JALALUDEEN BOOK COMPELET HAUSA NOVELS PDF AYUSHER MUHD.doc

Author :  Ayusher Muhammad Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 37

3K to 6K   out of 109.4K words

munyi fad'a tunda bai tab'a gani ba, zuwa gun Habib kuwa na amince."
Ihu tasa ta kara rungume dad tace " Dad shiyasa nake bala'in sanka."
Dariya suka mata Dad yace " Amma in zaki inaji sai na had'aki da securities da zasu d'inga kula dake, haka kawai Habib na can gun aiki ke kuma kina guri ke kad'ai bazan bar hakan ta kasance ba."



Ta kalli Ammar tad'an lagwab'ar dakai kamar zatai kuka Ammar yace " Dad amma ina ganin kabari kawai in yaso in taje can sai a sanar da Habib ya samarmata bodyguards dazasuna kula da ita. "

Dad ya kalle Ammar yace "kana ganin hakan ya fi?" Dasauri Seemah tace eh mana Dad.





Nace uhmm..................

****************************

Yau Seemah tun Safe akai wanka dan flight d'in sukai booking, Sauda tafi kowa murnar wannan tafiya d'an ko Seemah dazatai tafiyar ta fita murna.

Seemah ta shirya cikin riga da wando d'an ita banaji akayanta akwai atamfa ko ince bata tab'a gwada sawa bama, bayan tasa riga da wandon sai kuma ta d'auko rigar sanyi tasa, d'an garin sai da rigar sanyi, ta yi kyau Anna ta kalleta tace " Madam I will miss you."
Harararta Seemah tai tace " bayan yanzu kin rage damuwa dani?"

Anna ta karaso ta rungumeta a hankali kwalla ya zubo mata, Seemah ta juyo tace " wasa nake Anna na sani kin damu dani sosai, tun ina karama, nima I will miss u."

Tare suka fito Anna na rik'e da jakarta, a falo sukaga Sauda sai murmushi take, suna saukowa ta kalli Seemah cikin tsananin farin cikin da kana gani zaka gane tace " Seemah yanzu tafiya zakiyi? Sai kuma yaushe?"

Seemah ta kalleta ta had'e rai tace " Small mom nasani kinfi kowa murnar tafiya tai, sai dai ba dad'ewa zanyi ba."tana kainan tai waje gun dasu Dad ke jiranta a mota.


Kowa yana zaune a cikin motarsa da driver d'insa, ta kallesu tare da sa dariya tace " Dad ahaka za'ayi rakiyar? Kowa na motarsa? Nima in shiga tawa?"

Junaid yace " to a ya za'ayi?"

Ta bud'e motar junaid tace yaya fito, junaid ya fito, ta bud'e motar Ammar tace bros kaima fito, shima ya fito, sukace me za'ayi? Motar Abba ta bud'e ta gaba tace Ya junad shiga nan, ya kalleta yace tohh.
Nan ya shiga ta kalli driver d'in Dad tace fito shima ya fito ta kalli Ammar tace bros jamu.........tafad'a tare da shiga kusa da Dad.


Dariya sukai nan suka shiga tare da fara tafiya, Dad yace " kai Seema zamuyi missing d'inki, baki tab'ayin tafiya ba tunda aka haifeki."

Tai raurau da ido tace " yauwa, dole ne kowa a rana ya kirani sau 5 in ba so yake muyi fad'a ba."

Haka suka cigaba da tafiya ana raha, Dad yace" na fad'ama Habib ya kularmin dake sosai duk abinda kikeso a tabbatar an miki shi."
Dariya tai tace " inada Dad irinka me zai dameni?" Sun isa takira Habib tafad'amai zasu taho.

Sai da aka gama musu checking suka shiga jirgi sannan suka juya zuciyarsu duk ba dad'i.



**************************



Habib na isa company d'insu ya fara shiga meeting, sun dad'e kafin su gama suka fito sukai sallar azahar, ya duba agoggo akala saura hour d'aya su seemah su iso, yana komawa yataradda wani aikin ya kara tasowa dolene su shiga wani meeting d'in gashi baisan sanda zai fito ba, Secretary d'insa ya kalla yace " Kanwata tana hanya gashi zamu shiga meeting kasa wani ya je airport nan da minti 30 ya jirata ta iso ya tahomin da ita nan, sunanta Seemah, ka tabbatar wanda ka tura mutum ne mai hankali yakuma je ya jirata yanda tana isow zai kawomin ita."

