammar?"
Zaid ya matso tare da cewa ni kuma Zaid, ta kalli Zaid da mamaki tace " tare kuke?"

Ammar ya daga kai, Zaid ne ya karasa kusa da Zahida dake jingine da gado, fuskarta ya tsaya kallo, inya kalli nan sai ya juya kansa ta daya barin, Zahi ta gaji da wannan abin nasa ta kalleshi tace " malam lafiya?"
Zaid yace " wow! Ahh dan sake fada kinji?"
Zahi tace " me zan sake?"

Zaid ya rike kirjinsa bangaren zuciyarsa yace " Ammar wannan muryar tamin dayawa."

Kai Ammar ya girgiza ya kalli umma yace " karki damu Umma haka yake."
Umma tai murmushi tace " da alama yanada san wasa."

Zaid ya dago cikin shagwaba ya kalli Zahida yace " Yanzu bazaki sake fada ba."
Zahi ta makamai harara tare da cizan leb'enta tace " Naki d'in, kuma ka matsamin daga sai tin fuska."


Zaid ya sa dariya tare da toshe baki yace " in naki fa? Me zakiyi?"

Ya fada tare dasa hannu a haba, Zahi ta juya kanta gefe tace " Umma kice ya matsa min."
Tai maganar kamar zatai kuka, Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid ka matsa mata mana tace bataso."

Zaid ya kalli Ammar yace " meya dameka? Hira muje tsakanin masoya ko patient. ...ahhh dama karatun likita na karanta."

Zahi tai wani irin dariya ta kularwa tace " masoya? Ha ha lalai mutumin nan da alama kai player ne, harda wani dama karatun likita ka karanta? Ahhh Allah yasa duk da akwance nake inajin labarai, dan yayata tana karantamin har littafin hausa, nasani sarai in naga mutun na neman yaudara."

Ta hade rai tare da juya kai.


Zaid ya matso kusa da Umma yace " Umma kun tabbatar yarinyar nan mara lafiya ce da gaske? Bakinta abude fa yake?"

Umma tai murmushi tace " to ko zata mik'e ta rakaka unguwa?"
Da sauri Zaid yace " Eh Umma in....."
Kafa Ammar yasa ya takamai kafa da karfi Zaid yai kara tare da cewa " me kuma nai?

Ammar yace " bata fa tafiya akwance take tun tana karama, Zaid meke damunka ne?"

Jikin Zaid ne yai sanyi ya kalli Zahi sannan ya kalli Umma yace " Bansani ba Umma nadaiji jiya ana cewa ta fara magana nadauka matsalar ta magana ce kawai. "
Umma tai murmushi tace " ba komai zuwanku ma ya isheni farinciki tun balle ganin Ammar danai wanda ban taba zata ba."

Ta fada tare da kallan Ammar.






...?
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*



@&
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?






Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com



No.7? 2?




Seemah na xaune a daki tana cin Abinci Dad ya shigo, kallansa tai cikin sakin fuska tace " Dad shigo mana."
Dad ya karaso tare da zama kusa da ita ya anshi cokalin da take cin abincin ya deba tare da kaiwa kusa da bakinta yace Ahh....
Murmushi tai sannan ta bude bakin ya zuba mata, tanaci tana murmushi, Dad ya kalleta cikin tsananin kulawa yace " babban farinciki na bai wuce inganki kina cikin farin ciki ba."
Murmushi Seemah tai tace " Dad daga yanzu ko banasan dariya inna ganka zan dinga washe baki."
Dariya yasa mata yace " ni bance kuma a dingamin haka ba."
Kallansa tai cikin kulawa tace " Dad su ya Ammar fa? Sam na kasa samunshi a waya."
Dad yai shiru batare daya bata amsa ba cikin wata murya yace " Seemah?"
Kallansa tai cikin mamaki da tattara nutsuwarta saboda yanda ya kirata.
Dad ya kalleta cikin kulawa yace " Seemah ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bakyajin ba dadi ko bacin rai? "
Cikin mamaki ta kalleshi tace " saboda me kenan Dad?"

Yai murmushin karfin hali yace " Seemah nasani sarai Jalal kike so amma na hadaki aure da Ammar bakyajin haushin hakan a kasan ranki?"

Iska tadan furzar sannan ta rangwabar da kanta

33 / 37