Secretary d'in ya amsa da to, nan ya shiga tunanin wazai tura, abokinshi ya tuno, dasauri ya danna number, daga can aka d'aga yace " ya akai Sagir?"

Sagir yace " Jalal please kataimakamin meeting zamu shiga da Chairman to kuma kafin mu fito kanwarsa ta iso shine ya keso a taimaka d'aukota, nikuma banyi tunanin kowa a company d'in nan ba sai kai."

Jalal yai tsaki yace " ta hawo taxi mana? Dole sai an d'aukota? Ni ma aiki nakeyi."

Sagir yai dariya yace " Taxi jalal? Kanwar Chairman d'in company d'inmu fa nace? Kuma bana tunanin ma ta tab'a zuwa kasar'"


Jalal ya nisa yace" to kanwar Chairman tafi karfin taxi?"
"Nidai plz kataimakamin abokina d'an Allah, sunnanta Seemah, bari na shiga meeting zan ba da makullin motar chairman d'in akawo maka, nan da 30mins zasu iso."Sagir nakainan ya kashe wayar.

Tsaki Jalal yai sannan ya kalli takardun da aka bashi yai sorting, shifa baisan rainin hankali, shi driver ne? Dandai Sagir ne amma da ina..............





By *Ayusher Mohd*
? *NWA*
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *JALALUDEEN*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?







Na *AYUSHER MOHD*








NO 3?








A hankali Jalal ya mik'e ganin minti 30 d'in tayi, tsaki ya sakeyi yace amma Sagir ya ci mutuncina.

Kallan 'yan uwansa nagun aiki yai yad'an sosq k'eya yace " zan d'an fita gun wani friend d'ina."

Sukace sai ya dawo, waje yai yana cewa haka kawai da mutuncina an sani karya, makulli ya amsa tare da tambayar security d'in ina motar take? Nan ya nuna mai, ya kalli motar tayi kyau sosai, bud'ewa yai ya shiga tare da jaa....

Ya isa airport sa alokacin yashiga tunanin wai ma yazaiyi yasan itace? Zuwa zaiyi yai ta tambayar mutane Seema ko me? Shiru yai can yace " Seemah? Amma sunan kamar ba na kasar nan ba, yai kama dana india, to amma Sagir yace wai kanwa" yai shiru a ranshi yace da alama Sagir d'in bai fahimta bane.


Ya dad'e a zaune baiga jirgi ya sauka ba, haushi ya isheshi ya kalli agoggo kusan mintinsa 30 kenan da zauwa, haushi ya isheshi ya mik'e zaiyi hanyar waje, karar jirgin dake alamar sauka ne yasa ya koma ya zauna.

Kallan mutane ya shigayi wad'anda sukazo d'aukar 'yan uwansu, to shi wai ya zaiyi ya ganeta? Ganin mutane sun fara tahowa yasa wata idea tazo mai, juyawa yai yaga wasu rik'e da manyan abu d'auke da sunayen wad'anda sukazo tarba, a ranshi yace nima bari nai haka.

Jakarsa ya bud'e ya d'auko littafin rubutunsa, ya gutsuro takarda karama, tare da rubuta Seemah da biro a jiki.
A zahiri in ba kazo kusa ba bazaka tab'a ganin me aka rubuta ba.

Nikam dariya ne ya rufeni ganin wata 'yar takarda d'auke da sunan Seemah gashi sai kunyar rike takardar yake da kyar ya d'aure ganin zai b'atama kansa lokaci yasa ya d'an rike da hannun hagu.

'Yan jirgi sun fara fitowa, Seemah kam duk ta gaji a jirgi ta fito sanye da glass ta cire rigar sanyin datasa ta jacket ta rik'e a hannunta, ga takalmin da tasa mai masifar tsinine, rigar jikinta takai gwiwarta sai wando pencil dake jikinta, tasha jambaki pink, gaskiya tayi kyau sai dai tunda ba al'adarmu bace hakan yasa kowa take kallanta, itakam ko ajikinta.

Raba ido kawai take taga an rubuta Seemah a katon symbol wanda zai d'au hankalin mutane, sai dai duk wanda ta leka sai taga ba sunanta, mamaki ya kamata nan tace ko dai yaya yana kunyar rubutawa ne? Nan ta shiga duba mutane ko zata ganshi, mamaki ne ya kamata ganin har ta iso gun da mutane ke tsaye suna jira bataga yayanta ba.


Jalal kam ya baza ido sai neman ba india yakeyi, sai dai turawa kad'an da suka fito.

Seemah da sauri ta kunna wayarta, sakon yaya ne ya shigo na zai shiga meeting amma ya turo a d'auketa, haushi ya kamata tace " akwai meeting d'in daya fini mahimmanci ne?...."
Maganarta ce ta katse ganin wata 'yar karamar takarda wani saurayi sanye da coat yana rik'e dashi, dariya ne yazo mata tace " lalai wasu basuda mutunci, yanzu wannan 'yar iskar takardar da ita za'a tarbi mutum? Da alama dai mutumin nan ko bashi da mutunci ko kuma mammako ne ya mai yawa.

Hartazo kusa dashi tana d'an duba mutane, to ta ina zata gane d'an aiken? Ga wayar yaya a kashe, idanta ne yakai kan rubutun dake jikin 'yar takardar, in batai kuskure ba *SEEMAH* taga an rubuta, wani kululun bakin cikine ya ziyarceta, badai ita Seeman ba d'an itakam tasan tafi karfin wannan takardar.

Karasawa tai kusa dashi, daidai nan shikuma wani Sagir ya kirashi, Jalal ya d'aga cikin kunnar rai yace " Sagir me kad'aukeni? Tun d'azu ka aikoni d'auko wata banza itakuma tana neman b'atamin lokaci, ce maka akai banda aikin, yi ko me?"

Sagir yace " Sorry Jalal yanzun ma ba gama meeting d'in mukai ba, Chairman ne ya kalleni, hakan yasa na gane so yake yaji maganar kanwarsa, dagani yanaji da ita."

Cikim zafinrai Jalal yace" me yadameni da wani ji da ita dayake? In hakane ya bar meeting d'in yad'aukota mana, ni mubar wannan maganar, india ce kome? Naji kace Seemah?"

Seemah dake tsaye tana jinsa bakin ciki yazo mata wuya, ita ake ciwa mutunci?

Haushi ya kamata ta juya ta kara juyawa nan taga wani rike da d'an karamin cup da alama ko lemo ko ruwa ko tea yake sha, ajiye trolly d'inta tai ta karasa gun mutumin, addu'ar ta d'aya Allah yasa tea ne mai zafi.

Tana isa gunsa tace sannu bawan Allah, ya kalleta ganin shigarta yasa yad'an had'iyi yawo, yace " mekikeso madan?"

Murmushi tai tace " please abinda kake sha nake so, "
Da sauri ya mik'a mata cup d'in ta kalli ciki, tea ne mai madara yaji milo sai dai abin haushi ba zafi sai dumi dai kawai, godiya tai ta juya tai gaba shikuma ya bita da kallo.


Seemah na isa kusa da mutumin, sai ta juya kai kamar bashi take kallo ba, shi kuma ya zak'e sai fad'a yake a waya sam bai kula da itaba, Seemah na matsowa ta saita takalminta ta takamai kafa da karfi, zai juyo ta kwaramai ruwan tea a cikin kayansa wajen farin coat d'in na ciki cikin tsananin mamaki Jalal ya d'ago d'an ganin wace 'yar duniyar ce wannan? Yana d'agowa Seema ta kwad'amai jacket d'inta, da karfi ya zare jacket d'in takard'ar hannunsa ta fad'i.
Cikin wani irin takaici yace " wani irin hauka ne wannan?"
Kallansa tai shima ya kalleta, tab'e baki tai tace " Sorry ban kula ba."
Tafad'a tare da juyawa, da karfi Jalal ya d'amko hannunta ta tsaya tare da d'an kara d'an taji zafin damkar, ta juyo tace " Malam wani irin rainin hankali ne wannan? Sakeni ko?"

Jalal yai wani mugun Murmushi yace " me da me kika ce? Bakiga ke abinda kika min ba?" Ya fad'a yana kallan kayan jikinsa ga kafarsa dake zafi.

Tace "sake ni ko? Kai meye dalilinka na tsaya a hanya? Ko nan gidanku ne dazaka tsaya kana gulmar mutane a waya. "

Jalal yazabura yace " Gulma? Ke tsaya in ma gulmar ce meye naki a ciki? Ohh shine kikamin haka da sanin ki kenan ko me?"

Seemah ta kalleshi tace sakeni ko? Jalal ya zare hannunshi tare da cewa " tambayar ki nake? Meke damunki? Kuma a wani dalilin zaki min haka? Banasan rainin hankali kuma akanki bazan jura ba, kawai kiyi godiya d'aya ke macece dabadan haka ba I don't know what will happen. "


Seemah ta makamai harara tace " ka kuma d'auko jakar ka taho mu tafi."

Jalal kam ranshi ya kai matuka gun b'aci yace " what?"

Seema tace "kanaso in kara fad'ane? Ko ba Seemah kazo d'aukaba?"

Jalal yai wani murmushi yanzu ya gane wai itace yace " ko ita nazo d'auka bata isa tasani ind'aukar mata jaka ba, d'an banaji nid'in mai aikinta ne." Yafad'a tare dayin gaba yace " kibiyoni zan jiraki a mota."


Seemah ta bishi da kallo tare da d'anyin kara tace " wannan wani irin mutum ne? Wayyo bakin ciki zai kasheni."
Yazatai? Haka taja jakarta, yana tsaye jikin mota takarasa fuskarnan a had'e duk da da glass a idanta.


Jalal ya shiga mota, itama ta karasa ta shiga baya ta zauna, lalai ba shakka sai ta gyarama mutumin nan zama, shi harya isa? Shid'in wa?

Tafiya suka fara bamaima kowa magana, shi haushinshi ma maidashi driver datai, Seemah kam waka tasa a wayarta ta kuma kuri volume, Jalal ya juyo tare da ciro earphone ya cilla mata yace " malama yi amfani da wannan banaso a cika min kunne."

Cillamai a binsa tai tace " sai kuma naga kamar ba a kanka nake ba, sannan ta kalli motar ganin abin bit da ta ba yaya habib a jikin madubin gabar motar yasa tace "sai kuma naga motar yayanace bana tunanin kanada iko da ita."

Jalal yai tsaki tare da juyawa, yanaji bai tab'a ganin mace 'yar rainin hankali irin wannan ba.

Seemah ta kauda kai a ranta tace wannan wani irjn mutum ne? Da alama kuma ba wani kud'i gareshi ba ganin coat d'in jikinsa bamai tsada bace.

Yana talaka shine zai raina mata hankali? Tafi karfin a wulakanta, ita datakesan taga kowa na mutuntata yana santa shine yau zata had'u da wannan wanda ko kwayar mutinci bataji yanada shi.





By *Ayusher Mohd*
? *NWA*
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?
=?>? *J?9?9??*=?>?
=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?=?>?









Na *AYUSHER MOHD*







4?



Har suka isa Company d'in ba wanda yama wani magana a cikinsu, haushi duk ya cika Jalal aikuwa da yazo taka burki da karfi ya taka har sai dayasa Seema ta bugi kujarar gaba, cikin b'acin rai ta d'ago tare da dafa gun kamar tai kuka dan taji zafi.

Jalal ya juyo yace " Sorry bankula bane."

Ta tuna itama haka tace data mai tsiya a airport wato ramawa yai ko me? Juyawa tai ta kalli Company d'in, babban ne sosai duk an bishi da glass lekawa tai taga kamar mutane sun taro daga bakin kofar, ido ta kura nan ta hango yayanta, wani murmushin dad'i ta saki tanaso taga ana ji da ita, wannan tarbar da aka mata yasa taji zafin goshin ya tafi, kallan Jalal tai dake miko mata key, yace " gashi kyaba yayanki."

Ta kalleshi tace " bud'emin kofa."
Jalal ya kalleta cikin rashin fahimta yace " what did you just say? "
Ta murgud'a baki tace " bakaga an taro ana jirana ba? Ko so kake ka b'atama yaya na rai?"

Jalal yad'an yi wani dariya dakanaji kasan ta bakin ciki ce, yace " Servant d'inki ne ni?"
Zatai magana taga an bud'e mata kofa, cikin mamaki ta kalli waje, wani saurayi ne yace " Welcome Madam"

A hankali ta zuro takalminta mai mugun tsini sannan ta fito, sai dataje tsakiya yanda jalal zai jita haka kuma mutanen dake jiranta zasu jita, ta juyo cikin wani rainin hankali takalli jalal dake tsaye jikin mota, tace " Mr Pride d'an Allah jakata na manta nan kawomin."

Jalal ya kalleta tare da nuna kansa da hannu yace " Me?"
Ta d'aga kai tace" Sorry."


Wanda ya bud'e mata kofa yace " bari na anso miki madam.
Seemah tace " barshi shi nakeso ya kawomin."
Tana kainan ta cigaba da tafiya.

Jalal ya furzar da wata iska cikin takaici ya bud'e boot ya d'auko trolly d'in.

Seemah ta karasa gunsu yaya tana tafe tana murmushi, Habib na gani ta kusa zuwa ya karasa tare da rike hannuwanta duka biyu, tab'e baki tai tace "yaya haka ake oyoyon?"

Yace " Sorry Seemah ta bakiga da mutane bane? Kuma kinsan a kasa na suke kar su rainani."
Tace " nagane, oh ni yaya ashe zanganka?"
Dariya yai yace "mu wuce office d'ina muyi murnar ganin juna, ko?" Cikin zumud'i ta d'aga kai, nan suka fara tafiya, nan ta waiga ko zataga d'an rainin hankalin nan, sai dai ga mamakinta duk inda ta duba bayannan mamaki ya kamata, ina yaje? Jakarta ta hango a hanyar shiga, wato har ya ajiye ya tafi? Lebenta tad'an ciza tare dayin kwafa a hankali.

Sun isa mutane na ta gaisheta tana amsawa, farinciki ya cikata tanasan kulawa, har suka isa office d'in kowa ya gansu sai ya gaidasu, suna isa suka rungume juna, ta rik'e hannun Habib tace " Yaya I really miss you. "
Yace "nima kanwata, ni kad'ai nasan dad'in danakeji na ganinki."
Dariya tai tace " yaya sai yau nazo mahaifata, bakaji dad'in da nakeji ba dan ma d'an......." sai kuma tai shiro.
Habib yai dariya yace" badai daga isowar kanwata har an samu rikaken dazai b'ata mata rai ba? "
Ta turo baki tace " sosai ma kuwa yaya, kuma nad'au alwashin sai ya tsugunna ya nemi yafiyar abubuwan dayamin."
Dariya sosai Habib yai yace " namanta ashefa Seemah aka tab'o wacce bata hakuri in aka mata abu."
Tai dariya itama tace " yaya dad'i nakeji sosai."
Sun dad'e suna hira, har waya sukai dasu dad yakara tunamai ya kular masa da Seemah, suna gama waya Habib yace " kai dad ma ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sai a hankali, tun kafin kizo yake tunamin in kula dake."
Dariya tai tace " ai nasani dad duk yafi sona akanku, bayasan abu ya tab'ani."

Habib yace "muma duk muna sanki sosai, yanzu dai dolene in samarmiki wanda zai dunga kula dake a duk harkokin da zakiyi a nan kasar, amma kamar mutane nawa kikeso?"

Shiru tai can wani abu ya fad'o mata wani mik'ewa tai tare dayin tsalle, tace " kaii!!!!! Amma naji dad'i."
Kallanta Habib yai tare da tambayarta mene? Ta tsugunna agabanshi tace " yaya wani abu nakesan kataimakamin dashi."

Yace menene wannan? Seemah ta saki murmushi tace " akwai wanda nakesan yazama driver

2 / 37